Auren Wata Uku Book Complete By Sameena Aliyu.doc

Author :  SAMEENA ALIYU Category :  Arewa Pen

Chapter   12 / 52

33K to 36K   out of 153.1K words

saba da mutane kuma idan baka mance ba na sanar dakai ina koyar da sana ar d inki ma  yanmata. Toh Ummul tana cikin d alibai na.

Hisham ya jinjina kansa a hankali  And she s from around this neighborhood..?

Hajja ta kuma murmusawa kad an dan ta lura da curiosity na d an nata gameda Ummul. Ita idan har abinda take hasashe ya tabbata zatafi kowa farin ciki. Dan Ummul yarinyar kirkici wacce jarabawa da k alubalen rayuwa sukai marfi ma rayuwar nata.

Gyara zamanta ta d anyi ta kaikato sosai tana duban Hisham  Naga alama dai tambayoyi ne kazo dasu wann karon.. Amma ka bari har Allah ya wayi gari lafiya kaga yanda ranar yau d in ta kasance mai tsawo. Idan ka samu ka huta zuwa gobe da safe idan Allah ya nufemu da kaiwa sai na amsa maka duka tambayoyinka.. Maza tashi kaje ka kwanta haka ka huce gajiya kuma. Kaga nima kwanciya zanyi haka nan. Ta k arashe tana k ok arin tattare kayan.

Hisham ya amshe yana linke mata su . Dan yanda ya kwana biyu baya tareda ita d in nan dik abinda zaisa ya samu albarkanta baya wasa da wann abun komin k ank ancinsa.

**

Sassafe Mommy ta fito da zummar komawa Abuja dan dama day trip tayi niyyan yi amma sabida accident da suka d an samu dole ta bari sai Washe gari bayan an duba lafiyan motar an tabbatar zata iya tafiya.

Ta dubi Asshe  Na bar miki wuk a da nama amma ki tabbata wacce duk za a samu tanada futures da qualities da zamu iya jan ra ayin Haidar dasu in just a short time. Lafiyayya wacce batada wani cutan da zai iya shafan d ana.

Asshe ta d an numfasa  Bakida matsala Aunty Kwaise ai kaman yanda kikace ne a duniyar nan babu abinda kud i bazai sai maka su ba. Ni yanzu damuwata matar da muka bige wacce har yanzu Ke asibiti gashi babu wani means of identification tareda ita balle a samu wani nata.

Mommy tace  Aff kinga ni na mance ma da batun wann matar. Yanzu tareda waye aka barta a asibiti.?

Asshe tace  Mai aikina Marka ita ta kwana da ita suna can tare yanzu haka..

Mommy ta jinina Kai dan dama wani private hospital suka kaita  Duk abinda ake ciki dai kin sanar dani. Ni yanzu tafiya ya kamani, dan kinsan na fad a miki Engr baisan na taho ba shima baya nan ya tafi Lagos tafiyar da ta shafi Kasuwancinsa.. So bani so ya dawo gidan ya tarar bana nan. Anisa ce kawai gidan kinsan kuma yanda take saitin da sauk i.

Asshe ta kuma jinjina kai  Zakiji komai in sha Allah Aunty Kwaise. Allah ya tsare hanya.

Suna tsaka da sallaman Hilal ya k araso wajen. Mommy ta dubesa  Bazan amsa goodbye d inka ba tinda har zaka zo hutu k asar nan kuma jirginka ya sauk a a Abuja ka kasa zuwa ka dubani.. Inji kaima kabi sahun d an uwanka Haidar ne.?

Hilal matashin saurayi d a ga k anwar Mommy Wato Asshe ya d an murmusa yana shafa kansa. Baifi sati da zuwa Nigeria ba karatu yake a k asar Cyprus. Ya samu zangon hutu.

 Haba mana Mommy ta kinsan bazan miki haka ba. Tareda Abba da matarsa muka dawo Kano daga Abuja shiyasa. Nasan duk Anisa ce ta had ani dake. Amma kafin hutuna ya k are zaki ganni in sha Allah. I still have 2 weeks here.

Mommy ta murmusa  Toh shikenan sai na ganka.. Ina nan Ina zuba ido.

Hilal ya murmusa yana tabbatar mata zaizo. Ya nufi wajen driver yana tambayarsa hope motar bata samu matsala ba.

Mommy ta dubi Asshe ta d anyi k asa da murya  Oh kiji min Hilal wai Abbansa da matarsa. Kinji yaro na taya mahaifiyarsa kishi.

Asshe ta tab e baki  Yo yarinya ce k arama Anisa ma ta fita Kinga kuwa yaushe zai wani bata matsayi.

Mommy tai yar bazawarar dariya  Allah ya rufa asiri dai bai had eku gida d aya ba dan nasan da sai an kwashi  yan kallo tsakanin yarinyar da Anisa wataran.

Asshe ta kuma tab e baki  Ai Anisa gaba take da Uban nasu tinda yayi wann jarababben Aure. Sun had e kai da sauran  yanuwanta  yanmata yaran uwar gidana suna gaba da ubansu ya auro sa arsu. Shiyasa ma bata cika son zaman Kano yanzu ba tafi son zama can Abuja wajenki to avoid seeing her father here.

Mommy tai shiru tana tuna case d in dake nata gidan. Ta d an numfasa  Gwara su idan sunyi gaba da Ubansu sunada dalili. Tai maganar tana k ok arin shigewa mota suna kuma sallama da  yaruwarta.

Kasancewar fitan sassafe tayi yasa ta samu isowa da wuri. Tuni tasa ma aikata an soma dafe dafen abincin da za a tarbi Daddy dasu.

Suna zaune shida ita a parlor bayan ya ida cin abinci magazine rik e cikin hannunsa yana dubawa.

Mommy dai sai digesting maganganun da boka ya sanar da ita take. Ta rasa ta yanda za ayi ta soma sanar da mijinta batun. Toh ma mai zata soma sanar dashi. Cewa d ansu yayi Aure ba da saninsu ba.? Kodai mugun asirin da aka jefesa dashi.? Ko kuma auren da Malaminta yace a masa wanda shine makarin sihirin. Ta ina zata faro. Tana tsaka da tunanin kaman wanda aka jefo sa suka sinkayo sallamansa.

Yau Mommy ta rasa duban tausayi take masa ne ko duban sakacinta akansa.

Kallo d aya mahaifinsa ya masa ya watsar.

Ya k ariso hannunsa rik eda shud in Folder mai d aukeda logo na Kampanin mahaifinsa jiki Wato (MB).

Gaisar da iyayen nasa ya soma yi daga nan yanda yake tsaye bayan kujera dan yasan he s always not welcome. A gidan da ya kamata ya kira da home.

Mommy ce ta amsa gaisuwarsa yau d in da sakin fuska. Ga wani mugun sanyi da tayi. Mahaifinsa kaw bai samu zarafin amsa masa ba.

Mommy ta d anyi murmushin da yafi kama da yak e tana duban mijin nata da kacaukam hankalinsa Ke bisa Magazine d in dake hannunsa. Wani article ne ya d auki hankalinsa yanda aka rubuta  FG to approve the billion dollars bridge project to Maitama Builders. Project din da Haidar keta fad I tashi akai ganin an zab esa matsayin Project Manager.

Mommy ta d anyi gyaran murya  Engr Haidar na gaidaka.

Har lokacin idanunsa naga magazine d in  Na ganshi ai.. Sai ya fad i abinda ya kawo shi. Yai maganar ko kallon yanda Haidar yake baiba.

Haidar ya had iyi bak in cikin da ya tokare masa mak oshi.

Mommy dai gaba d aya jikinta a sanyaye yake yanzu tinda Malaminta ya sanar da ita abinda Ke faruwa. Ya zama dole ta bada himma wajen had in kan ahalinta bazata bari azzalumai suyi nasara akansu ba. Ta dubi Haidar wanda ya kafe mahaifina da ido kaida gani kasan ba kallon komai yake masa ba face tsana. Ta k ak aro murmushi  Haidar you heard your Dad.. Ka shigo ka gabatar masa abinda ya kawo ka nasan ya shafi aiki tinda ga company s folder hannunka.

Bai dubi Mommy ba tinda dukansu haushi suke basa ya k arasa yanda mahaifinsa yake. Ya aje folder d in gefensa kad an  This is the new proposal my team and I have been working on.. It contains all the details, the construction deliverables.. The scope and budget of the project.. Ya d anyi fasali jin bai amsa sa ba kafin yaci gaba  You..can go through it and see, before we present it to the board of directors..

Har lokacin bai amsa sa ba. Kaman ba dashi yake ba haka Daddy yayi. Haidar ya kuma had iyan k uncinsa. Duk abinda mahaifinsa zai masa akan wann project d in ya zama dole ya shanye. Alk awari yayi sai yasa mahaifinsa ya cinye duka kalamansa. He never backs down. He must fulfill all his promises. Zai wanke kansa zai kuma sa mahaifinsa ya cinye kalamansa sann daga k arshe he will personally take the company down to the ground. To the last kobo. Ya ranste sai ya tarwatsa mahaifinsa da kansa.

Sai matse file d in yake cikin hannuna jijiyoyin jikinsa na kuma tashi kaikace ketata zai.

Muryar Mommy ya sinkayo tana tausan mijin nata da yaji bayanan d an nasa ya kuma sauraresa.

Kaman bazaice komai ba sai yai masa nuni da hanyar da zai sadaka da study d insa daga nan cikin parlorn.

 You can leave it over there. Maybe, I ll go through it when I m less busy&  Daddy yace yana mai rufe magazine d in had i da zame farin glasses na k ara k arfin gani  I just hope it is not one of your foolishness.

Haidar ya rintse idanunsa yana jin abun har cikin k ahon zuciyarsa. Bai kuma juyowa ya dubi mahaifan nasa ba yasa kai ya shige cikin sauri kafin zuciya ta d ibeshi.

Yana shigewa Mommy ta mik e tabi bayansa da sauri dan wani tunani ne ya fad o mata wanda k ila damarta kenan akansa.


A waje yanda ya aje motarsa ta cimmasa.
Ta bud e murya ta kirawo sunansa.

Kaman bazai tsaya baya, sai kuma ya dakata ba tareda ya juyo ba yana mai furzar da huci a hankali.

Mommy tai saurin k arisowa yanda Haidar ya kaikaito yana dubanta.

 What now.? Kin mance ne baki bani naki insults d in ba shine kika biyoni waje..? Ya fad i idanunsa akan mahaifiyarsa.

Mommy tai k ok arin dannewa dan yanzu ta tabbata he s not in his right state of mind.

 Kaga Haidar I m not your enemy here.. In fact taimakonka nake so nayi.. Naga yanda kake matuk ar so kai handling project d in nan& Kuma nima na tabbata kai kafi cancanta kayi d in& I can be your ally until your achievement.


Murmushi Haidar yai hannayensa dafe da kunkumi yake duban Mommy. Sai kuma ya girgiza kai yace  Seriously Mommy.. You wanna be my Ally..? Since when Mommy..? Yaushe kika fara damuwa dani da abinda ya shafe ni..?

Mommy ta zuba masa idanu.

Haidar yaci gaba  Kinsan meye damuwarki Mommy.. Shine ya amince na jagoranci aikin sabida personal interest d inki. Kinsan na jima da sanin ni a wajenki ba komai bane face weapon. Makaminki.. Kuma kar ki mance na fad a miki bazaki sake amfani dani ba wajen cimma wasu mnufofinki. Wancan Aliyun ya Riga ya mutu Mommy.. He s long been dead.!

Yana ida fad in haka yasa kai ya shige motarsa sai sakin huci yake.

Zai bud e marfin motar kenan Mommy tai saurin dafa hannunta saman nasa. Hawaye suka soma gangaro mata. Cikin tsananin rawar murya take furta  Haidar& What did they give you.. What have they done to you to turn you against us like this..?

Cikeda k osawa ya zame hannun Mommy daga saman nasa  Ba hawayen da zaki zubar da zaisa na yarda dake Mommy. You destroyed that bond tin da jimawa. So kar ki saka ma kanki ciwo Mommy.. I do not give a damn about this family. I m doing this project for my own personal interest of course. Kuma bazaki tab a sani ba until my mission is accomplished. Yana ida fad in haka yasa kai zai shige motarsa.

Mommy ta bud e murya tace  Idan ni ce Matar Aliyu Maitama har sai kazo nan ka amince da buk ata ta kafin ya saka hannu da sunanka saman project d in nan.! Tana ida fad in haka tasa kai ta juya cikin gida ba tareda ta kuma sauraronsa ba.

Juyowa yai yana duban Mommy yana so ya fahimci mai take nufi cikin kalamanta. Yasan mahaifiyarsa tinda ta fad i haka tanada wani babban dalili a k asa tana kuma so ya tank wara shi ne yayi wani abinda take so. Zaiyi duk yanda zaiyi ya tabbata bai fad a tarkon da take k ok arin d ana masa ba.

**

Kano.


Waya ta ida yi da Marka yanda ta sanar da ita Matar ta farka amma bata cewa komai. Kuma bata fad i yanda danginta suke ba balle a nemsu. Ga dukkan alamu idan ba mai tab in kai bane k ila had arin ya tab a mata kai.


Hilal ne ya tuk ota zuwa asibitin. Ta dubi Marka ta dubi matar wacce Ke ta zabga kuka saman gadon asibiti.

Marka taci gaba da fad in  Ayya Hajiya  yan jikokina suna gida basu ganni ba tun jiya. Wllhi duk na gaji gida nake son zuwa ga wann asibitin babu mutane sosai balle likitoci kinsan yanda asibitin kud in nan suke zuwan likita nada k aida da lokaci. Tak i magana tinda ta tashi kuka take. Inaga Hajiya kawai idan likita yazo ruwan da aka d aura mata ya kare kisa a sallameta ai kunyi naku Allah ya gani.

Hilal ya girgiza kai yana duban Matar cikeda tausayi  No Ammi. Ba haka za ayi ba. Inaga kamata yayi akaita wajen k wararru su sake dubata. Watak ila ta sami wani internal injury. Kamata yayi akaita a dubata a bata all the treatment that s needed. Idan ya kama mu mik a case d inta ma hukuma su zasu bincika yanda danginta suke. But we can t abandon her not knowing ina danginta suke. Watak ila sunata nemanta tin faruwar had arin.

Asshe ta katsesa  Kai Hilal nayi na musulunci tinda har asibiti mun kawota. Har wacce zata kwana da ita na bari. So bazanyi treating ciwon haukanta ba. Tafiya take tsakiyar kwalta dama can k ila da guntun haukarta. Ta dubi Marka tace  Marka jeki abinki zan fad awa nurses d in da suke bakin duty da zaran likita yazo suna iya sallamarta.

Marka tai godiya da fatan samun sauk i ta fice.

Hilal ya girgiza kai zai kuma magana ta nuna masa waje  Fita mota ka sameni ina zuwa zanyi magana da mutanen asibitin.

Ba Don yaso ba ya girgiza kai ya fice.

Asshe zata take masa baya kenan ta sinkayo muryar Matar tana fad in  Lafiyata garau. Kuma duk ina sauraronku. So nake ku d aukeni ku kaini can babban asibitin koyarwa yanda mijina yake ko zan samu na ganshi. Tani ta hana ni ganin shi tace nida Ummul mu muka taru muka saka masa ciwo.. Ta ina zan soma neman kud ad en da Tani tace na nemo na jinyar Malam. Tani takai mak ura wajen makirci da zalunci. Ta soma kokawan sauk owa daga gado dikda drip dake d aure hannunta. Fad i take  Na tabbata tana can ta d aura laifin komai akan Ummul da bak in k addarar da yai ma rayuwarta dabaibayi.

Asshe tai saurin k arisowa ta dakatar da ita.

Umma ta d ago ta dubeta sai ta fashe da kuka  Wllhi lafiyata k alau ina cikin hayyacina. Sun kasa gane banida wani buri da ya wuce naga Ummul a d akin mijinta. Toh meyasa Tani zata d aura alhakin ciwon Malam akaina da Ummul.? Taci gaba da rera kuka irin na wanda damuwa ya masa dabaibayi.

Asshe ta janyo farar kujera a gefe ta zauna tana duban Matar  Sunana Hajiya Asshe, mun bigeki da mota akan hanyarmu.

 Yaya Tani ce tace lallai lallai sai na nemo kud ad en da za ayi ma mijinmu jinya idan har ina so na sake ganinsa. Ta nad i sautin muryata cikin waya itada Badi a sunce ko Kotu akaje ya iashesu Hujja.

Asshe ta zuba mata idanu jin yanda taketa maganganu marassa ma ana. Labarun da yafi kama da wanda ke cikin depression. A hankali ta d an jinjina kai ta dubi Matar  Akwai yanda yake miki ciwo ne. Kina so na kira Likita.?

Umma ta girgiza mata kai alamun a a Baiwar Allah ni fah lafiyata lau. Yaya Tani ce ta yanka ragon hauka ta d aura mun dan kawai Ummul ta kasance  yata. Sai ta d anyi fasali ta kuma duban Asshe  Amma wacece ke.?

Asshe ta k ura mata idanu tana karantarta sai tace  Toh ma sha Allah. Tinda kince babu yanda yake miki ciwo. Tai fasali dan sosai take so taji labarin Matar musamman da taji abubuwan dake fita bakinta shan cikin Matar bazai mata wahala ba  Ki kirani maganin matsalolinki.! Ta matso had ida d aura hannunta saman na Umma  Ki yarda dani zaki iya sanar dani duk damuwarki. Ni ba muguwa bace nasan zaki fahimci haka tinda bayan bigeki da mukayi bamu k yaleki ba saida muka tabbata mun d aukoki mun kawoki asibiti. Kuma ban barki ke kad ai ba har saida na ajiye wacce zata kula dake. A nan muka shigo da yarona kikaji yana cewa kar mu kyaleki har sai mun tabbata kin isa ga ahalinki lafiya. Wann kawai ya isheki ki yarda mu mutanen k warai ne ba masu cutarwa ba. Kuma a yanda yanzu duniya ta koma babu yarda tinda har ni nayi shahada na yarda dake ya kamata nima ki d auki duk yarda ki bani. Watak ila Allah ne ya dubeki ya had aki da maganin matsalolonki.

Da mamaki Umma Ke dubanta  Maganin matsalolina ni Suwaiba..? Tai maganar tana nuni da kanta.  Baiwar Allah anya kaw kinsan matsalolina..? Ai inaji kaf fad in garin Kano da kewaye babu matar da ta kaini matsaloli tinda har na kasance mahaifiya ga Ummulkhairi.!

Asshe ta kuma gyara zama cikin son jin taji komai  Wacece Ummulkhairy.?

Umma ta kamo bakin zaninta tana share hawayen dake kuma zubo mata  Ummulkhairi,  Yata da na mata lak abi da Uwar alkhairi..!  Yata da naci mata buruna da dama. Ta kuma duban Asshe sai

12 / 52