Auren Wata Uku Book Complete By Sameena Aliyu.doc

Author :  SAMEENA ALIYU Category :  Arewa Pen

Chapter   3 / 52

6K to 9K   out of 153.1K words



 Aunty Kwaise.. Ta kira Mommy da sunanta kafin taci gaba  Wai meke faruwa ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ne.. Ina zaije shi da suitcase..?

 Ban sani ba mana Anisa. amma hala Ke zaki iya sani.. Mommy tace a hasale.

Anisa da mamaki bai saketa ba tace  Mommy ta ya zan sani nida jiya jiya nazo gidan..

Mommy ta shiga janyo hannunta cikin sauri tana fad in  Binshi zakiyi ki gane mana yanda zaije& Maza maza kafin ya b ace kinsan yanda car keys suke ai. D au d aya ki bi mana bayansa. Kar barshi ya b ace ma ganinki Anisa..

Anisa kaw tamkar wacce take jira gudu gudu tai yanda Mommy tace.

Tana tafe saman kwalta cikin k ok arin bin hanyar da taga Haidar yabi ganin bai b ace mata ba kaman daga sama taji an daki bayan motarta da k arfin gaske wanda hakan yai sanadiyar da motar Haidar ta b ace mata.

A dole ta danna birki kanta ya daki jikin staring wheel. Kafin ta sami zarafin fitowa daga cikin motar mutumin da ya daki nata motar ya b ace bashi a wajen. Mamaki ya cika Anisa ganin babu kowa bayanta da alama wanda ya mata wann aika aikan yayi gaba. Ta furzar da huci a hankali tana kuma duba bayan motar.

Bin bayan Haidar da batai ba kenan dole ta koma gida.

**

KANO

Yau d in yaran Mama sunzo yini daga gidan mazajensu dan tini Mama ta kirasu a waya d aya bayan d aya ta sanar dasu abinda ya faru na amshe lefen Ummulkhairy da akai. Dan haka washe gari kaf suka hallara. Sukai bak e bak e tsakar gidan suna watsa habaice habaice. Idan an Fad i abinda ya basu dariya kaji Sun saki shewa harda gud a.

Umma kaw ta kasa ko fita tsakar gida sabida habaice habaicensu. Ko abincin rana Sun kasa fita suci kasancewar girkin Maman ne. Ta kuma hana Ummul da Khulsum fita ko k ofa.

Khulsum ta dubi agogo k arfe d aya saura na rana. Ta dubi Umma dake zaune ta rapka uban tagumi tana sauraron habaice habaicen Mama dasu Salima.

 Umma lokacin sallan azahar yayi zan fita nai alwala.. Ta Fad i tana k ok arin mik ewa.

Saurin janyota Umma tai tana aika mata mugun kallo  A haka ne zaki fita su cinyeki da habaice habaice.. Nemi waje ki zauna akwai sauran lokaci. Ta k arashe tana zaunar da Khulsum da k arfin gaske.

Khulsum ta dubi mahaifiyarta da tsanin mamaki  Haba Umma dan Allah shikenan har ibada ma kar muyi sabida muna tsoron maganan mutane.. Umma shikenan yau a d aki zamu yini sabida maganganun mutane.. Umma dan Allah ina kika tab a Jin mutane Sun fasa magana.. Kuma waye magana ya taba kashewa.? Umma komai mukai wllhi sai anyi magana gara ma ki bari mu fita muyi ibada mu rok i Allah mafita da zaman tagumin da muke uwar d aki.. Umma zaman mu a d aki fah bazai sa su fasa maganganunsu ba..

Kuka Umma ta kece dashi tana fad in  Dik ba kece kika jawo ba.. Kin tsaya kina dambe bakin kwalta.. Yo ba da dole Zubairu da yaga haka yak i dawowa ba.. Nayi imani ba don ya hanngi Ummul na rabon fad a ba da ya taho ya nemi afuwa ya kuma sa an maido da lefen nan dan Zubairu yaron kirki ne.. Amma jarabar fad anki ya jawo Zubair ya kufce ma  yaruwarki.. Dole ma kice kar mu damu da maganganun mutane sabida ba lefenki aka amshe ba.. Wayyo ni Suwaiba wani laifi nai nake fuskantar irin wann iftil ai..! Ta kuma d aura hannayenta aka tana kuka.

Su Mama dake mak ale bakin k ofa komai a kunnuwansu. Badia ta janye labule ta lek o tana fad in  Gaskiya Khulsum bakida mutunci wann ai zubar mana da mutuncin gida ne dambe da k artai a bakin layi..!

Mama tai karaf tace  Ah toh hassada take maku ku da kuka samu Allah ya rufa maku asiri kuke d akin mazajenku bari tai abinda zai Shafa maku bak in fenti wajen dangin mazajenku.. Yo sukaji  yaruwarku guda an kuma amshe lefe da sadakinta d aya kuma tana dambe da k artai a bakin layi ai cewa zasuyi duk zuri arku haka kuke ke Salima me kishiya ta samu abun goranta Miki..

Haba nan fah Salima ta kuma harzuk a ta fad a d akin tana kokawan janyo Khulsum tana fad in wllhi bata isa ta kashe mata aure ba.

Umma na kuka take rok on Mama da yaranta da sukai ma Khulsum taron dangi suyi hak uri su fice. Itakam Ummulkhairy kuka ma ya hanata katab us yayinda Mama ke kuma ingizasu. Kan kace me ayarin yan cikin gidan Sun cika a k ofan sashen su Ummulkhairy suna bama idanu abinci. Tuni masu jin haushin Khulsum suka goyi bayan Mama da yaranta cewa Khulsum zata b ata masu sunan ahali bayan fentin da Ummulkhairy ke Neman shafa masu suma ak i Neman auren yaransu.

Ana wann kacaniyar mahaifinsu ya dawo daga Kasuwa. Ganin iyalansa haka yasa shi Jin kaman wani abu ya sokesa a k ahon zuciya. A hankali ya dafe k orjinsa yana k ok arin silalewa.


SameenaAleeyou& =???
*AUREN WATA UKU.!*




*05*





*??Sameena Aleeyou&
'





K ara Badia ta saki sakamakon hango mahaifinsu da tai yana k ok arin kaiwa k asa. Nan kuma hankula suka koma kansa. Mama ta k araso da sauri ta tallafesa tana fad in  Malam dan Allah ka rufa mana asiri kar bak in cikin Ummulkhairy yai ajalinka.. Wayyo ni Tani.. Sannu Abban Salima.. A haka ta k arasa dashi madaidacin parlonsa tai masa masauk i saman d aya daga cikin lamusassun kujerun dake a cikin parlorn. Sai jero masa sannu take tana bangaje Umma daga kusansa. Badia ta kawo mafifici Mama ta amshe tana masa fifita tana fad in maza ta kawo ruwa.

Bayan shud ewan wasu mintoci Abba ya soma dawowa hayyacinsa.

Gaba d aya ya had e matan nasa guda biyu. Ya d an kishingid a yana dubansu. Lokaci guda yake furta  Tani, Suwaiba..

Kowaccesu ta amsa jiki a sanyaye.

Abba yaci gaba  Bazai yuwu ku maida min gida kaman gidan kallon kwallo ba.. Ke Tani kin gayyato yaranki Sunzo kuna murnan abinda ya samu  yaruwarsu.. Ke kuma Suwaiba kin saka ma ranki damuwan abinda Allah bai saka Miki ba.. Ita rayuwar nan wai duka kwana nawa ne za ayi.. Kun raba mun kan ahali kun maida min gida kaman gidan maguzawan farko.. Idan kaji hayaniya na tashi a gidan nan toh wann k ofan ne.. Akan wani dalili..? Ya d anyi fasali yana dubansu kafin yaci gaba  Toh ku kula.. Ku kuma tuna cewa duk abinda Kai a wann rayuwar shi zakaje ka cimma a cen.. Bazan gushe ba ina maku nasihan kubi duniya a sannu rayuwar duka ba yawa ne da ita ba.. Bazan bari ku saka mun ciwon da bani da shi ba..

Murya a sanyaye Umma tace  Kai hak uri Abban Ummul in sha Allah zamu gyara.. Ko Yaya..? Tai maganar tana duban Mama.

Mama ta saci idanun mijin nasu kafin ta aikama Umma harara sama da k asa sai kuma ta juyo da duban nata ga Abba. Tai murmushi Wanda yafi Kama da yak e  Eh in sha Allah zamu gyara mun tuba Kaji Malam..Allah ya baka lafiya.

Jinjina Kai yai yace  Alhamdulillah.. Allah ya ganar damu baki d aya ya kuma had e mana kan ahalinmu ya shirya mana zuri armu.

Gaba d aya suka amsa da Ameen. Abba yai masu izinin tafiya sai kuma ya dakatar da Umma yace ita ta tsaya.

Wani birki Mama taja kaman zata dungura ta juyo tana duban Abba da yace Umma ta tsaya bayan yau girkinta ne.

 Malam ban gane Suwaiba ta tsaya ba.. Ni ce da alhakin abincika yau fah ko ka mance ne..? Tai maganar tana tururi kai kace ba itace yanzu ta gama ce ta tuba ba.

Abba ya murmusa yana ayyanawa cikin zuciyarsa Mata sai a barsu wajen kishi. So tari yakan yi ma Mama uzuri dan kishi Tabbas akwai ciwo. Wani abun yasan zafin kishi ne kawai yake sanyata yi amma Tani d insa tanada halin k warai.

 Magan zamuyi Tani ba wani abu ba.. Abba yace cikin sigan lallama.

Mama ta kad a Kai  Aiho.. Kardai garin dad in zance a zarce a shiga hakki ehe..!

Murmusawa kurum Abba yai ba tareda yace komai ba.

Saida Mama ta fice ya dawo da dubansa ga Umma.

 Suwaiba.. Ya kirawo sunanta

 Na am Abban Ummul.

 D azu a kasuwa mak ocin shago na ke jajanta mun al amarin auren Ummulkhairy.

Umma ta jinjina Kai alamun tana sauraro.

Abba yaci gaba  Bansan ko kin gane shi ba mai babban kanti na kayan masarufi da yake jikin nawa kantin.. Wasu lokutan har rancen kaya yake bani idan na saida na mayar masa uwar kud i hardai jarin nawa ya d an ja baya. Mutumin kirki ne Alhaji Kamilu..

Umma ta jinjina Kai tace  Allah sarki..

Abba yaci gaba  Toh nan dai nake labarta masa al amarin ita wann yarinya nawa Ummulkhairy.. Toh kwatsam sai ya sanar Dani yana so na bashi auren ita Ummulkhairin idan babu wani matsala.. Toooh wato gaskiya banyi garajen amsa masa ba duba da irin abubuwan dake faruwa. Ak alla aure nawa ake sakawa na Ummulkhairy abu baya yuwa.. Sann ko sati ba ayi ba da abinda ya kuma faruwa na amshe lefen shi yaron nan Zubairu. Amma dukda haka bazaka yanke tsammani daga rahamar Ubangiji ba. Ba wann dalilin ne yasa nace ya dakata ba.. Babban dalilina shine sai naji daga bakin  yata idan tana sonsa.. Idan har bata sonsa JINKIRIN aurenta bazai sa na aura mata mutumin da bata so ba.. Sabida shi Alhaji Kamilun lallai lallai ya nuna mun yana son na basa dama kuma Kinga akwai  yar kunya a tsakaninmu& Tooooh dai gaba d aya kaman ya d aure ni ne.. Dan a gaskiya.. Sai ya d anyi Shiru kuma kaman mai nazari  Bana so Ummul taga kaman na tak ura mata da batun aure ne tinda dudu ba a jima da fasa..

Bai kai aya ba Umma ta katsesa  Haba Abban Ummul.. Ta ya ma zakace haka.. Yo har wani lokaci zaa d ibar mata.. Shifa lokaci baya jira. Ka duba sa anninta duk suna d aki daga masu yara uku hudu kai har masu shida akwai sa anninta& Yo ai ko ta gansa ko bata gansa ba tinda har zai rufa mana asiri ya aureta ai shikenan..

Katseta yai da fad in  A a Suwaiba, JINKIRIN Ummulkhairy ba zaisa na tilasta mata kasancewa da Wanda bata so ba.. Kece mahaifiyarta, ki kirata a d aki a natse ki sanar da ita. Idan tayi na am falillahil hamdu yau da dare sai na d aga waya na kirasa gobe idan Allah ya kaimu sai yazo su fahimci juna.. Alhaji Kamilu mutumin kirki ne kuma yanada matan aure biyu da yara da d an dama.. Ki kira ita Ummulkhairy ki sanar da ita a natse. Idan Sun daidaita kansu shikenan sai ai maganan aure tinda babban mutum ne ba wani Jan lokaci za ayi ba. Hasalima Jan lokacin baida wani alfanu..

Umma tai karaf tace  Ai ko gobe ma sai a d aura kawai nidai ta tafi d akinta.. Ta d aga hannu sama tana fad in  Oh Allah na gode maka ni Suwaiba.. Allah maji kukan bawansa mai maida asara da alkhairi..

Girgiza kai kurum Abba yai yana dubanta. Zaman Ummu a gabansa bai d aga masa hankali ba kaman fitinar mahaifiyarta matarsa Suwaiba . Fatansa Allah ya had a Ummul d insa da miji na gari wanda zai kular masa da ita ya kaunaceta tsakani da Allah dama sauran yaransa gaba d aya.

Cikeda farin ciki tamkar wacce aka yaye mata kaf damuwarta na gidan duniya haka Umma ta fito tana k wlla kiran Ummulkhairy.

A daidai bakin farandar d akin Abba ta riski Mama rik eda farantin abincin Abban. Umma tana ganinta ta tsuke Baki tana zancen zuci Wanda sam bata san ya fito fili ba tsaban farin cikin da ta tsunduma ciki  A sirrace nema a bayyana samu.

Rangaji Mama take tana dubanta daga sama zuwa k asa. Kafin tai murmushi mai sauti tace  Ayi dai mai mu gani wai gurguwa da auren nesa. Ta k arashe kaman zata bangaje Umman ta nufi parlorn Abba.

Umma ta tab e Baki ta nufi d akinta cikeda farin cikin abin alkhairin da ya sameta dan yau d in Ji take burinta na gidan duniya ya gama cika.

**

Abuja.

Cikin bacci yake Jin vibrating d in wayarsa na kuma k aruwa alamun wayar ta gaza yin Shiru. Yai k ok arin mik ewa had ida janye Dareen dake kwance saman k irjinsa. Hannu yasa ya d auki wayar dake aje gefen bedside yana ganin lokaci quart after six na safiya. Lokaci guda ya d anyi relaxing jikin pillow yana k ara wayar a kunnensa yana rage girman idanunsa masu cikeda bacci wanda hasken hantsi da ya soma bayyana ya tilasta masa yin hakan.

 What Hisham. Ya Fad i yana gyara zaman wayar a kunnensa.

Daga d aya b angaren Hisham Yace  Haidar, Kana Ina ne.. me kakeyi..?

Da mamaki Haidar yace  What kind of question is that..? What could I been possibly doing at this time..? Bacci nake obviously kafin ka tadani.

Hisham ya katsesa  Have you seen the news..?

 What news..? Haidar yace cikin muryarsa mai cikeda bacci.

Hisham ya furzar da huci  Lallai na yarda kana bacci.. Check your phone ka karanta labarun kasuwanci kaga abinda muka tashi dashi. Daga haka katse kiran yai yayinda Haidar ya shiga shafa wayarsa. Tin daga saman fuskar wayan yake karo da notifications.

Notification guda d aya ne ya d auki hankalinsa. THE BUSINESS PRESS. Yanda aka rubuta *Top Business Scandal.* Saurin clicking yai ya shiga kan labarin. Abinda ya soma karo dashi a labarin shine hotonsa da mahaifinsa lokacin da ya cakumosa a cikin Kampaninsu yana jijjigasa yana fad in yayi disappointing d insa, daidai wajen akai cutting a video d in Wanda aka fitar da hoton sosai yanda ya rik e kwalan Haidar d in ga jini gefen bakin Haidar. K asan hoton kad an an rubuta kamar haka *Owner of Maitama Builders Engr Aliyu Maitama gets into a physical fight with Son over augment.*

 Damn it..! This is not happening. Ya furta a hankali. Sauri sauri ya mik e ya shige bathroom dan shiryawa.

Dareen dake baccinta peacefully ta soma bud e idanunta masu cikeda bacci wanda ko shakka babu shirin da Haidar d in keyi ne ya katse mata baccin.

Ta zuba masa idanu tana duban yanda yake komai a gaggauce. Ta saki murmushi zallan k aunarsa cikin zuciyarta. A hankali ta sakalo k afafunta ta sauk o daga saman gadon.

Yana tsaye gaban full length mirror yana k arisa shiri yaji ta rungumosa ta baya had ida matsesa sosai cikin jikinta.

 Good morning.. Ta furta tana mai d aura hannayenta saman nasa ta amshe agogon da yake k ok arin d aurawa taci gaba da d aura masa
 Are you leaving this early..? Tace sanda take kaikaitowa ta dawo ta gabansa.

 I have to.. I need to take care of something.. I ll see you later.. Yace a tak aice yana d aukan wayarsa da mabud in mota

Ta take masa baya ganin zai fice cikin sauri. Ta kamo hannunsa guda  What about breakfast..? Your cool tea is in the fridge.. Tun asuba na had a maka.. The way you like it.. Should I serve you..?

D an dubanta yai kafin ta girgiza kai  Kar ki damu, I ll be fine..

Ta kuma rik e hannunsa  Does that mean ka amince da k orafina ka fasa aje aikinka a Kampanin Daddynka.? Tai maganar idanunta tar akansa.

Ya d anyi still yana dubanta  I don t know& I m not sure.. I.. must go now.. Take care.. Ya k arashe yana shafan b angaren fuskarta guda da tafin hannunsa.

Ta janyo hannunsa ta sumbaci tafin hannun kafin ta sakar masa murmushi tana masa fatan nasara har saida taga tashin motarsa. A hankali ta lumshe idanunta had Ida sauk e ajiyan zuciya kafin ta koma cikin gidan..



ya d auki car keys d insa da wayarsa ya fice a gaggauce.


Yana tafe saman kwalta wayar Hisham amininsa kuma abokinsa a wajen aiki ya kuma shigowa.

 Haidar this is bad.. Very bad.! Abinda Hisham yace kenan koda Haidar ya d aga kiran.

Jinjina Kai Haidar yai
 Yanzu zaka yarda da magana na.. Someone is sabotaging the company.. And trust me, I know exactly how to catch that rat. Shiru yai alamun yana sauraro daga b angaren Hisham.

Hisham yace  Kuma ba yanda za ai ka kamo wann b eran har sai kana aiki da Kampanin. Now more than ever you can t quit your job.. You need to fix this Haidar.. You need to clear your Dad s name.. Bazaka bari sunan Kampanin ya b aci ba..!

 Oh Shut up Hisham..! Ya fad i yana mai katse kiran lokaci guda yana mai k ara gudun motar.


A can gidan mahaifinsa kaw ya tsare mahaifiyarsa ta yanda yake shiga ba ta nan yake fita ba. Ga  yan jarida sunyi chaa a bakin gate suna jiran fitowarsa.

Yaci gaba da nuna Mommy da yatsa  Call that pathetic son of yours and tell him to fix this mess immediately.. Bayan asaran da zamu tapka sabida shashashancinsa, I won t allow him to ruin my company s image.! Ya k arashe cikin tsananin huci yana mai ci

3 / 52