Auren Wata Uku Book Complete By Sameena Aliyu.doc

Author :  SAMEENA ALIYU Category :  Arewa Pen

Chapter   13 / 52

36K to 39K   out of 153.1K words

ta girgiza kai wasu hawayen na kuma gangaro mata  Amma babu buri guda d aya da ya cika. Kinsan dalili..?

Asshe da ko kifta idanu batayi saurin girgiza kai tai alamun a a.

Umma taci gaba  Sabida mutane sun canfa mun ita.. Duk namijin da yazo neman aurenta guduwa yake. Kodai wani abu ya gifta a fasa Auren. Amma fah dukda wann guje mata da mazan keyi basu fah fasa neman aurenta ba. Kinsan meyasa..? Tai tambayar murmushi mai ciwo saman fuskarta kafin taci gaba  Sabida Ummul d ita tubarkallah ce san kowa k in wanda bai samu ba. Sai kuma ta fashe da kuka  Amma meyasa ta kasa Auruwa..? Meyasa duk masifa da nake fuskanta a nawa gidan Auren ta dalilinta ne.? Meyasa maza ke guje mata. Meyasa k addararta yazo a haka. Ta k arashe cikin gunjin kuka.

Asshe ta kamo hannayen Umma cikin nata tana k ok arin kwantar mata da hankali  Ki daina kuka. Shi Aure lokaci ne. Baya duba matsayi ko kyaun halitta. Wata da komai ta rasa miji wata ba komai Allah ya bata. Shi Aure kaman hab o ne da zaran lokaci yayi sai kiga anyi..

Cikin zuciyar Asshe fal mamaki. Ganin abun take kaman almara. Abinka da mai b atacciyar zuciya sai ta kuma gaskgata aikin bokansu. Gashi tin ba aje ko ina kaman sun had u da makarin sihirin dake jikin Haidar a sauk ak e. Sai ta kuma yarda gaskiya Malaminsu ya fad i ta mance cewa wann duk zai iya zama jarabawa daga Ubangiji mai komai ya baka abinda kake nema d in a kan gab ar da kake nema. Wani shikenan sai ya kuma dulmiya cikin b ata. (Allah kai mana tsari da shirka. Ameen)

Ta saki murmushi tana duban Umma  Ummulkhairinki zatayi Aure. Aure na bajinta. Aure irin na kece raini. Auren nuna ma duniya.!

Umma ta dubeta da mamaki. Sai ta girgiza kai tace  Anya kuwa Ummul d ina nada rabon Aure a wann duniyar.?

Asshe ta murmusa  Idan har kika aminta dani Ummul d inki zatayi Aure.. Tai maganar cikin jaddada kalamanta.

Hilal ne yai knocking ya lek o jin shirun yayi yawa. Nan ya hangi mahaifiyarsa da patient d in kaman sun jima da sanin juna. Mamaki ya cika Hilal. Ya d an girgiza kai yana mamakin saurin yarda da juna da mata keda shi saikace ba Ammi bace ta gama cewa su tafi su kyale matar. Bai gama mamaki ba saida yaga Amminsa sun fito tareda Matar dan dama da ya shiga tace masa bari likitan yazo ya masu sallama tinda taga isowar motarsa. Shidai Hilal haka ya tuk a su suka nufi gida tareda Matar dasu Ammi suka bige wacce ta zamto bak uwar Ammin tasa.

Suna isa gida Hilal ya tareta  Ammi Wai meke faruwa ne. Meyasa kika taho da matar nan.. Ammi I thought danginta za a nema.. Nowadays fah mutane ba abun yarda bane. This whole thing zai iya zama shiri bigeta da kukayi, kaita asibiti da duk wani maganganun da zata sanar dake. Ammi yanzu fah har gida ake ture a sace mutane. Ammi Abba sanannen mutum ne a garin nan. Iyalansa zasu iya zama target.

 Kai dallah rufe min baki. Duka duka yaushe ka sauk a k asar balle ka fad a min abinda Ke faruwa cikinta. Nafika sanin meke faruwa. Ina zuciyar taimakon taka? Inji kai ka fara cewa we shouldn t abandon her. Toh Shiyasa na taho da ita. Kuma ko mahaifinka yazo gidan nan ba ruwanka kar ka sanar dashi komai kaji na fad a maka.

D an girgiza kai yai  Fine, yanda kikace Ammi. Hilal yasa kai yai shigewarsa.

Yana shigewa ta d aga waya tai dialing wani layi. Ana d agawa ta soma fad in  Hello Yunusa kanajina. Zan turo maka information kan wata mata. Yanda take zama sunan mijinta da sauransu. Inaso ka gudanar min da binciken k wak waf kan ahalinta da abinda Ke faruwa dasu. Bana so a d auki lokaci. Ayi komai cikin gaggawa.

**

A can b angaren su Ummul kuwa hankulansu yakai matuk a wajen tashi. Dik yanda ake tunanin za a sami Umma anje ba a sameta ba. Hisham kaw da shi ake aiwatar da komai tuni sun bada cigiyan Umma.

Yai k uri yana duban Ummulkhairy dake ci gaba da kuka da gaske wann karon. Duk k ok arin ganin bata d aura alhakin iftila in dake faruwa cikin ahalinsu akanta ba saida zuciyarta ta raya mata hakan.
Da wanne zasuji? B acewar mahaifiyarsu ko kuwa mahaifinsu dake kwance gadon asibiti wanda har wann lokacin bai san yanda yake ba. Ga likitoci sun tabbatar masu idan har treatment d in da ake masa yaci gaba da failing jikinsa ya kasa amsa then he must have to undergo Cardiac surgery wanda zaici mak udan kud ad e ga had arin dake tareda hakan.

Hisham ya d anyi gyaran murya cikin k ok arin kwantar mata da hankali. Amma kaman cewa yai ta k ara. Ringing d in wayarsa yaja hankalinsa.

Abokin aikinsa ne kuma amininsa Haidar me kira. Ba tareda ya bar wajen ba dan baisan barinta ita kad ai farfajiyan asibitin suke yayinda Khulsum ke can wajensu mama sun hanata koda lek a Abba ne.

Daga d aya b angaren Sautin kuka ne yai Sallama ma Haidar. Ya d anyi still kafin yace  Wait..What s that noise.. Where exactly are you..?

Hisham ya dubeta sanda take k ok arin mak ale kukan nata bayan taji alamun yana amsa waya  You seem to forget things easily nowadays Engr. Ka mance na tafi gida ne.

Haidar ya d an d aga gira yana mai jinjina kai  I hope dai lafiya ka samu gidan. I mean lafiya ka samu Hajja..?

Hisham yace  Yeah lafiya.. Ya k arashe yana mai d an jan kalamansa.


Haidar ya kuma tambaya  So who s making that noise.?

Ciki Zuciyar Hisham ke ayyana isa da jin kan Haidar. Wato bazai iya tanbayarsa wacece ke kuka next to him ba shine wai hayaniyar me yake ji. D agowa yai Ya dubi Ummul wacce ke k ok arin tsagaita kukan nata. Ya d an mik e ya matsa gefe kad an . Ya saki murmushi mai kyau yana mai d an rage murya  Let s call her Someone.. Someone Very special.. Ka gane I ll call you back.

D an tab e yai  Let s talk business. Yace cikin katse Hisham d in.

Hisham ya d an kuma satan kallanta sanda Haidar ke sanar dashi sunada ganawa ta musamman gobe a Kampani. Ya zama dole ya katse hutunsa.

Hisham ya girgiza kai kad an  Wait what meeting Haidar.?

 Tomorrow by 9:00am.. Design Architect Hisham.! Abinda kawai Haidar yace kenan.

Hisham ya soma girgiza kai cikin rashin yarda  You know I can t make it to the meeting Haidar.. I mean I m not the only design architect in your team... Bai tsaya d aukan excuse d in Hisham ba ya katse kiran.

Furzar da huci Hisham yai yana shafan fuskarsa da tafukan hannayensa. Jiki a matuk ar sanyaye ya dawo yanda ya baro Ummul.
Ta ya zai barta ya tafi a lokacinda take tsananin buk atarsa. He needs to stay.. But what about aikinshi.. Baiso wani yai taking place d insa. Sun jima suna aiki tuk uru kan wann project din wanda yake da tabbacin idan ya zama a successful one ba darajan Kampaninsu kawai zai d aga ba. Zai taimaka wajen daidaita relationship d in Amininsa da mahaifinsa wanda a kullum yake burin faruwan hakan. Bayan haka Haidar is counting on him. Abokinsa needs him now. Amma kuma Ummul fah. Shin zai iya barinta ya tafi.? Shin waye zai kyale ciki su biyun.



SameenaAleeyou=???
*AUREN WATA UKU.!*


*13*


*??Sameena Aleeyou&
'

Akan idon su Mama Hisham yai ma Ummul sallama ya rakota har wajen Khulsum. Saidai bai sanar da ita batun tafiyarsa ba.

Mama da Azeema ko harma da Badi a ko k ifta idanu basuyi. Musamman da sukaga zankad ed en Saurayin dake tare da Ummul. Mama tace  Toooh shi kuma wann d in wai waye.?

Badi a tace  Wa ya sani masu ne Mama. Amma kaman saurayin Ummul..

Mama ta bige bakinta  A gidan uwar waye ya zama saurayin Ummul. Wann yafi k arfin Ummul inaga dai yayi zaton mabaraciya ce ya taimaka mata musamman da yaga tana cikin damuwa.

Badi a ta harari Mama yayinda Azeema ke hararar Khulsum tana cika. Lokaci guda ta katse Mama da fad in  Saurayinta ne mana shine yayi belin wancan k aramar  yariskar a police station bayan ta mareni.. Wllhi bazata saku ba. Ai na biya kud in kwananta a cell amma bata kwana ba.. Toh wllhi komawa zanyi ayi duk rikicin da za ayi. Ni da kaina na lale kud ad e na bawa Habibu ya biya  yansandan cewa su rufeta ta kwana. Wllhi komawa zanyi ko su biyani kudina ko su sanar dani dalilin bud eta. Ai ko Kotu akaje akwai kud in mari. Idan har ba biyana akayi ba wllhi rikicin nan bai k are ba ehe. Ta k arashe tana mik ewa fuuu.

Mama tai k ok arin dakatar da ita da fad in  Ke ke.. Ke ina zaki Azeema..?

Ko juyowa batai ba Azeema balle ta amsa ta. Saima dialing layin Habib da tai tana k arawa a kunne.


Mama ta???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? dubi Bad ia bayan Azeema ta shige. Ta janyota suka keb e  Yauwa Kinga d aga waya ki kira Tasi u yazo ayi maganar sayar da shagon Malam da d an sauran abinda Ke ciki. Kinga naji d azu likitocin nan suna bayanin aikin da za ayi ma Malam mak udan kud ad e zai lak ume wanda ko gaba d aya Kantin da kayan dake ciki aka sayar ba isa zasuyi ba. Kinga kafin Wann shago da abinda Ke ciki tsautsayin jinyar Malam ya hau kansu gwara mu dafe su tunda wuri dan bazai yuwu mu zuba d an abinda zamu samu ma jinyar Malam ba wanda su kansu likitocin k irdado suke amma ga dukkan alamu ciwon Malam ba na tashi bane.

Bad ia ta jinjina kai  Kuma ma Mama ai wanda suka fi cancanta su nemo kud in jinyar Abba wanda sukai masa sanadin ciwon ne. Ina nufin wancan annobar da uwarta. Tai nuni da yandasu Ummul Ke zaune.

Mama ta jinjina kai  Alhamdulillahi ina jin dad in yanda kike fahimta. Maza kirawo Tasi un.

Tuni Badi a ta d aga wa ta shiga dialing layin Tasi u mijinta.


Khulsum ta dubi  yaruwarta Ummulkhairi cikeda tausayawa  Adda yau d in fah duka baki saka komai cikinki ba. Dan Allah kiyi hak uri ki tashi haka nan mu tafi gida yamma ta riga tayi.

Ummul naci gaba da hawaye ta girgiza mata kai  A a Khulsum bazan iya tafiya gida ba. Watak ila Umma zata zo nan wajen Abba..! Tai maganar cikin tsananin rawar murya irinta mai kuka.

Muryar Mama suka sinkayo akansu  Au har yanzu Uwar taku bata bayyana ba. Ta tabbata dai Angulu ta koma gidanta na tsamiya.

Suka d ago suna duban Mama da Badi a tsaye kansu sai aika masu kallon wulak anci suke.

Ummul ta girgiza kai  Mama Umma b acewa tai bamu san yanda take ba.

Sai Mama ta shiga tafe hannaye tana salallami  Na shiga uku ni Tani. Ta nan Suwaiba ta b ullo..? Ta rasa abinda da zatai sai ta guji Malam sabida jinya ya kamasa ya zama kaya. Watau Suwaiba bazata iya jinyar Malam ba dai shine ta guje ta k yaleni da wahalar jinya.. Yanzu da zataji labarin Malam ya cika dik yanda take zata fito tazo amsa sunar matarsa dan ta amshi rabonta na gado.

Sai sann Khulsum ta finciki hannunta daga rik on da Ummul ke mata cikin k ok arin dakatar da ita. Sai huci take.

Badi a ce ta janyo hannun Mama hango mijinta Tasi u da tayi sai buga sauri yake ya nufosu  Muje Mama kar ma kiyi hayaniya dasu balle a ba ma masu gadi hujjar koranmu. Ganin Abba ne sai a k iyama idan sunada rabon had uwa a k iyamar.

Khulsum ta kuma fincika zatabi bayansu Ummul ta kuma dakatar da ita.

Cikin kuka Khulsum ke furta  Haba Adda Ummul. Haba ke kuwa.. Wai dan Allah meyasa kike dakatar dani.? Mutanen nan fah yaren da kawai suke fahimta kenan.

Ummul ta jinjina kai tana kuma share hawayenta  Abinda suke so kenan Khulsum kiyita biyesu kuna tashin hankali. Ki tuna Abba dake kwance cikin asibitin nan. Ki tuna halinda yake ciki. Sann ki tuna Umma da halinda take ciki. Dan Allah ki daina biyewa Mama da yaranta. Allah ya fisu Khulsum. Mu fawwala masa komai da sannu zaiyi ikonsa akan kowa. Da sannu zai ba ma Abba lafiya ya tashi kafad unsa kuma suna kallo. Muci gaba da yi masu add uan shiriya har kullum domin su d in ahalinmu ne komin lalacewarsu. Muje Khulsum, mu tafi gida mu kai kokenmu ga Rabbil izza wanda shike yaye dukkannin damuwa ya kuma kawo sauk i da maslaha. Tana ida fad in haka taji natsuwa ya sauk a cikin zuciyarta. Jiki a sanyaye suka fice daga asibitin.
**


Tasi u yau harda risinawa yake gaida Tani. A mutunce yau d in ya fito masu dan batu ake na kud i.

Mama kaw sai hura hanci take dan ba Wai ta masa afuwan musguna ma  yarta Badia yake bane. Yanzun ma dan Badi an ta nace ne sai an sako Tasi un cikin hidiman, ta tabbata amfani yayi da son da Badi a Ke masa ya saye zuciyarta da kalamai har ta aminta dashi. Dan dai ita kam har yanzu bawai ta yarda da tubansa bane. Tasan tuban D anmuzuru ne. So yake a bawa Badi a kasonta su lak ume tare da zaran kudi sun k are yaci gaba da mata iya shege.

Ta dubi mai sayen shagon da Tasi u yazo dashi dan tinda Badi a ta sanar dashi cikin waya ya taho da mai cinikinsa dan dama tuni ya tanadi mai saye tinda aka soma batun.

Mama sai cika take tana batsewa tana ciniki da mai sayen shago. Tasi u yana daga tsakiya a matsiyinsa na dillali sai gyaran waje yake. Mama ta narka masa harara ganin zak ewarsa.

 Amma dai Tasi u ka tab a dillanci ko..? Cewar Mama tana dubansa a dak ile.

Tasi u ya Washe baki  Yo Mama banda abinki meye ba a tab awa ai duk abinda aka samu bugawa ake baka san ta yanda wutan zai kawo ba. Sai faman Washe baki.

Ita kaw Hajiya Badi a sai karkad a k afafu take tana Jin kanta. Daga yanzu ta samu makamin rik e Tasi a hannunta. Tinda zata samu kud i abinda yafi naira dubu d ari aiko sai yanda tai da Tasi dole ta zama itace mijin itace mai basa doka da order. Tin yanzu ma biyayya yake mata balle ta dafe kud ad enta.

Aka tsaida cinikin Kantin Abba. Mai saye yace gobe suzo da takardu a saka hannu.. Nan fah Mama ta soma zare idanu dan bata San yanda ya aje ba. Tasi u yace wann ai ba abun tada hankali bane washe gari zaije yai sabbin takardu a gama komai. Yanda yake ladabi wa Mama da Badi a kai ka ranste yaron gidansu ne

**

A can station Habibu mijin Azeema sun keb e da sergeant d in da suka tafi sukai arresting Khulsum dan dama budurwarsa ce, ta cika tayi fam sai hura hanci take  Ni fah ba matsala ta bace dan an mari matarka. Yo a kasheta ma mana ai banida asara. Ni wllhi ba don ka min alk awarin aure ba wllhi kaji na ranste da bazanje nai arresting kowa ba. Kuma kafi kowa sanin sabida kai nai. Toh ya Oga na zai yanke hukunci tazo nan tana kawo mana hauka. Ce mata akayi nan tasha ne. Ko ka d auki matarka ka tafi ko a banza na jefata cikin cell a lakad a mata duka dan bazan bari ta mun sanadin aikina ba. We are talking about my superiors here. Ita har ta isa tazo nan tana mana zage zage da hauka. Tasan me ake kira hukuma ma kuwa. Na ranste maka Habib idan bakai controlling d inta ba zata gane ita k aramar mahaukaciya ce dan yanzu zata tabbata mahaukaciyar da Dawanau ma ya kasa mata. Ta k arashe tana jijjiga sai sakin huci take tana tsuma tana kad a kulkin cikin hannunta.

Ya murmusa yana shafa hab a lokaci guda yana lek en bayansa kar Azeema ta k araso wajen. Ya sassauta murya  Haba kurtuwata. Kema kinsan duk duniya babu macen da nake so sama dake.. Da kikaga ina biyeta amfani zata min. Yo banda abinki ni kaina sau nawa ina lakad a mata d anbanzan duka kuma duk akanki toh dan an mare Azeema har wani damuwa zanyi. Wllhi yanda kika san an mari wofi haka naji.. Ya kuma shafa fuskarsa yana lek en bayansa irin yanda marassa gaskiya keyi kafin ya matso da fuskar nasa saitin fuskan  yarsandar  Kinga ita Azeema Ubanta na asibiti rai hannun Allah. Ta tabbatar mun mutuwa zai. Kuma da zaran ya Mutu aka raba masu d an abinda zasu samu zan amshe komai nata. Tana mallaka min zan koreta da kud in gadon Uban nata zan aureki Kurtuwata. Ya k arashe yana wani washe baki yana wani kashe mata idanu  Toh d an yi mun murmushi mana na gani sahibata.. Inye kaga Kurtuwa Amaryar Habibi.. Ya k arashe kaman zai rungumota.

Yatsine fuska ta d anyi had ida turasa baya  Easy mana Alaji wajen aiki na muke.. Shikenan tinda haka

13 / 52