Auren Wata Uku Book Complete By Sameena Aliyu.doc

Author :  SAMEENA ALIYU Category :  Arewa Pen

Chapter   29 / 52

84K to 87K   out of 153.1K words

m jealous of her skin.. Ta k arashe tana dafe fuska.

Tsawa Anisa ta darara mata tana fad in ta shige mota su tafi ko ta tafi ta barta nan wajen.


 Oh hey. Easy girl, I m just joking.. You are still more beautiful than her. Leenah ta fad i tana take ma k awarta baya.

Haka suke tafe Mota Leenah na kuma tunzurata da surutanta har dai aka sauk e Leenah a destination dinta shak e da kayyayakinta da sukai shopping.


Mota ya rage saura Ummul da Anisa. Ba mai ce da kowa komai har suka iso gida.

Ummul ta dubi Anisa Tai mata godiya wann murmushin Wanda sam Anisa bata k aunar gani saman fuskarta.

Suna shigowa cikin gidan suka tadda Mommy zaune da wasu mata masu sanye da rigar kampani na tailoring a first parlor.

Ma aikatan gidan da kusan ko yaushe suke cikin shiga ta uniform suka soma amsan kayyakin hannunsu suna masu sannu da zuwa cikeda girmamawa had ida ladabi.

Ita dai Ummul duk ba wai ta Saba da irin wad ann abubuwan bane. Musamman idan taga manyan mutane suna girmamata suna gaisheta koda kuwa masu aiki ne. Sam batajin dadin irin abun. Sosai abun ya bata mamaki da safe kafin su fita yanda Anisa ta dinga masifa ma babban mata dake kitchen wai dan kawai bata kawo mata abinda ta buk ata kan lokaci ba. Tana jin wacce ta amsa Kayan hannunta tana tambayarta  Ma am, should I take these to your section..? Kasancewar akasarin ma aikatan gidan hiring d insu akai daga registered company na masu aikace aikacen gida da Office ba hausawa bane ba sosai suke hausa ba.

Sai Ummul tai sakare tana dubanta. Ba wai dan bataji mai tace bane, kawai sabo ne da irin rayuwar da Sam batai ba. Rayuwar da gaba d aya ya banbanta daga irin rayuwar da ta girma ciki tai wayo ciki.

Mommy ce ta bata amsa da fad in ta kai mata su side dinta. Wato b angaren Haidar.

Maid din ta amsa da  Yes Ma. Cikeda risinawa.

Mommy ta k araso ga Ummul wacce tuni ta risina tana gaisheta.

Bata amsa gaisuwar ba sai kamo hannunta da Tai tana fad in suje ga masu d inki zasu gwadata su d auki measurement dinta. zasu d inka mata atamfofi da laces daidai size d inta.

Anisa ta saki baki tana kallon ikon Allah musamman da ta ga babban tailoring company da Mommy ta kira Wanda a garin ma ba ma kowa suke d inki ba sai ka cika elite. Ko ita kanta Anisa basu tab a mata d inki ba sai gashi wai zasuyi ma wann kucakar. Zuciyar Anisa ta kuma tunzura. Tsanar Ummul ya kuma cika mata zuciya. Ko ta kanta fah Mommy bata bi ba balle taga abinda ya samu fuskarta. Cikin k unan rai ta nufi d aki tana tuanin sabon hanyar da zata bi ta b ullo ma Ummul dan bata tunanin zata iya hak uri da Ummul d in kaman yanda Leenah ta bata shawari.

**

Kano&

Da kyar Mama ta amince ta fito wajen ganawa da mutane yanda Umma ke jiranta a nan police station da akai detaining dinta.

Umma ta zuba tagumi tana duban Mama yanda ta jeme ta rame duk tsawo da jiki irin na Tani duk ta lalace cikin k ank anin lokaci ta zama abun tausayi.

Banda Uwar harara Mama bata aika mata komai.

 Kinzo ne kimin dariya Suwaiba.? Kinzo ne dan kiji dadin ganina a k ask ance..? Muryar Mama ya soma rawa  Ki amsa min Suwaiba. Kinzo ne dan ki min dariyar abubuwan dake faruwa dani..? Ina nufin  Ya yana Sun jirge gida. Badia miji ya gudu Ya barta ita kuma Azeema miji ya koreta.. Ni kuma gani a nan cikin k ask anci da tozarci.. A yayinda ke Allah ya cika miki burinki. Ummul d inki tayi aure.. Aure na gani a fad a irin Wanda nawa  ya yan basu samu ba.. Mutanen unguwa sun bar nunaki da baki sun koma nuna ni nida nawa  ya yan.. Mijinmu kuma yanzu na k ark ashin kulawarki.. Ya zama naki ke kad ai.. Haka ne Suwaiba..? Ta k arashe kuka na b alle mata yayinda Umma ma kukan take. Cikin zuciyarta cewa take Allah sarki Yaya baki san tashin hankalin da kike ciki mai sauk i ne gaban Wanda nake ciki. Baki san wani irin aure Ummul Tai ba. Baki san cewa Aure ne mai k ayyadadden wa adi ba. Baki san Aure ne da aka k ullasa bisa yarjejeniya na tsawon watanni uku.. Aure mai gib i auren da zan jima ina d an dana sanin yi ma Ummul irin wann auren Har tsawon rayuwata. Sann Mijinmu banida ikon taka yanda yake.

Muryar Tani ya kuma katseta cikin karaji sanda ta soma janyo Umma tana fad in  Tashi ki tafi Suwaiba. Ki tashi nace ki tafi kuma kar ki sake takowa yanda nake.!

Kuka Umma take tana girgiza kai  A a Yaya.. Dan Allah ki saurareni.. Wllhi ko d aya banzo nan dan abubuwan da kika zayyano ba.. Yaya ki saurareni.. Sai Umma ta rungume Tani tana kuka.. Su duka biyun kuka suke Wanda yafi kama da kukan nadaman rayuwa.

Mama ta fincike jikinta daga rik on da Umma tai mata. Zata sa kai ta shige Umma ta kuma rik o hannunta  Yaya dan Allah ki saurareni.. A halin yanzu bamuda kowa sai mu biyun..

Mama Tani ta goge hawaye da bakin zaninta Wanda yai duk un duk un  Yayane Suwaiba..? Ki sanar Dani yayane..?

Umma ta goge hawayenta da bakin mayafi  Yaya yanzu ba lokaci bane da zamu rik e juna abokan gaba. Lokaci ne da zamu fahimci dukkanmu masu kuskure ne.. Kuma Allah yana sonmu da ya nuna mana kura kurenmu tun a nan gidan duniya.. Saura ya rage namu mu d auki darasi ko mu bijire.

Jikin Tani ya kuma yin sanyi wasu hawayen na zubo mata yayinda Umma taci gaba  Yaya babban abinda ya jefa mu cikin halinda muka tsinci kanmu shine son kanmu, rashin tawakkali da yin abu dan mu burge mutane Wanda Har yasa mun mance su waye mu. Mun mance auren mu, mun mance  ya yanmu da Allah ya dank a mana amanarsu. Mun mance mijinmu da yakeda girman hakki akanmu.. Sabida son zuciya irin namu.. Mun mance mu masu kiwo ne kuma za a tambayemu bisa abinda aka bamu kiwo.. Yaya duk mun mance wad ann mun saka son zuciya a farko.. Wanda shi ya kai mu ga halinda muka tsinci kawunanmu. Ta kuma jinjina kai tana hawaye  Watak ila Ummul tayi aure.. Amma ba irin auren da naci mata buri ba.. Dije ta rabani da Khulsum kaman yanda ta rabani da mijinmu.. Nida ke bamuda wani maraba Yaya. Yanda kike rufe a nan babu walwala nima a b angare na haka take.. Kullum ina kulle ne cikin d aki Babu walwala. Ta kuma share hawayenta yayinda Tani ta katseta  Wani irin aure ne Ummul Tai Wanda baki ci mata buri ba Suwiaba.?

Tambayar da ya haifar ma Umma fad uwan gaba. Koda Ummul AUREN WATA UKU Tai bazata so ta sanar da Tani ga irin auren ba. Hasalima bazata iya ba. Batada wann k warin gwiwar.

Girgiza mata kai tai  Ki yarda dani Yaya na tapka babban kuskure.. Tai maganar cikin tsananin rawar murya irinta mai kuka.

Mama ta jinjina kai  Na yarda da duka abubuwan da kika fad a Suwaiba.. Mun tapka kuskure.. Kuma idan bamu had e kawunanmu yanzu ba bazamu tab a k wato mijinmu daga hannun Dije ba. Tazo Har nan ta min d iban albarka ta kuma jaddada min tinda naci amanar d anuwanta dake kwance nida fita a gidan yari sai Randa jakin Baba yayi k aho. Zata tabbata ban samu wani k ofa da zan tsira ba. Sann yarana sun guje ni. Salima ce kawai ke zuwa nan ta dubani. Amma Azeema da Badia Wanda nake gark ame nan sabida su sun wofantar dani Suwaiba.. Ta kamo hannayen Umma  Suwaiba dan girman Allah ki taimaka min kafin a tafi Kotu. Sunce cikin satin nan za a shiga Kotu da mutumin k auye mai kudi. Dan girman Allah Suwaiba ki taimaka ki nemo kud d en nan a fitar dani.. Naga Sirakan Ummul masu hannu da shuni ne. Ki taimaka min Suwiaba ko wajensu kije ki nemo kud ad en nan ki fitar Dani a nan.. Ta k arshe tana tsare Umma da ido. Zuciyarta na tabbatar mata hanyar da zata bi kenan ta samu ta fita daga wann tuggun. Ta nuna ma Suwaiba nadamarta a fili Har dai Suwaiban Tai mata hanyar fita..

Dum!! Haka k irjin Umma ya buga dan ita kanta bata isa tace ga kalan sirakan Ummul ba. Uwa uba rabuwar da sukai da Asshe Wanda Asshe tai mata iyaka da gidanta.

Tani ta tsare Umma da ido. Cikin zuciyarta take ayyana tinda na sauko da kaina Suwaiba dole kimin abinda nake so. Ta haka ne kawai zan samu na fito har na fahimci mai kike b oye min gameda auren Ummul.

 Ke nake sauraro Suwaiba, zaki min wann alfarmar.? Mama tace tana tsareta da ido.

Zuciyar Umma ya kuma tsinkewa. Ta d ago tana duban Mama cikin sanyin jiki&


SameenaAleeyou=???
*AUREN WATA UKU..!*



*27*





*??Sameena Aleeyou&
'






Umma ta girgiza kai a hankali  Kiyi hak uri Yaya.. Bazan iya Miki alk awarin komai ba a halin yanzu. Tai maganar ba tareda ta iya duban fuskar Mama Tani ba.

A dak ile Mama ke dubanta  Suwaiba.. Kina nufin bazaki taimake ni ba..? Kenan kema kin zab i a tura ni kurkuku kaman Dije.?

Umma tai saurin d ago kai tana girgizawa alamun a a.

Tani ta gyara zama  Toh idan ba haka ba yaya ne.? Bakida wani maraba da Dije Suwaiba.. Banyi zaton haka daga wajenki ba Suwaiba.. Sai ta fara hawaye  Bayan ke banida kowa Suwaiba..  Ya ya na Sun guje ni.. Mijina na kwance jinya ta cinyesa.. Ke da nake zaton zamu taru mu rufa asirin juna kema kin juya mun baya Suwaiba.? Sai ta fashe da kuka tana fad in bata zaci haka daga Umma ba.

Lokaci guda Mama ta mik e tana huci  Tinda haka kika ce Suwaiba.. Shikenan kije abinki.. Kije kici arzikin sirakanki ke kad ai. Ni kuma in sha Allahu babu ni babu Ke Suwaiba. Kar ki sake tako inda nake idan har ba taimako na zakiyi ba. Tasa kai zata shige Umma tai saurin mik ewa ta tareta  A a Yaya. Dan Allah kar kice haka.. Ni ahalin yanzu banida kowa nima sai ke. Bamuda kowa sai mu biyun.. Amma..

Katseta Tani tai  Amma me Suwaiba.? Tai maganar tana tsare Umma da ido.

Gaba d aya Umma ta daburce bata San mai zata sanar da Mama Tani ba. Bata san ta yanda za ayi ta sanar da ita cewa itama ta riga ta k are mata ba. Tai saurin jinjina kai  Toh. Toh.. Yaya.. In sha Allah zan nemo hanyar da zaki fita..

Mama ta jinjina kai  Yanzu naji batu Suwaiba. Kar ki mance fitowa zanyi muyi yak in k wato mijinmu daga hannun azzalumar  yar uwarsa wacce babu komai cikin zuciyarta face burin fansa dan nayi imani ba tsakani da Allah Dije ke ma Isubu jinya ba. Shi kansa yasan halin Dije Shiyasa tun yanada lafiya ya mata iyaka da yanda yake. Ko dan wann Suwaiba bazamu bari Dije ta rab esa ba. Ki nemo kud ad en bak auye a biyasa na fito mu k wato mijinmu uban  ya yanmu. Ta haka ne kawai ahalinmu zai kuma samun daidaito. Kin fahimta.

Umma tai Shiru kaman mai nazari sai kuma ta shiga jinjina kai  Na fahimta Yaya. Nima zanso muyi jinyar mijinmu mu samu ladansa. Kuma kuskure ne mun riga Munyi amma munyi nadama. Kuma Allah mai afuwa ne mai yawan gafara.

 Yauwa dai Suwaiba ko ke fah. Nasan kinada fahimta Shiyasa munafukai basu tab a samun nasaran shiga tsakaninmu ba. Ni  yaruwa na d auke ki Suwaiba ba kishiya ba. Kuma  yan sa insa da sab ani da muke samu a baya zama ne Ya kawo haka. Dama shi kansa rayuwar zo mu zauna ne zo mu sab a. Harshe da hakori ma suna samun sab ani ballantana mu  yan adam.

Umma ta jinjina kai  Haka ne Yaya. Zanyi iyaka kokari na in sha Allahu. Allah ya mana jagora.

Mama ta murmusa had ida amsawa da  Yauwa yanzu naji batu Suwaiba. Ina nan ina saka tsammani. Na d aura duka yardana akanki Suwaiba. Ta k arashe cikin yanayi na tausayawa.

A hankali Umma ta jinjina kai duk jikinta a mace haka sukai Sallama da Tani. Tana ficewa Tani ta kece da dariya. A fili take furta  Saidai ba Suwaiba matar Malam Isubu ba. Muje zuwa, da kanki zaki fiddani ni kuma na fidda  yar naki a gidan auren nata. Tinda  ya yana basu zauna d akin miji ba naki  yarma bazata zauna ba. Abun yazo gidan sauki dan da alama akwai abinda kike b oyewa gameda auren. Bazan yi k asa a gwiwa ba har sai na shak a iskar  yanci dan na cimma burina. Ta kuma murmusawa daidai sanda wata  yar sanda tazo maidata cell dinta.

Umma tana tafe tana lazimi da tinanin ta yanda zata b ullo ma al amarin Tani. Zatai iyaka yinta dan ta taimaki Tani tinda ta tabbata idan yau mijinta ya farka Ya gansu sun had e kawunansu kuma sunyi nadaman duk abubuwan da suka aikata a baya zaifi kowa farin ciki kuma Watak ila fushin da yake dasu ya gushe. Watak ila hakan ya zama silan yafe masu duk wasu kurakuren da sukai sanda yake kwance. Toh amma ina ta nufa..? Ina zataje .? Wajen waye zata je ta samo kud ad en da za a fidda Tani.? Asshe kawai ta fad o ranta. Dan idan ba Asshen ba bata kuma san wajen waye zataje ba. Toh amma sanin irin rabuwar da sukai da Asshe sai ya kuma haifar mata da sanyin jiki. Asshe ta bada umarni ma masu tsaron gidanta cewa ko mai kamanninta suka gani kar su bari ta shiga. Uwa uba had e kan da Dije da Asshen sukai mata kafin a tafi da Ummul. Ta tabbata idan Har Dije ta k ulla aminta da Asshe zuwa wajen Asshe had ari ne. Dan idan har Dije ta fahimci Matan Isubu Sun had e kai. Wato ita Suwaibar da Tani wani sabon wuta zata kunna masu. Snn abinda take k ok arin b oye ma Tani gameda auren Ummul kuma shikenan ya tashi daga sirri. Dan tayi imani Dije bazata so taga wann had in kan ba Wanda yake nufin rugujewar shirin duk wani fansarta akansu. Dole tai taka tsantsan. Dole tabi komai a tsanake idan har tana so ta taimaki abokiyar zamanta Tani ta fita daga kurkuku. Da wann tunanin ta sallami mai adaidaita ta shigo gida. Saidai tana shigowa abinda Tai karo dashi ne Ya mugun bata mamaki. Dije ta gani tsaye tsakar gidan ga kayan abinci da kwanaki Suwaibar ta kawo lokacin sunayi da Asshe lokacin yak in auren Ummul jirge gaban Dije ta kirawo yara tana fad in maza su fidda mata kayayyakin su kai mata cikin adaidaita dake jiranta k ofar gidan.

Umma ta saki baki tana kallon ikon Allah  Dije.. Lafiya mai nake gani haka..? Ina zaki kai mana kayan abincin.?

Kallonta Inna Dije Tai daga sama zuwa k asa  Makauniya ce ke.? Bayan shahshanci kuma idonki Ya rufe ne Suwaiba.? Tafiya dasu zanyi. Tinda na tabbata da kud ad en da kika saida d iyar D anuwana kika sayi kayan abincin nan. Ko ma ince su suka baki. Kaman yanda kika sani da zaran an sallamesa daga asibiti ko gidan nan bazai taka ba balle yayi karo da wani tashin hankalin da tsautsayi. Dutse zan wuce dashi ya samu hutu da jinya a can. Kayan abinci kuma zamu buk ata. Ta k arashe tana d aura ma yaro guda kwalin taliya akai.

Umma ta girgiza kai  Amma Dije mai zamuci.? Kar ki mance ba ni kad ai ce a gidan nan ba. Akwai Badi a sann akwai Azeema. Idan kika kwashe komai mai zaki barmu dashi.?

Dariya Inna Dije tai harda shewa kafin tace  Lallai Suwaiba. Yau kece mai fafutakan abinda yaran Tani zasu ci.? Saikace ba kece Tani ke hana naki yaran abincin da ubansu Ya kawo ba. A cewarta bazata girka ma k artan banza Wanda suka ki aure abinci ba.? Ikon Allah sai gashi yau ke Suwaiba kece kika nemo abinci kika ba ma yaran Tani da suka k i zaman aure harma girka masu kike. Yaran da ko ganin mutuncinki basayi. Lallai na yarda kin tabbata shashasha Suwaiba.

Umma ta girgiza kai  Dije rayuwar duka nawa take. Ciyar da rai lada ne dashi balle  ya yan mijina Wanda jarabawar rayuwa ya fad a kansu suka baro gidan mazajensu. Babu mahaifinsu a gidan Babu mahaifiyarsu. Gatansu Allah sai ni kad ai da na rage masu cikin gidan kuma in sha Allahu bazan wofantar dasu ba. Idan Allah ya bani dama da iko na zama mahaifiya a garesu zan zama. Idan ban samu daman gyara kura kuran da nai a baya kan nawa  ya yan Ummulkhairi da UmmuKhulsum ba zan kwatanta gyara akan Azeema da Badia cikin yardar Ubangiji Dije. Ki kirani da duk sunan da kikaga dama amma in sha Allahu ni Suwaiba bazan sake maimaita kura kuren da nai a baya ba.

Inna Dije ta murmusa ta matso kusan Umma sosai  Idan dai Tani da iyalanta ne gaki gasu. Sai ki fita ki nemo ki dafa ki basu. Idan ma aikatau zakiyi ki nemo masu wann ke ta shafa. Amma kinga

29 / 52