Auren Wata Uku Book Complete By Sameena Aliyu.doc

Author :  SAMEENA ALIYU Category :  Arewa Pen

Chapter   25 / 52

72K to 75K   out of 153.1K words

ita tana mai d ora yatsa ta guda saman labb anta  Duk draman da akayi mijina baida masaniya Suwaiba.. Ni Ina son mijina kuma ina daraja aurena.. Ni ba irinki bace wacce ta watsar da mijinta dake kwance yana jinya sabida cikan burinta. Bazan bari mace irinki ta lalata mun aure ba.. Dan haka bake ba ni. Dama kema kinsan hanyar jirgi ba daidai bane da na mota. Ni da Ke ba d aya bane. Ciniki Ya had amu kuma ta k are. Babban goro sai magogin k arfe bayan wata uku zaki sake haduwa da  yarki idan d anmu Ya gama kwangilarsa dan ita ba ajinsa bane. Zaren ba kalar yadin bane. Tashi ki fice kafin nasa su fitar dake..! Ta k arashe tana nuna mata k ofa.

Jiki Babu k wari Umma ta mik e tana ganin duhu na gauraye mata k wayan idanu. Ta shiga had e hanya tana takawa da kyar tana jin wani abu mai zafi na yawo cikin k irjinta.. A haka Umma ta fice daga gidan ga duhun dare ba tareda tasan ina take zuwa ba.




SameenaAleeyou=???
*AUREN WATA UKU.!*



*22*




*??Sameena Aleeyou&
'


A b angaren Inna Dije kaw koda ta fice sai ta tadda Khulsum a yanda tace ta zauna ta jirata. Dan dama lokacin da Umma ta kori Khulsum daga wajen Ummul Inna Dije ta had u da ita a k ofan gidan tana kuka. Nan take sanar da Inna Dije ga yanda sukai ita da Ummanta hakan yasa Inna Dije Tai mata umarni da ta jirata Har ta shiga ta fito zasu tafi tare.

Basu zarce ko ina ba sai asibiti wajen Abba.

Inna Dije ta k ura ma D anuwanta dake kwance idanu. Ta shiga jinjina kai tana mai furtawa a fili  Lallai Yaya ka gamu da jarabawan shed anun Mata.. Amma da izinin Allah ba macen da zata saka samun damar cutar dakai cikinsu.. Bazan bari hakan ta kasance ba.. Na maka alk awari D anuwana. Ta k arashe tana dafe hannunsa guda.

Khulsum dake zaune gefe ta goge hawayen da suka gangaro mata tana jin ciwon abinda mahaifiyarta da abokiyar zaman mahaifiyar nata sukai ma mahaifinta Wanda Babu mijin da Ya cancanci mata Irinsu.

Mama Dije ta matso ta rungume Khulsum tace  Kar ki damu Khulsumu. In sha Allahu mahaifinki zai samu lafiya, zan d auke shi daga nan.. Zamu tafi gaba dayanmu.. Zamu fara sabuwar rayuwa gaba d ayanmu tare.. Su kuma Suwaiba da Tani ko waccensu zata girbi abinda ta shuka ne..

Khulsum bata iya cewa komai ba sai kauda fuskanta gefe da Tai tana mai kuma goge hawayen dake zubo mata. Dan Allah ya gani dukda Umma ta kasance mahaifiyarta sai taji sam bata ko k aunar a ambato mata sunan mahaifiyar tata musamman bayan rabuwar da sukai a daren yau d in.

Mama Dije sai duban Khulsum take tana sak a abubuwa cikin zuciyarta  Tabbas sai ta cika Zuciyar Khulsum da tsanar mahaifiyarta.. Suwaiba zata rasa yaranta gaba d aya.. Bayan ta rasa Ummul zata rasa Khulsum ma. Zata rasa ahalinta gaba d aya dan mijin ma ta rasa shi kenan rashi na Har abada.. Sai ta tabbata rayuwa yayi k unci ma Suwaiba, k uncin da sai ta gwammaci mutuwa da wann rayuwar& Kaman yanda ta rasa Fa iz d inta D anuwanta tilo Ya kuma k ullaceta sabida soyayyan Suwaiba da ya rufe masa ido. Ta rasa soyayyan D anuwanta na tsawon shekaru zata tabbata tayi amfani da wann damar ta dawo da shak uwa da soyayya dake tsakaninta da D anuwanta.. Snn zata rattaba Auren Ummul ya Mutu kafin wa adinsa ya cika. Bayan auren ya Mutu ta bi ta sanar da Ummul irin auren tozarci da Suwaiba tai mata. Sai ta kwance ma Suwaiba zani kasuwa gaban  ya yanta. Dik irin biyayya da Ummul ke ma Suwaiba sai ta tabbata ta masu farrak u bayan ta kashe wulak antaccen auren da tai ma Ummul. Suwaiba zata zama batada tsuntsu batada tarko. Zata rasa kowa tin daga kan Yayanta Isubu da zata masa jinya a yanzu wanda makahon soyayyan da yake ma Suwaiba ya hanasa ganin aibun Suwaiban har dai suka sami sab ani mai muni duk sabida Suwaiba har izuwa kan yaranta guda biyu Ummulkhairy da kuma Ummulkhulsum.. Wann alwashi ne da ta d auka ma kanta. Ta saki murmushi a hankali tana jin zuciyarta na mata sanyi al amara suna tafiya mata yanda take so.

**

Ikon Allah ne ya kawo Umma gida. Tana isowa ta hangi fitilan d akin Tani a kashe. A nata tunanin Tani ta kwanta bacci tinda tasan kaman yanda Dije tace bazata kuma barin d aya daga cikinsu ta kusanci Abba ba tasan bazata bar Tani ta zauna can asibiti wajen Abba ba. Hakan yasa ta shiga sand a a hankali alamun bata so Tani taji dawowarta.

Kaman Wata b arauniya haka ta shige d akinta cikin sand a tana addu an Allah yasa ta tadda Khulsum na bacci. Saidai koda ta shige d akin babu Khulsum Babu alamunta. Umma ta silale ta zauna da kyar tana duban gadon yaran nata da angle din da ko wacce ta Saba kwanciya.. Sai ta tuna irin rabuwar da sukai da Khulsum duk Akan Auren Ummul. Datse alak a tai tsakaninta da  yarta Khulsum. Innalillahi wa inna ilaihi raji un tana cikin hayyacinta ta aikata makamancin wann abu. Sai ta soma tunanin toh ina Khulsum ta shige.? Take zuciyarta ta bata amsa da fad in tana wajen mahaifinta a asibiti kaman yanda kika koreta daga gareki. Khulsum bata da wajen zuwa da ya shige wajen mahaifinta. Umma ta silale a hankali hawaye na kuma b alle mata. Sai tana jin wani abu da yafi yanayi da tashin hankali na ziyartarta& Yau dai Babu Ummul a cikin gidan, wacce a kullum idan ta bud e idanu ta ganta cikin gidan Babu aure zuciyarta ke mata ciwo, hankalinta ke tashi. Haka zalika taita kausasa harshenta Akan k addarar  yar tata. Meyasa bataji ciwon ya tafi ba..? Meyasa duk tulin damuwar da Tai a baya Wanda a nata zaton ganin Ummul ne a gida ba tareda aure ba ya haddasa mata. Meyasa taji babu abinda ya ragu a k uncin da takeji cikin ranta sai ma abinda ya k aru..? Meyasa..? Meyasa abubuwa suka kwabe meyasa auren Ummul da tai zaton zai zamto mabudin farin cikin ta da na ahalinta meyasa bai zama haka ba.. Meyasa auren Ummul ke barazanan zama mabudi da Mafarin tarwatsewar Ahalinta.. Ta rintse idanunta wasu hawayen masu tsananin ciwo suna zubo mata. Saida Umma tai kuka mai isanta ita kad ai cikin d aki with no shoulder to lean on. Babu wanda zaiji sautin kukan nata balle Ya lallasheta.. Ita kadanta cikin d aki tasha kukanta. Dakin ya mata girma, daren ya mata tsayi& Haka Umma taci kukanta a d aki cikin dare tamkar marainiyar kenwa.

**


Washe gari sassafe ake shirin tafiya da Amarya Ummulkhairi gidan mijinta dake Abuja.

Asshe ta fito taci uwar gayu yayinda Ummul ta kasa fitowa sai shesshek ar kuka take Wanda ya riga ya zame mata jiki. Tin Daren jiya take aikin abu d aya Akan dole Asshe ta tilasta ma cin abinci ma saida tai da gaske kafin ta saka ruwan shayi a cikinta. Kallo guda zaka mata ta baka tausayi. Asshe sai sababi take tana fad in haka za a Kai amarya a k anjale jiki duk yunwa kaman wata kazar mayu. Cikin ranta kuwa addu a take Allah yasa Ummul tafi haka lalacewa ko dan kar idon Haidar da hankalinsa ya sauk a kanta.

A haka suka fito da k yar bayan Asshe ta sanar da Ummul kar ta mance kud in Aurenta shine kud in jinyar mahaifinta dan haka tafiya gidan Miji ya zame mata dole idan har ba so take su janye komai ba.

Ummul na hawaye take janyo k afafunta. Tabbas wann auren sadaukarwa ne ga illahirin ahalinta. Bayan datse alak a da ita da Umma tai a daren jiya na tsawon watanni uku na farkon aurenta bata jin Umma zata tab a yafe mata idan tace ta fasa wann aure. Ta rintse idanunta zuciyarta na tausarta da cewa irin nata k addaran kenan. Watak ila hakan shine alkhairi ga d aukacin ahalinta. Idan tai nesa dasu Watak ila farin ciki da kwanciyar hankali zai wanzu cikin ahalin irin Wanda basu samu a baya ba.

Fitowar da zasuyi da zummar shiga mota kenan suka sinkayo wata murya.

 Ku dakata ku dakata. Direba a dakata ga pasinja d aya.! Ta k arashe tana kuma mak ale k aramar jakar Ghana must go d inta a hammata sai faman buga sauri take.

Asshe ta zaro ido tana duban matar nan shaye da tsananin mamaki  Dije.! Ta furta da k arfi.

Inna Dije taci gaba da sakin murmushi tana duban Asshe  Haba k awa ban gane wasa tare ci banban ba. Haka kika shirya tafiya da  yarmu babu wani nata. Ce Miki akai batada dangi ko tsawa akai ta fad o da zaki rufeta ki kaita kamar wata maras gata.

Ummul tai saurin yaye rufin kanta hawaye na kuma b alle mata  Inna Dije. Ta furta a hankali tana duban Dije. Dije tai saurin k arasawa ta rungumi  yar D anuwanta  Ni ce nan Goggonki Ummul.. Innarki Dije, bazan bari a kaiki gidan miji kamar maras gata ba. Shige muje.! Ta k arashe tana mai shigar da Ummul cikin mota.

Har lokacin mamaki Ya kasa sakin Asshe. Watau matar nan ta ranste sai ta tona mata asiri. Inaa bazata bari hakan ta kasance ba.. Kafin Tai aune taji Inna Dije ta janyo hannunta ta jefata cikin mota. Fad i take  Direba tada mota muje birnin tarayya ba nan kusa ba.

Asshe ta matse hannun Inna Dije da k arfi tana k ok arin fiddota waje amma sai taji Inna Dije ko gizau bata motsa ba. Saitin kunnen Asshe take rad a mata  Kar kiyi wann ganganci dan tsaf zan kwance Miki zani a Kasuwa. Kama daga kan mijinki da kishiyoyinki Har izuwa kan  yaruwarki. Dan haka cikin salama ki shige mu tafi.! Ta k arashe tana firfito da idanu waje.

Asshe ta had iyi abinda Ya tsaya mata a mak oshi da k yar. Cikin sigan rad a take tambayarta  Fad a mun nawa kike so.?

Inna Dije ta murmusa, cikin sigan rad a ta bata amsa da fad in Ki bari mu isa can zamuyi ciniki a tsanake. Sai ta murmusa tana k are ma Asshe kallo harda kashe mata ido  Kar ki damu k awalliya zamu sha hirarmu ta k awaye a mota. Ta k arashe tana d aka ma Asshe bugu a cinya harda kecewa da dariya. Ta dubi driver tace yaja mota su tafi kar rana yai masu a hanya. Driver kaw yai yanda tace dan dai Asshe kam ta kasa katab us cikin motan. Abun matar Ya koma bata tsoro. Ta d auki Suwaiba shashasha amma wann kam ko shakka babu gogaggiya ce . Tanaji tana gani suka d auki hanya tareda Dije babu kuma yanda ta iya. Abinda take tsoro ne yake gab da aukuwa. Mai zai faru idan wann matar da ta zame mata k arfen k afa ta bud e baki ta sanar da uwar Haidar komai. Ta tabbata Kwaise zata iya d aureta Har igiya yayi saura sann asirinta gaban miji da kishiyoyi harma da yaranta Ya tonu. Lallai Ya zama dole ta san yanda zata b ullo ma wann matar. Idan ta kama ta b atar da ita tun akan hanya ne kafin su isa zatai hakan. Dole ta canza salon yanda zata tunk ari wann mahaukaciyar Matar da burin fansan ran D anta Ya rufe mata ido. Haka dai Asshe taita sak awa tana kwancewa cikin mota. Gaba d aya kallo d aya zaka mata ka gane a birkice take.

**

A b angaren Umma kaw sassafe da rabon fad an yaran Mama ta tashi. Badia da Azeema sai tona ma juna asiri suke Azeema na fad in sai Badia ta nemo B arawon mijinta yanda ya shiga ya fita. Yayinda Badia ke fad in gwara nata mijin a sata Ya tsaya ita kaw Azeema ba Wanda baisan Habibu k aton kwarto bane Wanda baya raina mai d ankwali. Nan dai akaita fad a Umma na k ok arin rabiya amma inaa saida dai akai chaa a k ofan b angaren nasu kaman ko yaushe ana bama ido abinci.

Azeema taci gaba da fad in  Oho dai gwara ni mijina baiyi sanadin rufe uwata a police station ba. Hasalima fad i tashi yake ba dare ba rana dan ya fidda mahaifiyarmu da wann macucin mijin naki ya jefata ciki.. Kuma wllhi idan Har baki fito da Tasi ba zan tona miki asiri wajen Jami an tsaro dan ba Mama bace kawai ta saka hannu a takardun bogin da mijinki ya kawo na saida Shagon Abba harda ke macuciya azzaluma.!

Haba nan fah Badia ta janyo Azeema dambe ya kaure tsakaninsu. Umma ta shiga tsakiya tana k ok arin rabiya aikaw akai jifa da ita gefe. K um kakeji jini ya b alle a goshin Umma. Ta dafe kanta dake juya mata tana shafan jinin dake zubowa daga goshinta. Da rarrafe Umma ta bar wajen ta shige d aki dan ba mutan gidan kawai ba har mak ota lek ensu suke suna Allah wadai irin wann ahali. Saikace ba jiya akai auren Ummul ba wacce kowa yake tunanin sabida ita ahalin suka gaza samun kwamciyar hankali. Sai gashi yau an wayi gari babu Ummul da akai mata lak abi da annoba cikin gidan amma da tashin hankali suka wayi gari kaman dai ko yaushe.

Umma ta matse bakinta tana jin kukan gaske mai k arfi na taso mata musamman da taji abubuwan da mutane ke fad i. Ta kuma shafan goshinta taga jini. Ta rintse idanunta tana tunanin  ya yanta a daidai lokacin da jini ke fitowa daga goshinta. Ta aurar da Ummul bisa son zuciyarta sann ta kori Khulsum. Ummul take hangowa tana share mata jinin goshinta cikin tsananin nuna soyayya da kulawa yayinda take hango Khulsum tsakiyan Azeema da Badia tana k ok arin k watar wa mahaifiyarta hakkin rauni da sukai mata a goshi.

Umma ta fashe da wani irin kuka mai ciwo. Lallai mutum baya gane kiman wani ni ima da Ubangiji yai masa baiwa dashi sai ya rasa wann abun.

A haka Umma taci kuka da suntumemmen goshi ita kad ai a d aki.

Rayuwa kenan ko babu rabuwa akwai mutuwa. Mu zama masu godiya ga d imbin rahamomin ubangijinmu garemu tun kafin daman hakan ya kufce mana. Tomorrow is not promised. Mu so juna muyi hakuri da juna. Mutanen da Allah ya albarkace mu dasu cikin rayuwarmu. Walau iyaye,  ya ya, miji, mata abokan zama da sauransu. Rayuwar duka batada tsawo. Abinda hak uri bai kawo shi ba tashin hankali bazai bayar ba. Allah ya mana muwafak a duniya da lahira. Ameen.

**


A can b angaren Mama Tani kuwa yanda taga rana haka taga dare a police station. Fuskarta ta kumbura suntum sakamon Mari da tasha hannun tsagerun  yanmatan da aka had asu cell d aya. Sallah ne kawai yake ceton Mama daga bugun da take sha hannun tsagerun nan.

Saiga Mama tana sallah cikin cell harda nafilfili. Har bata fatan ta ida sallah gudun kar su ci gaba da cutar da ita. Yara k anana Har tausa suke sa ta masu idan batayi ba taci bugu.

Ta kula ko neman agaji take wajen  yansandan basu kawo mata d auki musamman wann matar da ta gansu da Habibu.

Ta nemi a fitar da ita zataje fitsari. Da k yar da sid in goshi aka fitar da ita tinda bata jima da fita alola ba. Addu a take Allah Ya had ata da Habibu Ya sanar da ita yaushe za a fiddata. Kaman daga sama ta bayan d akin da aka kaita fitsari yanda band akin suke a jere ta soma jin maganganun ta wata  yar window. Muryar Habibu takeji daga window d in yana kwantar ma  yarsandar hankali da fad in shi fah ba taimakon Mama Tani zai ba. Dama yayi zaton zai cimma Tasi u ne kafin abubuwa su lalace. Dan haka bazai jefa kansa a uku ba dan wann bakwaiye Ya rantse har kotu sai an tafi. K arshe gidan Kasu Tani zata tafi babu ranar fita.  Yarta kuma babu amfanin da take masa saima cike masa d aki da tai dan haka a yau d in nan zai rubuta mata takarda tinda Tasi u Ya gudu da kud ad en. Aure zaiyi Ya saka amaryarsa a d akin.

Sai ga Mama tana sakin fitsarin jikinta. Ta kama k arfen window ta d ale tana dubansu  Habibu.. Irin cin amana da yaudara da zakai ma Azeema kenan..! Amma Habibu Allah Ya tsine maka albarka. Ka cuceni ka cuci Azeema. Habibu Allah bazai barka ba. Kan wann kilakir ka wulak anta Azeema.?

Kafin takai aya taji sauk an tagwayen Mari a fuskarta.  Yar sandar Habibu ce tai mata Marin  Ki iya bakinki kisan a ina kike. Cewar budurwar Habibu Yayinda Habibu ke mik a mata farar takarda  Tazo gidan sauk i tinda kina kusa. Ga wann ki bawa  yarki idan gantalinta Ya d ebota ta nan tinda ba mutuncinki suke gani ba balle suzo dubiyanki. Kar na koma gida na tadda tsummokaranta cikin d akina. Sak o na baki ki sanar da ita. Gyara zan fara a gaggauce dan amarya ta zan aje ciki. Ya k arashe yana kashe  yarsandarsa da murmushi.

Mama sai Tai mutuwar tsaye tana juya takardan da Habibu Ya mik a mata cikin hannunta. Bata san meke wakana ba har saida  yarsandar da tai mata rakiya fitsari ta tasa k eyarta.

Fitsarin da ta juyesa jikinta kenan ba tareda taje band

25 / 52