Auren Wata Uku Book Complete By Sameena Aliyu.doc

Author :  SAMEENA ALIYU Category :  Arewa Pen

Chapter   19 / 52

54K to 57K   out of 153.1K words

Umma wacce ta koma mata tamkar bak uwa.

Umma ta dafata tana murmushi  Ki saki jikinki Ummul d ita. Ban kawo ki yanda za a cutar dake ba. Domin kaw ni mahaifiyarki ce. Tin haihuwarki burina shine rayuwarki ya cika da d imbin alkhairai kaman dai yanda sunanki yake. Ta d an numfasa kafin taci gaba  Kinga nan gidan.. Gidan da za a share mana hawaye ne.. Gidan da za a cika mana burinmu da yardar Ubangiji. Kukanmu yazo k arshe Ummul.. Taho muje.. Ta k arashe tana mai janyo hannun Ummul. Amma sai Ummul ta tarje.

Umma ta juyo tana dubanta  Ummul ya kika ja kika tsaya, kinga nasan damuwarki bai wuce tafiya da mukai muka k yale  yaruwarki Khulsum ba. Sanin halinta, sanin duk abinda aka saka da ita sai ya lalace shisa bamu taho da ita ba.. Shige muje kinji.

Hawaye sukaci gaba da gangaro ma Ummul. Cikin rawar murya take furta  Umma gidan da za a cika mana buri fah kikace& Umma Ashe har akwai mahaluk in da zai cika ma wani mahaluk i burinsa..? Umma idan kinga burin d an adam ya cika ya bar duniyar nan ne..

Bata Kai aya ba Umma ta hanb are mata baki  Ke ke meye haka.. Daina kira mana mutuwa a nan.. Nidai bazan Mutu ba sai burina ya cika in sha Allahu. Shiyasa nace da yardar Ubangiji. Kuma burina shine na ganki a d akinki dik rintsi.. Koda k arshen abinda zan aiwatar kenan a rayuwana..

Jikin Ummul ya kuma yin sanyin Jin kamar mahaifiyarta ta riga ta zauce. Cak tai tsaye tana duban mahaifiyarta, ta rasa tausayin kanta ne ko tausayin mahaifiyarta take. Muryar wata mata ce ya dawo da Ummul daga duniyar tunanin da ta tafi  Ummul d inmu ta iso..! Ta fad i kyakkyawan murmushi saman fuskarta.

Ummul ta karkato tana duban matar wacce keta faman fad ad a murmushinta. Kafin tai wani aune ta k araso ta rungumeta tana fad in finally sun had u. Lokaci guda kuma ta shiga janyo Ummulkhairy tana fad in maza ta shigo ta shirya mai hoto yanzu zai iso bada jimawa ba.

Tambayarta kanta take Wacece wann matar..? Ina Umma ta santa..? Hoto kuma..? Wane irin hoto..? Meke faruwa ne wai..? Anya zata iya jurewa..? Anya batai gangancin biyo Umma ba kaman yanda Khulsum tace.. Amma idan mutanen suka cutar da mahaifiyarsu fah.. Zuwanta shine daidai ko dan tasan wani hali Mahaifiyarsu ke ciki.

Jikin Ummul sai rawa yake yayinda Asshe taci gaba da janyota Har suka shige cikin gidan Umma na biye dasu baki har kunnenta.

*
A b angaren Khulsum kaw tinda ta shigo gidan ta rasa wani b angare suka shige. Nan ta hangi wani section daga farko. Ganin k ofan wajen a bud e Ya sanyata nufan k ofan cikin tunanin nan su Umma suka shige. Saidai tana shiga wayam bataga kowa ba. Shiru alamun babu kowa. A hankali cikin sand a ta soma jada baya zata fice. Saidai tana cikin sand an da baya da baya taji ta bangaji mutum. A tsorace ta juyo zuciyarta na tsinkewa dukda bata bari tsoron Ya nuna saman fuskarta ba saima sauk e huci da take.

Wani matashin saurayi ta gani ya zuba mata ido, hannayensa hard e. Yana binta da kallo mai d aukeda alaman tambaya.

Taci gaba da huci tana hura hanci basu daina duban juna ba.

 Ina  yaruwata.. Mai kuka mata.. Su waye ku.?

Hilal ya girgiza kai kad an  Excuse me, what are you talking about..? Wait, Who are you..? And what exactly are you doing in here.?

Gajeren tsaki tai had ada sa kai zata shige. Hilal ya kuma tare gabanta Yana girgiza yatsa alamun bazai barta ta fice ba har sai ta amsa masa tambayoyin sa  Oh wait. Dakata dakata. Ai bazaki fita ba sai kin sanar dani wacece ke. Daga ina kike..? Kuma mai ya shigo dake b angare na.?

Ya d an girgiza kai ganin har lokacin hararsa kurum take. A tunaninsa sabuwar mai aikin Amminsa ce a gidan. Ya katse shirun da fad in  You must be new here? Basu fad a miki masu aiki basa shigowa b angarena ba saida izinina.?

Kallonsa tai daga sama zuwa k asa jin ya kirata da mai aiki  Kaga Malam ka bani hanya na wuce. Banida lokacinka balle na tambayoyinka. Watak ila ba kai nazo nema ba.! Ta k arashe kaman zata bangajesa ta shige.

Ya d an matsa Ya bata hanya ganin da gaske bangajesa zatayi. Lokaci guda yabi bayanta da kallo  Who s she.? She doesn t sound like mai aiki. Ya d an girgiza kai har lokacin yana duban k ofan  She s so tough. Ya fad i yana mai tab e baki had ida girgiza kai.
*

Suna shigewa d akin Ummul ta juyo ta dubi matar amma bataga Umma tareda ita ba. Nan fah tsoronta Ya ninku.

Asshe ta murmusa ganin har lokacin jikin Ummul bai daina rawa ba  Ki kwantar da hankalinki Ummulkhairi. Ki saki nan gidanku ne kinji.. Ga bathroom ki shiga kiyi wanka duk abubuwan buk ata zaki samu cikin band akin.

Asshe tasa kai zata fice kenan Ummul tai saurin kamo hannunta  A a dan Allah kar ki cutar dani.. Dan Allah kar cutar da mahaifyata.. Na San tanada nata irin matsalar amma ita d in ba mai kwad ayin abin duniya bace.. Bansan mai ya sameta ba har ta mance damu da mahaifinmu dake kwance gadon asibiti ta zab i wann rayuwar.. Kiji tsoron Allah kar ki cutar damu.. Na rok eki..! Ta k arashe tana mai duk awa gaban Asshe tana kuka sosai.

Tallafota Asshe tai ta d agota cikin k ok arin kwantar mata da hankali take fad in  Ki kwantar da hankalinki Ummul banida wani k ulli cikin zuciyata taimakonku nai niyya.. Kar ki min mummunan fahimta..

Ummul taci gaba da kuka har lokacin jikinta rawa yake  Dan Allah kar ki cutar damu kar ki cutar damu..

Ganin gaba d aya ta birkice yasa Asshe daka mata tsawa da fad in  Ke ki mun shiru.. Yi mun shiru dallah.. Kar ki mun shashashanci a nan.. Shige maza kiyi wanka kafin masu kwalliya da mai hoto su iso.. Tai maganar tana k ok arin tura Ummul cikin bathroom Ummul tana tarjewa tana fad in  A a dan Allah.. Dan Allah a a..!

Daidai lokacin Khulsum ta k araso ta finciki hannun Ummul daga rik on da Asshe tai mata  Sakar mun  Yaruwata.! Ta fad i da k arfin gaske tana fincikan Ummul.

Asshe tai tsaye tana duban Khulsum wacce tuni ta soma tambayar Ummul koda abinda ya sameta  Adda sun Miki wani abu ne.. Muje zo mu gudu.. Zo mu tafi..!

Kaman daga sama suka sinkayo muryar Umma tana fad in  Babu yanda zaki kaita.. Sakar mun  ya..!

Da mamaki Khulsum da Ummul suke dubanta.

Khulsum tace  Umma Allah bazai baki damar cutar da  Yaruwata ba sabida tin tasowarta biyayya take Miki. Dani da  Yaruwata zamu tafi.. Zamu fice daga rayuwarki Umma idan Har haka kike so.. Muryar Khulsum ya soma rowa sosai  Umma me ya sameki..? Su waye wad ann..? Menene gaskiyan rad e rad in da mutane suke akanki.. Umma shin kin manta da k alubalen da ahalinmu suke fuskanta..? Shin har akwai abinda Yafi Miki ahalinki mahimmanci..? Umma Abba yana kwance a asibiti tsakanin mutanen da suke mafarki da burin ganin bayansa.. A daren da kika zab i ki tafi ki barmu Har kusan kwana nayi a police station.. Duk ina kike Umma.. Ina kike sanda mahaifinmu yake tsananin buk atarki kusan shi.. A kullum muna fita mu fuskanci mutane da maganganun da suke jifanmu dasu.. Yanzu kin zagayo kin d auke  Yaruwata kin kawota nan ayi tsafi da ita.!

Bata kai aya ba taji sauk an mari a k uncinta. Ta d ago tana duban Umma dake sakin huci.

Lokaci guda take nuna Khulsum hawaye na gangaro mata  Ke baki san komai ba.. Baki san abinda ke faruwa ba.. Zo ki fice& Shiyasa tin farko ban gayyatoki ba dan nasan ke dai kam ba a k ulla alkahiri dake.. Zo ki fice..

Muryar Asshe ne ya katse su. Ta dubi Khulsum tace  Kar ki Fad i abinda baki Sani ba yarinya. Duk fad i tashin da mahaifiyarku keyi akanku ne da mahaifinku. Ina kuke a lokacin da kishiyar mahaifiyarku ta koreta tace taje ta nemo kud ad en da za ayi ma mahaifinku jinya..?

Khulsum ta kaikaito tana mata wani irin duba  Wacece ke..? Me kike nema daga wajen mahaifiyata..?

 Ki kirani Sirkar  yaruwarki Ummul.. Domin kaw nan bada jimawa ba Ummulkhairi zata zamto matar D ana.!

Da mugun mamaki dukansu suke duban matar da kuma Umma.. suka kuma juyowa suna ma Umma wane irin duba Wanda su kansu basu san duban me suke mata ba a halin yanzu.

 Sirka..! Matar D ah..! Khulsum ta nanata tana duban Asshe da Umma kafin ta kuma juyowa ta dubi Ummul wacce ita kanta cikin rud ani da duhu take.

Umma ta jinjina kai  K warai kinji da kyau.. Wann matar da kike gani k anwa take wa mahaifiyar mijin Ummul d ita.. Wnn karan bazan bama wani k ofa Ya lalata auren Ummul d ina ba, ba ke ba Khulsum ba Tani da  ya yanta ba ba kuma sauran munafukan mutanen layinmu ba.. Dan haka zo ki fice..!

Ta k arashe tana k ok arin rab a hannun Khulsum dana Ummul amma sai taji wann karon Ummul ta rik e hannun  yaruwarta k am tak i saki hawayen dake idanunta sun kafe sun daina zuba.

Ummul ta girgiza kai tana duban mahaifiyar tasu cikin rashin yarda  Har yanzu wann ne damuwarki Umma.. Ki aurar Dani kota halin k ak a..? Shin Umma rashin aurena ne kawai k alubalen da muke fuskanta a rayuwa..? Muryarta Ya soma rawa sosai  Abba yana cikin wann yanayi.. Ahalinmu suna cikin wann jarabawa amma ke damuwarki har yanzu guda d aya ne Umma.. Shin Umma bakida sauran matsaloli na rayuwa ne sai wann..? Umma iyakacin kiman da nake dashi kenan a wajenki a matsayina na  yarki..? Iyakacin kiman da mahaifina yake dashi kenan a wajenki matsayinsa na mijinki.. Umma ina zaki kai girman hakkin Abba.. Ta Ya zaki shirya aurar da  yarsa yana kwance cikin wann hali.

Khulsum na hawaye ta katseta  Ta Ya zata shirya sayar masa da  Ya dai.. Adda dan Allah kizo muje.. Muje mu nemi agaji daga hukumar hisba wllhi Umma bata a hayyacinta.. Ta k arashe tana kuka sosai.

Ummul na hawaye take girgiza kai  kiyi hak uri Umma.. Ki yafe mun amma.. amma Bana tunanin wann karon zan iya Miki biyayya.. Kiyi hak uri zanbi  Yaruwata mu tafi.! Tana ida fad in haka ta janyo hannun Khulsum  Muje Khulsum..!

Umma ta dubi Asshe hawaye na k ok arin ciko idanunta  Kin gani ko kinga abinda nake fad a Miki.. Wann  yaruwar tata ta kora mata mazan aure sunfi abinda suka fi da wann bak ar Zuciyar nata. Kin gani hassada take da ita.. Toh wllhi wann karon ban shirya jin kunyan duniya ba.! Tana huci take duban su Ummul da k iris Ya rage basu fidda k afafunsa daga cikin d akin ba.

Umma ta bud e murya tace  Ummulkhairi.! Idan kika saka k afa kika fice daga d akin nan.. Ki mance kinada mahaifiya Suwaiba..! Wllhi wllhi idan Har ki kai sanadin da mutanen nan zasu ce sun fasa auren nan toh Babu ni babu Ke kuma ke ba  Yata bace daga wann lokacin.. Ki nemi wata mahaifyar amma ba ni ba..! Ta k arashe tana sakin huci.

Cak Ummul ta tsaya ta kasa koda motsa k afarta guda.

Gani haka yasa Asshe bud e murya  Ba sai kin mata baki ba! Baza kuma a mata dole ba. Yardarta da amincewarta shi zaisa ayi wann Auren. Ta maidoda dubanta ga Ummul  Har yau ba a biya kud in surgery da za ayi wa mahaifinki ba. Anyi masa komai, an canza masa d aki. Yana samun duk wani kulawa saidai kud in aiki ne kawai yai saura.. Kinsan dalili..?

Ummul ta dubeta cikin tsananin sanyin jiki  Sadakin ki shine kud in da za a biya ai ma mahaifinki aiki Ummulkhairy..

Asshe taci gaba da takowa gaban Ummulkhairy, su duka biyun suna duban juna  Nasan za a iso wann gab ar. Shiyasa ban bari an biya kud in aikin ba. Har sai nida Ke mun gana da juna. A halin yanzu, ki sani Aurenki shi kad ai ne zai ceci mahaifinki. Domin kuwa sadakinki da zamu biya shine kud in da za a masa aiki a ceci rayuwarsa.. Wuk a da nama na hannunki... Yanzu idan kika ce baki amince ba. Ni kuma zan janye komai ku nemi wani hanyar da za ayi wa mahaifinki aiki..

Umma ta kuma bud e murya ganin Asshe tayi nasaran dakatar da Ummul.

 Wacece matsalar ahalinmu Ummul. Kece matsalar mu. K addararki shi yai silan kwanciyar mahaifinki.. Idan Har akwai wacce tafi cancanta tai sadaukarwa mai girma wa mahaifinku.. Toh ki sani kece kika fi cancanta Ummul.!

Khulsum ta soma girgiza kai tana duban Ummul  A a Adda, dan Allah karki amince.. Akwai na gari da yawa. Na Allah basa k arewa.. Dan Allah kar ki amince da wann auren na rashin galihu Wanda ko sanin mijin bakiyi ba. Ta k arashe tana ci gaba da janyo hannun Ummulkhairy alamun tazo su tafi. Amma sai taji Ummulkhairy ta doge. Lokaci guda take girgiza kai tana duban Khulsum  Kiyi hak uri Khulsum.. Na zab i ceto rayuwar mahaifina koda shine abinda zanyi na k arshe a rayuwata. Zanyi auren.. Zan auri ko waye Umma ta kawo dan na ceci rayuwar mahaifina.. Gaskiyar Umma ne. Watak ila idan nayi auren komai zai zo k arshe. Watak ila matsalar ahalinmu zai k are. Watak ila ni ce matsalar kaman yanda Umma tace.

Khulsum na hawaye take girgiza mata kai alamun a a.

Cikeda k osawa Umma ta dubi Khulsum. Kinji abinda tace  Ita d in  ya mai biyayya ce ba irinki ba. Sakar min hannun  ya kafin ki mata sanadin abun alheri da ya sameta.

Khulsum ta girgiza kai tana duban Umma. Lokaci guda ta soma jada baya. Tana duban Ummul hawaye na gangaro masu su duka biyun.

**

A can gida kaw Mama tana zaune tsakar gida ta rapka tagumi ga su Azeema da Badia sai dadd age Kayan masarufin da Suwaiba ta kawo suke. Yaran Salima suna gefe an had asu da Kayan mak ulashe. Babu yanda Mama batayi ba kar su tab a Kayan Suwaiba Kayan Shan jini amma babu wacce ta kula mama cikinsu sai Salima wacce ta tayata da tagumi. Gashi Salimar ta basu labarin irin kud ad en da Umman ta kashe a asibiti. Amenity ma aka maida Abba executive room kula ake basa na musamman. Su Azeema kam har so take washe gari yayi ko Umma zata sake zuwa ta rok eta Aron tufafin kece raini taje bikin dangin mijinta da suke dashi a satin.

Mama ta kuma sauk e kakkauran ajiyan zuciya tana tuna Suwaiba a baya Suwaiba fah data maidata bora cikin gidan farkon aurota wai itace yanzu duniyar nan ta juya akeyi da ita. Gashi har  ya yanta na cikinta sun fara son Suwaiba da tarayya da ita. Ikon Allah Lallai ta yarda babu mayaudariyar aba irin duniya. Yanzu zata rud eka ka zata tanayi dakai anjima kad an ta sake ta Kama wani a Barka bakin Tasha. Ita yanzu haka tanaji tana gani Suwaiba zata ci gaba da zuba mata bariki a gida. Lallai bataci ta zama ba. Ya zama dole ta san abinyi.

**

Abuja


Saukowa yai cikin shirin fita waya manne kunnensa  Family dinner?

Ya d an girgiza kai yana ci gaba da sauk owa  This is not part of the agreement Mommy. You know we can t stand each other.

Shiru yai alamun yana sauraro daga mahaifiyarsa  Fine, I m on my way there. Amma wann zai zama na k arshe. Daga haka katse kiran yai.

Dareen ta k araso tana dub??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ansa  Going somewhere.? Tace tana mai kamo hannayensa murmushi saman fuskarta.

 To my Mom s Ya fad i a tak aice sai kuma ya k ara da  Don t wait for me for dinner.. Maybe I ll be back late. Ya fad i yana shafan b angaren fuskarta guda.

Ta d an jinjina kai  Haidar, don t you think it s high time you introduce me to your family. After all, we ve been married for months now.

Hannayenta ya kamo cikin nasa  I don t think it s necessary. Those people mean nothing to me. I don t even consider them family.. Na rubuta yarjejenyar rabuwa dasu. Rabuwa ta har abada.

Tai masa k uri tana dubansa, Ya d an janyota cikin jikinsa suna fuskantar juna sosai  You.. And only you.. You are the only family I have.

Murmushi ta saki zuciyarta zallan k aunarsa. Ta shafi gefen fuskarsa tana fad in  And I ll love you till my last breath.

Ya murmusa had ida manna mata light kiss. Lokaci guda Ya kuma mata Sallama kafin ya fice.

Tabi bayansa da kallo cikin d aurewar kai. This is not like him. Ya canza gaba d aya. Mutumin da ya tsana ai masa zancen iyayensa shine yanzu yake zuwa wajensu akai akai.. Sann mai yake nufi da ya rubuta yarjejeniyar rabuwa dasu..? Shin Wai meke shirin faruwa ne..? Haidar ya canza gaba d aya wani sabon kusanci na neman shiga tsakaninsa da ahalinsa.. At the same time yana cewa

19 / 52