Auren Wata Uku Book Complete By Sameena Aliyu.doc

Author :  SAMEENA ALIYU Category :  Arewa Pen

Chapter   33 / 52

96K to 99K   out of 153.1K words

faruwa. Do I make myself clear.?

Gaba d aya suka jinjina mata kai hadida amsawa cikeda risinawa

**
Bayan Ummul ta koma sashenta tana zaune saman darduma Ida sallarta kenan Anisa ta shigo da murmushi saman fuskarta.

Ummul bata nuna mata komai ba dan itama wann sassanyar murmushin wanda a baya Anisa ta d aukesa shashanci da gidadanci a halin yanzu shakkar wann murmushin take shine dai saman fuskar Ummul.

Ta zauna tana tambayarta an sha ruwa lafiya.

Ummul ta amsa mata da sakin fuska. Nan Anisa ta soma bata hakurin abinda Leenah Tai tana mai kuma tabbatar mata Lallai Babu hannunta cikin abinda Leenah da Vicky suka k ulla mata.

Murmushi Ummul ta kuma yi  Babu komai Anisa kar ki damu. Suma ban k ullacesu ba. Daga k arshe Allah Ya bayyana gaskiya. Ba wayona bane ba kuma dabarata bace. Allah ne Ya dube ni da rahamarsa Ya wanke ni daga k agen da aka so min. Na kuma gode masa da Ya wanke sunana daga k agen sata. Ina kuma fata ya shiryi duk masu tunani irin nasu damu baki d aya.

Anisa ta jinina kai  You are a good person Ummul. You have a clean heart that s willing to forgive and forget. Yanda kika wanke kanki cikin hikima ya burgeni. I wish zan zama kaman ke.

Ummul ta murmusa  Duk wanda ya dogara ga Allah Allah ya isar masa. Kuma duk wanda yaji tsoron Allah Allah zai samar masa mafita. Ba yin kaina bane Allah yakan wanke bayinsa da akai masu k age ba tareda sun aikata laifin ba. Kaman yanda Ya wanke Ummuna Aisha (RA) daga k agen da azzalumai suka mata. Kaman yanda Ya wanke Annabi Yusuf (AS) daga k agen da aka masa. Kaman yanda Ya wanke bayinsa muminai da dama daga k agen da aka masu. Kaman haka yanke wanke bayinsa da basuda hakki. Na gode masa da ya wanke ni daga k agen da aka min ba tareda hakki ba. Amma ni Ummulkhair banida wani wayo. Saidai Inaso mutane irinki da Leenah su fahimci English is just a language and not a means to measure one s intelligence or education. Snn duk wani wayewar da yai karo da koyarwar addininmu da d abi u da kyawawan al adunmu ba sunansa wayewa ba. Tai maganar murmushi saman fuskarta.

Baki sake Anisa ke kallonta  So you can speak English.?

Ummul ta murmusa  Ba sosai ba abinki da Wanda taje makaranta na gwabnati.

A hankali Anisa ke jinjina kai  Na yarda da duk abubuwan da kika ce. A yau kin kuma tabbatar min da haka.  Ta kamo hannayen Ummul  Mommy tayi zaton ni zan koya miki abubuwa musamman zamantakewan rayuwar civilized world. But it turned out ni ce wacce ke koyo wajenki. Yau na raina duk wani exposure na Ummul.

Ummul ta girgiza kai  A kullum ko wani shafi na rayuwar mu darasi yakan bude mana dan mu koya. Kullum cikin koyo muke a duniyar nan. Kaman yanda muke had uwa da mutane iri daban daban. Ta d an murmusa  Nima ina koyo daga gareki Anisa.

Shiru Anisa Tai sai kuma ta saki murmushi da yafi kama da yak e.

Tin daga wann rana Ummul ta samu sanyin abubuwan da Anisa ke mata. Sai ta koma kaman tana shakkan Ummul d in koda bata nuna a fili ba. A kwanakin da alama Anisa ta maida makaman yak inta.

**

Kano&


Batai k asa a gwiwa ba dukda fargabn abinda ka iya zuwa yazo ta nufi gidan Hajiya Asshe. Juyin duniya Umma tayi amma masu gadi sun hanata shiga sabida dokan da Asshen ta basu tin kwanakin baya.

Asshe na kitchen tana had a ma maigidanta abinci kasancewar ranar yake dawowa daga tafiya kuma gidanta yake. Mai gadi yai Sallama ya sanar da zuwan Umma wacce babu yanda basuyi ba amma tak i barin bakin gate din tace sai ta gana da Hajiyar.

Zuciyar Asshe ya tsinke yanzu idan matar nan ta tada mata hargitsi a k ofan gida har mijinta ya iso ya tadda wann al amari mai zata ce masa. Oh! Ita kam dai ta d ebo ruwan dafa kanta. Wann wasu irin ahali ta kwaso masu ne wai ita Asshe. Bata gama da fitinan Dije ba ga Suwaiba da tai tunanin ta ajeta yanda ya kamaceta yanzu ta dawo. Toh uban mai ta dawo zata mata.?

Fuuu ta nufo gate tana huci dan wllhi bazata bari d aya daga cikin watsatsun matan nan su mata sanadin aurenta da take lallab awa ba.


Tana fitowa ta shiga janyo Umma tana fad in yau hukuma ce zasu mata iyaka da ita muddin bata bar mata k ofan gida ba.

Umma bata tafi ba bata fasa rok on Asshe tana fad in ta dubi girman Allah ta saurareta.

Hilal daga sashensa yake jiyo haniya yak i k arewa daga gate. Babu shiri ya bar abinda yake ya nufo gate d in.




SameenaAleeyou=???..
*AUREN WATA UKU..!*



*29*





*??Sameena Aleeyou&
'



Asshe taci gaba da janyo Umma tana fad in kodai ta bar mata k ofar gida ta mik a mata ma  yansandan dan ta gaji da fitinan fitinannun mata Irinsu. Wanda tin had uwar ta dasu Masifan yau daban na gobe daban.

Umma taci gaba da girgiza kai  Idan kina ma Allah ki tsaya ki saurareni Hajiya Asshe.

 Na saurareki na saurari mi inyi.?  Yarki ce nace Miki akwai wa adin da na d ibar Wanda zan dawo da ita gareki. Amma a halin yanzu ni Asshe banida wani sauran alak a dake da sauran zuri arku. Na gode ma Allah da yasa auren Ummul ba mai d orewa bane. Mi za ayi da zuri arku dangin masifa dangin mayu dangin matsafa.. Zo ki wuce.. Idan kika kara minti d aya k ofar gidan nan ki kwana ofishin  yansandan Ta k arashe tana hankad a Umma da iyaka k arfinta Wanda saida ta kaita k asa.

Daidai nan Hilal Ya fito ya taddasu. Ya isa da sauri yana ma Umma sannu had ida tambayar bataji ciwo ba.

Umma ta d ago tana girgiza masa kai alamun a a.

Da tsananin mamaki yake duban mahaifiyarsa  Ammi what s the meaning of this.? Kan wani dalili zaki aikata abu makamancin haka..? Mai yayi zafi..? Wai meke faruwa ne ma.? Ya k arashe damuwa saman fuskarsa.

Asshe na huci take furta  Babu ruwanka Hilal. Ba abinda ya had aka da Matar nan zo ka shige gida.

Hilal ya girgiza kai  Ammi matar nan sirkar Haidar ce..  Yarta Haidar ke aure.. We are practically family now.

Bai kai aya ba Asshe ta k araso a guje ta toshe bakinsa  Allah tsari gatari da saran shuka. Allah mana tsari da had a iri da wann zuri a.. Shige gida kar na sake jin bakinka. Ta k arshe tana nuna masa k ofa.

Girgiza kai Hilal Ya kumayi  Ammi I m sorry. Bazan iya barin Umma a nan ba har sai na san abinda ke faruwa.

Baki sake Asshe ke dubansa  Umma.? Ta nanata a fili.  Umma ka kirata.? Toh sunanta Suwaiba. Kanwar uwarka ko na ubansa da zaka kirata da Umma.?. Ka sake kiran mahaukaciyar nan Umma sai naci maka. Zo ka shige kafin Abbanka Ya k araso. Ta k arashe tana janyo Hilal yana tirjewa haka Har ta shigar dashi cikin gidan ta janyo k ofa tana fad in masu gadi kar su bari Suwaiba ta zo koda kusan gate din ne.

Mamaki Ya cika Hilal. Shi Ya kasa gane wann irin al amari ne wann da kuma abindake tsakanin mahaifiyarsa da da Umma.


After some hrs da faruwan hakan. Tsaye yai bayan mahaifiyar tasa sanda take lek e daga window ko zata hango Umma. Cikin zuciyarta tana addu an Allah yasa mayyar ta tafi dan bata fata mijinta ya dawo ya tadda Suwaiba kofan gidan balle asirinta ya tonu.

Ya girgiza kai kad an yana kuma takowa kusan mahaifiyarsa. Aiko a firgice ta juyo tamkar maras gaskiya. Ta dafe k irjinta tana fad in  Haba Hilal, halin Anisa na lab e ka koya kaima. K iris zuciyata bata buga ba. Ta k arashe har lokacin hannunta dafe da k irji. Sai kuma ta canza maganan da fad in  Lek e nake naga ko Abban naka Ya iso.. Gashi dai da alama har yanzu bai iso ba.. Lallai da alama zai dare. Ta kuma duban Hilal tana tsimewa  Waima mai ya shigo da Kai nan ne. Mai kake nema.?

 Dama na shigo ne na fad a Miki zan d an kwanta kafin la asar tinda naga har yanzu Abban bai iso ba.

Ta jinjina Kai tana dubansa  Idan ya iso zan tada Kai. Ta fad i tana nufan k ofa yayinda Hilal ya take mata baya.

*

Fitowan Hilal sallar la asar bayan an Ida sallah a masallaci a hanyar sa ta dawowa gida ya hangi Umma tana sallah jikin wani gini dake manne da karantar gidansu. Kasancewar akwai interlocks wajen. Mamaki ya cika Hilal. Ikon Allah yanzu dama ashe matar nan bata tafi ba. Lallai ba k aramin Abu ya zaunar da ita ba.

Ya k araso gefenta daga can ya tsuguna kan k afafunsa har ta Ida addu arta. Hilal ya tayata shafawa.

 Umma. Ya ambaci sunanta daga nan yanda yake tsugune kaman dai yanda yaji Khulsum na kiranta.

Umma ta d ago ta dubesa sai ta sakar masa murmushi  Hilal d an albarka. Ta fad i tana dubansa dan bazata tab a mance alkhairan yaron ba koda kuwa ita mahaifiyarsa suna buga dabi. Kaman yanda nata yaran basuyi halinta ba haka zalika Hilal baiyi halin mahaifiyarsa ba a cewarta.

Hilal ya gaisheta kafin ya k arada  Umma mai kikeyi a nan.? Mai ya zaunar dake nan.? Ya dan numfasa kiyi hak uri da tambayar da zan Miki  Shin akwai wani matsala ne tsakaninki da mahaifiyata.? Meke faruwa tsakanin ku biyun.?

Umma ta girgiza Kai kad an  Babu komai Hilal. Amma Kai hakuri bazan bar k ofar gidan nan ba har sai mahaifiyarka ta saurareni.

Hilal ya zuba ma sarautar Allah ido yana tuno yanda sukai da Amminsa. Ya d an kuma girgiza Kai  Amma.. Kiyi hak uri da tambayarta da zan Miki.. Wani abu ne kike nema wajen mahaifiyata.? Ki sanar dani dan Allah idan wani Abu ne da zan iya taimakawa.

Umma ta kuma murmusawa  A a Hilal. K arshen abinda zanyi shine na saka ka cikin matsalolinmu. Kai d in kanada zuciya mai kyau. Ina rok on Allah yasa D anuwanka dake auren Ummul d ina ya zama mai kyaun hali da d abi u irin naka.. Ta k arashe cikin rawar murya irin na mai kuka hawaye na gangaro mata dan a koda yaushe cikin tunanin Ummul d inta take da halinda zata iya kasancewa ciki. A gaggauce tai k ok arin goge fuskarta kafin ta kuma duban Hilal tace  Mahaifiyarka nake son magana da, sabida wajenta nazo. Domin dani da mahaifiyarka munada alak a mai kyau. Ta k arashe murmushi saman fuskarta.

Mamaki ya kuma cika Hilal. Kansa ya kuma k ullewa. Tabbas wad ann mata wato Amminsa da Umma al amarinsu abin dubawa ne sann yanada rikitarwa. A b angare guda mahaifiyarsa tana ikirarin datse alak a da Umma da ahalinta. A b angaren Umma tana fad in itada mahaifiyarsa sunada alak a mai kyau. Shin na waye zai d auka cikin su biyun.?

Juyin duniya Hilal yayi Umma ta hakura ta koma gida amma fir fir tak i ta kafe lallai lallai sai Asshe ta saurareta. Ganin yamma nayi yasa Hilal d aukan mota ya fice daga gidan. Dan yasan watak ila maganarta kawai Umma zata saurara ta amince ta bar k ofar gidansu.

A bakin ward din ya hangeta tana k ok arin shiga. Sauri sauri ya k arasa ya cimmata.


Kaman Wanda aka jefo shi haka Khulsum taga Hilal gabanta.

Da mamaki take dubansa.

 It s a good thing that I found you here. You need to come with me. Abinda kawai Hilal yace kenan.

Khulsum ta girgiza Kai cikeda mamaki  Malam lafiya.?

Yai gajeren tsaki  Wai ke ko yaushe haka kike ne. Abun fad a baya Miki kad an ne.? Ya kuma girgiza Kai  I need you to come with me right away. And please you alone. You don t need to inform that aunt of yours& She might stop you. Dan bai mance ba kwanakin can da suka shige ita ce ta hana Khulsum bin Umma Akan idonsa. Daga haka sa Kai yai ya soma tafiya yana fad in tai sauri ba lokaci.

Takaici ya cika Khulsum, mai wann D an rainin hankalin ya d auketa da zaice tazo ta bisa. Ina ma zata bisa.? Mai ya maidata.?

Ganin ya soma tafiya ya nufi mota yasata bin bayansa da sauri tana fad in  Kai Malam.. D an dakata.? Kana tunanin kai waye.? Mai ka d auke ni.. Mai ka maidani da zaka tako har yanda nake kace nazo na bika kuma kar na sanar da Innata.. Ce maka akai..

Bata Kai aya ba Hilal ya kaikaito yana dubanta cikeda takaicin kuskuren fahimtar da tai masa  Hey cut it out will you.! Ya katseta da fad in haka kafin yaci gaba  Seriously, is that what you think of me.? Har lokacin da mamaki yake dubanta kafin yaci gaba  If that s what I wanted I d have gone straight to a hotel or club, and not a hospital. Ya dan girgiza Kai  Look, ni ba irin wad ann mutanen bane. And I m not kidnapping you.. Idan na zo nan kawai nazo ne sabida mahaifiyarki dake zaune k ofar gidanmu through out the day. Idan Ammi na ta fito ta taddata wajen it would be a disaster. Idan akwai girman mahaifiyarki da kike gani kike ji a cikin Zuciyar ki koda kad an ne zaki taho tare Dani dan na tabbata ke zata iya sauraronki. Ya k arashe yana bud e motar.

Jikin Khulsum yai sanyi ta dubesa da mamaki  Umma ce take k ofar gidanku.?

Hilal ya zuba mata ido yana dubanta. Baice komai ba sai tada motar da yai  Zakije ne ko nai tafiyata.?

Ta hareresa sai kuma tai still a wajen kaman mai tunani. Shin ta sanar da Inna Dije ne.? Toh amma idan ta sanar da Innah Dije wani wutan zata kunna tinda tasan Ummanta da Inna Dije basa jituwa. Sann Inna Dije zata iya hanata zuwa. Tana tsaka da tunanin taji sautin horn ya cika mata kunne alamun Hilal na jiran decision dinta. Harara ta b alla masa kafin ta bud e marfin motar ta shige.

Ya soma driving babu mai ce da kowa komai cikin su biyun har suka iso k ofar gidansu Hilal. Can Khulsum ta hangi Umma rakub e jikin gini tana lek en gate din gidansu Hilal kaman wata mabaraciya. Sosai abin ya mata ciwo ganin mahaifiyarta a haka. Hilal na Ida parking ta fito ta nufi Umma.

 Umma.! Khulsum tace daga nan yanda take tsaye kusan Umma.

Umma ta d ago tana dubanta. Khulsum tai saurin k arasowa ta duk a gaban Umma  Umma Mai kike a nan. Dan Allah mai kike haka a nan.? Umma wann fah zubda mutunci ne. Dan Allah ki tashi ki bar k ofar gidan nan. Duba fah kiga mutane masu shigewa suna kallonki.. Umma dan Allah ki tashi haka nan.

Hawaye Umma ta soma tana girgiza Kai  A a Khulsum bani tafiya sai Hajiya Asshe ta sauraren.

Khulsum ta juya ta dubi Hilal dake can jikin motarsa yana tsaye. Shid in ma su yake duba. Ko ba a ce ba damuwan halinda Umma ke ciki ne saman fuskarsa dukda baya iya sauraron mai uwa da  yar ke cewa.

Khulsum ta maidoda dubanta ga mahaifiyarta  Umma matar nan tareda ita ina nufin keda ita kuka k ulla auren  Yaruwata. Bansan dalilinta na juya Miki baya ba. Bansan meye ku biyun kuka bisne ba. Bansan meye a tsakaninku ba. Amma ke mahaifiyata ce kuma bazan so ki walak anta ba. Dan Allah Umma ko mai kike nema wajen matar nan kiyi hak uri ki bar k ofar gidan nan.

Umma ta kuma girgiza Kai tana hawaye  Khulsum idan na tafi mai zanje nace da Tani. Na mata alk awarin zan nemo kud ad en belinta. A nan ne kawai nake da yak inin zan samu kud in fiddo Tani Khulsum.

Baki sake Khulsum ke dubanta. Da mamaki tace  Umma wai dama kan kud ad en belin Mama kike nan.?

Umma ta jinjina mata Kai alamun eh.

Shiru Khulsum tai na d an lokaci kafin ta dubi mahaifiyar tata tace  Umma kece zakiyi belin Mama. Wai Mama Tani dai da ta saida shagon Abba.?

Umma ta kuma jinjina mata Kai  Dukkanmu masu kuskure ne Khulsum. Tani ta salwantar da dukiyar Malam ni kuma na salwantar da rayuwar  yarsa. Cikin mu biyun idan akwai Wanda tafi girman laifi toh ni ce Khulsum. Ni yafi cancanta na tafi gidan kasu ba Tani ba. Idan har zan zuba ido ni ina shak an iskan  yanci yayinda Tani ke gark ame kurkuku bana tsammanin nayi ma kaina adalci. Sann bana jin  yancin iskan da nake shak a a mak oshi na. Tani ta tuba Khulsum. Dukanmu mun gane kurakurenmu. A halin yanzu bamuda wani buri da ya wuce mu koma ga mijinmu mu kula dashi mu masa jinya mu samu aljannarmu. Ta k arashe cikin rawar murya irinta mai kuka.

Jikin Khulsum yai sanyi. Tasan mahaifiyarta tanada zuciya mai kyau Wanda da yawan mutane suna amfani da wann damar su shashashantar da ita. Kaman dai yanda takeda kokonto Akan tuban Mama Tani. Dan tasan kad anda aikin Mama ne ta shashantar da mahaifiyarta ta samu ta fito

33 / 52