Auren Wata Uku Book Complete By Sameena Aliyu.doc

Author :  SAMEENA ALIYU Category :  Arewa Pen

Chapter   26 / 52

75K to 78K   out of 153.1K words

aki ba. Innalillahi wa inna ilaihi raji un. Meke faruwa da ita da yaranta? Daga wacce miji Ya bata sak on sakinta ta hannun mahaifiyarta sai wacce miji Ya cuta ya kuma gudu Ya barta. Sann a dalilinsa aka kame uwarta aka gark ame. Shin wann wace irin rayuwa ce. Sai ga Mama tana kuka shar shar da hawaye hannaye biyu aka  Wayyo ni Tani naga takaina.! Habibu kaji tsoron Allah. Ka tuna ko mutuwa na kunyar idon uwa. Yanzu da wani bakin zan goranta ma Suwaiba ni Tani.  Yar Suwaiba ta tafi d akin Miji ni nawa yaran Sun dawo a jere. Wllhi bazata saku ba. da na koma na fuskanci tozarci yo gwara na Mutu a nan.! Ta kuma kurma kururwa.

Tsawa budurwar Habibu ta daka ma abokan aikinta cewa su shige da Tani cikin cell d inta su gark ame.


**

Abuja


Tsaye suke a can construction site d insu, yanda zasu gudanar da babban project na Kampaninsu.

Dukansu sanye suke da kaya irinta k wararrun Engrs. Reflective safety jacket kalan d orawa mai ratsin bak i sai safety helmet mai d aukeda tambarin kamfaninsu daga gaban *MB*

Su kusan hud u sunyi tsaye gaban wani tapkeken sketch. Design Architect Hisham sai kwararo bayani yake yayinda sauran ke jinjina Kai kowa yana fad in abinda ya k ware akai.

Hisham na hankalce da Haidar Wanda Sam hankalinsa bai tare dasu. Excusing Kansa yai ya k araso yanda Haidar ke tsaye jingine jikin mota. Shima d in cikin shiga irin tasu yake saidai shi babu jacket saman rigarsa sai ko helmet.

Hisham yai masa k uri hannayensa zube cikin aljihun jeans d insa. D an k arasowa yai kusan Haidar d in had ida jingina jikin motar. Ba tareda ya dubi Haidar d in ba ya soma fad in  This is not like you Engr. Ban Saba ganin ana aiki jikinka a mace ba.. I expect to see Haidar mai jajircewa da na sani dan ban tab a tsammanin Dad d inka zai mik a maka ragamar aikin nan cikin sauk I ba.. Snn kaji yanda abokinsa yake yabawa team d inmu baice komai ba baiyi yunk urin dakatar dashi ba kaman yanda ya saba a baya. Kawo yanzu sun hango future ma Kampanin tareda kai. Zan iya ce maka na hango yau d in a k awayar idanunsa. Ko bai furta maka ba he s proud of you..

Furzar da huci kad an Haidar yai yana mai gyara tsayuwarsa hannayensa zube cikin aljihunsa yake duban masu tonon k asa daga gefe  But unfortunately I m not a perfectionist, a workaholic like my Dad. Ya karkato yana duban Hisham sosai  Ban damu ba yayi alfahari dani ko kar yayi. I don t give a damn..

Hisham ya d an girgiza Kai yana duban Haidar d in  So tari mukan kasa ganin blessings da Allah ya mana baiwa dasu har sai mun rasa. Ka gode ma Allah Haidar ka girma da iyayenka biyu a raye kuma suna tareda kai. In my own case is a different story. Ban samu daman sanin mahaifina ba. Ban samu daman had uwa dashi ba. Ya d anyi fasali kafin ya murmusa  But it s fine I m not complaining. Alhamdulillah, At least I have my Mom with me. And to me she s more than enough you know. Ya kuma murmusawa yana jinina Kai  Bazamu iya k irga d inbin ni imomin Ubangijinmu garemu ba.

Dukda sanyi da jikin Haidar yai sai ya kauda Kai gefe dan shi gani yake da mahaifinsa da babu shi duk d aya ne gwara ma ace babun Watak ila bazai masa irin k iyayyan da yake masa a yanzu ba. Duban abokan aikinsu yai kana ya kauda zancen da fad in  Komai ya kammala saura fara aiki. Soil test ya rage. You take care of the report while I m away..

Hisham ya zuba masa ido shaye da mamaki. Ya d an girgiza kai  While you are away.? What does that mean..? What do you mean by that.?

Murmushi Haidar yai  It s good to take a break, don t you think.

Har lokacin dubansa Hisham yake da mamaki  Seriously.! Ina zaka Haidar.?

 To Cuba. Jirgina gobe da safe ne in sha Allah..

 Business trip.? Hisham ya tambaya yana dubansa.

 Am I using business terms here.? Bakaji mai nace maka bane. Vocation zan tafi of course.

Hisham ya d an Ware idanunsa. Kafin ya soma magana Haidar ya dakatar dashi  Don t even start.

Hisham ya jinjina Kansa a hankali  Bazaka saurareni ba na sani. But why Cuba.? Jiya fah nake gani a labarai Hurricane killed at least 6 people there& Couldn t she think of a better place. Ya tambaya yana duban Haidar d in tinda yasan wann bai wuce aikin Matarsa Dareen ba wacce yayi imani tarayyarta da Haidar d in Babu wani alheri tinda aure ne da Har yau iyayensa basuda labari.

K ok arin bud e motarsa ya soma  Zamuyi magana kaikam..

Har ya bud e m???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?otar zai shige Ya juyo ya dubi Hisham murmushi saman fuskarsa  C mon haka zaka barni na tafi bazaka min fatan alheri ba. What if this is the final goodbye. What if hurricane ya ritsa dani a can.?

Hisham ya k araso ya d an punching muscle d in Haidar guda  You shut up jerk.!

Dariya sukayi su duka biyun kafin suka rungume juna Hisham na fad in zasuyi aikinsu tareda nasara cikin yarda da ikon Ubangiji. A haka sukai sallama kowa naji a cikin zuciyarsa zasuyi kewan juna.


Hisham yai tsaye yana bin bayan motan Haidar da kallo. Murmushi ya saki yana mai ayyanawa cikin zuciyarsa tinda ba wani aiki mai tsanani da zasu fara yanzu zai tafi Kano. Ya kuma sakin murmushi sanda yake hango beautiful innocent face d inta a k awayar idonsa. Ya shirya tafiya neman aurenta wann karon. Ya shirya sanar da ita abinda yakeji gameda ita. Even though he s not expert a wann b angaren but zaiyi iya k ok arin sa ya tabbata bata kufce masa ba. He s been rejected so many times wanda hakan yasa neman aure da  yanmatan suka fita Kansa. But wann karon ya shirya yak in Neman auren Ummulkhairi da duka k arfinsa. Ya kuma sakin murmushi mai kyau zallan k aunarta na d awainiya dashi.

**

Yanda Mommy keta faman shiga da fice saida abun yai mugun d aure ma Anisa kai. Mommy fah tarba na musamman taketa faman shirya ma masu kawo Amaryar Haidar. Jikin Anisa gaba d aya ya mace, zuciyarta ta karaya ganin yanda Mommy keta d aukin wann aure. Ta tabbata ko wacece matar Haidar ta gama samun gurbi mai girma cikin zuciyar Mommy dan sosai take son wann aure. Ita gani take Ammi b ata lokacinta kawai take dan Mommy bazata bari Haidar Ya rabu da matar nan ba cikin watanni k alilan kaman yanda Ammin nata ta sanar da ita.

Suna jin shigowar Mota Mommy tai saurin mik ewa tana fad ad a murmushinta. Lokaci guda ta dubi Anisa tace maza su sauk a k asa ga matar Haidar ta iso.

Saurin rik o Mommy Anisa tai tana murmushi da yafi Kama da yak e  A a haba Mommy. D an dakata mana kefa uwa ce. Ki bari ni na sauk a. Ma shigo miki da ita.

Bata jira cewar Mommy ba ta nufi k asa tana mai rausayar da ido had ida furzar da huci dan wani mugun takaici ne Ya cika mata zuciya yacce kasan  yar gwal za a kawo gidan.




SameenaAleeyou=???
*AUREN WATA UKU.!*


*23*





*??Sameena Aleeyou&
'






Mommy ta gaza zaune ta gaza tsaye. Zuciyarta sai harbawa yake, ta rasa sukuni ne zuciyar nata ya samu sakamakon kawo makarin asirin Haidar da akayi kokuwa yarda da amincewan Haidar Wanda batada tabbas akai ne. Koma dai tsoron abin ya k unshi rasa rai ne. Sai ta fara tuhumar kanta anya bata kasance mai son zuciya ba. How could she kill another person s child for her own to survive. Saurin girgiza kai tai dan bata son irin tunanin nan su shige kanta. Dole ne yasa tayi hakan. Ance so so ne amma son kai yafi. She needs to save her only son no matter the cost, koda kuwa Ya k unshi rasa rai ne. Da wann tunanin zuciyarta ya samu natsuwa. Tai zaune cikin kujera tana jiran shigowarsu.


Inna Dije na rik e da hannun Ummul gam take k are ma katafaren gidan kallo Wanda ta masa lak abi da fadan shugaban k asa.

Suna shigowa wani irin k amshi ne da zatace hancinta bai tab a karo da irin shi ba tsaban dad i shi ya daki hancinta, nan ta hangi wata hamshak iyar mace wacce kallo guda zakai mata ka tabbata tayima babu bugun girma. Tana ganin Asshe jik akk iyar mace wayyaya sai taga ashe gaban Hajiya Kwaise Asshe ba komai bace. Kama daga yanayin suturan dake jikinta muhallinta harma da gogewar fatar ta. Dije ta jinjina kai tana kuma tabbatarwa. Waima Tani bataga wann daula da Ummul ta shiga ba kenan koda kaw ace na wutin gadi ne. Dole Tani ta zauce ta haukace.

Mommy ta fad ad a murmushinta tana fad in su k araso su k araso bismillah.

Yayinda Zuciyar Ummul yaci gaba da tsinkewa. Har lokacin kanta rufe yake cikin mayafi.

Daga yanda take zaune saman carpet tana jin yanda su Inna Dije dasu Aunty Asshe suke gaisuwa da muryar wata mata mai yanayi da shige dana Aunty Asshe. Nan gaisuwar tasu ta sauya salo zuwa yaren k abilar shuwa arab tsakanin Asshe da  yaruwarta.

Ita dai Inna Dije tinaninta da k wak walwarta sun gaza tantance tsananin kyau da tsarin gidan. Sai juye juye take tana mamakin koda ace auren kwangila na wata uku d ansu zai da Ummul meyasa sai Ummul a wann irin arziki da suke dashi. Meyasa basu nemo mace da Babu aibu tattare da ita ba sai Ummul. Itafa wann aure Sam bata amince iyaka cin gaskiya Asshe ta sanar dasu ba. Dik yanda akai akwai wata a k asa. Tunaninta ne Ya katse sanda taga matar ta k araso gaban Ummul murmushi fal saman kyakkyawar fuskarta.

Zuciyar Ummul yaci gaba da tsinkewa sanda taga hannun matar saman nata.

Lokaci guda Mommy ke ci gaba da fad in  Welcome my daughter. Sannu da zuwa cikin ahalinmu. I can t believe this is happening.. Finally Matar Aliyu na ta iso. Sai ta k arashe tana rungume Ummul daga zaune.

Anisa da Tai mutuwar zaune tana dubansu. Sai ta rausayar da ido cikeda k osawa tana mai aika ma Amminta wani kallo wacce itama jiki a sanyaye take duban Mommy dake rungume da Ummul tana ayyana farin cikinta a fili.

Mommy kaw cikin zuciyarta take ayyanawa  Zan kula dake a tsawon watanni uku da zakiyi damu. Sabida kin cancanta. You are my son s savior. Kin sadaukar da rayuwarki dan rayuwar nawa d an Ya inganta koda ace bakida masaniya akan hakan. This is the least I can do for you bayan sadaukarwa mai girma da kika mana. Zan baki dukkan soyayya da kulawa Har kawo lokacin da zaki warware mugun k ullin da akai ma D ana harma da ahalina. Ta k arashe tinanin nata idanunta harda guntun k walla. A hankali ta saka hannu ta yaye rufin da akai ma Ummul. Wani ikon Allah Sai Zuciyar Mommy ya kuma karaya. Fuskar yarinyar take kallo.. She looks so innocent and totally naive. She couldn t help but to feel guilty.. Meyasa rauni Ya cika zuciyarta a kallon farko da Tai ma fuskar yarinyar a zahiri. Tai k ok arin saita kanta tana fad ad a murmushinta  Barka da zuwa Ummulkhairi, d ago ki kalleni.. Sabuwar Mamanki..! Ta k arashe tana mai tallafo fuskar Ummul wacce ta kasa d ago idonta ta dubi matar amma jin kalamanta na k arshe yasa ta soma k ok arin d ago idonta masu cikeda rauni hawaye tab cikinsu.

Dubanta Mommy take Har lokacin tana rik eda hab arta murmushi saman fuskarta.

Sai Ummul taji kuka da gaske na zuwa mata musamman da taji matar ta ambaceta da sabuwar Mamanta. Shin tasan Ummanta ta datse alak a da ita ne..?

Mommy ta soma girgiza mata kai alamun banda kuka. Ta shiga share mata hawayen tana fad in ta daina kuka ta saki ranta kaman tana cikin Ahalinta.

Mik ewa Anisa Tai cikeda k osawa tana rausayar da ido. Ta dubi Amminta ta furta a hankali  I m tired of this drama.! Tana fad in haka tasa kai ta shige.

Su Inna Dije Anci an sha an masu tarban girma ta kuma yarda Lallai Ummul gidan girma ta arziki ta shigo dan ko matar nan bata masu tarba da kayan arziki ba tarban fuska da ta masu da yanda ta amshi Ummul kawai sun isa ta shaida gidan girma da arziki Ummul ta shigo. Koda yake amma Asshe ta sanar da ita Auren na wata uku ne sann ga dalilin auren cewa kwangila suke so a bama d ansu a kampanin mahaifinsa mahaifin nasa yace bazai bada ba har sai ya kawo masa mata ma ana Har sai yayi Aure. Shin duk akan AUREN WATA UKU matar nan tai masu irin wann tarba ta kuma karb i Ummul hannu bibbiyu kaman  yarda ta haifa.. Anya kuwa..? Ita fah duka abubuwan dake faruwa Sun fara kwance mata kai. Ji take ta gaza fahimtar komai. Koda sukazo tafiya da Ummulkhairi b angaren Haidar Mommy ce ta rik e Ummul da kanta tace ita zatai ma  yarta rakiya. Kan Inna Dije Ya kuma d aurewa. Suka dubi juna itada Asshe. Asshe ta k ifta mata ido alamun kar tace komai.

A haka dai aka bama Inna Dije ma nata masauk in nan cikin gidan da nufin washe gari idan Allah yakai rai zasu koma Kano itada abokiyar tafiyarta Asshe.

Ita kad ai a d aki sai sak awa da warwarewa take. Ta d au d amarar kafin su bar gidan kafin su koma garin Kano sai tayi yanda tasan ta fahimci duk abubuwan dake wakana. Batai ma Ummul rakiya zuwa garin ba sai don su koma tare da Ummul d in. Amma yanda taga Uwar mijin Ummul na kaffa kaffa da ita tana nan nan da ita bata tsammanin Auren zai Mutu a sauk ak e. Abu guda ne zai kashe auren nan shine kawai ta bud e bakinta ta sanar da matar cewa ajalinta D anta Asshe ta kawo mata cikin gida.

Ta mik e da zummar fitowa nan taga Asshe tsaye gabanta.

Girgiza mata kai Asshe Tai tace  Koma ki zauna Tun muna mu biyu.

Inna Dije ta dubeta da mamaki. Sai kuma Tai  yar bazawarar murmushi  Aw baki so mu kasance mu uku ne. Ina nufin ni da Ke da kuma  yaruwarki wacce kikai mata rufa rufa ki aura ma D anta ajalinsa. Kar ki tausareni da abun duniya dan yanzu na fahimci kema gaban  yaruwar taki almajira ce. Sunan mijinki ne kawai kike tink aho da tak ama dashi amma da alama Babu abinda auren naki ke tsinana Miki. Da alama yayinki ya k are wajen miji dole ki nemi hanyar neman kud i kota halin k ak a.

A zuciye Asshe ta dakatar da ita  Kar ki kuskura ki bada shaida kan abinda bakida masaniya. Ina shawartanki kar kiyi gangancin shiga tsakanin  yanuwa guda biyu. Ina nufin nida  yaruwata. Ta k arashe maganar nata tana sakin murmushi kamar ba itace ta sha mur ba.

Lokaci guda Asshe ta k araso ta dafa kad an Inna Dije guda tana sakin murmushi  Ki kwanta a saman gado irin Wanda baki tab a mafarkinsa ba. Ki yada gajiya, kafin ki d auki hanyar gida gobe dan ba Lallai ki sake karo da irin wann gadon ba. Kar ki mance  yarku wata uku kacal zatai a gidan nan.! Ta k arashe tana k irga uku da yatsunsa. Lokaci guda ta zaunar da Dije saman gado sai itama ta zauna a gefenta  Ya kamata mu tab a hira ta k awaye kafin safiya.. Baki tunani.? Ta k arashe tana kashe ma Dije ido. Daidai lokacin Anisa ta shigo da tea cups guda biyu.

Asshe ta fad ad a murmushinta  Yauwa  yar albarka. Kin kawo mana shayin nida k awata.

Anisa ta jinina kai tana mai ajewa gaba garesu.

Asshe ta d auko ta mik a ma Dije  Ga shayin gidan shugaban k asa. Irin wann ganyen shayin a gidan shugaban k asa kawai kike gani ki sha ki kafa tarihi ki goranta ma sirakanki ina nufin Tani da Suwaiba. Ta k arashe tana kurb an wanda ke d aya hannun nata.

Ganin Dije ta k ek ashe ido tana dubanta Ya sanyata sakin murmushi  Aw na zaci k awa kika d aukeni. Kindai san k awar arziki bazata baki guba ba. Ko dama k arya kike da kika kirani k awa.? Ta murmusa tana kurban shayinta hankali  Ashe k aryar gogewa kike Dije. TaI maganar tana kuma kurban shayin. Harda lumshe ido tana fad in  Wani abu sai a fadan shugaban k asa. Ta shanye nata tana k ok arin janyo na Inna Dije da niyyan shanyewa Inna Dije Tai saurin rik e hannunta ta amshe tea d in.

Inna Dije na murmushi tace  Yo Dije nake muricin kan Dutse . Idan baki sani ba ban fito ba saida na shirya. Ba wani barikinki da gogewarki da zai bani tsoro. Ta k arashe tana kafa kai ta soma kurb an shayi tana lumshe ido.

Kan kace me Inna Dije ta zube kan gado bacci yayi awon gaba da ita. Asshe ta kece dariya tana jinjina k ok arin

26 / 52