Author : Badiat Ibrahim Mrs Bukhari Category : Read Hausa Novels
ni rabuwa da shi zan yi gaskiya.
Lafiya lau kawai Ammina ce bata da lafiya shine duk hankalina ya tashi. A gigice yace.
"Subuhanallahi, yaya jikin nata amma?" Nace.
Da sauk'i"
"Ki gaishe mun da ita da jiki, bari in barki sai na zo da daddare." Katse wayata nayi ina cizon
yatsa. Ko yace zai zo ya dubata ma. duk da ciwon k'arya ne. k'wafa nayi, komawa nayi wajansu
Ammi. Nan muka soma yagar kaji. Wayar Jamila ta soma kuka. Nan muka fashe mata da
dariya. Saurayinta ne mai kaji yake kiranta. A turb'une ta amsa.
"Hello" Ba mu ji mai yace mata ba, sai ji mu ka yi tace.
"Gani nan fitowa." karyawa taci gaba dayi har sai da ta gama tsab ta fita. Bata dawo ba sai da
ledar kaji guda biyu manya manya, a gyare a fige. Gud'a Ammi ta saka tace.
"Haihuwa ta yi rana. Ƴaƴa mata jarine. Yafi duk wata hajar da me haja zai baza dancin riba. kai
masha Allah, ya ga jan baki da hoda, yarinya fara mai diri." Hon d'in motar saurayin Hafsa ne ya
katse Ammi.
"Hafsa maza je ki shigo dashi, ni kuma bari in kwanta. Hauwa d'akko mayafi da filo." Da sauri
na d'akko mata. Ba shiri ta kwanta na rufeta. Yarane suka shigo da katon na ruwan Faro. da
katon biyu na moltina. Sannan sai ga Alh da Hafsa sun shigo, wata dakakkiyar bazin ce a
jikinshi. sai maik'o take yi. Duk girmanshi a gaban Ammi ya zube yana gaisheta. Nera dubu
ashirin ya ajjiye a gabanta yai mana sallama. Hafsa data tashi shigowa da kayan mak'ulashe ta
shigo. Wunin ranar sam saina kasa sukuni. Aminu ne yake ta kirana a waya. Agogon wayar na
kalla k'arfe takwas na dare. Da kyar na d'aga wayar, ban iya cewa komai ba.
"Hauwa ina waje a k'ofar gidanku, kamar yanda ki kai mun kwatance." Wayar na kashe, na
mik'e kwallin da Ammi ta had'a mana na musamman dan jan hankalin d'a namiji na ranbad'a a
idanuna, dama hodar farin jini da jan hankalin ɗa namiji ita muke shafawa a koda yaushe.
sannan na fita dan cikin kwalliya nake tsab. Yana rab'e a jikin bangon gidanmu. Hafsa kuma tana zaune a bakin ƙofar motar Alhnta, shi
kuma yana tsaye sai zuba yake yi mata. Jamila kuma tana zaune akan roba robar saurayinta
mai kaji. Takaici duk ya cika ni. yanzu a dakali zamu zauna kenan, irin matsiyacin dana
yayiɓoma kaina kenan? Bafa zata saɓu ba bindiga a ruwa. Fuu na wuce dakalin gidanmu na
zauna, na bud'e Aminu da k'amshina mai janye hankalin mai shaƙa. Isowa yayi wajan ya zauna.
"Hauwa amma kamar an tab'amun ke ko?" K'inyin fara'a nayi, sai ma sake haɗe raina da nayi
nace.
"Kaza nake ta son inci tun safe, ban samu ba har yanzu." Murmushi yayi mun yace.
"Kaza fa, ke bakya jin garinne Hauwa? Kaza fa dubu uku take, dubu uku ai garinta da nisa.
Harararshi nayi, kaina na juya.
Kenan bazaka iya siya mun kaza ba ko Aminu, a haka ne zaka iya soyayya dani? Toh bari kaji
duk wani fitowa da zanyi wajanka saika biya dan wallahi bazan yi fitowar banza, in sha sanyin
banza ba. Kai nifa in bazaka iyaba kaje kawai." Iska ya busar a bakinshi, shiru yayi yana kallona
k'ur, bagabaki d'aya hankalinshi na lura ya tashi. Da gaske Aminu ya zurfafani a zuchiyarshi
sosai. sai naji ya d'an bani tausayi, amma dole in matse dan bazan iya zancen banza ba.
"Hauwa bari in fito in zaiyana miki koni waye tun yanzu. Domun na lura tafiyarmu kamar bazata
yiwu ba, danni talakane, kuma aure ya kawoni ba shashanci ba.
Ni dai marayane, mahaifina ya rasu tun ina k'arami. Mu biyu mahaifiyarmu ta Haifa, dani da
k'anwata Tahira. Nauyin gidanmu tun ina d'an shekara goma sha biyu ya hau kaina. hakanne
yasa ban samu damar karatun boko can ba, iyakata faramare, amma nayi karatun addini
madaidaici. Mu fulanin Adamawane, danginmu duk suna can. Ni ma aikacine a babban shagon
sai da iskar gas, wanda yake kan titin mandawari, albashi nake d'auka duk sati. Hauwa wannan
shine Aminu a tak'aice, ba da yaudara na zo ba, zan baki kulawa daidai k'arfina, zan kula da ke
in sha Allah. Duk abunda kike so zanyi miki, kin amince dani ko kuma in yayyafama zuchiyata
ruwan salama?" Tsintar kaina nayi da amincewa. Daga nan muka b'alle da hirar soyayya. Na
saki jikina har da dariya. Da zan shiga gida ya kawo nera dubu biyu ya mik'o mun.
"Ga kud'in zancan ina fatan bai yi kad'an ba?" Hannu nasa na amsa.
Babu laifi dai, amma dan kad'an kam yayi." Murmushi yayi.
"Hauwa rigima.Zan tafi ni kam. Ki gaishe da Ammi da jiki. Sai gobe inna dawo, kya ban labarinki
ko, dan sanin dawa nake taraiya. Sallama mukai da juna na shiga gida. Ammi na samu a tsakar
gida, hannunta ta mik'o.
"Bani kud'in zancan, ko a haka kika bari ya tafi baki yago komai ba?
Dubu biyun na mik'a mata.
"Hauwa matsiyacine kika tsaya b'ata lokaci a kanshi, nera dubu biyu ya baki da zai tafi? Amman
kin cika asararriya, ai ko kuɗin turaren da kika shafe jiki dashi bai biya ba, balle azo kan jan baki
da hoda" Hafsa da ta shigo ta saki shewa tace.
"Bari kiga masu yi dan Allah Ammi.
Dubu goma ta mik'a ma Ammi. Tsaki nayi na shige ciki, baƙin cikin Hafsa yayi mun katutu sosai.
Ba dan Aminu yayi mun ba da dole in yima Hafsa ƙarfa_ƙarfan Alh kota halin ƙaƙa ne"
Soyayyarmu sati biyu kenan da somata, kuma kullum Aminu yana xuwa zance, wataran ya bani
dubu biyu, watarana ya bani dubu d'aya. Iyakar kyautata da shi kenan. Yau kam ina zaune ina
jiran ko ni ko Aminu, dan dole ya siyamun babbar waya gorin ya isheni haka. Bayan isha kuwa
saiga kiranshi. Ina fita na zauna a dakali ina d'igar hawaye. gabaki d'aya Aminu ya birkice sai aikin lallashina ya
ke yi. Idanu ya runtse yasa.
"Ya salam, Hauwa kina bani ciwon kai, dan kinga ina mugun sanki, yanzu menene fad'amun
nasan bazai wuci wani abun kike buk'ata ba, ko kudi ko?" Harararshi nayi nace.
Wato kasanma baka wadatani yanda ya dace ba ko?" Yace.
"Bafa haka nake nufi ba. Amma fad'amun damuwarki in sha Allah zanyi miki.
Yauwa ko kai fa. Babbar waya nake son ka siya mun, 'yan gidanmu sai gori suke yi mun. Had'e
ranshi yayi tamau, da dukkan alama maganar da na furta ta jagula mishi ranshi ainun. Kanshi
ya girgiza kawai yace.
"Zan sai miki nanda sati d'aya masu zuwa. Amma yakamata kifasan k'arfina ba d'aya bane da
Alhn da yake zuwa k'ofar gidanku wajan Hafsa ba. Ni mai k'aramin k'arfine sosai."
sabida tsabar b'acin ran daya shiga, bai jima ba ya tafi abunshi. Gida na shiga ina k'unk'unni
sabida ya matuk'ar bani haushi. Amma satin na cika ya kawo mun sabuwar waya vivo
A haka mu kai ta takusawa har tsawon shekara guda, kullum sai mun samu sab'ani da Aminu,
kuma a hakan shi ke mun komai, hatta kud'in abinci shi yake bani. Kud'in gyaran kai, kud'in
kitso , kud'in kayan kwalliya, kud'in sutura, kud'in kashewa, duk fa shine. Ammi da kanta ta yaba
da Aminu sosai, yaki ya nuna gazawarshi, kuma hanya k'iris muke jira ya gaza mu sallameshi,
dan Ammi tace bazan aureshi ba sam. Tatsarshi kawai zanyi.
Aminu
Dada na zaune a d'aki tana damun fura, Aminu ya shigo da sallamarshi. Idanu ta zuba mishi har
wata rama yayi, a watanninnan ta rasa gane kan Aminu sam.
"Wai kai lafiyarka k'alau kuwa, ni naga duk ka fice a hayyacina ne. Bai bata amsaba wayarshi
ta shiga ruri, Hauwa ke kiranshi. Da sauri ya d'aga.
"Hello Hauwa. Ya akayi ya gida?" A turb'une na Amsa mishi.
"Lafiya lau, Ammi na son ganinka da daddare, shine tace in kiraka." K'it na kashe wayata.
Aminu
Ahankali ya sauke wayar a kunnenshi jikinshi a mace mus.
"Tambayarka fa nake Aminu am."
"Dada babu komai, kawai kwana biyu bana wani jin dad'ine sosai shi yasa." Kallonshi kawai tayi
tace.
"Allah ya kawo sauk'i. Amma ai yakamata tunda k'anwarka ta yi aure, kaima kayi zaka fi samun
nutsuwa ko, daga kai har Saminu shiru abunku babu mai budurwa." Saminu ne ya shigo da
sallama ya zauna yana dariya.
"Dada daga ni har shi muna da matan da muke so, ni har ma an kai mun sadakinta yau d'innan.
Shima yana da budurwa duk da sai wahalashi take ta faman yi, shiyasa duk ya sukurkuce, ni
gani nake kamar bazata aureshi ba Dada." Hannu Dada ta shiga tafawa tace.
"Yanzu akan mace ne ya jefa kanshi a wannan halin, toh yankarka take yi ne in kaje duk ka
tsomare haka?" Shi dai Aminu ya kasa cewa komai, Saminu yace.
"Yarinyace 'yar shuwa, kinsan Dada in mata na da kyau sai a hankali."
" 'yar shuwa fa kace Saminu? Ni bada ni ba da yin suruka da shuwa, wad'annan masu mallakar,
da nuna mulki. Inama Aminu yaga kud'in auren 'yar shuwa ma toh, kasan irin kud'i da ake
kashewa kafin a auresu kuwa? ka kiyayeni wallahi, na faɗa maka kenan. Kar kaje ka ɗebo
mana kara da kiyashi, ina kai ina shuwa." Aminu jikinshi ya mace mus, dama shi kanshi tunani
yake kamar bazai iya auren Hauwa ba. Duba da yanda son abun duniyarta yayi yawa. Amma
bazai iya rayuwa ba in dai bai mallaki Hauwa ba. Zai iya salwantar da dukiya ko nawace dan
ganin ya kashe ya kawo Hauwa cikin gidanshi." Fita su ka yi da Saminu bayan sun yi ma Dada
sallama.
"Saminu gaskiyar fa Dada ne, bani da kud'in auren Hauwa, amma bazan soma bari Hauwa ta
kufce mun ba. Nasha wahallalu a kanta sosai, kuma ina sonta da yawan gaske." Saminu yace.
"Yarinyar ce iyayenta suna baka wahala da yawa, sun saka buri da kwad'ayi akan yaransu yai
yawa. Amma ni kaina zan so ka mallaketa, kar wahalar daka sha ta tafi a iska.
"Ameen Saminu, yanzu mahaifiyarta ta buk'aci ganina yau da daddare. Zamu je ka raka ni,
Allah yasa mu ji alkhairi." Saminu yace.
"Babu damuwa, Allah ya kaimu daren. Sai kaji na kai Sadakin Farida ko?" Dariya Aminu yayi
yace.
"Wallahi kuwa, kai abokina na tayaka murna fa, yaushe aka tsayar ranar bikin?" Saminu yace.
"Da waini naso ad'an dakata ko za'a had'e da naka, tunda ai kun dad'e da Hauwa. Kunfi
shekara guda fa, ni yaushe yaushe na had'u da Farida? Gashi har an kai kud'ina gidsnsu.
"Ka bari kawai. Ni na zuba idanune inga yaushe Hauwa zata bani damar turo magabatanane,
na jima da gaje take_takenta, gashi samari suita zuwa wajanta. Ni gani nake yi tana samun me
mota toh a ranar zata yi mun ritaya. Dan Hauwa mayyar mota ce." Dariya su ka saka dukkansu"
Jacara
Ammi wai meye dabararki na yin hakanne?" Dariya ta yi mun tace.
" Hauwa ho. Kora da hali nake son yi mishi, gazawa nakeso yayi da kanshi dan kar yaga an
yaudareshi. Haka Jamila, da Sameera. Duk zanyi ma samarinsu tarasu zanyi waje guda in
zayyane musu abunda ya dace, su kansu za'a samu masu janyewa a cikinsu." Ajjiyar zuchiya
na sauke nace.
"Ammi in Aminu ya tsallake fa, ni yaya zanyi auren nashi zanyi kenan?"
"Hauwa ho, saiki bari ya tsallake tukunna ai.
Da daddare kuwa sai ga surukan Ammi duk sun hallara a falon gidanmu.
"Am dama ba wani abu bane yasa nace aimun kiranku ba, sai dan akan maganar yarana da
kuke naima. Toh dama a tsarin dana tsarama kaina shine su su hud'un da suka taso a tare zan
had'esu ayi aurensu lokaci guda ne. Allah cikin ikonshi d'aya dags cikin manaima sai yayi
maganar zai turo da magabatanshi gobe, kuma baya so abun ya wuce wata guda. Ni kuma a
shirye nake. Toh dalilin kiranku kenan, ina fatan kuma kun shirya ko." Aminu sai kallon Ammi
yake yi yanda take magana gatse gatse yau ya gane ba banza yasa Hauwa bata iya magana
ba." Lawan me kaji yace.
"Toh ni dai zan iya cewa na shirya ban shirya ba, domun wata d'aya dai yayi mun kad'an. Sai
dai bazai gagaraba in sha Allah.
Yusuf saurayin Sameera yace.
"Babu komai zan sanar a gida." Aminu kuma yace.
"Ni dai ban shirya ba gaskiya. wata d'aya yayi mun kad'an, ni ba mai ƙarfi bane
marayane.".Saminu yayi gyaran murya yace.
"Babu damuwa Allah ya kaimu za'ayi in sha Allah." Ammi tace.
"Toh dukkanku kun Amince da wannan batu. Amma ba anan gizo ke sak'ar ba, dan akwai
sauran rina a kaba.
Mu shuwa muna da al'adun aure iri iri, kuma duk wata cikakkiyar 'yar shuwa, da sisin gwal ake
biyan sadakinta. A matsayinku na marasa k'arfi zaku biya sisin gwal biyar a matsayin sadaki.
Dan Hafsa sisin gwal goma sha biyu za'a biya sadakinta. Kuma mu shuwa anayi ma amarya
akwatuna cike da tsadaddun kaya. Kuma muna yin kayan d'aki sosai, dan haka babban waje
muke so a kama musu, ta yanda duk kayan da aka narka musu zai cinye ɗakin. Banda dai
sauran hidindimu da zaku ji a makin amaren naku. Na baku nan da sati guda, ko wanne ya
tabbatar sadakinshi bai wuce wannan lokacinba. In ya wuce toh ya rasa mata. Zaku iya tafiya
na k'are magana." Aminu da jan k'afa ya fita waje. Dakali ya samu ya zauna zaman 'yan bori.
Saminu yace.
"Tabb babu tarbiyya a gidannan sam Aminu, wannan wacce iriyar surukace sai kace magajiyar
karuwai. Aminu ya rasa me zaice, dan wani matsanancin ciwon kai da fad'uwar gabane ya
dameshi.
Hauwa
Assalamu Alaikum Kaga abokin ango da angon da kanshi" Kallon Aminu nayi na tab'e baki.
Saminu yace.
"Amarya bakya laifi, masha Allah sai muka ji sa biki sama ta ka haka.
"wallahi kuwa Saminu, muma bamu san da zancan ba sai yau d'innan. Ni fargabata shine kar in
rasa Aminu Saminu. Kuka na fashe dashi na munafurci. Aminu abubbuwa suka kuma jagwale
mishi, yau ga Hauwa tana kuka dan bata son ta rabu da shi.
"Hauwa ki dena kuka zanyi iyakar iyawata inga na aureki in sha Allah. Karki saka ni kuka dan
Allah. Rauni sosai naji a muryar Aminu.
"Aminu sisin gwal guda biyar ya kusan dubu d'ari shida zuwa bakwai fa. Ina zaka samu kud'in
sadaki ma kawai. Nifa mutuwa zanyi in ban mallakeka ba. A guje na shiga gida, Aminu na
kwad'amun kira amma ina. Ina shiga tsakar gida na tuntsire da wata wawuyar dariya.
Shashasha baka da ko sisine zan tsaya yin kuka a kan ka haka?" Hmm shigewa ta nayi cikin su
Ammi, anata shewa.
Aminu
"Aminu tawo mu tafi kaji."
"Saminu Hauwa zata shiga wani hali inta rasani, haka nima kuma bazaku gane mun ba, a jinina
nake jin san Hauwa. Sonta ya tasirantu a rayuwata." Idanun Aminu ya zama jawur, iya tashin
hankali yana ciki. Saminu ne ya rik'o hannunshi yace.
"Allah ya kawo mana d'auki. Dama kora da hali ita mahaifiyar Hauwan ta yi mana. Ina zamu
samu dubu d'ari shidda a wannan marrar. Kuma kud'in sadaki kawai banda sauran hidindimun
akwati, da kama haya. Ni na amsa mata ne da mun amince, sabida ina duba irin hidimtawa
Hauwa da kayi. Kuma kuna son junanku, duk da Hauwan kanta tana da nata tsayata kun" Haka Saminu ya dinga jan Aminu, shi kuwa jefa k'afarshi kawai yake yi. Abun hawa su ka hau
har zuwa gida. Kafin su isa gidan Aminu sau biyu yayi amai, zazzab'i mai zafi ne ya rabkeshi
cikin k'ank'anin lokaci. idanunshi har hawaye su ke yi. a haka suka shiga gida.
Dada ta fito band'aki kenan taga shigowarsu. Butar hannunta ta yar.
"Saminu lafiya kuwa, meke damunshi.?
"wallahi Dada zazzab'ine ya saukar mishi yanzu muna hanya. Matsala aka d'an samu ne a
gidansu ita yarinyar da yake nema." Dada tace.
"kai shi d'aki gani nan." Fita su ka yi, Saminu ya shinfid'eshi a katifarshi. Dada bata jima ba ta
shigo. Hannunta rik'e da kofin magani. Saminu ne ya bashi maganin yasa.
"Sannu Aminu, akan mace kake son halaka kan ka?" Saminu yace.
"Ba haka bane. Ita kanta yarinyar ta yiwu tafi Aminu shiga halin tashin hankali. Dan mun barota
tana kuka. Mahaifiyarta ce ke son rabasu." Saminu ya zayyane ma Dada yanda akayi. Kai take
ta jinjinawa tace.
"Wannan sadaki haka sai kace zata siyar da yaranta? Gobe zan shiga mak'otanmu nan gidan
'yar shuwa muji shin haka suke yi, ko kuwa ha'intarmu za'ayi. In tace haka suke yi, in sha Allah
Aminu bazan barka ka rasa yarinyarnan ba, tunda dai itama yarinya tana sonka. ka kwantar da
hankalinka." Sallama Dada ta yi musu ta fita. Saminu ne ya kwana d abokinshi yanai jinya. Da
sassafe kuwa Dada ta nufi gidan 'yar shuwa mak'ociyarsu."
Mrs Bukhari ce
*TALLAH*
Ina kuke amare uwayen gida kai har ma da ƴan mata? Ko kun san Mrs Bukhari mai kayan
ƙamshi, ai in dai batu na kayan ƙamshi gyaran jiki da na ɗaki to kai tsaye ku ne mi Badi'at
domin gwana ce ta ko wanne fanni a ciki. "Wai ƙamshi kina nufin Badi'at dai marubuciyar nan
tamu mai nishaɗantar da mu?" "Tabbas Fati ita take magana, ai kin dai ji yadda ake magana a kai na, hatta me gidana ya
jinjinawa Badi'at domin duk wani ƙamshi da zaki ji a jikina tare da gidana to daga ita ne, ke me
kankat ma har gyara na nake yi domin gyaran aurena daga gareta ne, shi ya sa bana wasa da
gyaran jikina da na gidana har kuke kirana da ƙamshi."
"Eh tabbas nima na jinjina mata, kuma zaki bani addireshinta domin nima na kwankwati wannan
garaɓasa. Ko zaki iya faɗa mini abubuwan da take sayarwa.?"
"Bari na faɗa miki akwai...
Humra
Kulacca
Sudanese Humra
Kulacca ta gashi.
Turaren wuta ɗan gaske, iri daban daban.
Turaren mopping
Room freshner
Turaren turara kaya.
Turaren wuta na toilet
Sannan akwai