Author : Badiat Ibrahim Mrs Bukhari Category : Read Hausa Novels
wata siyayya data dace duk mun kammaleta tsab, a waje guda aka ajjiye kayan
kan cewar gobe za'azo da mota ta kwashe daga nan a tafi a jerama ko wacce.
Ni banda k'awaye 'yan uwana sune k'awayena sai kuma Zalika. Toh tayi Aure a Zaria ta bar
kano.
da d'aya da d'aya masu kawo akwati duk suka kawo, gaskiya kowa ta more kaya. Amma har
zuwa yamma lis su Aminu basu kawo nasu ba. Ina d'aki Ammi ta shigo.
"ke Hauwa ki kira talakan yaronnan, yaya akaji shiru basu kawo kaya ba har yanzu. Kuma ki
sanar mishi gobe da sassafe su zo da motar kaya a kwashi kayan kitchen d'inki na gida, a tafi
kasuwa a kwashi kaya sai a wuce jeren, sannan ki tuno mishi da dubu ɗarin da nake binshi
bashi. Tsaki taja ta fice a d'akin. ni kuma na shiga kiran Aminu. Aminu masu kawo akwati basu zo ba har yanzu ko lafiya? cewa yayi dani.
"Lafiya. Dangin Abbanane basu isoba tukunna, suna hanya. Amma in sun iso dare baiyi cancan
ba. zasu kawo yau. In kuma basu iso da wuri ba, sai gobe da wuri. Na ce mishi
Sannan gobe zaku tawo da sassafe da motar d'iban kaya nan gida. Za'a d'ibi kaya, sauran suna
kasuwa, sai dubu ɗari da Ammi ta ranta maka na gyaran jiki da baka bayar ba tana buƙatar
kuɗaɗenta." Ajjiyar zuchiya ya sauke yace.
"Allah ya kaimu Hauwa nagode." Wayata na kashe Abina.
Aminu
"Lafiya Aminu naga kayi sanyi da yawa ne?" Saminu ke tambayarshi, bayan ya tsireshi da idanu
danjin me zai ce mishi.
"Ka bari Saminu. Nifa kud'in hannuna sun k'are, wallahi k'ark'ab nake. Maganar motar d'akko
kaya fa Hauwa take yi mun, harda wai bashin dubu ɗari da mahaifiyarta ta ƙaƙaba mun na
gyaran jiki wai." Saminu yace.
"Abokai sun d'an zauna zaman meeting kamar yanda ake yi. Kuma sun gaggand'a maka dubu
ashirin.Da naso sai an kai ka sai in d'an baka a hannunka dan wata buk'atar. Amma sahun giwa
ya take na raqumi sai ayi amfani da ita. Maganar wannan magajiya mai idon cin nerar kuma ka
barshi a gefe. Wallahi ba sisin da zaka bayar kaji ma na rantse" Ajjiyar zuchiya Aminu ya sauke,
bakinshi duk a bushe yace.
"wallahi tsadar aure tayi yawa sosai saminu, ka duba irin kud'in da aka narkar wajan neman
auren dama auren. Kai talaka shi yasa baya samun mata mai kyau. Kyawawan iyayensu sun
cika zuchiyarsu da buri. Sai gidan get da mota. Mu kuma marasa k'arfi sai dai mu auri mata
dai_dai mu." "Kai dai bari, bama irin na shuwa, shuwanma irinsu Hauwa. Yanxu na gane dalilin da yasa sai
kaga yarinya 'yar shekara arba'in hamshin a Borno babu aure tana yawo da sunan budurwa.
Ashe tsauwalawa harkar auren su ka yi. Dole sai mutum yayi dogon shiri zai iya aurensu. Kai
dai Allah ya baka.
"Hauwa "Hauwa!!. Asuba ta yi ki lallab'a ki tashi ki yi sallah ko?
Idanuna na lumshe wanda su ka kumbura ainun, k'irjina ya sake yin nauyin gaske.
Toh Uwatale. Na furta tare da mik'ewa zuwa cikin bayi. Alwala na d'auro na gabatar da sallah.
Na jima ina istingifari Kan mummunar b'arnar dana aikata. Tare da adda'ar Allah yasa in samu
haske a gaba. Gaisawa nayi da jama'ar d'akin. Sai tambayata jikina suke yi. Uwatale tace.
"Bamu samu damar gabatar miki da kanmu ba Hauwa. Duba da kina hali na jinya. Ni Sunana
Maryam Ana kirana Uwatale. wannan kuma sunanta Zainab. Ga Zakiya. Ga Ramla.
Haka ta dinga jero mun sunayensu baki d'aya. Ta d'aura da cewa.
"Ki taso mu je kitchen ki ga yanayin yanda muke gudanar da aikin girki a gidan. Ko hakan zai
d'an k'arfafa miki jikinki ki d'an warware.
Ba tare da musu ba na mik'e na bi bayanta. A bakin k'ofa ta tsaya. Sai ga wata gandiroba ta zo
da sauri ta bud'e k'ofar.
"Uwatale da mai jikin yau zaki fita?" Uwatale tace.
"Eh tare zamu dinga fita. Domun ta samu ta sake ta warware, kinsan ciwo baya son zama waje
d'aya.
"Hakane uwatale."
Ni dai ina biye da ita, har zuwa can bayan wani gini. Anan naga mata 'yan firsina masu manyan
shekaru. Anata had'a wuta ga k'atuwar tukunya a gefe.
"Ahh Uwatale wannan itace bak'uwar d'akin ku ko?" Uwatale tace.
"Eh itace Hauwa sunanta" Wata tsohuwa tace.
"Hauwa mu nai miki maraba da shigowa gidan albarka, gidan da ke mai da 'yar fashi ko mai
kisan kai mutum. Ba kamar yanda al'umma zasu k'yamace ka a waje ba. Da sannu zaki saba da
kowa har kiji bakison fita waccen duniyar mai cike da mayaudara da fasik'ai. Ni dai sai ido nake
binsu dashi. Da gasken gaske sunajin dad'in rayuwarsu a gidan. Tunda gashi suna hirarsu da
raha. Ga soyayya da nuna 'yan uwantaka, nima na shaida wannan. Duk da ni kaina zamana a
gidannan yafi mun kwanciyar hankali. fiye da zaman da zanyi a waccan duniyar da an sake ni.
Wata k'ila ma in sha guba in hallaka kaina. Amma anan na samu sabuwar duniya da sabuwar
rayuwa, sababbin 'yan uwa.
Waje suka bani na zauna. Inata kallonsu. Aka dama ruwan kokko, tare da mazaikwaila. Aka
kafa kaskon tuya. K'osai aka toya manya manya. Ga gandirobobi zagaye damu suna duba aikin
namu. Cikin awa uku aka kammala. Nanfa aka soma zuzzubawa kwano kwano. Ma'aikatan
gidan yarin suna d'auka suna fita dashi. Ni kunun kawai nake sha. tsami tsaminshi yayi mun
dad'i, sabida bakin nawa babu text. Da d'aya da d'aya aka kwashe abincin tas. Sannan su
Uwatale suka zauna zaman cin nashi. Da sha'awa nake kallonsu, dan sun burgeni sosai. Da
suka gama kuma su ka wanke komai, aka tsabtace wajan. Sannan uwatale tace.
"Mu je Hauwa. Kinji ma an buga k'ararrawa, lokacin fitowa yadi ne yayi. k'arfe goman safiya
ake bud'e kowa. Zuwa shiddan yamma kuma a kulle kowa. Nace.
"Amma ni kam jiri nake ji Uwatale zan je in kwanta. Zuwa azahar zan fito." Kallona ta yi tace.
"Shikenan Hauwa. Amma kisha maganinki kamun ki kwanta."
Kai kawai na gyad'a mata. Ahankali nake ta tafiya. Mata sun firfito anata hira ana dariya. ku ba
kwa ce hukuncin d'aurin rai da rai a kan da dama daga cikin matan ba.
Jagwab na zauna akan gadona. Aminu ya fad'omun. Ni nasan duk inda yake da tunanina a
zuchiyarshi zai ta rayuwarshi. Sake tsunduma cikin tunanin rayuwa ta baya nayi.
KOMAWA LABARI
Sai washe gari dangin Aminu su ka kawo kayan lefe da toshi a tare. A gaskiya an raina kayan a
gida sosai. Ammi da kanta ta kira Aminu. A lokacin bai jima da barin k'ofar gidanmu ba. sun zo
da mota sun d'ibi kaya, suna hanyar kasuwa.
Aminu.
Suna kasuwa ana loda kaya a mota wayarshi ta soma kuka. Da sauri ya d'aga duk da baisan
wake kiraba.
"Toh matsiyaci kayan lefenka da na toshinka sun iso, kayan ba su kai darajar 'yata ba. Ko bazin
babu a cikin akwatin balle zinare da manyan atampopi. koddibuwa ce kad'ai babbar atampa fa a
cikin kayan. Kasan me zaka yi. Ko wallahi kanaji kana gani in ba Hauwa wani mijin daya dace
da'ita, sannan ina binka bashin dubu ɗari" K'it ta kashe wayarta. Sororo Aminu yabi wayar da
kallo zuchiyarshi cike da mamaki ji yake yi uwa a mafarki, wannan wacce irin suruka ce haka to.
Saminu ne ya iso yace.
"Anfa gama Aminu. Mu je mu sauke su, muje wajan karb'ar dinkinnan ko?" Yanayin yanda yaga
idanun Aminu ya kad'a nan ya gane lallai da matsala.
"Aminu. Tunda ka soma soyayya da Hauwa take saka a cikin matsaloli barin ma da aurennan
ya matso dab. Yanxu dai meye kuma?"
"Saminu nifa na sare da lamarin gidansu Hauwa. Domun mahaifiyarsu son abun duniyarta fa
yayi yawa." Bama Saminu labarin komai yayi. ya d'aura da cewa.
"Ni fa akan wannan zan iya hak'uri da Hauwa. Bazai yiwu ace tun yanzu za'a dinga juyani daga
gidansu ba. Saminu ni na hak'ura da Hauwa."
Tafiya yayi ya bar Saminu a wajan. Sai shi ya raka motar kaya gidan da za su zauna. Nan ma
Hauwa ta kirashi tana kuka akan ita gidan baiyi mata ba, ance da mutane da yawa a gidan.
Wayarshi ya kashe baki d'aya. ya lumshe idanunshi son Hauwa na kuma nunkuwa a
zuchiyarshi. Sonta ya riga yayi tasiri a jikinshi.
Sai yamma lis Saminu ya shigo shagon kwanan su, anan ya iske Aminu a kwance, kanshi sai
bugawa yake yi.
"Yaya ake ciki, sunyi jeren ko sun koma da kayansu?" cewar Aminu. Dariya Saminu yasa yace.
"Anyi jere da k'yar, dan sai da aka yi sa'in sa a tsakanin Dangin Dada da Dangin Hauwa. Kai a
tak'aice matan gidanne su ka raba wannan fad'an, dangin Hauwa suna da mugun fitina, kai in
taƙaice maka faɗa har waje. Harda masu cire kallabi za'a daku. Ban bar wajan ba sai da su ka
gama jere tsab. Kai d'aki yayi kyau sosai Aminu. kai kaga d'akinka kamar wani Alh. Ko ina
shinfid'un lallausan kafet akayi mishi. D'akinka kaima daban.
Aminu baice komai ba. Sai lumshe idanu da yayi. Ya shiga tunanin irin tattalin Hauwa da zaiyi.
washe gari aka sa Amarya a lalle. Akasha shagulgulan biki.
Ranar juma'a Aka d'aura auren A babban masallacin jacara.
Hauwa
Ashe wani irin canji jiki da zuchiya take samu yayinda aka d'aureta da igiyoyin auren sunnah har
uku?" Jikina gabaki d'aya yayi wani irin mugun taushi. muna ta shirye shiryen zuwa wajan bikin
da za'a gabatar da bikin al'ada mai suna Hannono. shigace akeyi ta jajayen kaya da
gwalagwalai ga wad'anda suke da hali. Wani irin bikin aure ne na Al'ada wanda shuwa su ke ji
da shi. Mun yi kyau iya kyau. Sai kiran wayar Aminu nake yi Amma a kashe. dole nayi hak'uri da
zuwa wajan bikin. Gidan kab ya watse sai ni kad'ai kamar manya.
Nayi kuka ma'ishi. Sannan na tashi na sake wanka. Nayi adon lafaya ja mai adon juwatsu
jajaye. Suna dawowa motocin d'aukar Amare su ka soma zuwa.
Hafsa aka soma d'auka. Sai Jamila. A tak'aice nice ta k'arshe. Ina kuka aka tafi dani. bayan
Ammi ta d'auramun layar dake k'unshe da fatar kaciyana a jikin jigidar dake k'uguna.
An shigar dani d'akina. Wani sanyi da dad'ine ya mamayeni a zuchiyata. 'Yan uwana basu jima
ba kowa ya watse tas. Daga baya dangin Aminu suma suka gama fulatancinsu suka watse.
Mayafina na yaye. Nanfa na soma bin uwar d'akina da kallo komai ya tsaru sosai. Fita nayi falo,
tv k'ato na gani manne a bango. Murmushi nayi kawai. Na shige kitchen nanma na dudduba
komai yayi. D'ayan d'akin na tura na le'ka shima ya had'u sosai. Nanne wato d'akin da su
Ummu su ka ce mun na Aminu ne. Ko ina sai k'amshin turaren maiduri yake yi. dan mun tawo
da kasko na tuwa, muna shigowa aka kukkunna sune suke ci ko wacce kusurwa.
A falo na zauna ina kallon k'atuwar durowar turaren wuta da humra dake falon.
Ina zaune naji motsin 'kofa. Ko gezau banyi yunkurin tashiba. Aminu ne shi kad'ai hannunshi
rik'e da wata leda mara girma. Nasan dai ledar kazar amarya shak'e ake shigo da ita. ba
lak'wam kamar ta hannun Aminu ba.
Sai wani washe baki iyake yi, kamar wanda yaga wawan xama.
"Amarya bakya laifi." Zama yayi a kusa dani, tare da tallafoni zuwa jikinshi. Duk yanda naso in
cika Aminu da masifa sai naji na kasa irin kyakkyawan rok'on da yayi mun, da kuma irin kallon
soyayyar daya cikani dashi. Dole nayi lak'was.
"Hauwa yau dai na zama mijinki da k'yar. nasha wuya sosai, sonki ya wahalani. Harfa rama na
dinga yi. Barka da shigowa gidana Hauwa."
Zame jikinshi yayi ya dawo k'asa da zama. kaza ya ciro a fuwel na ganta mitsitsiya da ita. Sai
wani yogot 'karamin gora d'an d'ari da hamsin. Kai kawai na jijiga.
"Hauwa dakko plate da kofi a kitchen, ki zo ki ci abinci." Mik'ewa nayi na wuce. Ina juyo idanun
Aminu na yawo a jikina. Plate na d'akko da glass cup kamar yanda yace.
Mik'amai nayi Yasa hannu ya amsa. A gefenshi na zauna. Rabin kaza naga Aminu ya ciro ya
d'aura a plate. ya d'auki yogot d'innan ya zuba a glass cup d'innan. Iyakar yogot d'in cikin kofin.
"Ki yi hak'uri Hauwa Kinga rabin kaza ko? Iyakar k'arfina kenan. Duk kud'adena sun k'are.
Tab'dijan ni nafi k'arfin rabin kaza Aminu. Amma ka tusa a gaba kaci abunka zai fi maka.
Mik'ewa nayi da zummar wucewa ciki. Carab Aminu ya rik'i hannuna. Banyi aune ba naji na
fad'o jikinshi. kafin inyi wani yunk'uri sai jin bakin Aminu nayi a cikin nawa. Tsigar jikina take ta
soma zullo. A karon farko dana tab'a shiga irin wannan yanayin kenan. Daga ni har Aminu
jikinmu rawa yake yi. Da k'yar Aminu ya zare bakinshi a cikin nawa. Murya a mak'oshi yace. "Haba Amarya. Yaufa daren tarihine a cikin rayuwarmu. Ki daure ki had'iye fishinnan naki kici
kazar haka nan. Baki na cuno nace.
"Sai in ka yi mun alk'awarin kaini gidan Hafsa gobe, nima inje in ba idanuna abinci.
Wuyana ya shafa yace.
"Na yi miki alk'awari zan kai ki. Murmushi nayi. nan na hau cin kazar nan. Tas na cinye abata
ina korawa da yogot. Brush naje nayo. Aminu yace.
"Da kin d'auro alwala ai, sai mu gabatar da nafila ko?"
Toh" Kawai nace mishi. Tun akan sallaya Aminu ya cikani da sak'onnin dayake ta aikama jikina.
Daga nan kuma muka haye gado. A cikin minti goma Aminu ya samu nutsuwarshi dani. Nasha
zafi sosai. Jawo ni yayi jikinshi wani irin bacci mai cike da nutsuwa ya suremu. Baccine wanda
daga ni har Aminu bamu tab'ayin irinshi ba, har makara mu ka yi. "Subuhanallah, Hauwa tashi ki d'aura mana ruwan wanka, kinga gari ya waye." Mik'a na yi na
bud'e idanuna a hankali.
Ruwan wanka fa Aminu? Bani da kananzir gas d'in da aka kawo ni dashi babu iskar gas a ciki."
"Okey bari in yi da ruwan sanyi sai in nemo miki ruwan d'umi.
Da sauri ya fice. Tsaki nayi na koma baccina.
"Hauwa tashi ga ruwan zafin na siyo miki, ki yi wanka ki samu kiyi sallah." Mik'ewa nayi, ina
d'anjin zafi kad'an amma, ina yin wanka dana gasa jikina sai na ji sawai. Na fito na samu Aminu
ya fita. Sallah na soma yi. Kwalliya na cancara. na cakud'e jikina da humrori iri iri, na kashe
d'auri. Gyaran gado nayi komai tsab yake, gawayin kanti na kunna na turare gidana da turare
d'an maiduguri. Nan na zauna a falo ina jiran Aminu.
Da sallama ya shigo. Idanu ya xuba mun kawai yana kallona. Murmushi na yi mishi nace.
Kar ka cinyeni ka iso mana." A hankali ya iso ya zauna a kujerar da nake zaune.
"Hauwa kinyi bala'in kyau mara misaltuwa, ke da gidan sai k'amshi kuke yi. tun daga get d'in
shigowa gidannan fa na soma jiyo k'amshi. Hauwa ina son ganinki a cikin yanayi na kwalliya da
k'amshi, ina mugun son tsabta a gidana."
Aminu! Ni ka bani abinci inci yunwa nake ji. Da kanshi yaje kitchen ya d'auko kofina da plates.
Tea ya xuba mana wanda ya tawo dashi a filas. Sai wainar k'wai da biredi. Sakkowa nayi, muna
karyawa muna hirarmu har muka kammala. Gyara wajan nayi, na wanke plates da kofunan,
sannan na dawo a kwance na samu Aminu a kafet idanunshi a lumshe ya mik'omun hannu.
Shigewa jikin Aminu nayi. Yai mun kyakkyawan tarba. Sai hirarmu muke yi ta soyayya. Sai
wajejen goman safe jama'a suka soma zuwa, da k'yar na lallab'a Aminu ya fice a gidan.
Wuni nayi ina tarbar dangin Aminu, nawa dangin kad'anne su ka zo duk suna gidan Hafsa. Sai
zancan gidan Hafsa ake yi. Allah Allah nake yi dare yayi Aminu ya kaini. Da yamma Dada ta
aiko mana da tuwon shinkafa miyar taushe taji kabewa da awarar waken suya. Sai bayan Isha
Aminu ya shigo da jakar kayanshi a hannunshi. ina zaune ban tashi ba, harya iso ya zauna a
kusa dani.
"Barka da gida Hauwa. Gaskiya kinyi kyau kin kuma san makamar kamani sosai, inason
kwalliya da kunshi Hauwa.
"Aminu nifa tuntuni na shirya kai nake ta jira fa. Ya kalleni da kyau.
"Ni kike jira ai gani Hauwa."
Maganar zuwa gidan Hafsa fa."
"Ahh aini na manta, kaimun ruwan wanka in nayi saimu tafi ko?" Rai na had'e.
Ni fa Aminu bani da abun dafa ruwan Zafi. Kallona yayi, na had'e rai .
"Hauwa ko jiya dana shiga kitchen naga hita naga electiric a ciki. Ruwanne bazaki iya kaimun
ba ga wuta ga komai?"
Bai jira nace komai ba. Ya mik'e ya shige kitchen Ina zaune a wajan ya fito da ruwan zafinshi a
bokiti d'akinshi ya shige. minti goma haka sai gashi ya sake fitowa da towel a k'ugunshi. Jakar
kayanshi ya sunkuta.
Sai ga Aminu ya fito cikin adon farin yad'i wanda d'inkin ya amsheshi, ranshi a sake yace.
"Muje Hauwa." Lafaya na nad'a na d'auki takalmi da jaka wanda nazo dashi a k'afata jiya. muka
fice a gidan.
Kafin mu isa titi duk na galabaita. Aminu kuwa sai hira yake jana dashi. Wasu mata da miji ne
suka wuce ta gabanmu a k'atuwar mota. Yuuu na bisu da idanu. Har Aminu ya tare d'an sahu
ban sani ba. Ma'auratan sun d'auki hankalina sosai da sosai.
"Hauwa ko gida zamu koma, duk sanda na sai mota ma je?" Harararshi nayi, na shige cikin d'an
sahun muka wuce."
Anan k'arshen free page ya tsaya, ki biya ki samu naki 'yar uwa. Yanxu aka soma labarin Zaki
k'aru da darussan rayuwa sosai.
Nagode
Mrs Bukhari ce
_Ummu Maheer_
*DINYAR MAKAHO*
_Miss Hajo_
*KHADIJATUL SABREEN*
_Mrs Bukhari_
*ANGULU DAKAN ZABO*
_Ummu Affan_
*SANDAR MAKAUNIYA*
_Mom Islam_
*TSAUTSAYIN TAUNA*
*Ga tsarin yanda biyan yake*
_Guda d'aya 300_
_Guda biyu 500_
_Guda Ukku 700_
_Guda hudu 800_
_Guda Biyar 1k_
Kai tsaye