Angulu Da Kan Zabo Book By Badiat Ibrahim

Author :  Badiat Ibrahim Mrs Bukhari Category :  Read Hausa Novels

Chapter   7 / 14

18K to 21K   out of 40.5K words


"D'iba gashi nan, yanzu na kunna ma. Marne bata kuma kallon Inda Baba take ba balle ta tanka
mata. Wuta ta d'iba ta yi shigewarta d'aki. Can gidan ya kaure da hayak'i. Harira da Baba ne su
ka yi girki. Har d'aki Baba ta sa Harira ta kai ma Marne. Tana zaune a falo wannan karon.
"Amarya ga Abikinci." Ajjiye kwanon ta yi, Marne tace.
"Nagode" Su Sada ba su suka shigoba sai dare, bayan sun shiga d'akin Baba, daga nan kuma
kowa ya shige d'akin Amaryarshi.
A daren Marne ta dinga yi ma Sada k'orafe _k'orafe mara sa kai da gindi. Shi dai sai lallab'ata
yake yi. A daren ya mantar da'ita komai, ya samu budurcinta cikakke. Satin su guda suna cin
Amarci, a kwanakin amarcinnan Marne bata cin abinci daga nama sai shayin wajan mai tsayi da
Sada ke siyo mata. Yau ta kasance Sada zai soma fita kasuwar Kurmi dan ci gaba da
sana'arshi dai ta siyar da itacen turaruka.
"Sada yanzu zaka fita ni me zanci da rana, tunda yanxu naci ragowar balangun jiya da
daddare?"
"Haba gimbiyar Mata, ki yi hak'uri ki daure inzan dawo zan tawo miki da balango. Harararshi tayi
tace.
"Harda tsirenma inaso ka siyo mini, sai shayi Sada sai gurasar kano yau dai zanci. Dariya yai
mata kawai yace.

"uwar rigima, yau dai sai dai in Baba zaki yi ma." Had'e rai ta yi data ji ya ambaci Baba. Sallama
yai mata ya fice. D'akin Baba ya shiga.
"Baba barka da safiya, ina kwana?"
"Lafiya lau, yau zaka soma fita ko? Toh ka rik'ema wannan bawan Allah dukiya da amana.
Tunda ya amince ya baka kayanshi ka tawo dashi, ka daure ka rik'e amana har Allah ya baka
naka jarin. Kai ya sauke yace.
"Ameen Baba, ni zan wuce." Har ya mik'e tace.
"Abb dawo ka zauna ina da magana." Dawowa yayi ya zauna.
"Matarka bata tab'a zuwa ta gaisheni ba. tunda aka kawota. Tana d'aki zata jiyomu a tsakar gida
ni da Harira, amma yarinyarnan in ka ga ta fito, toh band'aki zata shiga, ko ta fito ta tone mana
itace ta d'ibi wuta. Irinfa hali da d'abi'un shuwa kenan. shi yasa mazan yarensu ne kad'ai ke iya
aurensu, ko hamshak'an masu kud'i, mugun kwad'ayin abun duniya ne dasu sosai, basu cika
yarda da talakaba. Dan daga k'auye ma ta fito kenan. Sada dai yayi shiru baice komaiba Har sai
da Baba ta gama sannan yace.
"Ki yi hak'uri Baba, zan yi mata magana zata gyara." Sallama yayi mata ya tafi.
Haka dai zaman nasu yaci gaba da gudana, kullum sai Sada ya shigo da tsire ma'ishi ya ba
Marne, dan sam bata cin abincin gidan. Gashi ta raina kowa, har fad'i in fad'e Marne ta ke yi da
Baba. Sada kuma tsabar son da yake ma Marne baya iya tsawatar mata. Sai dai yaita lallab'ata,
dan wani tsoro tsoronta yake ji. Da asuba Sada ya tashi Marne a bacci. "Marne ki tashi kije ki tsarkake jikinki sai ki yi sallah ko?"
"Toh" Kawai tace mishi, shi kuma ya fita zuwa masallaci. Ya shigo ya sameta a tsaye tana goge
jikinta. Kanta ya kalla yaga babu ruwa.
"Marne kinyi wankan tsarkin kuwa?" Dariya tayi tace.
"Ji wani tambayan renin hankali. Sada tuwo ka manna a idanunka ne?"
"Marne naga banga kanki na d'igar ruwa bane"Dubanshi ta yi tace.
"Ana wanke kaine dole Sada?" Hankalinshi ne ya tashi. hannunta ya rik'o suka zauna yace.
"Marne wanne irin wanka kikeyi in munyi mu'amalar Aure dake ne?"
"Wankan da kowa yake yi na soso da sabulu. Ya jinjina yarinta da wautar Marne sosai.
Tambayoyi ya soma yi mata a addinance. Abun mamaki bata iya komai ba, dai_dai da sallah
dungurawa kawai take yi, babu abunda take cewa. Ai a ranar Sada ya sa Marne a makarantar
Addini ta matan aure wacce take can k'asan layinsu. Ringid'i_ringid'i Marne ta soma zuwa
makaranta tana d'aukar darasi, cikin wata biyu ta haddace ixu biyu, sannan ta iya wankan tsarki
dana haida. wannan zuwa makaranta da cud'anya da mata da Marne ta soma yi, harta soma jin
hausa jifa jifa, dan ta yi k'awaye da dama, tama dena zama a gida sam Sada nasa k'afa ya fita
zata fice a gidan itama. Harira kuwa cikinta ya tsufa zama da kyar tashi da kyar, Marne ta sake
gogewa sosai, ta d'anyi k'iba da hasken sabon jinjirin ciki, irin wanda masu juna biyu ke yi. Ta
d'anyace sosai. Tana jin Hausa daidai gwargwado. Kullum Marne a cikin yawo take.


Mrs Bukhari ce


*TALLAH*

Ina kuke amare uwayen gida kai har ma da ƴan mata? Ko kun san Mrs Bukhari mai kayan
ƙamshi, ai in dai batu na kayan ƙamshi gyaran jiki da na ɗaki to kai tsaye ku ne mi Badi'at
domin gwana ce ta ko wanne fanni a ciki. "Wai ƙamshi kina nufin Badi'at dai marubuciyar nan
tamu mai nishaɗantar da mu?" "Tabbas Fati ita take magana, ai kin dai ji yadda ake magana a kai na, hatta me gidana ya
jinjinawa Badi'at domin duk wani ƙamshi da zaki ji a jikina tare da gidana to daga ita ne, ke me
kankat ma har gyara na nake yi domin gyaran aurena daga gareta ne, shi ya sa bana wasa da
gyaran jikina da na gidana har kuke kirana da ƙamshi." "Eh tabbas nima na jinjina mata, kuma zaki bani addireshinta domin nima na kwankwati wannan
garaɓasa. Ko zaki iya faɗa mini abubuwan da take sayarwa.?"
"Bari na faɗa miki akwai...

Humra
Kulacca
Sudanese Humra
Kulacca ta gashi.
Turaren wuta ɗan gaske, iri daban daban.
Turaren mopping
Room freshner
Turaren turara kaya.
Turaren wuta na toilet
Sannan akwai ingantaccen maganin infection
Ina da magungunan mata, wanda zai gyara amarya da uwar gida.
Wanda zasu shiga daga ciki kuma
Akwai sabulun amare, da dilka ta amare, wanda zaisa amarya ta fito ta haska tas
Kabbasa
Setin kujerar tsugunno
Sannan inayin turaren wuta da kasko, da ashana wanda ake rabawa a taron biki ko suna.
Ina bayar da sari.

Ma sha Allahu to taya zan sameta domin mallakar nawa?

"Kai tsaye zaki mata magana ta whatsApp ko kiranta ta wannan number.

08179523215


*TALLAH*
A yau nazo muku da manya manyan magunguna domin gyaran Auranmu! Saboda yadda
zamantakewarmu ta AURE keta kara tabarbarewa. Mata iyayenmu ku fito ku gyara jikinku ,
domin wallahi har Abadan macen da bata gyara bata isa ta hada kanta da mace me gyara ba
har abadan! Mu gane yaku yan uwana mata, ma’aurata! wallahi gyara shine mace Akwai mata
dayawa dasuka san magunguna na, a online Suna siya kuma Alhmdulillahi ba wadda ta siya

bata dawo tamin godiya ba, Alhmdulillahi!Alhmdulillahi! Alhmdulillahi! Yawancin mata dayawa
na nemana ta dayan sim dina sede nayi losing dinsa sede wannan shi yake Aiki 08104335144,
A YAU NAZO MUKU DA MAGUNGUNA INGANCI DA IZININ UBANGIJI, WATO AINIFIN HADI
Iri ~iri na MALLAKA D’ANA MIJI ALFARMAR ANNABI SAW, ina tabbatar muku da magunguna
na babu shamaki base na tsaya bata lokaci a bayaniba zanso ku gwada dan tantance GASKIYA
* Akwai cututtukan dake hana maganin mata aiki idan kinason sani ki tuntubeni ta wannan
lambar 08104335144 wadannan cututtukan inhar kinadasu wallahi duk maganin daza kisha
bazeyi Aiki ba, kuma bazaki taba fahimtar komiba a harkar dadih na magungunan mata.

*MUNADA MAGUNGUNA AVAILABLE KAMAR HAKA*

*ingantaccen maganin infection *

Ingantaccen maganin basir

Ingantaccen maganin gyaran nono

Ingantaccen maganin gyaran hips

Ingantaccen maganin kara kiba kiyi dumur~mur dake

Ingantaccen maganin rage tumbi meyi tsakani da Allah

Ingantaccen maganin matsin farji mesa dadin farji ga azzakarin d’ana miji.

Ingantaccen MALLAKA TA DOMIN ALLAH (Bata harkoki) shine sunansa, hmmmm Wannan
magani inada tabbaci a kansa shidin hadine kawai na mallakar d’ana miji akwai komi a cikinsa
na mallaka hajiya ki gwada kisha mamaki Alfarmar Annabi SAW.

Se matsin (GAMADIDI) wannan matsi in kikayi amfani dashi har abadan abidina mijinki baze
kawo a gaban wata ya mace ba in har ba gabanki bane wannan inada tabbaci a knsa kuma
wadanda suka saya ma sun kara tabbatarmin da kyaunsa na mamaki.

Akwai zallan hadi na amarya

Akwai hadi na uwar gida sarautar mata wannan seat ne akwai komi a cikinsa.

Akwai ingantattun gumba iri iri kamar haka

Akwai gumbar Madara
Akwai gumba me rubutu
Akwai gumbar kankana
Akwai gumbar giginya (sa megida kuka)

Akwai ingantacciyar gumba me suna (BARIN MAKAUNIYA)
Akwai gumbar hasi
Akwai zallar gumba wadda ita ta rubutuce zallarta zaki ganta baka karki damu Aikin kawai zaki
duba
Akwai gumbar gero
Akwai gumbar ridi
Akwai gumbar garin gamadidi ita ta mallaka ce zallarta.

Akwai tsumi iri iri sunansu sha yanzu magani yanzu

Akwai tsumin kankana
Akwai tsumin baure
Akwai tsumin rubutun Ayar Allah
Akwai tsumin kwakwa
Akwai tsumin giginya
Akwai tsumin GORON SUDAN (wannan special ne dan kudinsa ma daban yake)
Akwai ingantattun magunguna na tada shaawah kama daga na turawa har zuwa na Islamic
wato namu na gangajiya. Akwaifa maganin maza madam na hausa dana turawa duk basuda
side effects

Akwai rubutun mallaka
Akwai zoben mallaka
Akwai hayakin mallaka
Akwai zani na mallaka
Akwai hadin ci da kaza
Akwai hadin yan shillah
(Muna dafa kaji da yan shillar ma dade sauran abubuwa da dama,)
Akwai dambun nama na mata wanda ke dauke da magungunan sirri na mata mesa tsantsi da
laushi da ruwa a farjin mace

Akwai magunguna na ban mamaki wadanda base na rubutasu ba saboda SIRRI
Muna aika magungunan mu kasa kasa gari gari *UWAR GIDA KI GARZAYO QUEN SANAF
Islamic chemist kise magunguna na ingantattun ne insha Allahu kin wuce takaicin d’ANA MIJI *
direct to me 08104335144 muna sauraron masu shawarwari a kan zaman AURE insha Allahu,
amma in knsan baki shirya siyan magungunan jima’i ba na mata ko na maza pls karki kirani.
_Ummu Maheer_
*DINYAR MAKAHO*


_Miss Hajo_
*KHADIJATUL SABREEN*

_Mrs Bukhari_
*ANGULU DAKAN ZABO*

_Ummu Affan_
*SANDAR MAKAUNIYA*

_Mom Islam_
*TSAUTSAYIN TAUNA*

*Ga tsarin yanda biyan yake*

_Guda d'aya 300_
_Guda biyu 500_
_Guda Ukku 700_
_Guda hudu 800_
_Guda Biyar 1k_

Kai tsaye zaku iya turo kuɗinku ta wannan hanya.

0037219728
FATIMA RABIU SUNUSI
StanbicIBTC BANK

Shaidar biya ta nan

0810 433 5144

Masu turo kati MTN ta wannan number.

0702 616 6536

Ƴan Niger zaku turo da naku kai tsaye ta wanna number.

0706 860 6171

*Mun gode da kasancewa da gawurtattu biyar taku na biyu*
[09/12, 19:49] Badi at: GAWURTATTU BIYAR
DAGA ALK'ALAMIN
BADI'AT IBRAHIM
MRS BUKHARI (B4B)

*ANGULU*

*DA*
*KAN ZABO*
11/12

Saƙon gaisuwata zuwa gareku na hannun damana.

Maman Yaseer
Ummu nabeeha
Ummu Neehad
Maman Khairat
Oum Shuraim
Anty Hadiza Gidan Iko
Ruƙayya Ibrahim Gawata

Alkhairin Alla ya isar muku.


Na sadaukar da wannan shafin sukutum zuwa gareki ( Laila Ali Othman) Fara mai farar aniya,
baya goya marayu, masu uwa da ubanma baki barsu ba. Kin bada taki gudunmawar cikin
wannan tafiyar, ina kuma godiya da dama da kika bani.


Safiyar ranar juma'a Harira ta wayi gari da ciwon nak'uda sai fama taketa tayi, an kira mata
anguwar zoman cikin anguwar, wacce ita take karb'ar haihuwa sama da shekaru talatin a
anguwar. Ana cikin haka Marne ta fito da jakar makaranta a rataye a kafad'arta. Baba kuma ta
fito daga d'akin Harira kenan. "Marne zo ki taimaka ki had'a mun wuta kinga Harira ke nakuda zata haihu, ki ajjiye zuwa
makarantar yau kinji?" Marne ta dubi Baba a wulak'ance cikin tsiwa tace.
"Baba bazan iya barin makaranta ba, tunda mijina ne yace inje, maganar had'a wuta bazan
iyaba. Nifa ko a gida bana aikin wahala ban sababa ehe." cikin mamaki Baba ta dubi Marne
tace.
"Marne ni kike fad'ama wannan maganar a matsayina na uwar mijinki?" Gatsine Marne tayi
tace.
"Na fad'a yo haifata kika yi ni? Aikin banza iyaka kisa Sada ya sakeni Da kuwa naji dadi, dan
yanxu nafi k'arfinshi wallahi, ko da d'inma k'addarace.
"Yayi kyau Marne kin wanku kam, ya cika miki ciki da tsire da balangun da ni uwarshi bai kawo
mun naci na saka mishi Albarka ba, yanzu kin tsiyatashi da yawan buk'atu ta kai yanzu ya
koma yaron jiran shago,bakya samun balangu yanzu dole kice haka." Marne tayi tafi tayi
girgiza tace. "Au ashe kina ɗaya daga cikin iyayen mijin dake kishi da matan yaransu kenan ko?
Toh ni nafi ƙarfinki. Baba baki a buɗe tace.
"Marne ni kike yaɓama magana haka?"
"Na yaɓa, in ɗan naki ya dawo dan Allah kisa ya sake ni in huta da ƙaddararren aurenshi. Baba
ta nufi wajan murhu tana hawaye, Marne kuma ta saka kai ta fice abunta. Cikin awa hud'u

Harira ta sauka lafiya, ta samu yaronta namiji santalelen gaske. Baba ta yi farin ciki sosai da
samun jika. Ranar suna yaro yaci Sunan Sada. Bayan suna da kwana biyu aka tafi da Harira
wankan gida. Gida ya rage daga Baba sai Marne. Baba ita ke gudanar da duk wani aikin gidan,
Marne kuwa kullum bata zama sam itace yawon suna da biki, Sada kuwa ya tabbata tsoron
Marne yake yi, dan har zaginshi take yi, ta gama shanyeshi, baya iya tsawatar mata sam. Harira
ta dawo daga wankan gida, ta ci gaba da shayar da Sada, yaro sai k'iba yake yi, gashi yana
samun tsabtataccen goyo sosai. ranar wata monday da daddare nak'uda ta tasarma Marne,
Sada hankalinshi duk yabi ya tashi sosai. Sai sintiri yake yi a tsakar gida. Anguwar zoma tana
kan Marne suna fafatawa. Kafin gari ya waye ta haifi kyakkyawar d'iyarta mace, bak'a k'irin da
ita, amma fa kyakkyawar gaske mai gashi, fatarta sumul_sumul. Bayan Marne ta kintsa kanta,
jaririya an yi mata wanka. Harira ta gyara ko ina a d'akin ta bunka turaren wuta. Baba ce tai
sallama ta shiga cikin d'akin.
Sada na zaune da Jaririya a Hannunshi ya gama mata hud'uba. Baba tace.
"Sannu Marne, barka da samun kai. Hannu tasa ta karb'i yarinyar tace.
"Iko sai Allah, yarinya bata san kakanta ba amma ta d'auko bak'ar fatarshi na fulanin asali.
Babanku fa. Sada yace.
"Nima haka nace, dukkanmu farare amma Ita ta d'auko Abba. Baba tace.
"Allah ya raya ki Hauwa u, takwarata. Sunan da zaka sa mata kenan in samu takwara tun ina da
raina." Sada ya dubi Marne wacce ta turb'une ranta yace.
"Baba ai da an soma sa sunan mahaifiyar marne tukunna ko?. Hawayene suka sulalo a
kumatun Baba tace.
"Toh Babu damuwa kasa sunan mahaifiyar tata, tunda ta fika alfahari da uwarta, kai kuma
wulak'anta taka uwar kake yi." Yarinyar ta ajjiye mishi a cinyarshi ta fita. Bata ko iya gani sosai
haka ta shiga d'aki.
"Tabb d'i jan Sada ai wallahi bazai yiwu ba. Ka riga da ka yi mun alk'awarin sunan Ammi zaka
sa mun. Ka fad'ama uwarka nifa baza'a samun sunanta ba banaso. Sannan in mai aski yazo ka
fad'a mishi yai mata kaciya, sannan ya baka fatar daya yanke ka kawo mun, in adana mata
amfaninshi na nan zuwa" "Haba Marne kiyi hak'uri kinji kar ranki ya b'aci. Zanje in sameta" Ko da Sada ya je ya tunkari
Baba da wannan zancan, tas tayi mishi ta kuma koreshi. Bashi da yanda zaiyi dole yaima
yarinyar hud'uba da Hauwa. Sai ranar suna Marne da 'yan uwanta da aka tura aka fad'a musu
haihuwa, su ka ji sunan yarinya. Nanfa Marne ta dinga zage _zage a tsakar gida tana habaice
_habaice. K'awayenta ne su kai ta bata hak'uri.
Baba kuwa tana cikin d'akinta sai kuka take yi, wai ita da d'anta anason lallai sai an yi mata
k'arfa_k'arfa a kanshi. Ta yadda lallai asiri Marne ta yi ma Sada dan ko wanne irin abu Marne
tayi baya iya cewa da'ita komai. Kuma har cukumeshi take yi, wataran har sai Junaidu ya zo ya
kwaceshi. Duk irin abubbuwan da take guje mai kenan da auren matan shuwa domun su
juninsu shine mulkar miji da dukiyar daya tara, Allah ya ƙaddari Marne rabon Sada ce kawai, ga
zuria an soma had'awa. Washe gari a ka yi suyan naman suna, su Baba kuwa sai k'amshi
kawai. Marne 'yan uwanta suka wuce da'ita wankan gida ba tare da sun nemi izinin Sada ba. Da
yamma ya dawo daga aiki ya tarad d'akin a kulle. D'akin Baba ya shiga ya sameta a kwance.
"Baba ba lafiya ne?" Kallonshi tayi, taga duk ya sake sirancewa ga duhu da yayi. tace.
"Kaga irin matsalolin da nake guje maka kenan. Yanzu ka duba k'aninka yanda Harira take

mishi biyayya. Har wanki take yi mishi, amma kai sai dai ka yi ma Marne wanki duk ranar lahadi,
ni uwarka ina kallo, bak'in ciki saiya kasheni tukunna za ku ji dad'i ko? Babu komai." Shiru yayi
kawai, shi kanshi yana mai nadamar auren Marne da yayi a rayuwarshi, kuma baisan me yasa
baya iya taka mata burki ko tana fad'ama mahaifiyarshi magana ba. Shi kuwa ai babu irin d'iban
albarka da bata mishi. Dan dai ya riga ya aureta ne kawai.
"Baba ki yi hak'uri ni kaina ina mai nadamar auren Marne da nayi wallahi. Yanzun ina su ka je,
ko raka 'yan uwan nata ta yi ne?" Baba ta dubeshi tace.
"Au basu fad'a maka dama za su d'auketa wanka ba?" Da sauri ya d'ago yace.
"Wallahi babu abunda su ka ce mun Baba, tafiya da ita su ka yi?" Baki Baba ta tab'e.
"Ai kuwa sun tafi, ai yanzu sunfi rabi. Dan tun safe suka tafi. Ni dai abunda zan ce da kai shine.
Ka dage da ibada domun ban yarda da matarnan taka ba, karka dinga sake baki kana kwana
bacci, A'a rabi a gado, rabi goshinka a k'asa zai fi maka alkhairi. Nima

7 / 14