Author : Badiat Ibrahim Mrs Bukhari Category : Read Hausa Novels
zo ya same ni a kasuwa, yake sanar dani cewar iyayenshi sun ce wai bazai auri
Mardiyya ba, sakamakon Abunda Hauwa ta aikata. Kuma yace ya yafe sadakinshi ya barma ita
Mardiyyan, sabida kyautatawa. hakanne ya bani dama nace bari in yi amfani da wannan damar
in gabatar maka da kaina a matsayin manemin mardiyya mai neman auranta, izinin zuwa zance
zaka bani, ni zan zame mata gata, mijin rufin asiri." Ajjiyar zuchiya Aminu ya sauke, ya runtse
idanunshi yana sauraron bugun zuchiyarshi wanda ta tsinke yanzu. Yafi kowa sanin waye
Saminu, mutumin kirki ne Aminin arziki. Amma kuma yasan iyalinshi bata da mutunci, kuma
bata daraja Saminu, sannan Saminu mai k'aramin k'arfine sosai, dakon kaya yake yi a kasuwa,
mata biyu basu kamace shi ba sam, in yace bai amincewa Saminu ba kuma, ta yuwu ya
fahimceshi, ta yuwu yai mishi fassara mara kyau, kanshi yayi zafi, gashi ya fi son ya aurad da
Mardiyya da wuri, dan tsoro wannan duniyar take bashi. Amma ya rasa wacce amma zai yi
amfani da ita ga Aminin nashi, nisawa yayi.
"Saminu yanzu abunda nake so da kai shine ka d'an bamu lokaci daga ni har Mardiyya, yanxu
muna cikin wani yanayi na damuwa da son kad'aici. Amma ba zai gagaraba Abokina." Ajjiyar
zuchiya Saminu ya sauke ranshi fari fat kamar audiga. Wayar Aminu ce ta soma ruri, Lubabatu
ce ke kiranshi, yau kwana uku cikakku basa waya, kuma yana ganin missed calls d'inta barkatai
da messeges d'inta. Bashi da nutsuwa sam da zai iya ara mata lokacinshi, bikinsu saura kwana
tara ya rage. Idanu ya kuma lumshewa yana mai da numfashin daya jawo cikin huhunshi,
Saminu ne ya d'auki wayar.
"Assalamu Alaikum Amarya bakya laifi ko kin kashe 'ya'yan masu gida." Daga cikin wayar
Lubabatu tace.
"Saminu ni kam lafiya laifi naima Aminu daya shareni ya dena d'aukar wayata, ko dai dan
abunda ya faru da tsohuwar matarshi ne?" Saminu yace.
"Lubabatu da farko zan soma da baki hak'urine, domun tun ranar da abun ya faru ba mu zauna
ba muna ta cuku cukun ganin an gama shariar, toh kinga an kammala komai, ayi hak'uri dai."
Murmushin takaici kawai ta yi tace.
"Dama Mama ce tace in sanar muku suna so su zo jere, gobe toh shine tace in kira." Zufa ce ta
karyo ma Saminu, sai da yai nadamar d'aga wayar ma baki d'aya.
"uhm Lubabatu, za mu zo dai gidan zuwa dare koma me ake ciki zaki ji, amma akwai d'an
matsala ne."
"Matsala sabida tsohuwar matarshi ko? Dama ai nasan za'a rina. k'it ta kashe wayarta.
"Hello Hello Lubabatu!!! Shiru.
wayar ya sauke yace.
"Abokina na rok'eka da girman Allah kar a d'aga wannan bikin ka daure, nasan a rashin uwa ne
za'ayi uwar d'aki, kuma a halin da kake kad'aici bai kamaceka ba, yaushe ka rabu da deepretion
yanzu gashi zaka kuma haifarma da kanka wata damuwar, nayi imani da Allah da za'ayi ma
gwajin zuchiya yanzu haka k'ila a samu bata watsa jini a gangar jikinka yanda ya kamata." "Saminu ina gudun in kasa ba Lubabatu lokacin da zata buk'ata a gareni ne. bana son in shiga
hakkinta. Babu wata nutsuwa a tare dani, wanne aure ne? ni na fasa."
"Ah wallahi baka isaba, aure ba fashi, kar ka yi ma yarinyarnan haka Aminu." Harararshi Aminu
yayi yace.
"A d'aga toh, in samu in d'an warke, kuma yarannan kulawata sukafi buk'ata a halin yanzu."
Dada ce ta shigo hannunta rik'e da bak'ar leda. Da sauri Saminu ya je ya karb'ota.
"Sannu Dada kin dawo?" Mayafinta ta cire ta rataye a igiya. Sannan ta zauna a dokin k'ofa tace.
"Nadawo Saminu kazo gun abokin naka ko? ai gara ka taya ni yi. na rasa da me Hauwa ta
lashe mai zuchiya haka, dubi yanda ya rame ya fice a haiyacinshi, yaushe muka gama
jinyarshine ne, so yake Hauwa ta kashe shi ma huta duka dallah" Saminu yai gyaran murya
yace. "Dada ayi hak'uri dai ai duk k'ulafucin Hauwa da yake yi dole ya barta, tunda a gidan d'an kande
zata idasa rayuwarta. Duk abun ƙyamar data aikata. shi nemo mayafi yake yi a shirinshi na
lullub'e mata aibi.
"Da nasan haka aurannan zai zame mana jaraba da sam ban amince mishi ba wlh tun farko,
wacce wahala ce bai sha ba tun neman? Ashe da gaskene da akace matan shuwa mallake miji
suke yi. Gashi ta jefa rayuwar yaranta mata cikin garari, har Muktar ya fasa auran ita mardiyya,
kuma wallahi basu da laifi, bak'ar uwarta ce sila." Saminu yace.
"Dada ayi hak'uri dai wannan lamari babu dad'i. Lubabatu ta kira tana sanar da mu iyayenta
suna son su yi jere zuwa gobe. Dada tace.
"Toh babu laifi ai, fenti za'aima d'akin kawai. adashen kayan akwati da yake yi a wajan mai
adashen gata kuma. zanje in yi magana da ita zuwa goben saita had'a abunda ya samu, Allah
ya sa a dace."
"Dada ni sai nake ganin kamar a d'an d'aga bikinnan ko da wata biyu a k'ara, kinga yanxu d'an
aikin dana dogara dashi babu, shagonma an rufe, inaso dai in soma bin Saminu kasuwa in sha
Allah, toh sai nake ganin sake wannan gidan zanyi kawai, kud'in hayar gidan dubu tamanin ne,
kuma yanzu bani da halin biyan hakan." Dada ta yi shiru tana nazarinshi da kyau, tabbas ita
uwace mai son ganin 'ya'yanta a cikin walwala, bata fatan Aminu ya kuma shan wahala akan
mace kamar yanda ya sha a baya.
"Ku na ji ko Saminu, Aminu?" da
"Eh" suka amsa mata
"Aminu ka daure ka auri Lubabatu, karka fasa, nasan kana cikin halin damuwa dole. Ni zan
koma wancan d'akin da Mardiyya ta gyara musu, inda zan fitan tunda ciki biyu ne sai a yi fenti
da gyaran silin ita Lubabatun sai ta zauna anan. In dinga ganinku kusa dani d'in ai yafi mun.
Can d'in sai ka sake. dama can yafi k'arfinka 'yar gwalce ta matsa nan d'in take so. Ala tilas
Aminu ya amince ma su Dada kan abinda su ke so.
"Mardiyya na son ta kama sana'a dan dogaro da kai masa zata soma toyawa da miya na
siyarwa, amma tace in tambaya mata kai."Murmushi yayi kawai yace.
"Masa kuma? Mardiyya rigima, toh sai abunda kika ce Dada." Dada tace.
"Ah ni kam na amince kaga harna siyo mata cefane, nera dubu uku tace in kazo ka bata, a cikin
kud'in sadakin muktar dan yace ya bata duniya da lahira, shauran kuma tace ka rik'e. A aljihu
yasa hannu ya ciro dubu shida ya mik'ama Dada.
"Gashi Dada, ki bata dubu hud'u, dubu biyun kuma kwa yi cefane. Bari mu je can gidan mu
kwaso kayan su Mardiyya. Daga nan sai a siyo fenti."
"Toh Allah yayi Albarka."
"Ameen Dada" Sallama Saminu yai ma Dada, sannan suka fice sai gidansu inda Hauwa ta
zauna. Motar kaya suka hayo ta kwashe musu komatsan tsunmokaransu, daga nan suka siyo
fenti da siminti, kana suka dawo gida.
Da kyar Aminu ya daure ya sha kunu mai zafi, Fatin mami tana jikinshi sai surutai take yi
mishi,shi kuma yayi jigum yana tunanin rayuwa. Saminu kuma yana cikin d'akin Dada da suka
gama kwashe kaya. 'Yan ramukan b'era ya tottoshe,yayi ciko a k'asa inda plastan ya farfashe,
sannan yai fenti, duk shi kad'ai. "Saminu ka gama?" Saminu da ya fito duk ya had'a xufa yace.
"Na fito, lokacin Sallah yayi mu je masallaci." Tare su ka je masallaci su ka yi sallah, da yamma
kuma Saminu yasa Aminu a gaba zuwa gidansu Lubabatu.
Anguwar kurawa
LubabatuTana k'ofar gida gaban bokitin fentin kunun gyad'a dake gabanta, ga Alala cikin
k'atuwar kula, samari sun baibayeta anata siya. K'awarta Amira tace.
"La Lubabatu ga ango fa da wannan abokin nashi, maza jeki bari in sallami jama'a. Da sauri
Lubabatu ta mik'e tana yak'e, Tahowa tayi inda suka zauna a dakanin gidan nasu.
"Assalamu Alaikum" Saminu ne ya amsa mata. Aminu kuma da ido ya bita kawai. Waje ta samu
ta zauna da ladabi ta gaishesu. Lubabatu yarinya ce d'anya dan da kad'an tafi Mardiyya
shekaru. Amma ita mai garin jiki ce, dan ta na da k'iba, hakan yasa ta cika ido.
"Lubabatu kiyi hak'uri da rashin jinmu da ki ka yi, wallahi al'amuran dai ke kinsan komai, toh
amma yanzu an gama case d'in duka." Lubabatu tace.
"An yanke mata hukunci kenan Saminu?" D'an yamutse fuska Saminu yayi yace.
"An yanke mata d'aurin rai da rai, amma yanxu haka tana asibiti tana jinyar hawan jini." Wani
irin dad'ine ya lullub'e zuchiyar Lubabatu. A fili kuma sai tace."
"Kai amma abun baiyi dad'i ba gaskiya." Aminu ya dubeta yace.
"Ya su mama, ya shirye _shirye kuma?" Kallonshi tayi da soyayya tace.
"Shiri ana ta kan yi, saura k'iris in zama mallakinka." Murmushi yai mata mai burgewa yace.
"Kina farin ciki kenan?" Far tayi da ido tace.
"Sosai ma. Inda kake nan za'ayi jeren ko?"
"A'a Lubabatu, a gidanmu zamu zauna, kinga yanzu bana aiki tukunna, duk da zan soma bin
Saminu kasuwa, amma dubu tamanin ina na ganta yanzu ai da yawa. Ki fad'a musu a can
gidanmu za'a kai kayan." Shiru ta yi, ita da take shirin b'alle amarci da rayuwar shagwab'a ya
zai ce mata tare da mayaifiyarshi zata zauna, bayan gida guda ɗaya ne tak a gidan, ita da take
da burin ta dinga wanka da mijinta tare harma da irin wasan soyayya na guje gujennan. Amma
da yake Lubabatu yarinya ce mai shegen wayau da kissa irinta yaran zamani sai tace."
"Nima zan fi so in zauna kusa da Dada, da yarana ko dan in samu ladansu duka. Aminu yaji
dad'in batun Lubabatu, hakanne yasa har ya saki jiki da ita su ka tab'a hira. da zasu tafi ta d'ura
musu kunu cikin gorunan swan manya, ta xuba musu Alala kowa da kwanonshi, ta sama kowa
a leda, ta d'akko dubu biyu ta basu kud'in mota."
Jacara
Malaman da zasu rabo gadon su Jamila ne suka iso, suna tsakar gida an shinfid'a musu
tabarma. Baffa bai jima ba ya iso, Hafsa ce ta kawo takaddar da suka rubuta duk wata kadarar
da mahaifiyarsu ta mallaka, mahaifinsu gida ya bari shine wanda suke ciki. malamai suka gama
ganin komai su kai ma komai kud'i. "Toh zamu raba gadon yanxu, tana da 'yan uwane na jini ita mai rasuwar?. Malam ne yake
tambaya, Baffa yace.
"Ta na da k'anne wanda suka fito ciki d'aya su biyu, ga su nan, amma kuma iyaye basa raye.
dangi duk basa raye, sun d'an fad'a iftila'in boma bomai da su kaita tashi a Borno, da yawan
danginsu ta wannan hanyar suka mutu, sauran kuma lokacine ya cika. Nanne tace.
"Ni da 'yar uwata bamu da buk'atar gadon 'yar uwarmu, a rabe ma yaran kawai. Baffa yace.
"A'a nanne, ke dai ki bari a baku, in yaso kwa basu da hannunku. malam yace.
"Toh ita Hauwa an cireta a cikin wannan lissafin domun bata da gadon mahaifiyarta sam. Nan
malam ya shiga rabo, tsab aka raba aka ba kowa nashi. Hafsa jikinta ne ya shiga kakkarwa da
ta ga wata sark'ar gwal wanda ta tuno tabbas ta san sark'arnan toh me sark'ar take yi a wajan
mahaifiyarsu? Bata da mai bata wannan amsar, amma kuma ta had'iye mamakinta da d'aura
d'amarar bincike tuk'uru har sai ta gano bakin zaren. Da yamma kowa ya watse ya nufi gidan
Auranshi."
Saminu
Da sallama ya shiga cikin gidan nashi. Yaranshi suka nufoshi da gudu.
"Baba Baba Baba." Farida tana gaban murhu ita da Murja babbar 'yarta k'awar Mardiyya, tuwo
Farida take tuk'awa, Murja na warwara mata gari. Kawar da kai ta yi akan Saminu tare da had'e
rai. Murja tace.
"Sannu da zuwa Baba"
Kujerar tsugunno ya ja tare da zama, Aminu takwaran amininshi na mak'ale dashi, hancinshi
duk majina."
"Yauwa Murja, zo ki d'au Aminu a share mishi hanci." Farida dai bata ko sake kallon inda ya ke
ba, sai tuwanta take tuk'awa.
"Kai Musa d'auko kofi in zuba muku kunu ku sha. Farida kin gama miyar tuwanne?" Kamar
jiranshi take yi tace.
"Tunda ka bayar da kud'in miyar ba. Ko kuma shekaruna zan siyar in yi cefanen miyar ba."
Musa a guje ya je a kawo kwano da kofuna. Saminu ya zuba musu kunu ya sa musu Alala."
Murja ce ta kawo Aminu kusa da kwanon nashi, har ta juya yace.
"Zo murja ki je ki siyo kayan miya na d'ari,sai ki siyo manja na hamsin, maggin talatin, sai ki d'an
karb'o mana kullin bushsshen kifi na d'ari, yau mu d'anji zak'i ko?" Dubu d'ayar da Aminu ya
bashi ya mik'a mata, sai da ta fita ya dubi Farida yace."
"Farida me yasa baki da wani aiki daya wuce ki tsinkani a gaban yarannan. Yanxu bazan iya
samun magana me dad'i daga bakinki ba?" Harara ta watsa mishi tace.
"Ai babu wani taushi da zaka iya samu daga gareni, tun safe rabonmu da abinci, amma yanzu
daka shigo yaranka ka sani ai. Ni baka bani alalarba bare kunun." Mik'a mata gorar da kwanon
yayi, tako sa hannu ta karb'a.
"Ki rage ma Murja nata."
Yaranshi yake kallo yanda su ke cin Alalen kamar nama. Murja ce ta kawo cefanen, canjinshi ta
bashi. cikin k'ank'anin lokaci aka gama had'a komai. Tuwon aka kwashe aka xuba a faranti dan
ya huce, dan bashi da maraba da talge, iyakar garin kenan a gidan. Sai wajajen bayan isha aka
sauke tukunyar miya, d'an ragowar itacen daya saura ta d'aura ruwan wanka. Murja ta gama yi ma k'annenta shinfid'a a falo, suna zaune akan katifa suna cin tuwonsu. A
haka Farida ta shigo ta same su."
"Murja sai da safe, ni kam na gaji kwanciya zanyi. Tana gama fad'ar haka ta shige ciki."
Gadalanci
Aminu
Zaune yake a d'akin da Dada ta koma, Fatin Mami da Zarah har sun yi Bacci, Mardiyya tana
waje tana gyara shinkafar masar gobe.
"Aminu shikenan ka dena cin abinci sai kunu Ka yi hak'uri da rayuwa dan Allah ka ji ko?
Murmusawa yayi yace.
"Bakin nawa ne babu dad'i Dada. Zama ta gyara tace.
"Ni so nake yi da zai yiwu me zai hana ka koma tsohuwar sana'arka ta sai da kayan gwari, sai
ka kafa d'an teburinka a bakin titi, ni bana son dakonnan, dubi fa yanda Abokinka Saminu yanda
ya tsofe, in tsufa ya saukar mai jikinshi zai fad'a fa." Aminu ya d'ago kanshi yace.
"Toh Dada nima inata tunanin wacce sana'a zan kama tunda na d'an tara kud'ina. Amma Dada
na amshi kud'ad'e a wajan mai adashen gata, sabida hidimar asibitin Hauwa. Dada ta kalleshi
rai a b'ace tace.
"Au kai ya dace kenan ka d'auki nauyin Hauwa Aminu? Ina 'yan uwan nata, mijin Hafsa ai mai
kud'ine tunda shago gareshi babba a kasuwa na atampopi.
"Ki yi hak'uri Dada, wallahi nine naso in yi mata, dan Jamila ma da Baffa sun so a siyar da gwal
d'in ita Hauwan ayi amfani da kud'in toh nine nak'i." Zuchiya ta ja kawai tace.
"Allah ya kyauta, ni kam zan kwanta kuma."
"A tashi lafiya Dada." Mik'ewa yayi ya fita tsakar gida. Mardiyya tana zaune ta gasa tagumi tana
tunanin mahaifiyarta, Aminu ya zuba mata idanu cike da tausayawa. Har ya isa gareta bata sani
ba, sai da ya dafata.
"Mardiyya karki bari rayuwarki ta yi k'unci, ki bi mahaifiyarki da adda'a Allah ya yafe mata
kurakuranta. Maganar Muktar kuma karki sa damuwarshi ta dame ki, akwai zab'in miji da zan yi
miki, ina nazari tukunna." Rarrashinta ya dinga yi, har sai da yaga ta yi murmushi, kuma yaga
shigewarta d'aki sannan ya fita a gidan zuwa shago a waje.
*TALLAH*
Ina kuke amare uwayen gida kai har ma da ƴan mata? Ko kun san Mrs Bukhari mai kayan
ƙamshi, ai in dai batu na kayan ƙamshi gyaran jiki da na ɗaki to kai tsaye ku ne mi Badi'at
domin gwana ce ta ko wanne fanni a ciki. "Wai ƙamshi kina nufin Badi'at dai marubuciyar nan
tamu mai nishaɗantar da mu?" "Tabbas Fati ita take magana, ai kin dai ji yadda ake magana a kai na, hatta me gidana ya
jinjinawa Badi'at domin duk wani ƙamshi da zaki ji a jikina tare da gidana to daga ita ne, ke me
kankat ma har gyara na nake yi domin gyaran aurena daga gareta ne, shi ya sa bana wasa da
gyaran jikina da na gidana har kuke kirana da ƙamshi." "Eh tabbas nima na jinjina mata, kuma zaki bani addireshinta domin nima na kwankwati wannan
garaɓasa. Ko zaki iya faɗa mini abubuwan da take sayarwa.?"
"Bari na faɗa miki akwai...
Humra
Kulacca
Sudanese Humra
Kulacca ta gashi.
Turaren wuta ɗan gaske, iri daban daban.
Turaren mopping
Room freshner
Turaren turara kaya.
Turaren wuta na toilet
Sannan akwai ingantaccen maganin infection
Ina da magungunan mata, wanda zai gyara amarya da uwar gida.
Wanda zasu shiga daga ciki kuma
Akwai sabulun amare, da dilka ta amare, wanda zaisa amarya ta fito ta haska tas
Kabbasa
Setin kujerar tsugunno
Sannan inayin turaren wuta da kasko, da ashana wanda ake rabawa a taron biki ko suna.
Ina bayar da sari.
Ma sha Allahu to taya zan sameta domin mallakar nawa?
"Kai tsaye zaki mata magana ta whatsApp ko kiranta ta wannan number.
08179523215
*TALLAH*
A yau nazo muku da manya manyan magunguna domin gyaran Auranmu! Saboda yadda
zamantakewarmu ta AURE keta kara tabarbarewa. Mata iyayenmu ku fito ku gyara jikinku ,
domin wallahi har Abadan macen da bata gyara bata isa ta hada kanta da mace me gyara ba
har abadan! Mu gane yaku yan uwana mata, ma’aurata! wallahi gyara shine mace Akwai mata
dayawa dasuka san magunguna na, a online Suna siya kuma Alhmdulillahi ba wadda ta siya
bata dawo tamin godiya ba, Alhmdulillahi!Alhmdulillahi! Alhmdulillahi! Yawancin mata dayawa
na nemana ta dayan sim dina sede nayi losing dinsa sede wannan shi yake Aiki 08104335144,
A YAU NAZO MUKU DA MAGUNGUNA INGANCI DA IZININ UBANGIJI, WATO AINIFIN HADI
Iri