Author : Badiat Ibrahim Mrs Bukhari Category : Read Hausa Novels
ilimin arabi da boko ba, ya bazamu shiga masifa ba? Jahilar uwa ita tai sanadiyyar zuwanmu
duniya nonuwanta muka tsotsa muka tashi, jininta ke yawo a cikin jikinmu.
Kaico kaico. na fad'a a fili hakanne yasa Jamila farkawa.
"Yaya Hauwa kin farka? Sannu ko. Murmushi nayi mata nace
"Jamila kin kasa bacci ko, ai har abada rayuwarmu ba zata sake samun farin ciki ba. Ku yi
hak'uri da abunda na aikata. Na gwammaci da mutuwa nayi na bar wannan duniyar mai cike da
k'azamai, fasik'ai mushirikai. azzalamai. Na yarda da kalmar da hausawa ke cewa shi sharri
d'an aike ne, duk in da ka aike shi, duk nisan dad'ewa zai dawo maka, kamar haushin karene
me bin bayan me shi." Jamila ta yi wuff ta rufe mun bakina tana kuka tace.
"Yaya Hauwa ki yi shiru kar zuchiyata ta tarwatse, ji nake yi inama ba'a haifeni nazo duniya ba
dana more, da nazo duniyar inama ace na tsaya a zamanin k'uruciya mai dad'i dana more. Baki
da ishasshiyar lafiya Hauwa ki yi shiru hakanan muita jinyar zuchiyoyimu kawai. Amma
hukuncin da kika yanke yayi dai_dai a wajena ni, koni irinshi zan yanke." wata gandiroba
macece ta shigo d'akin ita da likita, a gabana Dr ya tsaya yai duk aune aunen daya dace.
"Hauwa Sada zamu sallameki ki koma firsina akwai magunguna da zamu d'auraki a kansu, duk
bayan wata guda za su dinga kawo ki asibiti muna duba lafiyarki tare da baki magunguna. Abu
na gaba ki daure ki rage yawan tunani dan zuchiyarki ta na dab da kamuwa da ciwo, ga hawan
jini da yake damunki, duk abunda kika ga ya faru a rayuwar d'an Adam daga Allah ne, rayuwar
gidan firzin ba mutuwa bace." Lumshe idanuna kawai nayi inajiyo rawar da jikina da zuchiyata
su ke yi, amma na kasa furta komai. Kunce mun hannuna aka yi daga jikin gadon, aka sake
ƙulle hannun nawa. Ruwan tea kawai na sha, shima mak'ociyarmu ce ta zubo ta bani na sha. a
hankali na sakko gandirobobinnan su sukai mun garkuwa. Jamila na biye damu har zuwa bakin
motar gidan firzin. Hafsa ce ta iso, gabana sai da ya fad'i dana kalli tashin hankalin dake
shinfid'e akan farar fuskarta. Amma bani da damar tsaiwa in saurari 'yar uwata. Inaji ina gani
aka shiga dani cikin mota da ledar magungunana. Jamila ta yi carab ta rik'e hannun Hafsa dake
k'ok'arin zubewa. Ni dai ina kallonsu har muka fice a cikin Asibitin.
"Lafiya Hafsa meke faruwa dake haka? Dr ne ya katse zancan nasu da cewa.
"Kud'in gado kune zaku biya ko yayanku ne?" Jamila ta nemi waje ta zaunar da Hafsa tukunna
tare da ajjiye basket d'in da tazo dashi gefe. Aminu ta hango yana shigowa. Ajjiyar zuchiya ta
sauke.
Hannu ya ba Dr su ka gaisa, sannan Jamila ta gaisheshi, Hafsa na zaune sai haki take fama
dashi.
"Sallamarta aka yi ne Dr? Aminu ya tambaya a kid'ime.
"Eh Aminu jikin nata yayi sauk'i babu laifi, anyi mata allurai kuma an had'a magunguna zuwa dai
wani watan zasu kawota a kuma dubata. Yanzu nake musu maganar biyan kud'ima." Aminu ya
dafe kanshi kawai shi abunda ya so shine a barta a asibitin har sai ta warware. Amma ya zaiyi
bashi da ta cewa. Bayan likita yabi zuwa ciki, ya biya duk abunda ya kamata ya fito." "Hafsa karki jefa kanki a masifa meke faruwane?" Cikin nunfarfashi Hafsa tace.
"Na riga na jefa kaina a masifa ai Jamila, wallah sai naji Yaya Hauwa ta bani sha'awa dama nice
ita, in tafi can in k'arke rayuwata hankali kwance. Kuka ta fashe dashi mara hawaye sai dai
gunji, a haka Aminu ya fito ya samesu a wajan Jamila na rarrashin Hafsa kamar wata yarinya
k'arama. A tunaninshi sabida Hauwa suka shiga wannan halin, shima taya Jamila rarrashin
Hafsa yayi. A tare suka fito kowa ya kama gabanshi.
A kasuwar 'yan kaba Aminu ya had'u da Saminu, nanne kasuwar da yake yin dakon kayan
gwari da kayan lambu."
"Yaya harka fito daga asibitin? Saminu ke tambayarshi
"Na fito, kafin inje har ma'aikatan gidan yarin sun nemi sallama an basu, banma samu damar
ganinta ba."
"Ah ke duniya, yanxu Hauwa zata k'arashe rayuwarta a gidan kurkuku,? Duniya abun tsoro ce
Aminu." Murmushi kawai Aminu yayi yace.
"Saminu Dada ta bani shawarar yin sana'ar saida kayan gwari a tebur kamar yanda nayi a
shekarun baya, abunda yasa nace zanzo wajanka kenan tunda anan wajan kake aiki, kai
kasan yanayin kayan." Murna ce ta bayyana k'arara a fuskar Saminu yace.
"Kai masha Allah da jin wannan daddad'an labarin, wallahi ni kaina da zan samu jari zan bar
wannan aikin wahalar, ko tallar kwakwa ni sai in yi. Aminu ya dubi Aminin nashi wanda yai mai
dukkan alkhairai a rayuwarshi, tun suna yara in zai fad'i Saminu ke tayar dashi da ikon Allah,
Har Ragon sunan d'anshi ya tab'a shiyarwa ya ba Aminu kud'in. A lokacin yana cikin tsananin
buk'atar kud'in, Ragon da ba'a yanka ma yaronnan ba kenan, sannan ya taɓa bashi ragon
sunan daya siya, yana jiran haihuwar Farida matarshi ta farko, shi kuma a lokacin Hauwa ta
haifa mai Mardiyya. Ajjiyar Zuchiya ya sauke, yasa hannu a ajjihu ya zaro dubu goma, ya raba
ta biyu ya mik'ama Saminu dubu biyar, cikin tuhuma Saminu yace.
"Meye kuma wannan?"
"Kai dai karb'a abokina. Hannu yasa ya amsa yana sauraron me Aminu zai ce mai.
"Dubu biyar ce ka ja jari, shawara ka sari lemo da kankana ka kafa teburi a kusa da nawa, ni ina
da teburina a gida, nima zan sari gwari ta dubu biyar." Hawayene suka sulalo a kumatun
Saminu yayi yink'urin yima Aminu godiya amma fur ya hana shi."
"Haba Saminu kafa huce haka guna, Amini kake a wajena, k'ila kuma siriki. Dariya suka saka
harda tafawa.
"Yanxu abunda za'ayi teburi zamu bazama nema, muje wajan kafintoci muga ya za'ayi, sai mu
nemi inda ya dace kuma mu rok'a mu kafa teburin namu, in yaso zuwa gobe da sassafe kai kayi
'yan lemo na'ibawa, ni kuma inyo 'yan kaba, ma had'e a wajan sana'a." Hakan kuwa akayi, gari
suka shiga dan neman inda yayi fuskar jama'a dan su nemi alfarma su kafa teburansu. Amma
sun wahala gashi ba'a samu ba, sai bakin titin Galadanci dai layin su Aminu anan suka samu
aka amince musu gindin wata bishiya. Sannan suka nufi wajan kafintoci nanma aka yi teburi,
suka kawo gindin bishiyarnan kowa ya kafa nashi.
Mardiyya kuwa, ta jima a gaban kaskon masarta kafin ta k'are, har mai k'osan kusa da'ita ta
kammala kasuwancinta ta tafi gida, ita tana zaune masa bata k'areba, sai wajajen sha d'ayan
rana ta k'are. ta tattara inata inata ta tafi gida.
Hauwa
Gidan yarin Kurmawa
motarmu ce ta shiga gidan yarin. Ahankali gandirobobinnan suka taimaka mun na fito, wani irin
sanyi da jiri ke damuna. kai tsaya aka wuce dani block d'inmu cikin d'akinmu. Babu kowa a cikin
d'akunan baki d'aya, kuma banga kowa a cikin yadin ba. Bayan na zauna a gadona saina dubi
gandiroba guda nace. "Dan Allah ina 'yan uwana suka je, naga babu kowa?" Saida ta mik'amun ledar maganina na
amsa sannan tace.
"Yanzu lokacin d'aukar karatune, wad'anda basu da ra'ayin karatun kuma suna d'akin koyon
sana'a dan dogaro da kai." Idanuna da suke mun yaji na lumshe, bance mata komai ba.
"Ki daure kisha magungunanki sai ki kwanta." Kai kawai na d'aga mata, kwanciya nayi dan
bana buk'atar tsawon rayuwa balle har in samu lafiya, addu'ata da fatana shine Allah ya d'au
rayuwata in huta. Nan rayuwarmu ta soma dawomun turyan turyan a kaina. Da tunanin dama
hannun agogo zai iya komawa baya da ba haka zan kasance ba, duk da bawa baya wuce
k'addarshi a rayuwa.
*Asalin labarina da ahalina*
*TALLAH*
Ina kuke amare uwayen gida kai har ma da ƴan mata? Ko kun san Mrs Bukhari mai kayan
ƙamshi, ai in dai batu na kayan ƙamshi gyaran jiki da na ɗaki to kai tsaye ku ne mi Badi'at
domin gwana ce ta ko wanne fanni a ciki. "Wai ƙamshi kina nufin Badi'at dai marubuciyar nan
tamu mai nishaɗantar da mu?" "Tabbas Fati ita take magana, ai kin dai ji yadda ake magana a kai na, hatta me gidana ya
jinjinawa Badi'at domin duk wani ƙamshi da zaki ji a jikina tare da gidana to daga ita ne, ke me
kankat ma har gyara na nake yi domin gyaran aurena daga gareta ne, shi ya sa bana wasa da
gyaran jikina da na gidana har kuke kirana da ƙamshi." "Eh tabbas nima na jinjina mata, kuma zaki bani addireshinta domin nima na kwankwati wannan
garaɓasa. Ko zaki iya faɗa mini abubuwan da take sayarwa.?"
"Bari na faɗa miki akwai...
Humra
Kulacca
Sudanese Humra
Kulacca ta gashi.
Turaren wuta ɗan gaske, iri daban daban.
Turaren mopping
Room freshner
Turaren turara kaya.
Turaren wuta na toilet
Sannan akwai ingantaccen maganin infection
Ina da magungunan mata, wanda zai gyara amarya da uwar gida.
Wanda zasu shiga daga ciki kuma
Akwai sabulun amare, da dilka ta amare, wanda zaisa amarya ta fito ta haska tas
Kabbasa
Setin kujerar tsugunno
Sannan inayin turaren wuta da kasko, da ashana wanda ake rabawa a taron biki ko suna.
Ina bayar da sari.
Ma sha Allahu to taya zan sameta domin mallakar nawa?
"Kai tsaye zaki mata magana ta whatsApp ko kiranta ta wannan number.
08179523215
*TALLAH*
A yau nazo muku da manya manyan magunguna domin gyaran Auranmu! Saboda yadda
zamantakewarmu ta AURE keta kara tabarbarewa. Mata iyayenmu ku fito ku gyara jikinku ,
domin wallahi har Abadan macen da bata gyara bata isa ta hada kanta da mace me gyara ba
har abadan! Mu gane yaku yan uwana mata, ma’aurata! wallahi gyara shine mace Akwai mata
dayawa dasuka san magunguna na, a online Suna siya kuma Alhmdulillahi ba wadda ta siya
bata dawo tamin godiya ba, Alhmdulillahi!Alhmdulillahi! Alhmdulillahi! Yawancin mata dayawa
na nemana ta dayan sim dina sede nayi losing dinsa sede wannan shi yake Aiki 08104335144,
A YAU NAZO MUKU DA MAGUNGUNA INGANCI DA IZININ UBANGIJI, WATO AINIFIN HADI
Iri ~iri na MALLAKA D’ANA MIJI ALFARMAR ANNABI SAW, ina tabbatar muku da magunguna
na babu shamaki base na tsaya bata lokaci a bayaniba zanso ku gwada dan tantance GASKIYA
* Akwai cututtukan dake hana maganin mata aiki idan kinason sani ki tuntubeni ta wannan
lambar 08104335144 wadannan cututtukan inhar kinadasu wallahi duk maganin daza kisha
bazeyi Aiki ba, kuma bazaki taba fahimtar komiba a harkar dadih na magungunan mata.
*MUNADA MAGUNGUNA AVAILABLE KAMAR HAKA*
*ingantaccen maganin infection *
Ingantaccen maganin basir
Ingantaccen maganin gyaran nono
Ingantaccen maganin gyaran hips
Ingantaccen maganin kara kiba kiyi dumur~mur dake
Ingantaccen maganin rage tumbi meyi tsakani da Allah
Ingantaccen maganin matsin farji mesa dadin farji ga azzakarin d’ana miji.
Ingantaccen MALLAKA TA DOMIN ALLAH (Bata harkoki) shine sunansa, hmmmm Wannan
magani inada tabbaci a kansa shidin hadine kawai na mallakar d’ana miji akwai komi a cikinsa
na mallaka hajiya ki gwada kisha mamaki Alfarmar Annabi SAW.
Se matsin (GAMADIDI) wannan matsi in kikayi amfani dashi har abadan abidina mijinki baze
kawo a gaban wata ya mace ba in har ba gabanki bane wannan inada tabbaci a knsa kuma
wadanda suka saya ma sun kara tabbatarmin da kyaunsa na mamaki.
Akwai zallan hadi na amarya
Akwai hadi na uwar gida sarautar mata wannan seat ne akwai komi a cikinsa.
Akwai ingantattun gumba iri iri kamar haka
Akwai gumbar Madara
Akwai gumba me rubutu
Akwai gumbar kankana
Akwai gumbar giginya (sa megida kuka)
Akwai ingantacciyar gumba me suna (BARIN MAKAUNIYA)
Akwai gumbar hasi
Akwai zallar gumba wadda ita ta rubutuce zallarta zaki ganta baka karki damu Aikin kawai zaki
duba
Akwai gumbar gero
Akwai gumbar ridi
Akwai gumbar garin gamadidi ita ta mallaka ce zallarta.
Akwai tsumi iri iri sunansu sha yanzu magani yanzu
Akwai tsumin kankana
Akwai tsumin baure
Akwai tsumin rubutun Ayar Allah
Akwai tsumin kwakwa
Akwai tsumin giginya
Akwai tsumin GORON SUDAN (wannan special ne dan kudinsa ma daban yake)
Akwai ingantattun magunguna na tada shaawah kama daga na turawa har zuwa na Islamic
wato namu na gangajiya. Akwaifa maganin maza madam na hausa dana turawa duk basuda
side effects
Akwai rubutun mallaka
Akwai zoben mallaka
Akwai hayakin mallaka
Akwai zani na mallaka
Akwai hadin ci da kaza
Akwai hadin yan shillah
(Muna dafa kaji da yan shillar ma dade sauran abubuwa da dama,)
Akwai dambun nama na mata wanda ke dauke da magungunan sirri na mata mesa tsantsi da
laushi da ruwa a farjin mace
Akwai magunguna na ban mamaki wadanda base na rubutasu ba saboda SIRRI
Muna aika magungunan mu kasa kasa gari gari *UWAR GIDA KI GARZAYO QUEN SANAF
Islamic chemist kise magunguna na ingantattun ne insha Allahu kin wuce takaicin d’ANA MIJI *
direct to me 08104335144 muna sauraron masu shawarwari a kan zaman AURE insha Allahu,
amma in knsan baki shirya siyan magungunan jima’i ba na mata ko na maza pls karki kirani.
_Ummu Maheer_
*DINYAR MAKAHO*
_Miss Hajo_
*KHADIJATUL SABREEN*
_Mrs Bukhari_
*ANGULU DAKAN ZABO*
_Ummu Affan_
*SANDAR MAKAUNIYA*
_Mom Islam_
*TSAUTSAYIN TAUNA*
*Ga tsarin yanda biyan yake*
_Guda d'aya 300_
_Guda biyu 500_
_Guda Ukku 700_
_Guda hudu 800_
_Guda Biyar 1k_
Kai tsaye zaku iya turo kuɗinku ta wannan hanya.
0037219728
FATIMA RABIU SUNUSI
StanbicIBTC BANK
Shaidar biya ta nan
0810 433 5144
Masu turo kati MTN ta wannan number.
0702 616 6536
Ƴan Niger zaku turo da naku kai tsaye ta wanna number.
0706 860 6171
*Mun gode da kasancewa da gawurtattu biyar taku na biyu*
mrs Bukhari ce
[09/12, 19:49] Badi at: GAWURTATTU BIYAR
DAGA ALK'ALAMIN
BADI'AT IBRAHIM
MRS BUKHARI (B4B)
*ANGULU*
*DA*
*KAN ZABO*
GAWURTATTU BIYAR ✋
3/4
A daidaita sahun su Mardiyya ne ya sauke su a bakin titin anguwar galadanci, ta ja hannun
k'annenta suka soma takawa.
"Anty mardiyya Mami tana gidan su Dada ne itama?" Cewar Fatima k'aramar k'anwarsu mai
shekara bakwai Zara'u me shekara goma sha biyu tace."
"Fatin mami, Mami bata nan ta yi tafiya ba yanzu zata dawo ba" Mardiyya me shekara goma
sha shida. babbar 'ya a wajan Hauwa da Aminu ta kasa cewa komai, sai had'id'iye kuka take yi."
"Mardiyya" Dam gabanta ya fad'i data jiyo amon muryar Muktar wanda tun sanda abun ya faru
take wasan b'uya dashi. Cak ta tsaya, Zara'u kuma ta kama hannun Fatima suka soma gaba,
bayan sun gaishe da Muktar.
Gefe guda Mardiyya da Muktar suka samu, a gefen wani d'an dakali suka zauna."
"Ya k'arin hak'urinmu kuma Mardiyya?" A mugun tsarge tace.
"Mungode Allah, ina yini muktar." Idanu ya lumshe ya na jin sonta na nunkuwa a zuchiyarshi.
mardiyya yarinyace mai nutsuwa da shegewa rai ta yi daram, sabida kyawawan d'abiunta da su
kai mata k'awa.
"Lafiya lau Mardiyya, yaya ake ciki maganar case d'in Mami?" Kai ta sauke ta soma kuka k'asa
_k'asa. Kallonta yayi cikin tausayawa yace."
"Ya isa daina kukan Mardiyya kinji ko? Dama wata magana na zo miki da shi, wanda ya dace
ace kin ji tun wuri, sai dai bamu samu damar keɓewa ba sai yau. Amma ki mun uziri ba laifina
bane." Da sauri ta d'ago idanuwanta sharkab da ruwan hawaye, tace."
"Iyayenka sun janye maganar Aurenmu ko, a sakamakon abunda mami ta aikata ko Muktar?
Wani malolo ta had'iye mu'kut. taci gaba da ajjiyar zuchiya.
"Eh Mardiyya hakane, wallahi sun matsa akan lallai sai dai in hak'ura da auranki..." Saurin
dakatar dashi tayi, ta hanyar d'aga mishi hannu, shiru yayi ya zuba mata idanu. Hak'ik'a ya
gasgata son da Mardiyya take yi mishi, kuma ya gamsu da ita a matsayin uwar 'ya'ya. Amma ya
zaiyi iyayenshi, da mahaifiyar Mardiyya sun sa shi a uku." "Na ji Muktar na fahimta, Muktar bazan mutu ba in ka rabu dani. A halin yanzu nafi son in zauna
in kula da k'annena in basu kariya kuma." Mik'ewa tayi ta soma tafiya ta share hawayenta tas.
"Mardiyya ki tsaya kiji dan Allah." Ko waige ta kasa yi, sai sauri take ta zubawa bata ko iya
ganin gabanta. Hannunta yayi maza ya rik'e a zafafe ta juyo tare da fisge hannunta.
"Meye Muktar. kafison kaga na sume ko na mutu sabida ka rabu dani ko? Toh bazan mutu ba,
hakan ma dama ya bani da zan ci gaba da karatuna, kuma in kama sana'a. Sadakinka ka turo
a karb'ama abunka." A marairaice yace.
"Wallahi Mardiyya na bar miki duniya da lahira." Murmushin takaici Mardiyya ta yi mishi tace."
"Nagode" Tafiyarta ta yi ta barshi a wajan.
A guje ta shiga cikin gidan tana isa kan tabarmar da ta ga su Dada a zaune ta hau, ta fashe da
wani irin mugun kuka mai shesshek'a. Dada ta bar kwad'on garin rogon da take yi ta ce.
"Menene ya faru Mardiyya, an yanke ma Hauwa hukuncinne? Kallon su Zara'u Dada ta yi tace."
"Zara'u d'auki kwad'onnan ku shiga ciki, ki d'iban muku naku, saiku rufema yayarku sauran.
Saida taga su Zara'u sun shiga ciki sannan ta kuma duban mardiyya tace."
"Mardiyya fad'amun menene?" Cikin muryar kuka tace.
"Dama Muktar ne wai iyayenshi su ka ce bazai aure ni ba, sun fasa. Mami kuma an yanke mata
hukuncin d'aurin rai da rai." Sallallami Dada ta shiga yi, tare da tafa hannayenta biyu tace.
"Ni haihuwar fulani, Hauwa ta jawo muku abun fad'en da har abada ba'a dena fad'e ba. Gaku
yara mata." mardiyya ta dubi Dada tace.
"Ni Dada inaso in ci gaba da karatuna, sannan ki rok'amun Abba ko da waina in