Angulu Da Kan Zabo Book By Badiat Ibrahim

Author :  Badiat Ibrahim Mrs Bukhari Category :  Read Hausa Novels

Chapter   10 / 14

27K to 30K   out of 40.5K words

ingantaccen maganin infection
Ina da magungunan mata, wanda zai gyara amarya da uwar gida.
Wanda zasu shiga daga ciki kuma
Akwai sabulun amare, da dilka ta amare, wanda zaisa amarya ta fito ta haska tas
Kabbasa
Setin kujerar tsugunno
Sannan inayin turaren wuta da kasko, da ashana wanda ake rabawa a taron biki ko suna.
Ina bayar da sari.

Ma sha Allahu to taya zan sameta domin mallakar nawa?

"Kai tsaye zaki mata magana ta whatsApp ko kiranta ta wannan number.

08179523215


*TALLAH*
A yau nazo muku da manya manyan magunguna domin gyaran Auranmu! Saboda yadda
zamantakewarmu ta AURE keta kara tabarbarewa. Mata iyayenmu ku fito ku gyara jikinku ,
domin wallahi har Abadan macen da bata gyara bata isa ta hada kanta da mace me gyara ba
har abadan! Mu gane yaku yan uwana mata, ma’aurata! wallahi gyara shine mace Akwai mata
dayawa dasuka san magunguna na, a online Suna siya kuma Alhmdulillahi ba wadda ta siya
bata dawo tamin godiya ba, Alhmdulillahi!Alhmdulillahi! Alhmdulillahi! Yawancin mata dayawa
na nemana ta dayan sim dina sede nayi losing dinsa sede wannan shi yake Aiki 08104335144,
A YAU NAZO MUKU DA MAGUNGUNA INGANCI DA IZININ UBANGIJI, WATO AINIFIN HADI
Iri ~iri na MALLAKA D’ANA MIJI ALFARMAR ANNABI SAW, ina tabbatar muku da magunguna
na babu shamaki base na tsaya bata lokaci a bayaniba zanso ku gwada dan tantance GASKIYA
* Akwai cututtukan dake hana maganin mata aiki idan kinason sani ki tuntubeni ta wannan

lambar 08104335144 wadannan cututtukan inhar kinadasu wallahi duk maganin daza kisha
bazeyi Aiki ba, kuma bazaki taba fahimtar komiba a harkar dadih na magungunan mata.

*MUNADA MAGUNGUNA AVAILABLE KAMAR HAKA*

*ingantaccen maganin infection *

Ingantaccen maganin basir

Ingantaccen maganin gyaran nono

Ingantaccen maganin gyaran hips

Ingantaccen maganin kara kiba kiyi dumur~mur dake

Ingantaccen maganin rage tumbi meyi tsakani da Allah

Ingantaccen maganin matsin farji mesa dadin farji ga azzakarin d’ana miji.

Ingantaccen MALLAKA TA DOMIN ALLAH (Bata harkoki) shine sunansa, hmmmm Wannan
magani inada tabbaci a kansa shidin hadine kawai na mallakar d’ana miji akwai komi a cikinsa
na mallaka hajiya ki gwada kisha mamaki Alfarmar Annabi SAW.

Se matsin (GAMADIDI) wannan matsi in kikayi amfani dashi har abadan abidina mijinki baze
kawo a gaban wata ya mace ba in har ba gabanki bane wannan inada tabbaci a knsa kuma
wadanda suka saya ma sun kara tabbatarmin da kyaunsa na mamaki.

Akwai zallan hadi na amarya

Akwai hadi na uwar gida sarautar mata wannan seat ne akwai komi a cikinsa.

Akwai ingantattun gumba iri iri kamar haka

Akwai gumbar Madara
Akwai gumba me rubutu
Akwai gumbar kankana
Akwai gumbar giginya (sa megida kuka)
Akwai ingantacciyar gumba me suna (BARIN MAKAUNIYA)
Akwai gumbar hasi
Akwai zallar gumba wadda ita ta rubutuce zallarta zaki ganta baka karki damu Aikin kawai zaki
duba
Akwai gumbar gero
Akwai gumbar ridi

Akwai gumbar garin gamadidi ita ta mallaka ce zallarta.

Akwai tsumi iri iri sunansu sha yanzu magani yanzu

Akwai tsumin kankana
Akwai tsumin baure
Akwai tsumin rubutun Ayar Allah
Akwai tsumin kwakwa
Akwai tsumin giginya
Akwai tsumin GORON SUDAN (wannan special ne dan kudinsa ma daban yake)
Akwai ingantattun magunguna na tada shaawah kama daga na turawa har zuwa na Islamic
wato namu na gangajiya. Akwaifa maganin maza madam na hausa dana turawa duk basuda
side effects

Akwai rubutun mallaka
Akwai zoben mallaka
Akwai hayakin mallaka
Akwai zani na mallaka
Akwai hadin ci da kaza
Akwai hadin yan shillah
(Muna dafa kaji da yan shillar ma dade sauran abubuwa da dama,)
Akwai dambun nama na mata wanda ke dauke da magungunan sirri na mata mesa tsantsi da
laushi da ruwa a farjin mace

Akwai magunguna na ban mamaki wadanda base na rubutasu ba saboda SIRRI
Muna aika magungunan mu kasa kasa gari gari *UWAR GIDA KI GARZAYO QUEN SANAF
Islamic chemist kise magunguna na ingantattun ne insha Allahu kin wuce takaicin d’ANA MIJI *
direct to me 08104335144 muna sauraron masu shawarwari a kan zaman AURE insha Allahu,
amma in knsan baki shirya siyan magungunan jima’i ba na mata ko na maza pls karki kirani.
_Ummu Maheer_
*DINYAR MAKAHO*


_Miss Hajo_
*KHADIJATUL SABREEN*


_Mrs Bukhari_
*ANGULU DAKAN ZABO*

_Ummu Affan_
*SANDAR MAKAUNIYA*

_Mom Islam_
*TSAUTSAYIN TAUNA*

*Ga tsarin yanda biyan yake*

_Guda d'aya 300_
_Guda biyu 500_
_Guda Ukku 700_
_Guda hudu 800_
_Guda Biyar 1k_

Kai tsaye zaku iya turo kuɗinku ta wannan hanya.

0037219728
FATIMA RABIU SUNUSI
StanbicIBTC BANK

Shaidar biya ta nan

0810 433 5144

Masu turo kati MTN ta wannan number.

0702 616 6536

Ƴan Niger zaku turo da naku kai tsaye ta wanna number.

0706 860 6171

*Mun gode da kasancewa da gawurtattu biyar taku na biyu*
[09/12, 19:49] Badi at: GAWURTATTU BIYAR
DAGA ALK'ALAMIN
BADI'AT IBRAHIM
MRS BUKHARI (B4B)

*ANGULU*
*DA*
*KAN ZABO*
13/14
Mardiyya ce ta shiga gida da sallama d'auke a bakinta. Su Zara'u ne suka amsa mata Dada
tana zaune ta zabga tagumi sai tunanin Aminu take yi. Mardiyya ta k'araso ta dafata.
"DAda, ku dena wannan tunane_tunanen dan Allah, hakan zai iya sake jefamu a wani halin

kuma fa Dada. Ajjiyar zuchiya Dada ta sauke tace.
"Mardiyya Abbanku ne yake bani tausayi Sosai, nasan rashin mahaifiyarku bazai bari ya samu
nutsuwar data dace ba. Amma zanyi k'ok'arin kawar da damuwata ko dan farin cikin ku.
Murmushi tayi tace.
"ya masa ta k'are?" Dariya nayi nima.
"Tak'are tas, kinga cinikin da akayi duka." Amsar kud'in tayi ta k'irga tana dariya tace.
"Ai kuwa an samu har ribar d'ari bakwai, ina laifi. Yanxu abunda nake so dake, ki shiga nan
gidan k'awata Gwamma ki sanar mata, cewar nace in jini tazo. Masu gere wai za su zo yau.
"Toh Dada, dan Allah Dada inna dawo zamu je gidansu Murja ni da su Zara'u.
"Babu komai Mardiyya, daga nan saiki shiga kasuwa, ki yi siyayyan kayan masa."
Mardiyya bata jima ba ta je ta dawo daga aikenta.
wanka ta yi, ta sanya kaya, hijabine yadi uku a jikinta. K'annenta ta kama su kaima Dada
sallama. A lokacin tana gaban murhu zata aza tukunyar girkin 'yan jere.

Gidan Saminu:
Murja! Murja!! Farida ce a tsaye da mayafi a kanta, jikinnan nata duk datti, k'afarta duk jirwaye.
Murja ta amsa da k'arfi. Da sauri ta iso.
"umma fita zaki yi wai?".
"Ba nisa zanyi ba Murja gidan 'yar sokoto zan shiga. Bazan jima ba. Ga d'ari biyar, ayo fenane,
kayan miya na d'ari. maggi na d'ari, sai a siyo taliya leda d'aya, itacen hamsin. D'ari biyar ta
mutu. Ina da gari da k'uli ku yi kwado ku ci, taliyar ta rana ce inna dawo zan dafa, kayan miyar
da maggin da yai ragowa dashi zanyi miyar dare, zan shigo da manja. Fita tayi bazar _bazar ta
bar Murja anan a tsaye. Da safennen ace kwadon gari za su ci. Haka ta ja k'annenta tai musu
kwad'onnan su ka ci. ta mayar da sauran garin. Sannan ta soma gyaran gidan. Tana zaune har
rana mahaifiyarsu bata dawo ba, kwatsam ta jiyo muryar Mardiyya da su Fatin Ammi.
"wayyo k'awata kece da tsakar ranar nan?" Mardiyya tace.
"wallahi ke dai bari k'awata nazo ne in d'anji sanyi a raina." Murja ta ja hannun Mardiyya su ka
shiga ciki. Zama su ka yi a k'asa.
"K'awata kasa zuwa nayi ta'aziyya wallahi, na shiga tashin hankali matuk'a da abunda Ammi ta
aikata wallahi. Yanzu yaya ake ciki?" Mardiyya tace.
"Ke dai ki bari da ciwo fa, yanzu haka ai an yanke mata hukuncin d'aurin rai da rai ma. Gashi
Muktar ya fasa aure na, duk irin son da muke ma juna Murja Amma ya fasa, harma ya Samu
Abbanku a kasuwa ya sanar mishi, bayan tarata a titi da yayi."
"Na shiga uku Mardiyya, sabida abunda ya farunne yasa ya fasa aurenki?" Hawayene suka ciko
idanun Mardiyya, ta d'an tab'a kuka mara yawa. Sannan suka koma hirarsu ta matasa. Babu
walwala a tare da Mardiyya sam.

Farida
Da sallama ta shiga gidan 'yar sokoto mai maganin mata, matan anguwar suna yawan zuwa a
kai a kai. Gulma iri _iri a gidan ake shukata har tayi tsiro. Ko wacce mace ta baro gidanta bata
ko gyara ba, amma ta tawo yawon tsegumi.
"Uwar Murja, yanzu fa nake maganarki a falonnan, nace ban jiki ba yau. Ashe ina tafe." Shewa
mata suka saka, Farida tace.

"Ke dai bari 'yar sokoto ni da jiya maganinki ya kusan hanani bacci. Zane ta yaye ta zauna a
tsakiyar falon. Maman Saifullahi mak'ociyarsu tace.
"Kamarya fa maman Murja?" 'Yar sokoto tace.
"Shine nima na tsagu in ji kanun labarai. Farida tace.
"Uhmm ni da jiya na damu Baban Murja da lalurata, dama yaya nake balle na sha magani, a
daren sai da mu ka yi kaca kaca dashi, na fitineshi. Da k'yar nai bacci. Ni maganin ni'ima kawai
yau zan sha." Maman Zainab tace.
"Shi yasa fa har yanzu Baban Murja ya kasa yi miki kishiya, bakya wasa da kayan mata. Dariyar
jin dad'i tayi tace.
"Amma a banza, tunda ba za'ace maka anji dad'i ba, saidai kaga alama. kullum ni kuma a narka
kud'ina nake." Maman Saifullahi tace.
"Ina Maman Murja ki turke 'yar sokoto ta baki wannan wanda nace miki na yi amfani dashi. Nera
dubu goma Baban Saifullahi ya bani, banma san da kud'inba." Hannaye Farida ta tafa tace.
"A bani bashi 'yar sokoto kinsan ina biyan bashi. 'Yar sokoto ba tai musu ba ta d'ebo wani ruwa
mai yauk'i a cikin gora ta mik'ama Farida tace.
"wannan shi ake kira da mazari, zan barki kya bani labari da kanki, zaki samu kud'i a wajan me
gida Hajiya. Farida ta karb'a ta kurb'e. 'yar sokoto tace.
"Dubu biyar kika kurb'e a take." Tsurewa Farida tayi da ta ji rikicin data b'alloma kanta. Duk
siyan magungunanta bata wuce d'ari uku, d'ari biyar. "Yar sokoto tace.
"Da zaki had'a da wannan ki sha, yau kam zaki dawo tamkar amarya tsabar dad'i. Amma dubu
uku yake shi kuma. Farida tace.
"Bani bazai gagaraba, zan kawo miki shaddar dana samu a cikin kayan sunan autana, sai ki yi
mata kud'i, in tayi kud'in magungunan shikenan, in basu yi ba, zan k'ara miki da atampa."

Galadanci
Dada da k'awarta Gwamma da k'anwar Aminu Tahira. wacce tazo bayan fitar su Mardiyya, bata
ma san da zancan jeren ba sam. Suna gama abincin Masu jere su ka iso. Mata ne suka shigo
da sallama, nan aka tarbesu cikin girma da mutunci. Tahira ce ta nuna musu d'akin Amaryar.
Nan suka soma jere, ledar ruwan pure water Tahira ta kai musu, sannan ta dawo ta kai musu
shinkafa da miyar kazar da su ka yi, tare da kwanuka. Sun yaba sosai, a matsayinsu na masu
k'aramin k'arfi. Babu laifi Lubabatu ta samu kaya dai_dai na yaranmu na talakawa, dan komai
mai arhar kud'i aka sai mata. D'aki yayi kyau sosai da sosai, basu wani jima ba suka kammala.
Da za su tafi kuma su ka ba Tahira keyn d'akin akan a ajjiye. Sannan su kai musu sallama su ka
tafi." Tahira ta shigo da kular da aka zuba musu abincin da kwanon miyar duka. Gwamma bata
jima ba tai musu sallama ta koma gida.
"Tahira ya mai gidan naki? Tace.
"Toh sai dai godiya kawai Dada, dan bana iya gane mishi sam, infa yaso dukana haka dai zaita
jibgata ina ihu, kuma mahaifiyarshi tana ji Dada. Dada ta had'iye wani takaici da bak'in ciki tace.
"Tasi'u ya sammace mune kawai yai mana angulu da kan zabo, in ba haka ba me zai sa ki auri
mashayin giya madoki, ga yunwa ga takaici. Ni inaganin gaskiya tura ta kusan zuwa bango. Ni
banaso auranki ya mutu ne Ki dawo gida ki fitini kanki da tunanin 'ya'ya, kuma zawarcin ba dad'i
bane dashi shima. Kina gani a cikin gidan muma fama muke yi. Tahira ki ta hak'uri. Hawaye ta
share dama tasan zancan Dada baya wuce ayi hak'uri, su iyaye sai sunga ka fad'i ranga _ranga

ka mutu. Ko kuma ciwon zuchiya ya rabkekq. sannan kuma su sake shiga wata sabuwar
damuwar. "Dada mai makon a dak'ile abun tun yanzu, yara biyu kawai muka haifa dashi Dada,
kuma sharia ta bani damar in kula da yarana, ni ina tsoron abinda kaje kazo a gabane, amma
gara aima tubkar hanci. Dada tace. "Ki d'an dad'a hak'uri dai Tahira mu bashi lokaci, kinga yanxu ko kin kwaso jiki kin dawo gida da
yara, babu ɗakin da za ku zauna.
"Dada ga shagon Yaya Aminu, ba sai in koma ciki ba, tunda aure zaiyi, zan bari in na tawo bikin
sai in yi zamana, zai biyoni da takaddata, ko in sashi a kotu. Dada tace.
"Ki dai dakata tukunna nifa karkije ki kaso auranki Tahira. Ki dad'a hak'uri nace. Ki nemi kwano
ki zuba shinkafa da miya in kinje gidan kwaci, ke da 'ya'yan naki." Tahira tana kuka ta fita a cikin
gidan, a cikin tashin hankali take a gidan aure, duk bayanta a farfashe suke, kullum sai Tasi'u ya
daketa,ga aman giya da yake yi mata, wani sa'in har fitsarin kwance ya ke yi mata."
"Hafsa wai shin me yake faruwa ne, kink'i cemun komai nifa kin barni a duhu. Cikin kukan fitar
haiyaci Hafsa tace ma d'an sahu.
"Malam ka fara kaimu D'anladi na sidi. Daga nan sai mu wuce kasuwa, daga k'arshe ka sauke
mu a jacara." Mai d'an sahu ya amsa mata da "Toh" Jamila a cikin tashin hankali da rikici take
mai tarin yawa, zuchiyarta cike da nadamar rayuwa, bata san ma ta ina zata soma rok'on
afuwar mijinta ba, domun yayi hak'uri da'ita sosai. Hafsa kuwa ajjiyar zuchiya take ta faman
saukewa. Babu mai cewa da wani wani abun. A haka har suka isa anguwarsu Hafsa.
"Ki jirani a nan, yara kawai zan kwaso sai in zo mu wuce."
Fita tayi ta shige get d'in gidan nata. A farfajiyar gidan ta ga Alh yana kai kawo. Bata ko bi ta
kanshi ba, ta yi shigewarta ciki. Kai tsaye zuwa d'akin yaranta. Jaka ta bud'e ta soma loda
kayan yaranta. Bata d'iba duka ba. cikin d'akinta ta koma ta tattare 'yan kadarorinta. Ta had'e
kan suturunta. A harzuk'e ya shigo. "Hafsa wayata na fito nema tun tuni, yara suka ce mun kin fita da'ita bani wayata nace. A
zabure ta d'ago idanunta a bushe. Dan ji take yi zata iya kasheshi kowa ya huta, abunda zai
faru ya dad'e bai faru ba.
"Auwal na gama zama a gidanka, aurenmu ya k'are, k'azami wanda ya d'auki fasik'anci a
matsayin ado. Toh kasani abunda kuka jima kuna shukawa ya fito, kuma in kayi yunk'urin k'in
sakina wallahi saina yi ma bankad'ar da sai fita ya gagareka. Jakarta ta zuge ta ciro wayar tashi,
ta lalubo mishi abunda ta gani ta haska mishi. Bai iya ce mata komai ba, sai kallonta yake yi
kawai, zufa duk ta gama wankeshi tsab. A sanyaye yace.
"Hafsa ki yarda dani ba laifina bane. Zan yi miki cikakken bayanin da zaki fahimta." cije baki ta
yi kawai tace.
"Takaddata nake so, in ba hakaba narantse da Allah kasheka zanyi a cikin gidannan, saidai a
kasheni, ko kuma in je in taradda 'yar uwata a kurkuku, d'an bura uba mara mutunci." Dubanta
yayi yace.
"Na sakeki saki d'aya. Amma fa ki sani babu inda zaki tafi mun da yara suna gidan ubansu.
Dariya tayi, dukda xuchiyarta ta tsinke sosai, har kuka yaso ya xo mata, dannewa tayi kawai.
"Auwal kenan, ka kaini kotu sai su baka yaran naka, Amma ni ba shegiya bace dazan bar maka
yara a hannunka. Fuu ta fita a d'akin ta fitar da kayansu tas, sannan ta dawo ta tusa kan
yaranta. Har bakin D'an sahun ya je, ya rik'e k'arfen d'an sahun yace.

"Ki daure ki bar yarannan a gidansu shine gatansu, kar abun kunyar daya faru a gidanku ya
shafesu.
"Kaci bura ubanka, kai da abun kunyar, abun kunya har ya wuce na kanka. Mai d'an sahu ja mu
tafi. Jamila kuwa da mamaki take kallonsu, gani take yi abun tamkar almara. Mai d'an sahu ya
jasu zuwa kasuwa. Xinarenta na gado ta siyar, suka wuce jacara.

Aminu
Sai bayan isha ya shiga gida, su Zara'u kam sun jima da yin bacci, Mardiyya ce idanunta biyu,
yanzu ta gama tsinke alaiyawon miyar masa.
"Ka dawo?"
"Nadawo Dada, yau munsha zurga zurga ni da Saminu. Mun kammala komai, zuwa gobe zamu
bud'e sana'a, Saminu zai rik'a saida su lemo da ayaba. Dada tace.
"Masha Allah Abun yayi kyau. Mardiyya ta fita zuwa d'akko ma Abbanta abinci bayan ta yi mai
sannu da zuwa.Tuwon masara miyar kuka, ta ajjiye a gabanshi da ruwan sha, dana wanke
hannu. Sai ta fita tsakar gida gyara shinkafar tuwo.
"Dada, dama Saminu ne ya zo mun da wata magana akan ita Mardiyya, tunda maneminta
iyayenshi sunk'i amincewa da auran. Wai shi yana son ita Mardiyyan. Kinji fa abunda yake
tafiya." Dada ta jinjina sosai tace.
"Toh Saminu yayi k'ok'ari sosai Aminu. Amma yanda za'a k'arke da Farida shine abun dubawa.
Sannan zumuncin Mardiyya da Murja ka iya lalacewa. Sai dai in a ka yi duba da irin abun
kunyar daya b'ullo a gidansu Hauwa, toh fa yaron mutunci ba lallai bane ya fito neman auren
Mardiyya iyayenshi su amince mishi ba. Al'amarin yana da nauyi. Aminu yace. "Hakane duk tunane tunanennan nima su naita tattaunawa a raina, amma abunda yafi shine mu
yi istikara dukkanmu, Allah ya zab'ar mana abunda yafi zama alkairi shine kawai. Dada tace.
"Ameen, 'yar uwarka ma da kuka ta bar gidannan yau, sha'anin aure yanzu ya dawo

10 / 14