Author : Badiat Ibrahim Mrs Bukhari Category : Read Hausa Novels
dinga toyawa a
waje da yamma, domun mu d'an dinga juyawa." Hawaye Dada ta shiga zubarwa na Tausayin
Aminu da yaranshi, Hauwa ta cucesu sosai."
"Mardiyya kar ki bari takaici da bak'in cikin d'a namiji da takaicin rayuwa ya durk'usar dake, ni
inaso ki bar batun karatu ki fad'a koyan sana'ar hannu, ko dan ki dinga taimakama k'annenki
tunda kinga Abban ku bashi da hali sam, ni abunda nake so kenan amma sai abunda kika ce."
Mardiyya ta share hawayenta. bakinta na yi mata d'aci tace." "Dada na d'auki shawararki wallahi, kinga su Zara'u sa samu su ci gaba da karatu in Allah ya
so, amma wainar ma inaso in soma toyata zuwa gobe." Dada sai lokacin ta d'anji sanyi a ranta
tace."
"Gobe kuma? Ai dole sai da jari Mardiyya. a k'alla kina buk'atar nera dubu uku kafin ki soma
toya waina, tunda kinga za'a sai shinkafar tuwo ga cefanen kayan miya, ga kuma su itace da
man suya, ai sai mun had'a kud'in mardiyya."
"Dada Muktar yace ya bar mun sadaki halak malak harma na yi mishi godiya, ki bani dubu uku
zuwa yanma inyo cefanen komai da komai sauran ki ba Abba yayi amfani dashi." Dada tace.
"wayyo Allah Mardiyya Allah yayi albarka kinji, Allah ya sanya muku salama da juriyar rashin
Hauwa. Wancan d'akin saiku gyara ke da k'annenki kuma saiku dinga kwana. Abbanku kuma
zai koma shagon waje da kwana, Allah ya k'ara rufa asiri, kece babba mardiyya ki duba
k'annenki domun yanzu kallon uwa zasu dinga yi miki , duk da dama kece ke ɗawainiya dasu,
tun ƙarfinki baima kaiba. Amma yanzu dai ba Hauwa, tunda a kurkuku zata ƙarashe shingin
rayuwarta, sai kin cire damuwa a ranki tukunna. Gashi 'yan uwan gyatumar taki suma fama
suke yi da kansu wannan rayuwa sai dai godiya kawai, taso muje in taya ki gyaran d'akin. Dada
da mardiyya suka gyare d'akin tas su ka sanya wani cinyayyen labule da wata guntuwar
tabarma. mardiyya ta fice zuwa shagon waje dan gyara ma Abbansu nashi d'akin, cikin awa
guda ta tsabtace ko ina ta shinfid'a mishi zanen gado a katifarshi mai kamar tabarma. Kullo
shagon ta yi ta shiga ciki. Alwala ta yi sannan ta shiga d'akin Dada, tarad dasu ta yi duk suna
Allah. itama tada tata sallar tayi. Bayan sun idar Dada tace.
"Mardiyya ki ci kwad'on naki ni zan fita zamu je barkar haihuwar shatu ni da gwamma, in yaso
na ari kud'i a wajan gwamma in yo miki cefane ko tunda ta cikin kasuwa zamu ratsa. Mardiyya
tace.
"Yauwa Dada kinga na huta shikenan. Sai kun dawo." mai Dada ta shafa ta sake saka kwalli ta
d'auki mayafinta ta fice."
"Anty Mardiyya anan gidan zamu zauna kenan har da Abba?" Zara'u ce ta yi mata tambaya,
Fatima kuwa tsakar gida ta fice ta na ta wasanta abunka da yaro.
"Eh Zara'u kinga Abba ya samu damar sanya matar da zai aura acan kinga ya samu sauk'i."
"Toh yaushe zai kaimu wajan Mami kuma?"
"Toh Zara'u Mami yau aka tafi da'ita, kuma kinga sun je dubata yau, sai dai in zai kuma zuwa
sai ku bishi kuje tunda kunason ganinta." Hawayen bak'in ciki da takaici mardiyya take zubarwa
data tuno sanda Hauwa ta zubar dasu ta mance dasu, bata ko ji tausayinsu ba, balle ta ji na
Abbansu." "Ke bazaki je ba ko Anty?." Mik'ewa Mardiyya tayi ta fice. tsintsiya ta d'auka ta soma sharar
dole. Sai da ta share gidannan tsab, ta kuma wanke band'akin gidan. Wanke _wanke ta
tattarema Zara'u wacce take zaune a dokin k'ofar Dada ta yi tagumi."
"Zara'u zo ki yi wanke wankennan maza. Ni kuma bari in gyara ma Dada d'akinta.
JACARA
"To yanzu menene shawarinku akan gadonnan da za'a raba muku, na mahaifiyarku da
mahaifinku? ni shawarar da zan baku kusa haya a gidanku gadon mahaifinku, ko wacce tana
d'akin mijinta tana karb'ar hayan abunta tasan duk shekara tana da kud'i da zasu shigo mata.
Tunda gidan Hauwa ta gyara muku shi, zaku iya samun d'akuna guda guda. Ɗan abunda aka
raba aka baku gadon Marne kuma, sai ku gagganɗa kuyi wani abun." Nanne k'anwar
mahaifiyarsu Hauwa ce take ma su Hafsat bayani" Ummu tace."
"Hafsa, Sameerah, ku da sauran ƙannen naku. Ni abunda zan fad'a muku lokaci yayi da zaku
rungumi mazajenku kuyi musu biyayya dolenku, domun kunga ishara akan mahaifiyarku mai
rasuwa. da ma Hauwa, dan haka ruwa cikin cokali ya ishi mai hankali yai wanka. Ku nutsu sosai
ku yi zaman aure me kyau. Nanne kuma ta fad'a muku gaskiya, karku siyar da gidanku na gado,
ku xuba haya kuna d'an amsan abunda ya samu 'dan gadon mahaifiyarku kuma da zaku samu
sai ku ja jari da shi ku kama 'yar sana'a, tunda kunce har mota ta siya, mu dai mun yafe, ku d'in
dai ta taku muke yi koba gaskiya ba?. lokaci yayi da zaku xubar da makaman yak'inku, ku
daina azabtar da mazajenku zaifi muku. Ku ji da abun kunyar ma daya faru daku wanda k'ila da
ba dan kun jima da yin auren ba, da ba mai auranku ma, Hauwa ta ja ma mutane bala'i da
masifar da har abada da wannan ciwon zan koma ga mahaliccina, kuma babu mahaukacin da
zai auri 'ya'yanta dai." Haka su kaita tattauna matsalolin da suke ciki, a wannan lokaci."
Aminu
Tafiya kawai yake yi a k'afa da yaga tafiyar k'afa ba zata kaishi ba,sai ya tare abun hawa ya
hau, a daidai k'ofar gidan mai adashen gata ya tsaya, yaro ya aika yace ai mishi sallama da mai
adashen gata. Bata d'au loaciba ta fito.
"Aminu kaine a tafe?"
"Eh nine d'ari zaki d'an bani in sallami mai mashin tukunna." Lalitarta ta bud'e ta zaro d'ari ta
mik'a ma Aminu, amsa yayi ya sallami mai mashin d'in kana ya dawo."
"me adashen gata, dama zuwa na yi in amshi kud'ina da nake zubawa amma rabi, rashin lafiya
ce ta taso a family kuma kowa ba kud'i kinsan garin sai adda'a." Mai adashen gata tace."
"Babu komai Aminu ai amfanin ajjiyar kenan ita dama ajjiya dad'i gareta, bari in baka nera dubu
sittin da biyar kenan zan baka ko? kace rabi." Aminu yace.
"Eh haka zaki bani." Gida ta koma bata jima ba, sai gata da kudin ta bashi, bai ko tsaya kirga
kudin ba ya xura a aljihu ya wuce, kai tsaye ya koma asibiti ya je ya siyo allurannan da
magunguna. sai da ya kashe dubu ashirin da uku da d'ari biyu.
Da sallama ya shiga cikin d'akin, Hauwa har zuwa lokacin tana bacci bata farka ba, Jamila tana
zaune ta zuba uban tagumi, Baffa kuma yana tsaye yana kallon Hauwa. ga gandirobobi guda
biyu a gefe da gefen gadon."
"Aminu ka dawo?"
"Eh Baffa na dawo, bata farka ba ko?" Jamila ta sauke ajjiyar xuchiya tace.
"Bata farka ba, d'azu dai ta bud'e idanta sai kuma ta rufe. Likita dai yanata shigowa dubata."
Shiru Aminu yayi yana kallon fuskar Hauwa cike da tausayinta."
"Bari inje in kai mishi magungunan, daga nan zan d'anje gida da yamma zan dawo kafinnan ta
farka." Baffa yace.
"Allah yayi albarka Aminu wai duk tsiyar da Hauwa ta tabka amma baka gaji da hidimta mata
ba, sannu Allah ya baka mace ta gari wacce tasan mutuncinka. Nima zan tafi gida dan akwai
malamai masu rabon gadon ita uwar tasu, da na mahaifinsu da ba'a rababa, za su zo kar suita
jirana ba dad'i Jamila za'a aiko da abinci anjima." Tare Aminu da Baffa suka fice, Aminu saida
ya kaima Dr magungunan da alluran kuma ya shaida mishi zai je ya dawo zuwa yamma. Dr
yace.
"Dama ka bari sai zuwa gobe sai ka dawo dan bazata farka yau ba sai zuwa gobe, dan wannan
allurar da zan k'ara yi mata zata kuma sata baccine."
"Toh shikenan likita mungode." Sallama yayi mishi ya fice. Kai tsaye zuwa galadanci."
Mardiyya suna tsakar gida ita da k'annenta sai tunano Muktar take yi da irin son da yake yi
mata, amma gashi lokaci d'aya mahaifiyarta ta ruguje mata farin cikinta. Sallama su ka ji ana
dokawa daga k'ofar gida, mardiyya ta zari mayafi ta le'ka. Abokin Abbanta ta gani Saminu a
tsaye. "Sannu da zuwa Abba, ina yini?" Kallon mardiyya ya ke yi cike da tausayawa ya ce."
"Lafiya lau Mardiyya ya k'annenki?" Kanta na k'asa tace.
"Lafiyarsu k'alau Abba, ina su Murja?" murmushi yayi yace.
"Mardiyya ta Murja, Dada fa?.
"Ba ta nan ta fita barka" Kai ya kyad'a yace.
"Toh mu shiga daga ciki." Juyawa ta yi ya bi bayanta, sai k'arema takunta kallo yake yi. Fatin
Mami tana hangoshi ta zuro da gudu ta d'aneshi tana dariya."
"Abba kaine?" Sake rungumeta yayi a jikinshi yaima kanshi masauki a tabarma kusa da Zara'u."
Zara'u tace
"Abba ina wuni?" Kanta ya shafa cikin kulawa ya amsa gaisuwar tata, sannan ya dawo da
dubanshi ga Mardiyya yama kasa d'auke kai. Duk d'agowar da zata yi sai sun had'a idanu
hakan duk sai ya takurata. ba tun yau ya saba yi mata haka ba, kullum in yaje gidansu a cikin
kallonta kawai yake, haka in ita ce taje gidanshi wajan Murja 'yarshi kuma aminiyarta sai yaita
kallonta ita ta rasa dalili.
"Mardiyya! Muktar yaje wajan aikina a kasuwa, ya sanar da ni yanda iyayenshi suka kafe kan
lallai basu amince ya Aureki ba. Ki yi hak'uri in sha Allah wanda zai b'ullo miki ya fi shi alkhairi
kuma ya fishi sonki. Mahaifiyarki ki bita da adda'a kawai dan ta jefa kanta a cikin mummunan
hali. Hawaye Mardiyya take yi sosai da sosai. Da sallama Aminu ya shiga cikin gidan nasu. Duk
yaran suka nufoshi dan yi mai sannu kamar yanda su ka saba. Tsabar son su da tausayinsu ji
yake yi tamkar ya maida su ciki ya huta. Fatin Mami ya d'auka a kafa'darshi, cikin dariyar yak'e
yake yi ma Amininshi Saminu magana. "Kai kuma anan ka fake ko ka je nema na?" Zama yayi a kusa da Aminin nashi, mardiyya kuma
ta ja k'annenta suka shige ciki."
"Saminu zuchiyata har gaban abada ba zata iya daina son Hauwa ba. Ni nasan a cikin k'unci
zan rayu har abada, kamar yanda Hauwa zata kasance a gidan yari. Yanxu haka fa tana asibiti
hawan jini ya kamata, zuchiyarta na shirin kamuwa da ciwo. Kasan Allah ni Auran ma da zan yi
na fasa Saminu." Sororo Saminu ya shiga kallon Aminu, ranshi ya matuk'ar b'aci sosai. "Ka sani in ka fasa Auren Lubabatu a gaskiya ka yaudari xuchiyarta kuma ka cutar da ita. Ita
Hauwan lokacin da taso canji bata canja maka bane, dad'in Aure da Hauwa ai kai kanka kasan
babu meye matarnan ba taima a rayuwarka ba Aminu. Duk bala'in data hurgaka a ciki amma
har yanzu ka kasa dena sonta? Amma Allah ya tsine wannan soyayyar." Aminu wani irin zafi
zuchiyarshi take yi mishi mai wuyar fassara, shi kanshi yakan zauna yai tunanin shin wanne irin
so ya ke yi ma Hauwa Alhalin yasan ba sonshi take yi ba. Wanne irin azabtar da shine Hauwa
bata yi ba? Shi kanshi bazai iya k'irga sau nawa Hauwa ta hanashi bacci ba. Amma kuma yana
tuno soyayyar ta mai wuyar goguwa. soyayya mai sanyi.Idanu ya lumshe yama rasa me zaice
ma Amininshi dan ya fishi gaskiya."
*TALLAH*
Ina kuke amare uwayen gida kai har ma da ƴan mata? Ko kun san Mrs Bukhari mai kayan
ƙamshi, ai in dai batu na kayan ƙamshi gyaran jiki da na ɗaki to kai tsaye ku ne mi Badi'at
domin gwana ce ta ko wanne fanni a ciki. "Wai ƙamshi kina nufin Badi'at dai marubuciyar nan
tamu mai nishaɗantar da mu?" "Tabbas Fati ita take magana, ai kin dai ji yadda ake magana a kai na, hatta me gidana ya
jinjinawa Badi'at domin duk wani ƙamshi da zaki ji a jikina tare da gidana to daga ita ne, ke me
kankat ma har gyara na nake yi domin gyaran aurena daga gareta ne, shi ya sa bana wasa da
gyaran jikina da na gidana har kuke kirana da ƙamshi." "Eh tabbas nima na jinjina mata, kuma zaki bani addireshinta domin nima na kwankwati wannan
garaɓasa. Ko zaki iya faɗa mini abubuwan da take sayarwa.?"
"Bari na faɗa miki akwai...
Humra
Kulacca
Sudanese Humra
Kulacca ta gashi.
Turaren wuta ɗan gaske, iri daban daban.
Turaren mopping
Room freshner
Turaren turara kaya.
Turaren wuta na toilet
Sannan akwai ingantaccen maganin infection
Ina da magungunan mata, wanda zai gyara amarya da uwar gida.
Wanda zasu shiga daga ciki kuma
Akwai sabulun amare, da dilka ta amare, wanda zaisa amarya ta fito ta haska tas
Kabbasa
Setin kujerar tsugunno
Sannan inayin turaren wuta da kasko, da ashana wanda ake rabawa a taron biki ko suna.
Ina bayar da sari.
Ma sha Allahu to taya zan sameta domin mallakar nawa?
"Kai tsaye zaki mata magana ta whatsApp ko kiranta ta wannan number.
08179523215
*TALLAH*
A yau nazo muku da manya manyan magunguna domin gyaran Auranmu! Saboda yadda
zamantakewarmu ta AURE keta kara tabarbarewa. Mata iyayenmu ku fito ku gyara jikinku ,
domin wallahi har Abadan macen da bata gyara bata isa ta hada kanta da mace me gyara ba
har abadan! Mu gane yaku yan uwana mata, ma’aurata! wallahi gyara shine mace Akwai mata
dayawa dasuka san magunguna na, a online Suna siya kuma Alhmdulillahi ba wadda ta siya
bata dawo tamin godiya ba, Alhmdulillahi!Alhmdulillahi! Alhmdulillahi! Yawancin mata dayawa
na nemana ta dayan sim dina sede nayi losing dinsa sede wannan shi yake Aiki 08104335144,
A YAU NAZO MUKU DA MAGUNGUNA INGANCI DA IZININ UBANGIJI, WATO AINIFIN HADI
Iri ~iri na MALLAKA D’ANA MIJI ALFARMAR ANNABI SAW, ina tabbatar muku da magunguna
na babu shamaki base na tsaya bata lokaci a bayaniba zanso ku gwada dan tantance GASKIYA
* Akwai cututtukan dake hana maganin mata aiki idan kinason sani ki tuntubeni ta wannan
lambar 08104335144 wadannan cututtukan inhar kinadasu wallahi duk maganin daza kisha
bazeyi Aiki ba, kuma bazaki taba fahimtar komiba a harkar dadih na magungunan mata.
*MUNADA MAGUNGUNA AVAILABLE KAMAR HAKA*
*ingantaccen maganin infection *
Ingantaccen maganin basir
Ingantaccen maganin gyaran nono
Ingantaccen maganin gyaran hips
Ingantaccen maganin kara kiba kiyi dumur~mur dake
Ingantaccen maganin rage tumbi meyi tsakani da Allah
Ingantaccen maganin matsin farji mesa dadin farji ga azzakarin d’ana miji.
Ingantaccen MALLAKA TA DOMIN ALLAH (Bata harkoki) shine sunansa, hmmmm Wannan
magani inada tabbaci a kansa shidin hadine kawai na mallakar d’ana miji akwai komi a cikinsa
na mallaka hajiya ki gwada kisha mamaki Alfarmar Annabi SAW.
Se matsin (GAMADIDI) wannan matsi in kikayi amfani dashi har abadan abidina mijinki baze
kawo a gaban wata ya mace ba in har ba gabanki bane wannan inada tabbaci a knsa kuma
wadanda suka saya ma sun kara tabbatarmin da kyaunsa na mamaki.
Akwai zallan hadi na amarya
Akwai hadi na uwar gida sarautar mata wannan seat ne akwai komi a cikinsa.
Akwai ingantattun gumba iri iri kamar haka
Akwai gumbar Madara
Akwai gumba me rubutu
Akwai gumbar kankana
Akwai gumbar giginya (sa megida kuka)
Akwai ingantacciyar gumba me suna (BARIN MAKAUNIYA)
Akwai gumbar hasi
Akwai zallar gumba wadda ita ta rubutuce zallarta zaki ganta baka karki damu Aikin kawai zaki
duba
Akwai gumbar gero
Akwai gumbar ridi
Akwai gumbar garin gamadidi ita ta mallaka ce zallarta.
Akwai tsumi iri iri sunansu sha yanzu magani yanzu
Akwai tsumin kankana
Akwai tsumin baure
Akwai tsumin rubutun Ayar Allah
Akwai tsumin kwakwa
Akwai tsumin giginya
Akwai tsumin GORON SUDAN (wannan special ne dan kudinsa ma daban yake)
Akwai ingantattun magunguna na tada shaawah kama daga na turawa har zuwa na Islamic
wato namu na gangajiya. Akwaifa maganin maza madam na hausa dana turawa duk basuda
side effects
Akwai rubutun mallaka
Akwai zoben mallaka
Akwai hayakin mallaka
Akwai zani na mallaka
Akwai hadin ci da kaza
Akwai hadin yan shillah
(Muna dafa kaji da yan shillar ma dade sauran abubuwa da dama,)
Akwai dambun nama na mata wanda ke dauke da magungunan sirri na mata mesa tsantsi da
laushi da ruwa a farjin mace
Akwai magunguna na ban mamaki wadanda base na rubutasu ba saboda SIRRI
Muna aika magungunan mu kasa kasa gari gari *UWAR GIDA KI GARZAYO QUEN SANAF
Islamic chemist kise magunguna na ingantattun ne insha Allahu kin wuce takaicin d’ANA MIJI *
direct to me 08104335144 muna sauraron masu shawarwari a kan zaman AURE insha Allahu,
amma in knsan baki shirya siyan magungunan jima’i ba na mata ko na maza pls karki kirani.
_Ummu Maheer_
*DINYAR MAKAHO*
_Miss Hajo_
*KHADIJATUL SABREEN*
_Mrs Bukhari_
*ANGULU DAKAN ZABO*
_Ummu Affan_
*SANDAR MAKAUNIYA*
_Mom Islam_
*TSAUTSAYIN TAUNA*
*Ga tsarin yanda biyan yake*
_Guda d'aya 300_
_Guda biyu 500_
_Guda Ukku 700_
_Guda hudu 800_
_Guda Biyar 1k_
Kai tsaye zaku iya turo kuɗinku ta wannan hanya.
0037219728
FATIMA RABIU SUNUSI
StanbicIBTC BANK
Shaidar biya ta nan
0810 433 5144
Masu turo kati MTN ta wannan number.
0702 616 6536
Ƴan Niger zaku turo da naku kai tsaye ta wanna number.
0706 860 6171
*Mun gode da kasancewa da gawurtattu biyar taku na biyu*
mrs Bukhari ce
[09/12, 19:49] Badi at: GAWURTATTU BIYAR
DAGA ALK'ALAMIN
BADI'AT IBRAHIM
MRS BUKHARI (B4B)
*ANGULU*
*DA*
*KAN ZABO*
5/6
"Aminu ka yi hak'uri da fishin dana d'auka, Hauwa uwar 'ya'yanka ce dole ka mutuntata. Amma
nazo maka da maganganu biyu, wanda bansan tunanin za zai zo kanka ba in na sanar da kai
ba." Zama Saminu ya gyara sannan ya d'aura da cewa."
"Muktar ne ya