Angulu Da Kan Zabo Book By Badiat Ibrahim

Author :  Badiat Ibrahim Mrs Bukhari Category :  Read Hausa Novels

Chapter   6 / 14

15K to 18K   out of 40.5K words

~iri na MALLAKA D’ANA MIJI ALFARMAR ANNABI SAW, ina tabbatar muku da magunguna
na babu shamaki base na tsaya bata lokaci a bayaniba zanso ku gwada dan tantance GASKIYA
* Akwai cututtukan dake hana maganin mata aiki idan kinason sani ki tuntubeni ta wannan
lambar 08104335144 wadannan cututtukan inhar kinadasu wallahi duk maganin daza kisha
bazeyi Aiki ba, kuma bazaki taba fahimtar komiba a harkar dadih na magungunan mata.

*MUNADA MAGUNGUNA AVAILABLE KAMAR HAKA*

*ingantaccen maganin infection *

Ingantaccen maganin basir

Ingantaccen maganin gyaran nono

Ingantaccen maganin gyaran hips

Ingantaccen maganin kara kiba kiyi dumur~mur dake

Ingantaccen maganin rage tumbi meyi tsakani da Allah

Ingantaccen maganin matsin farji mesa dadin farji ga azzakarin d’ana miji.

Ingantaccen MALLAKA TA DOMIN ALLAH (Bata harkoki) shine sunansa, hmmmm Wannan
magani inada tabbaci a kansa shidin hadine kawai na mallakar d’ana miji akwai komi a cikinsa
na mallaka hajiya ki gwada kisha mamaki Alfarmar Annabi SAW.

Se matsin (GAMADIDI) wannan matsi in kikayi amfani dashi har abadan abidina mijinki baze
kawo a gaban wata ya mace ba in har ba gabanki bane wannan inada tabbaci a knsa kuma
wadanda suka saya ma sun kara tabbatarmin da kyaunsa na mamaki.

Akwai zallan hadi na amarya

Akwai hadi na uwar gida sarautar mata wannan seat ne akwai komi a cikinsa.

Akwai ingantattun gumba iri iri kamar haka

Akwai gumbar Madara
Akwai gumba me rubutu
Akwai gumbar kankana
Akwai gumbar giginya (sa megida kuka)
Akwai ingantacciyar gumba me suna (BARIN MAKAUNIYA)
Akwai gumbar hasi
Akwai zallar gumba wadda ita ta rubutuce zallarta zaki ganta baka karki damu Aikin kawai zaki
duba
Akwai gumbar gero
Akwai gumbar ridi
Akwai gumbar garin gamadidi ita ta mallaka ce zallarta.

Akwai tsumi iri iri sunansu sha yanzu magani yanzu

Akwai tsumin kankana
Akwai tsumin baure
Akwai tsumin rubutun Ayar Allah
Akwai tsumin kwakwa
Akwai tsumin giginya
Akwai tsumin GORON SUDAN (wannan special ne dan kudinsa ma daban yake)
Akwai ingantattun magunguna na tada shaawah kama daga na turawa har zuwa na Islamic
wato namu na gangajiya. Akwaifa maganin maza madam na hausa dana turawa duk basuda
side effects

Akwai rubutun mallaka
Akwai zoben mallaka
Akwai hayakin mallaka

Akwai zani na mallaka
Akwai hadin ci da kaza
Akwai hadin yan shillah
(Muna dafa kaji da yan shillar ma dade sauran abubuwa da dama,)
Akwai dambun nama na mata wanda ke dauke da magungunan sirri na mata mesa tsantsi da
laushi da ruwa a farjin mace

Akwai magunguna na ban mamaki wadanda base na rubutasu ba saboda SIRRI
Muna aika magungunan mu kasa kasa gari gari *UWAR GIDA KI GARZAYO QUEN SANAF
Islamic chemist kise magunguna na ingantattun ne insha Allahu kin wuce takaicin d’ANA MIJI *
direct to me 08104335144 muna sauraron masu shawarwari a kan zaman AURE insha Allahu,
amma in knsan baki shirya siyan magungunan jima’i ba na mata ko na maza pls karki kirani.
_Ummu Maheer_
*DINYAR MAKAHO*


_Miss Hajo_
*KHADIJATUL SABREEN*


_Mrs Bukhari_
*ANGULU DAKAN ZABO*

_Ummu Affan_
*SANDAR MAKAUNIYA*

_Mom Islam_
*TSAUTSAYIN TAUNA*

*Ga tsarin yanda biyan yake*

_Guda d'aya 300_
_Guda biyu 500_
_Guda Ukku 700_
_Guda hudu 800_
_Guda Biyar 1k_

Kai tsaye zaku iya turo kuɗinku ta wannan hanya.

0037219728
FATIMA RABIU SUNUSI
StanbicIBTC BANK

Shaidar biya ta nan

0810 433 5144

Masu turo kati MTN ta wannan number.

0702 616 6536

Ƴan Niger zaku turo da naku kai tsaye ta wanna number.

0706 860 6171

*Mun gode da kasancewa da gawurtattu biyar taku na biyu*

mrs Bukhari ce
[09/12, 19:49] Badi at: GAWURTATTU BIYAR
DAGA ALK'ALAMIN
BADI'AT IBRAHIM
MRS BUKHARI (B4B)

*ANGULU*
*DA*
*KAN ZABO*
9/10

Mu asalin shuwa arab ne. Duk da shuwa sun kasu kashi _kashi, akwai *kawalmee.* sune farare
fat_fat, suna da dabbabin kiwo, kuma suna shan madara, basa iya yin aikin wahala sam, masu
son jikine sosai. akwai kuma shuwa masu suna *wadel musa* wad'annan kuma, sune bak'ak'e
sutuk, suma suna da dabbobi, suna noma, kuma suna son tafiye tafiye, tamkar fulanin tashi. Toh mahaifiyarmu ta had'a duka wannan biyu, mahaifiyarta kawalmee ce, mahaifinta kuma
wadel musa ne.
Suna zaune a wani k'auye a cikin maiduguri mai suna KOSHOB'B'E, k'ark'ashin k'aramar
hukumar jere ta jihar Borno. su uku kacal iyayensu suka haifa. mahaifiyarmu mai suna Marne,
sai mai bi mata ummu kenan asalin sunanta shine Ajidde, sai kuma Nanne, ita kuma sunanta
Latifo. Sunayen yare dukkansu aka sanya musu, domun basa jin wani yare sai yarensu na
shuwa. mahaifina malam Sada bafulatanin asaline mazauna garin Adamawa cikin k'auyan
mayobelwa, cirani ne ya fito da iyayenshi suka yada zango a garin kano, cikin anguwar tarauni,
a gidan wani Alh daya ba kakana gadi, sukai zamansu anan gidan. A gidan aka haifi mahaifina,
daga nanne Kanana ya kama haya a waje ya mayar da Hauwa kakata can danta raini mahaifina
da kyau. shekara biyu ne tsakanin mahaifina da Baffa Junaidu. Mahaifina na da shekara goma
sha bakwai mahaifinshi Allah yai mishi rasuwa, sanadin ciwon ciki na dare d'aya, sai wayar gari
akayi babu shi. Tun daga wannan lokacin mahaifina suka soma wahala da buga bugar ciyar da

mahaifiyarsu, sukan shiga kasuwa suyi aiki dan samun kud'i. A haka mahaifina Sada ya yanke
hukuncin fita cirani. Bai yada zango a ko ina ba sai a maiduguri cikin k'auyen Mafa, mai gari
shine mai masaukin bak'i, a gidanshi Sada ya sauke a d'akin samarin da suka fito cirani. Suna
shiga kasuwar cikin garin Borno ne ranar cin kasuwa, mahaifina ya samu ubangida wanda yake
bashi kayan itatuwan turaren wuta, da turarukan binta sudan, da su kafin_ kafin, suna kaiwa
kasuwa. Kamar kullum.
Sada na cikin zauren mai gari yana ta zuba kayan itatuwa a cikin buhu, su kuma turarukan mai
a cikin k'atuwar robar fenti ya jerasu, abokin fita cin kasuwarshi Sani yace.
"Sada kayi sauri kasanfa in ba duku duku muka fice ba baza mu samu inda ya dace mu baza
kayanmu ba, kai sauri. Sada ya d'ago yace."
"Kama mun buhunnan kaji Sani izamun a ka, saimu kama hanya. Sani ya iza mai buhunnan a
ka ga nauyi, haka kuma ya d'auki robar fentin turarukanshi a hannu. Suka soma tafiya da duku
dukun asuba.
"Sani wannan karon kuma mai ka d'auka zaka siyar ne?" Sani yace.
"Dilka, da kurkum na d'auko wannan karon nifa riba nake bi, shi yasa ban yarda na nace ma
d'aukar itace kamarka ba, ko wacce kasuwa da abunda zan d'auka. Dariya Sada kawai yayi ma
Sani, suna tafe suna hirarrakinsu, a hanya su kaita had'uwa da abokan ciraninsu, ko wanne
cikinsu da buhun abunda zai kai kasuwa a kanshi. Sunyi tafiya mai nisa kafin suka iso titi, motar
zuwa kasuwa suka samu suka shiga, dasu da kayan nasu duk a waje d'aya, harda awakai,
suna tafe anata hira, Sani ya lura Sada baya magana sam.
"Sada kaddai tunanin wannan yarinyar da kunya ya hana ka tambayi sunanta kake yi, 'yar
fara?" Murmushi Sada yayi yace.
"Sani ai da ita nake kwana nake tashi, tayi nisan da banyi zatoba a tunanina, gashi gwarjininta
ya hanani tunkararta. Dariya Sani ya kwashe ma Sada dashi, yace."
"Ni kuma yau na yi ma alk'awarin zan tambaya ma sunanta da k'auyansu, tunda kullum a
wajanka take siyan itacen Dorot. Baki Sada ya washe yace.
"Da kuwa na gode Sani, dan ina sonta duk da ba lallai ta auri d'an cirani kamata ba. Sani yace.
"Duk matan dake cikin k'auye burinsu guda d'ayane. Su samu saurayin da zai auresu ya fitar
dasu daga k'auyansu zuwa birni, abunda ke cikin birnin ne basa sani, balle kai taji a kanon dabo
zaku zauna, Kano ai babban garine mai cike da masu arziki 'yan kasuwa dama masu ci a
gwamnatin. Ajjiyar zuchiya Sada ya sauke domin abokinshi ya k'arfafa mishi guiwa sosai akan
kyakkyawar 'yar shuwan da yake mafarkin mallaka. Da wannan tunane tunanen suka isa
kasuwa. Nan kowa ya shiga hada hadar baza kayanshi a inda ya dace. Sani da Sada tare suke
zama a gefen wata rumfar mai siyar da su lubban da farce da misik, kayayyakin humra dai. Sun
baza kolinsu, kasuwa ta soma d'aukar jama'a sai saye da sayarwa akeyi, 'yan mata kuwa
gasunan gungu_ gungu, sunata fitowa cin kasuwa. ansha kwalliyar janbaki da hoda da gazal,
sai rawar kai suke yi a kasuwa, su ne can, sune nan, su sayi wannan su taya wancan. Sada
kuwa matane suka rufeshi sai awun itatuwan turaren wuta suke yi, Sani ma sai ciniki yake tayi,
dama duk ranar kasuwa duk abinda suka kasa k'arewa yake yi tas, sabida jama'ar dake zuwa
yawa garesu.

Koshab'b'e
Marne tana gaban madubi tana gyara gashinta wanda ta shurb'uneshi da kulacca sai k'amshi

yake yi. Mayafi ta yane kanta dashi tsab, kayan jikinta a kod'e suke amma kuma tsab dasu babu
k'azanta a jiki, kuma an turare tsunman kayan da turaren kaya, sannan tabi jikinta ta shafe da
humra sai k'amshi take bazawa. Haka ma k'annenta Ajjide, da Latifo, duk suna cikin kwalliya.
Fararene su sol sabida mahaifiyarsu farace fat, mahaifinsu kuma bak'ine sosai shi. K'awayan su
marne ne suka shigo da Sallama a bakinsu, ko wacce a cikin k'amshi take. Nan suka rankaya
zuwa cin kasuwa, suna tafe suna wak'e wak'ensu da yaren shuwa. A bakin titin k'auyensu suka
samu motar kaya da zata kai mutane ciyo kasuwa, suma suka shiga.
Sada yana zaune jama'a sun ragu a kanshi sai tunanin Marne yake yi yana murmushi. Sani ne
ya dafashi yace.
"Gasu can fa sun shigo kasuwar Sada, ga mutuniyar taka, Sada in dai ta aureka ka more mace,
yaranku zasu yi kyau sosai Sada. Bakin Sada ya kasa rufuwa sam sai washewa kawai yake yi.
Dubanta yake yi tayi daban a cikin k'awayenta ta fisu kyau da bud'ewar idanu, fatarta sai shek'i
take yi a rana. Gabanshine ya shiga dokawa da k'arfi, saurim kawar da kanshi yayi gefe. Cikin
harshen fullanci tace.
"Inason itacen dorot, da turaren sasaboriya, da d'an duwala." Zak'in muryarta ya shigeshi sosai,
ji yayi kamar tafi kowa iya fullanci.
"Kwano nawa kike buk'ata 'yan mata?" Sani ne ya tambayeta, kallon Sada tayi tace.
"Shi baya maganane me kayan? Sani yace.
"Yanayi sosai ma, nauyinki kawai yake ji, kinsan 'yan mata irinku kwai kwarjini." murmushi kawai
tayi ta mik'a mishi kud'in hannunta tace.
"wannan na itacen, wannan kuma na turaren." Had'a mata kayan yayi a leda guda ya bata,
saida suka gama siyayyarsu suka kama hanya, sai Sani ya bisu da sauri.
" 'yan mata ji mana." Dukkansu suka juyo, Isowa yayi garesu sai ya nuna Marne.
"Dake nake yi dan Allah." Nan k'awayen Marne da k'annenta suka shiga yi mata dariyar tayi
saurayi, gefe guda suka koma."
"Dan Allah zan soma da tambayarki sunanki tukunna. Far Marne tayi da ido tace.
"Sunana Marne.
"A wanne k'auyan kike da zama?
"Ina cikin koshob'b'e da zama, gidan Ammi mai turare, in ka je babu wanda baisan gidanmu ba."
Murmushi Sani yayi yace.
"Dama abokinane ya gani kuma yake so, amma kunya irinta fulani yasa ya kasa taranki kai
tsaye. Sai dai ya jima da sonki a zuchiyarshi. Ki bashi dama. Murmushi Marne ta yi tace.
"Na bashi dama gobe zai iya zuwa da yamma sai mu yi magana. Tana kaiwa nan ta wuce suka
kama hanya.
Sani ya ba Sada labarin yanda suka yi da Marne. A daren ranar bacci gagaran idanun Sada
yayi, ko a k'aramar kasuwa inda anan suke gudanar da kasuwancinsu. kasa sukuni sam Sada
yayi. Da yamma kuwa suka shirya sai koshob'b'e shi da Sani.
Sun samu tarba mai kyau a wajan Marne dama iyayenta, harma mahaifinta yace ya ba ma
Sada nanda shekara mai zuwa ya turo magabatanshi.
Tun daga nan soyayya mai k'arfi ya shiga tsakanin Marne da Sada. mahaifiyar Sada ma tasan
da maganar Marne, taso tak'i amincewa amma Sada ya tusata a gaba da rok'o har ta amince
mishi yaci gaba da zuwa wajan Marne. Wasa_wasa lokaci sai tafiya yake yi, soyayyar
masoyannan biyu sai nisa take yi, wata rana da yamma Sada na wajan Marne yaxo yi mata

Sallama za shi ganin gida. Suna zaune a kan wasu duwatsu dake k'ark'ashin bishiyar gefen
gidansu Marne suna Sallama.
"Sada me kake tanadi game da aurenmu ne, kasanfa auranmu akwai kashe kud'i gashi yanzu
wata biyu ya rage ayi bikinmu, dan tare da k'annena za'a had'a." Sada yace.
"Ai duk wani tanadi yanzu da nake yi baya wuce na bikinmu Marne, zan fito dake a cikin
wannan k'auyan, zan yi miki kaya na gani na fad'e. Dariya suka saka baki d'aya tace.
"Ai nasan Sada bazaka bani kunya ba, amma yanzu Sada sai yaushe zaka dawo kuma?" Gyara
zama yayi yana fuskantarta.
"Marne magana ta gaskiya, in dai na tafi bazan dawo ba sai dai in zo bikin d'aurin auranmu,
akwai shirye shirye da zan gabatar a gida, kuma nima tare zamu yi aure da k'anina Junaidu. Ki
yi hak'uri kinji?" Kud'i masu yawa ya ba ma Marne yace in zata yi buk'ata tayi a cikin su. Sunyi
sallama Marne tana kuka a haka suka rabu.
Kano
"Baba Toh ni dai kinga iya abunda na tara, su kenan iyakar abunda nake da shi, amma cewa na
yi, mu je k'auye ayi maganar Gadonmu. A siyar da gonakan a bamu, in yaso sai mu nemi gida
mu siya, Ko Baba?" Junaidu yace.
"A'a Yaya Sada ni dai kar a siyar da nawa, gaba za su yi mun amfani sosai, d'an abunda na
tara, sun isheni in yima Harira komai. Baba tace.
"Nima ina ganin kamar a barshin zaifi ko, sabida gaba ake ji, da kunyi aurannan zaku soma
tara yara ne, ga ciyarwa fa, kuma babu mai k'wak'k'warar sana'a ta dogaro da kai. Sada yace.
"Ni matsalar shine. auran shuwa akwai kashe kashen kud'i, su basa yar da al'adarsu sam, kuma
kinga da sisin gwal zan biya sadaki shiyasa."
"Sisin gwal kuma wannan yaron?".Sunan da Mahaifiyarshi ke kiranshi dashi kenan.
kasancewarshi na babban d'anta.
"Eh Baba sisin gwal, toh kinga 'yan kud'ad'en dana tara ba za su isaba." Baba tace.
"Tun farko yarinyarnan tafi k'arfinka. Nifa shi yasa sam bansota ba sam, sabida matan shuwa
ba kirki bane da su, aikinsu shine mallaka da nuna kowa zasu iya mulkarshi. Amma tunda kai
zaka iya, sai mu je mayo a siyar da gona d'aya azo a sayi gida, sauran a gangand'a a gama
komai. Hakan ko akayi, sun je k'auye an siyar da gonarsu Babba ta gado. A Jacara suka sai gida mai
d'auke da d'akuna hud'u, ciki da falo falo, guda uku, sai d'add'aya guda biyu, da kitchen da
band'aki a tsakar gida. Tsakar gidan babu laifi da girma.
Sannu_ sannu lokacin biki nata k'aratowa, shiri ya kankama daga ko wanne b'angare. 'yan uwa
da abokan arziki sun soma zuwa daga gari_ gari, k'auye_ k'auye, Shagulgula na al'adar fulani
da ma na shuwa babu wanda aka zubar. Rana d'aya aka d'aura Auren, 'yan d'aurin aurene suka
tawo da Amarya Marne da gandinta. Haka ma Junaidu. 'yan d'aurin aurenne suka tawo tare da
zugar dangi da ƙawayen Amarya Harira. Da Yamma lis 'yan mayobelwa suka iso, nan kuma aka
shiga yin dank'in d'akin amarya.
Gadone mai rumfa, da doguwar kujera guda d'aya, sai tarkacen kayan k'ore, da kayan aikin
gida akaima Harira. Basu jima ba aka kammala komai, har amarya ta samu ta shiga d'akinta.
Mutanen maiduguri kuma sai cikin dare suka iso. Dole aka jibge tulin kayan Amarya a tsakar
gida, sannan aka cire kayan uwa da suke yi bisa al'ada aka mik'ama mahaifiyar Sada. 'yan

uwanta ne suka amsa su kai godiya.
Santin gidan dangin Marne suka shiga yi sosai da sosai, sun yaba da karamcin dangin Sada
matuk'a gaya. Washe gari aka yi jeren d'akin Amarya wanda yasha kaya sosai. Gado har biyu
aka kafa a uwar d'akin da mai rumfa da kuma bono . Ga daddumai da aka shinf'ida a ciki da
falo, dadduma har a bango aka kafa ta, gashi an zagaye bangon d'akin da cotin jajaye masu
kyau sosai. Kwanansu biyu a gidan sannan suka tattare yana su ya nasu.
Amarya Marne tana zaune a d'aki ita kad'ai sai tunane_tunane take ta faman yi. A haka ta jiyo
sallamar Mahaifiyar Sada da Harira. Gidan kowa ya watse. a yatsine ta amsa musu tana daga
uwar d'aki. sun jima a falon a zaune kafin ta fito cikin isa.
"Lafiya daga ina haka?" Da harshen fulatanci tayi magana. Cikin Fara'a Harira tace.
"Mahaifiyar Yaya Sada ce." D'an sakin fuska tayi tana tsaye ta gaisheta ta yi komawarta d'aki ta
yi zamanta.
Suna zaune sunyi tunanin ko wani abun taje d'akkowa amma sai suka ji shirun yayi yawa. Baba
ta girgiza kanta, ta yafici Harira suka fice.
"Koma d'akinki Harira mak'ota zaki gansu zuwa anjima sunzo ganin d'akunanku, ki gyara
ko'ina." Harira cikin ladabi ta amsa mata ta wuce.
Tsaki Marne ta saki tana maganganu k'us_k'us.
"Kawai zai wani had'ani da k'azamar uwarshi gida d'aya. Da ya fad'amun hakan ni mai zai sa
ma in aureshi? Na yi zaton gidansu yama fi haka, wannan dame yafi k'auyenmu?" Tana dai
zaune ta gama k'umewa da Sada.
Baba ce ta fito tsakar gidan ta kunna itace a murhu, sai ta d'auki tsintsiya tana sharar tsakar
gidan da yai kaca_kaca. Harira ce ta fito da sauri ta amshe tsintsiyar. Nan kuwa ta shiga aikin
shara. Baba tana zaune a dokin k'ofarta tana tsintar shinkafa. Sai ga Marne ta fito rik'e da
kaskon turare a hannunta. Baki Baba ta washe tace. "Masha Allah Marne kin fito ne?" D'an yak'e Marne ta yi tace.
"Eh na fito zan d'ebi wuta ne." Da fara'a Baba tace.

6 / 14