Angulu Da Kan Zabo Book By Badiat Ibrahim

Author :  Badiat Ibrahim Mrs Bukhari Category :  Read Hausa Novels

Chapter   2 / 14

3K to 6K   out of 40.5K words

zuchiya yace." "Ku kwantar da hankalunku, mun shawo kan matsalar, ta samu bacci ma, zaku iya zuwa ku
ganta ba wata matsala Baba. Dubanshi ya dawo kan Aminu yace. " Kai kuma sai ka biyoni
office akwai magunguna da zan rubuta maka sai a karb'o a ɗakin ƙarɓo magani.
A baya Aminu ya bi likita har zuwa ofishinshi, waje ya nuna mishi.
"Bismillah zauna mu yi magana." Zama Aminu yayi ya xuba ma Likita rinannun idanuwanshi da
suka rine, kanshi a mugun caje yake sosai."
"Hauwa Sada k'anwarka ce ko?" Aminu ya gyad'a mishi kai yace.
"Eh wanta ne ni.
"Toh na jawo ka nanne dankar in d'agama mahaifinku hankali, a gaskiya Hauwa bata da lafiya
sosai, ta kamu da hawan jini, har jijiyar bayan kunnenta ya kumbura, sannan kuma zuchiyarta ta
na d'an yi mata ciwo, amma bana nufin ta kamu da ciwon zuchiya, zan d'aurata a kan
magunguna, zan rubuta wasu allurai a siyo, sai dai gaskiya suna da d'an tsada." Aminu ya dafe
kanshi da yake shirin fad'uwa daga kan wuyanshi, da kyar ya saita kanshi, cikin d'acin yawu, da
sark'ewar harshe yace.
"Mungode Likita, kuma ka kyauta da baka fad'i wannan maganar a gaban Baffa ba, Allah ya
bata lafiya.
Dr ya rubuta ma Aminu magunguna da Allurai ya bashi, karb'a yayi ya fita, da gandiroba d'aya
yaci karo zata shiga office d'in Dr dan ta samu cikakken bayani gamsasshe daga gareshi.
D'akin da aka kwantar da Hauwa ya shiga, matane ratata a d'akin marasa lafiya, a cike gadajen
suke dam.
K'urama Hauwa idanu yayi. sonta da tausayinta na sake hudashi, ta fad'a a fuska sosai,
kyakykyawar bak'ar fuskarta ta yi fayau, har da d'an haske ta yi. Gani yake tamkar mardiyya
d'iyarsu ce, dan kamannin da mardiyya ta yi da mahaifiyarta Hauwa har ya b'aci. Idanu ya
lumshe. "Aminu ya dai?" Baffa ne ya ke tambayarshi, gandiribar da take zaune a gefen gadon Hauwa ya
kalla a.zuchiyarshi yace. "duk da d'aure hannayenta da kaca da akayi a jikin k'arfen gadon bai
ishesu ba har sai sun takura mata? tsaki ya saki a zahiri.
"Baffa babu komai magani suka rubuta mata da wasu allurai, zanje in d'an bubbuga mu ga
yanda hali zai kasance." Baffa yace
"A'a a siyar da d'ankunne Hauwa a yi duk wata hidimar asibiti da shi, karka d'aurama kan ka
nauyin da ya sauka tuni a kan ka, ke Jamila ki wuce kasuwa a siyar da d'ankunnen a biya mata
kud'in magani dashi."
"A'a Baffa baza'ayi haka ba abar mata abunta kawai, ku jirani in je in dawo."
Bai jira me za su ce ba yayi maza ya fice a cikin d'akin."
Kuka Baffa ya fashe dashi yace."
"Jamila, Hauwa ta cucemu ta cuci kanta da iyalanta."

mrs Bukhari ce

*TALLAH*
Ina kuke amare uwayen gida kai har ma da ƴan mata? Ko kun san Mrs Bukhari mai kayan
ƙamshi, ai in dai batu na kayan ƙamshi gyaran jiki da na ɗaki to kai tsaye ku ne mi Badi'at
domin gwana ce ta ko wanne fanni a ciki. "Wai ƙamshi kina nufin Badi'at dai marubuciyar nan
tamu mai nishaɗantar da mu?" "Tabbas Fati ita take magana, ai kin dai ji yadda ake magana a kai na, hatta me gidana ya
jinjinawa Badi'at domin duk wani ƙamshi da zaki ji a jikina tare da gidana to daga ita ne, ke me
kankat ma har gyara na nake yi domin gyaran aurena daga gareta ne, shi ya sa bana wasa da
gyaran jikina da na gidana har kuke kirana da ƙamshi." "Eh tabbas nima na jinjina mata, kuma zaki bani addireshinta domin nima na kwankwati wannan
garaɓasa. Ko zaki iya faɗa mini abubuwan da take sayarwa.?"
"Bari na faɗa miki akwai...

Humra
Kulacca
Sudanese Humra
Kulacca ta gashi.
Turaren wuta ɗan gaske, iri daban daban.
Turaren mopping
Room freshner
Turaren turara kaya.
Turaren wuta na toilet
Sannan akwai ingantaccen maganin infection
Ina da magungunan mata, wanda zai gyara amarya da uwar gida.
Wanda zasu shiga daga ciki kuma
Akwai sabulun amare, da dilka ta amare, wanda zaisa amarya ta fito ta haska tas
Kabbasa
Setin kujerar tsugunno
Sannan inayin turaren wuta da kasko, da ashana wanda ake rabawa a taron biki ko suna.
Ina bayar da sari.

Ma sha Allahu to taya zan sameta domin mallakar nawa?

"Kai tsaye zaki mata magana ta whatsApp ko kiranta ta wannan number.

08179523215


*TALLAH*
A yau nazo muku da manya manyan magunguna domin gyaran Auranmu! Saboda yadda

zamantakewarmu ta AURE keta kara tabarbarewa. Mata iyayenmu ku fito ku gyara jikinku ,
domin wallahi har Abadan macen da bata gyara bata isa ta hada kanta da mace me gyara ba
har abadan! Mu gane yaku yan uwana mata, ma’aurata! wallahi gyara shine mace Akwai mata
dayawa dasuka san magunguna na, a online Suna siya kuma Alhmdulillahi ba wadda ta siya
bata dawo tamin godiya ba, Alhmdulillahi!Alhmdulillahi! Alhmdulillahi! Yawancin mata dayawa
na nemana ta dayan sim dina sede nayi losing dinsa sede wannan shi yake Aiki 08104335144,
A YAU NAZO MUKU DA MAGUNGUNA INGANCI DA IZININ UBANGIJI, WATO AINIFIN HADI
Iri ~iri na MALLAKA D’ANA MIJI ALFARMAR ANNABI SAW, ina tabbatar muku da magunguna
na babu shamaki base na tsaya bata lokaci a bayaniba zanso ku gwada dan tantance GASKIYA
* Akwai cututtukan dake hana maganin mata aiki idan kinason sani ki tuntubeni ta wannan
lambar 08104335144 wadannan cututtukan inhar kinadasu wallahi duk maganin daza kisha
bazeyi Aiki ba, kuma bazaki taba fahimtar komiba a harkar dadih na magungunan mata.

*MUNADA MAGUNGUNA AVAILABLE KAMAR HAKA*

*ingantaccen maganin infection *

Ingantaccen maganin basir

Ingantaccen maganin gyaran nono

Ingantaccen maganin gyaran hips

Ingantaccen maganin kara kiba kiyi dumur~mur dake

Ingantaccen maganin rage tumbi meyi tsakani da Allah

Ingantaccen maganin matsin farji mesa dadin farji ga azzakarin d’ana miji.

Ingantaccen MALLAKA TA DOMIN ALLAH (Bata harkoki) shine sunansa, hmmmm Wannan
magani inada tabbaci a kansa shidin hadine kawai na mallakar d’ana miji akwai komi a cikinsa
na mallaka hajiya ki gwada kisha mamaki Alfarmar Annabi SAW.

Se matsin (GAMADIDI) wannan matsi in kikayi amfani dashi har abadan abidina mijinki baze
kawo a gaban wata ya mace ba in har ba gabanki bane wannan inada tabbaci a knsa kuma
wadanda suka saya ma sun kara tabbatarmin da kyaunsa na mamaki.

Akwai zallan hadi na amarya

Akwai hadi na uwar gida sarautar mata wannan seat ne akwai komi a cikinsa.

Akwai ingantattun gumba iri iri kamar haka

Akwai gumbar Madara
Akwai gumba me rubutu
Akwai gumbar kankana
Akwai gumbar giginya (sa megida kuka)
Akwai ingantacciyar gumba me suna (BARIN MAKAUNIYA)
Akwai gumbar hasi
Akwai zallar gumba wadda ita ta rubutuce zallarta zaki ganta baka karki damu Aikin kawai zaki
duba
Akwai gumbar gero
Akwai gumbar ridi
Akwai gumbar garin gamadidi ita ta mallaka ce zallarta.

Akwai tsumi iri iri sunansu sha yanzu magani yanzu

Akwai tsumin kankana
Akwai tsumin baure
Akwai tsumin rubutun Ayar Allah
Akwai tsumin kwakwa
Akwai tsumin giginya
Akwai tsumin GORON SUDAN (wannan special ne dan kudinsa ma daban yake)
Akwai ingantattun magunguna na tada shaawah kama daga na turawa har zuwa na Islamic
wato namu na gangajiya. Akwaifa maganin maza madam na hausa dana turawa duk basuda
side effects

Akwai rubutun mallaka
Akwai zoben mallaka
Akwai hayakin mallaka
Akwai zani na mallaka
Akwai hadin ci da kaza
Akwai hadin yan shillah
(Muna dafa kaji da yan shillar ma dade sauran abubuwa da dama,)
Akwai dambun nama na mata wanda ke dauke da magungunan sirri na mata mesa tsantsi da
laushi da ruwa a farjin mace

Akwai magunguna na ban mamaki wadanda base na rubutasu ba saboda SIRRI
Muna aika magungunan mu kasa kasa gari gari *UWAR GIDA KI GARZAYO QUEN SANAF
Islamic chemist kise magunguna na ingantattun ne insha Allahu kin wuce takaicin d’ANA MIJI *
direct to me 08104335144 muna sauraron masu shawarwari a kan zaman AURE insha Allahu,
amma in knsan baki shirya siyan magungunan jima’i ba na mata ko na maza pls karki kirani.
_Ummu Maheer_
*DINYAR MAKAHO*

_Miss Hajo_
*KHADIJATUL SABREEN*


_Mrs Bukhari_
*ANGULU DAKAN ZABO*

_Ummu Affan_
*SANDAR MAKAUNIYA*

_Mom Islam_
*TSAUTSAYIN TAUNA*

*Ga tsarin yanda biyan yake*

_Guda d'aya 300_
_Guda biyu 500_
_Guda Ukku 700_
_Guda hudu 800_
_Guda Biyar 1k_

Kai tsaye zaku iya turo kuɗinku ta wannan hanya.

0037219728
FATIMA RABIU SUNUSI
StanbicIBTC BANK

Shaidar biya ta nan

0810 433 5144

Masu turo kati MTN ta wannan number.

0702 616 6536

Ƴan Niger zaku turo da naku kai tsaye ta wanna number.

0706 860 6171

*Mun gode da kasancewa da gawurtattu biyar taku na biyu*
[09/12, 19:49] Badi at: GAWURTATTU BIYAR
DAGA ALK'ALAMIN

BADI'AT IBRAHIM
MRS BUKHARI (B4B)

*ANGULU*
*DA*
*KAN ZABO*
7/8

D'AN LADI NA SIDI
Hafsa ce a zaune a tabkeken falonta, tunane_ tunane ya gama cika mata kanta.
Ina mahaifiyarta ta samu wannan sark'ar gwal d'in wa kuma ya bata kuma yaushe???" Shine
tambayar da ta rasa waye zai bata amsarsu.
Mik'ewa ta yi zumbur, kai tsaye d'akin Alh mijinta ta tura ta shiga. Ko ina k'amshin turaren wuta
'dan maiduri yake yi d'an asali, ya kama d'akin daram ya zauna. Gaban dorowar gefe da gefen
gadon mijin nata ta nufa. nan kuwa ta shiga bincike. Ta bud'e can ta bud'e can, ita kanta ba ta
san me take nema ba. Zama ta yi jagwab a kan gadon ta fashe da kuka, Yayarta Hauwa ta
tuno, da kuma mahaifiyarsu data kwanta dama, tunaninta yai mugun zurfin gaske a cikin
wannan daren, ta rasa yaya rayuwarsu zata ci gaba da kasancewa kuma oho. Alh ne ya turo
k'ofar ya shigo d'akin kunnenshi mak'ale da waya yana shan soyayyarshi. Zama yayi a gefen
gadon tamkar bai ga Hafsa a cikin d'akin ba.
"A'a haba, ai ko nawa kike so zaki samu, cancantarki ce, akwati kuma kizo da kan ki shago ki
had'a abunda yai miki. Shiru yayi yana sauraren ta cikin wayar, murmushi yayi yace.
"Allah _Allah na ke yi in sauke k'ishin ruwan da ya jima yana damuna a kanki, kinsan matan
gidan sai a hankali. Idanu Hafsa ta runtse gabanta yai mummunan dokawa da k'arfi. Wai yau
itace reshe ya juye mata haka, ita da take taka Alh take yin yanda taso, ta murza mota ta shiga
gari, waya bata shekara a hannunta, gashi tun kafin aje ko ina ta lura yana son ya wulak'antata
ya k'ask'antar da ita a wajan kucakar matar da zai auro mata. Mik'ewa ta yi ta fita a d'akin, da
harara ya bi bayanta. Kwanciya ya gyara kawai yaci gaba da wayarshi cike da nishad'i."

Saminu
"Saminu nifa bai isheni ba, ka fi so kullum sai na yi magana tukunna. Zufa Saminu ya sharce
yace.
"Haba Farida in dai ba so kike ki tsotse mun jinina ba, ai yaci ya isa haka, sau uku fa?, Allah ya
ji ya gani bazan iya miki wani abunba. gyara kwanciyarshi yayi, Farida kuwa nan ta lullub'eshi
da masifa, shi dai baice mata komai ba, domun yasan duk abunda yace da ita sai dai su 'kara
haurawa sama, yafi mai yai baccinshi kar ya fita neman tuwo yai ta gyangyad'i. Ya lura Farida
bata tausaya mishi sam.

Aminu
Yana kwance shiru yana tunanin Hauwa, da mamakin k'arfin zuchiyarta da rashin tsoronta.
Murmushi yayi daya tunano soyayyarta mai tsayawa a rai, tuno ta ya kumayi da irin yanayin da
take tsaiwa a gabanshi ta zazzaga mishi rashin kunya. Murmushin shi ya fad'ad'a ya girgixa kai.
"Hauwa kin rusa mun rayuwa, kin kasa cika mana burinmu da muka jima muna mafarki. Har

abada ke tawa ce, bazan dena miki adda'a ubangiji ya baki mafita ba."
Mardiyya ma a cikin tunanin take. A kwance take amma ta yi sharkab da filon da take kai, sai
kuka kawai take yi. Ta rasa meye dalilin mahaifiyarsu na zab'an rayuwar data jefa kanta a ciki,
ta mayar da su marayun k'arfi da yaji. Ita bama ta kanta take yi ba ta k'annenta da Abbanta da
bai jima daga tashi a cikin cutar damuwa ba. Mik'ewa ta yi ta fita dan d'auro alwala. Abbanta ta
gani a tsakar gidan, gama alwalarshi kenan.
"Mardiyya baki yi bacci ba, ko fitsari kika fito yi? A jere yai mata tambayar cikin kulawa.
"Abba Alwala na fito yi zan yi nafila ko zan samu nutsuwa. Shiru Aminu yayi tare da juya
kalmomin Mardiyya a ranshi. Tsoronshi kar wani ciwon ya kamata yarinya k'arama da'ita."
"Mardiyya bana so sam in ganku a cikin damuwa, abun zai mun yawa, ki dage wajan sakin
jikinki ko dan k'annenki su samu farin ciki. Kuma in sha Allah zaku koma makaranta bazan bari
karatun naku ya tsaya ba kinji. Murmushi Mardiyya ta yi dan yarinyace mai son karatu daga na
bokon harna addinin, tayi saukar Qur'ani mai girma wasu littattafai yanzu take bi. "Toh Abba kaima ka dena damuwa dan Allah ka cire damuwar Mami a ranka." Wucewa tayi ta
d'auro alwala a wajan wanke _wanke ta koma d'aki. A kan sallaya Aminu da Mardiyya suka
kwana cur suna rok'on Allah ya sanya sanyi da salama a xukatansu, ya kawo musu mafitar
rayuwa."
D'an ladi na Sidi
tana tsaye a kichin tana had'a abincin kari da zata kaima 'yan asibiti a gaggauce take yin
komanta. Yaranta duk suna falo tayi musu wanka. Alh kuma yana cikin d'akinshi a kwance
sabida ba da wuri yake fita ba. Bayan ta kammala komai ta sa a baske, sai ta fito falo.
"Shamsu abincin ranan ku yana kitchen in lokacin ci yayi sai ka zuba muku ko? Zanje wajan
Mamin su Fati a asibiti in Babanku ya fito ku ce mishi na fita." Shamsuddin yace.
"Mama sai yaushe zamu koma makaranta anata karatu mu banda mu?" Hafsa ta ji wani kala a
ranta.
"Shamsu zaku koma makaranta sati mai zuwa amma zan sake muku makaranta kaji ko? Kuma
zan saka a shagon koyon aiki." Hawayenta take ta k'ok'arin shanyewa, dama ta d'au aniyar
daga asibiti zata biya kasuwa ta sai da warwarayen zinarinta dan ta mayar da yaranta
makaranta tunda ubansu ya kasa, sauran kuma kud'in zata nemi shawarar 'yan uwanta kan me
zata soma na sana'a dan dogaro da kai. Wayace ta soma ruri halamar shigowan sak'o, da
mamaki Hafsa ta kalli yaranta tace.
"Waya ce naji tayi kuka ko? Hajja tace.
"Mama wayar Baba ce" Wani sak'onne ya kuma shigowa sai kawai ta tsinci kanta da son ganin
meye a cikin wayar. Gaban wayar ta je ta d'auka zama ta gyara a kujera ta bud'e wayar.
Sak'one gajere da wata number mai suna kamar haka. *sexy* Gabanta take ya shiga fad'uwa
cikin hanzari ta bud'e sakon. ga abunda ya k'unsa. _Autan maza da fatan ka koma gida lafiya? ka barni da kewa da tunanin taraiyarmu ta jiya, a
gaskiya kai jarumine a cikin jarumai_ Hannun Hafsat na kakkarwa ta bud'e d'ayan sak'on
wannan sexy dai ita ta sake turo sak'on.
_komai yananan rad'au a k'wak'walwata ji nake yi tamkar in matso da dare dan mu kasance
tare._ Mik'ewa ta yi ta shige d'akinta ta shiga bincike wayarshi. Abunda ta gani kuma taci karo
dashi kad'an ya rage bai haukatata ba. fad'uwa a k'asa tayi tana dafe da k'irjinta da yake buga

mata da k'arfin tsiya. Idanu ta rintse tana adda'ar Allah yasa gizo idanunta suke yi mata.
Idanunta sun mugun cab'ewa da ruwan hawaye, shikenan itama tata ta k'are bata san meye
makomar auransu ba ma a yanzu ita da uban 'ya'yan nata, k'ila auran ya haramta, toh koma dai
bai haramta ba ta haramta zamanta a gidan. Kuka ta fashe dashi sosai, ta kwanta a k'asa
sanyin tayil na ratsata. Rayuwarsu na baya ta soma tunanowa da irin abubbuwa da
mahaifiyarsu ta d'aurasu akai ta kuma koya musu, tiryan tiryan ta soma tuno sanadin mutuwar
mahaifinsu. Mik'ewa tayi da sauri kamar mahaukaciya ta fita zuwa falo bata ko kalli yaran nata
ba ta d'auki basket d'inta ta wuce zuwa asibiti.

Saminu
Safiya
"Toh Farida ni kam zan fita ga kud'in cefane a jalauta har dare dan Allah." Nera dubu d'ayace ya
bata, babu hatsi ko d'igo a cikin gidan. A wulak'ance ta karb'i kud'in.
"Saminu nera dubu d'aya ita zata yi mana abinci uku a gidannan? Allah ya tsine talauci da
auran miji talaka Saminu ka cuceni daka aureni bazan yafe maka ba." Cikin mamaki Saminu ya
dubeta duk da wannan ba karon farko ba kenan a haka suka saba gudanar da rayuwarsu.
"Tur da auren jahilar mace kinji kunya Farida, in kin so karki dafa komai akwai ruwan sha, sai
kuita sha ku danne cikinku da duwatsu mtwss. Ya ja dogon tsaki ya fice ya barta a wajan tana
mayar mishi da martani, da mugun baki kamar ba mijinta uban 'ya'yanta ba."

Asibiti
Ahankali na soma motsa kunburarrun idanuna wanda su ka sha bacci su ka gode Allah,
Hannuna naji shi tamau da ankwa. Juyowa hagu da damana nayi, gandirobobine zaune a gefe
da gefena. 'Yar uwata Jamila na duba wacce take zaune a farar kujera tana gyangyad'i.
Hawayene suketa surnanowa daga gefen idanuwana, komai ya shiga yi mun yawo a kaina,
turyan turyan zuchiyata ta soma haskomun Irin rayuwar da muka taso muka samu mahaifiyarmu
na gudanarwa da mahaifinmu tun muna k'anana, duk da Mahaifinmu baiyi tsawon rayuwa tare
da mu ba ya amsa kiran ubangiji. Baki na cije ina kaico da mahaifiyarmu ta kasance uwa a gare
mu, Mahaifinmu ya bar kari tun ran tubani, kusan shi zamu tuhuma akan danme yasa yabi rud'in
soyayya da jan baki da hoda, wajan zab'ar mace. Me yasa bai zab'o mana uwa ta gari ba, mai

2 / 14