Angulu Da Kan Zabo Book By Badiat Ibrahim

Author :  Badiat Ibrahim Mrs Bukhari Category :  Read Hausa Novels

Chapter   1 / 14

1 to 3K   out of 40.5K words

DAGA ALK'ALAMIN
BADI'AT IBRAHIM
MRS BUKHARI (B4B)

*ANGULU*
*DA*
*KAN ZABO*

1_2
Da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai.
Ina miƙa godiyata ga Allah subuhanahu wata ala, sarkin da babu irinshi, daya bani damar
rubuta wannan littafin mai suna a sama. Wannan littafin tsumagiyane ga mata harda mazan ma.
Wannan labarin labarine wanda ya faru a gaske, babu abunda na ƙasa bisa labarin. Hatta
garurruwan ciki ban sake komai ba, unguwanni kawai na sassake, sai kuma sunayen jaruman
labarin. Ku biyoni da sannu zaku gane me labarin ya ƙunsa.


Kano:

Anguwar Court road:
High court
"Bayan sauraron wannan sharia da kotu ta yi, tare da gamsuwa da hujjojin da aka gabatar a
gaban wannan kotu mai alfarma, tare da takaddar asibiti data tabbatar mana Hauwa Sada a
cikin hankalinta take, bi ma'ana bata d'auke da matsalar data shafi k'wak'walwa. Kotu ta yi ma
Hauwa sassauci sabida bata wahalar da sharia ba, wajan amsar laifin data aikata. Kotu ta
yankema Hauwa hukuncin d'aurin rai da rai a gidan kaso." Damm Damm ya buga gudumar kotu
wacce take nuni da an gama wannan case d'in.
Hawaye nake zubarwa sosai, tashin hankalin da nake ciki a dai_dai wannan lokacin, ba abu
bane da zai fad'u balle harya rubutu masu karatu su fahimta ba.
Aminu na kalla, idanunshi sun k'ada sun yi jawur tabbas yama fini shiga tashin hankali. Dubana
ya sake sauka akan yarana mata, wanda naja musu abun fad'en da har abada baza'a dena
nuna su dashi ba. A gefe kuma ga k'annena wanda na kasance musu uwa da uba,
kasancewarmu marayu, duk da ko wacce a cikinsu a k'ark'ashin inuwar Aure take. Mak'otana
wad'anda akai zaman mutumci na kalla.
Duniya kenan, yanzu rayuwata a killace a waje guda zata k'are babu wani motsi?" wata
gandiroba macece ta iso cikin d'an akwakun da nake tsaye, hannayena sanye da ankwa, ta
ingiza k'eyata tana wani mun muruzai."
Kaina a k'asa muka sakko, 'yan sanda kuwa ta gaba da bayana duk gasunan, sabida tsaro. Ina
jiyo sautikan koke_koken dangina da masoyana, a cikin kunnena. Amma in d'ago in kallesu na
kasa. Hantar cikina sai rawa kawai take yi, hakan ya yaifar mun da zazzab'i me mugun zafi, da
jiri da naji yana shirin ka da ni. Ga k'irjina da nake ji tamkar yafi komai nauyi a jikina, tun sanda
wannan k'addarar ta faru na soma jin wannan ciwon k'irjin, wanda ban tab'a samun sauk'inshi

ba."
muna fitowa bakin k'ofar kotu, nan fa manaima labarai suma suka kunno dan gudanar da
aikinsu, wannan gandiroba dake rik'e dani sai naga taja ta tsaya." Nan suka shiga jero mun
tambayoyin da bansan ma ta ina zan soma amsasu ba."
"Ku yi hak'uri ba wani abu da zata iya cewa a halin yanzu, dan Allah ku barmu haka nan muji da
abunda ke damun mu" Cewar Aminu kenan Baban su Mardiyya."
Gandirobarnan ta jani har zuwa gaban motar da zata sada ni da gidan yari. Duk da dai kwanana
biyar a cikin gidan yarin, ina jiran sharia. Amma a waiting room nake ba asalin cikin yadi ba."
Waiting Room wani dogon ɗakine wanda anan ake ajjiye masu laifin da suke jiran shari'a.
Jikina da 'kafafuna na rawa na d'aga k'afata na shiga cikin motar na zauna.
D'ago kaina na yi da sauri dan yima Ahalina kallon k'arshe.
Aminu na gani a gaba, sai Mardiyya d'iyata tana rik'e a hannunshi. Idanu ya k'ura mun cikin
rauni da sarewa yace."
"Wannan itace k'addararki Hauwa ki yi hak'uri, sannan kiy ta yin istingifari, Allah mai sauraron
kukan bawane kuma maji roƙone."
Sabbin hawayene suka zubo mun. Hak'ik'a nayi rashin Aminu. Da yarana, ta tabbata na bar
ahalina."
K'ofar motar Aka rufe Direba kuma ya ja motarshi ya fice a cikin kotun."

Aminu
Dauriyace kawai ya ke yi, domun baya son yayi kuka a gaban yaranshi, ya sake tsinkar da
zukatansu, kuka suke yi sosai. dangin Hauwa ne su ke ta rarrashinsu.
Nanfa 'yan jarida suka yi ca akan Aminu, a k'ok'arinsu na lallai _lallai sai sun ji k'wak'wab. Da
kyar suka fita a cikin kotun, tare da taran abun hawa.

Jakara city Kano:
Anguwace ta talakawa masu fad'i tashin naiman na kai, dan ganin asiri ya rufu.

GIDAN IYAYEN HAUWA:
Maza ne a k'ofar gidan anata k'arbar gaisuwa, taburmai ne manya a shinfid'e, cike da dattawan
anguwa. Baffa Junaidu yana ganin tsaiwar Adaidaita sahun su Aminu, saiya tsallako ya taso.
Su mardiyya kuma suka shige cikin gida, inda ya kasance shima dank'am da mata 'yan
ta'aziyya. Baffa Junaidu, k'ane yake ga malam Sada mahaifinsu Hauwa, shima a cikin layin
yake tare da iyalanshi, gidajensu a jere suke dana juna.
"Aminu Yaya shariar ta kasance kuma me ake ciki, sunk'i ba da belin Hauwa ko?" Aminu ya
rasa me zaice, dan zazzab'ine a jikinshi yau kwana bakwai kenan, baya ko iya rintsawa tunda
ya ji labarin abunda Hauwa ta aikata, a cikin tashin hankali da jinyar rayuwarshi dake shirin
salwanta yake. Nunfashi ya ja yace." "Baffa Junaidu, Hauwa dai mun yi iya yinmu, dan ganin anyi duk binciken daya dace a gudanar,
dan wallahi duk inda lauyan yasa k'afa nima anan nake sawa, bamu zauna ba. Amma duk wata
hujja ta tabbata Hauwa ta aikata laifinta, dama ita bata wahalar da sharia ba, a zaman farko ta
sanar da gaskiyar lamarin." Muryar Baffa Junaidu na rawa yace.

"Hukuncin kisa ne ya tabbata a kanta ko?" kai kawai Aminu ya iya gyad'awa, zuchiyarshi na
tafasa sosai.
"Innalillahi wa'innailaihilrajium kaico kaico da wannan mummunan aiki da yarinyarnan ta aikata,
gashi ta jefa kanta da mu kanmu a cikin damuwa.Ni wallahi wannan zaman makokin ma da
akeyi wallahi kunya yake bani, dan kulma ce ta ajjiye mafi akasarin jama'ar dake zaune a wajan,
ga kunyar surukanmu. Aminu ka yi hak'uri naga yanda lamarinnan ya jijjigaka fiye damu dangin
Hauwa. Duk da abunda ta aikata maka amma kana cikin lammuranta dumu_ dumu." Guntun
hawayene ya taru a idanunshi guda d'aya. Aminu Namijine mai zuchiya da k'wazo, ba kasafai
damuwa ya cika bata dama ta rusa shi ba. Amma Hauwa ta rugurgushe mishi jarumtarshi da
k'wazonshi gabaki d'aya."
"Baffa nace ko zamu je gidan yarin muje mu dubota ne?" Baffa ya yi shiru yana nazari yace.
Sai daya nisa yace.
"Gaskiya ne Aminu, babu yanda zamu yi da wannan k'addarar, amma bari in kira Jamila me bin
ita Hauwan sai mu d'unguma ai. Jirani ina zuwa"
A tsaye Baffa ya tafi ya bar Aminu a tsaye a rana, yanayin yana ji tamkar wani irin nannauyan
mafarkine mai wuyar farkawa. k'arar kwarab'abbiyar wayarshi da ke ajjihun wandonshi ce ta
dawo dashi daga zauren tunanin daya lula. Saminu abokinshine yake kiranshi.
"Assalamu Alaikum Saminu, yaya akayi?" Daga cikin wayar Saminu yace.
"Ameen wa'alaikassalam, Aminu k'arfe nawa ne zaman kotun ne?" numfasawa yayi sannan
yace.
"Zaman kotu ya k'are Saminu, yanzu haka ma dubo Hauwa zanyi a gidan yari. Saminu yace.
"Au da gaske ashe rashin hankalin Hauwa yakai ta iya aikata wannan abun? Tabb lallai na
tsinke da lamarin Hauwa, ban tab'a cin karo da mace mai taurin zuchiya da kafiya irinta ba"
murmushin yak'e Aminu yaima Saminu yace.
"Ka fiye sharri, ka bari zamu yi magana inna koma gida, saima naje asibiti dan bana jin dad'i jiri
da ciwon kaine suka sani gaba. Irinna shekarun baya.
"Aminu dama nasan za'a rina an saci zanin mahaukaciya, amma na kusan shigowa kano,tunda
dai mun gama sauke lodinmu, dawowa kawai ya rage mana, dana dawo zan shigo, ka gaishe
da Dada. Sallama su ka yi Aminu ya sauke wayarshi a kunne."

Cikin gidan
Su Mardiyya na shiga cikin gidan nanfa idanu ya koma kansu, sai kallonsu akeyi. Jamila ta ja
hannun ummu da Nanne k'annen mahaifiyarsu da suka tawo daga maiduguri. A k'uryar d'aki
suka zauna dan tattaunawa.
"Ni ummu ki sallami matannan 'yan zaman makoki da suka cika gidannan,wallahi gulmace ta
kawo su ba gaisuwa ba. Tunda can ma Zaginmu suke yi balle yanzu." Hafsa tace.
"Ni fa naga har k'annen Baban shamsu, da matan yayyenshi duk sunzo suna tsakar gida, kuma
fa ba shiri muke yi da su ba. Gulma ce kawai.
Nanne tace.
"Ina zuwa bari inje in sallamesu su watse.
Fita tayi ta sallami kowa.
"Dan Allah kowacce mace ta tafi gidanta mun gode da gaisuwa Allah ya saka, adda'ar bakwai
an riga anyi tun asuba. Dan Allah kuje."

Nanfa wasu suka soma ya da habaici harda zagi, da d'aya da d'aya duk suka watse, sannan ta
shige d'aki wajan 'yan uwanta.
Baffa ne yaga mata sai fitowa suke yi a cikin gidan suna surutai harda masu shewa. Kai kawai
ya girgiza ya kutsa kai cikin gidan.
Har cikin uwar d'akin ya shiga.
"Nanne sai kuma kuka ji abunda ya faru a kotu, an yi ma Hauwa d'aurin rai da rai." Nanne ta
dafe k'irjinta tare da fashewa da kuka tace.
"Bamu ji ba, kai wannan masifa da yawa take. Ni wallahi abun yayi mun yawa wallahi." Ummu
tace
"Yanzu tana gidan firsina kenan? Yarinya da yarinta a jikinta bak'ar zuchiya yasa ta aikata
abunda ta jefa kowa a damuwa." Mardiyya tayi maza ta fice a d'akin ta koma falo. K'annenta ne
suka mara mata baya, nan suka shiga rera kuka abun tausayi.
Su Nanne ma kukan suke yi. Sai Sameera ce ta daure tace.
"Yanzu dai adda'a ya kamata mu bisu dashi kawai. A dena tono maganarnan sabida su
Mardiyya. Baffa yace.
"Yaron da zai Aurenta ma yana waje a cikin 'yan zaman makoki. Jamila ki taso mu je firsinan mu
duba ita Hauwan mu dawo kafin malaman da zasu raba gadon naku su iso, a raba a sauke ma
Marne nauyi."
mik'ewa Jamila ta yi dama da mayafi a jikinta bata cire ba. Fitowa su ka yi falo, Mardiyya tana
zaune k'annenta duk suna jikinta sun mayar da'ita uwa. Cikin rauni Jamila ta ciro nera d'ari biyu
a k'ulle a bakin zanenta tace.
"Kunga Mardiyya ku kama hanya ku tafi gida ku zauna a wajan Dada. Ki daure zuchiyarki
sabida k'annenki kuyi ta hak'uri. Mardiyya jikinta na rawa ta amshi kud'in ta ja k'annenta. Tare
suka fito da su Baffa. Wajan Aminu suka nufa.
"Mardiyya ina zaku je? Ya jefo musu tambaya, tausayinsu da kunyarsu duk ta gama cika shi.
Cikin shesshek'a mardiyya tace.
"Abba gida zamu tafi" Ajjihunshi ya laluba bashi da ko sisi yace.
"Ki kula dasu ku tafi a hankali har ku isa gida." Cike da mugun tausayinshi Jamila tace
"Na Basu kud'in abun hawa ma, su samu su isa da wuri.
"An gode Jamila" Titi suka nufa dukkansu. Su Aminu suka hau Adaidaita sahunsu, su mardiyya
ma su ka hau nasu.

GIDAN D'AN KANDE
KURMAWA PRISON:

Hauwa
motarmu ce ta tsaya a wajan ajjiye motoci, gandiroba ta fito dani daga cikin mota. Zuwa ciki.
Mata ne guda uku akan layi ana musu tambayoyi akan laifin da suka aikata. Duk da suna da
takaddu mai d'auke da bayanan mutum a ciki da irin laifinshi. Hakan baya sawa su kasa
tambayarka ka sake jaddada laifinka a gabansu. tsawa Gandirobar da ke zaune a kujera ta
daka ma wata data kira da Ramatu. "Nace laifin mai kika aikata aka kawo ki gidannan kiyi magana."
Cike da tsoro da fargaba Ramatu tace.

"Kisa na aikata aka kawoni gidannan." Kallonta gandirobar tayi kawai tace.
"Mariya a kaita a bata kaya, Ramatu in akwai waya a jikinki ki fito da ita kafin a bincikeki.
Sannan ki cire d'ankunnenki da sark'a da zobe ki ajjiye. Mariya zata kai ki block d'inku. Ke
matso kefa meye laifinki?"
ni dai ina tsaye ina sauraronsu har akazo kaina."
"A'a 'yar shuwa kun dawo, hala kotu ta yanke hukunci kenan?" Kai kawai na gyad'a mata.
Gandirobar da muka je kotu tare ta ajjiye takaddata. Karantawa tayi tace."
"Mariya Ga Hauwa d'akinsu d'aya da Ramatu, ku tafi tare a basu kaya." Jiki a mace dukkanmu
muke binta har zuwa wani ofishi. Kaya ta mik'a mana."
"Gashi zaku rik'e a hannunku, in lokacin fitowa waje yayi sai ku saka, amma in kuna d'aki zaku
iya zama da kayan gida a jikinku. Amma in zaku fito yadi ku tabbatar kunsa kayanku, dan a
tantance ku. Ku yi hak'uri k'addara kowa da irin tashi. Zaman gidan gyaran hali ba zama a
jahannama bane. Da sannu zaku yi walwala har nutsuwa ta saukar muku uhm?" ku muje in
rakaku block d'inku."
muna biye da ita a baya. Ni dai jefa k'afata kawai na ke yi amma babu nutsuwa a tare dani.
Hankalina ya na wajan Aminu da 'yan yarana."
*BLOCK B*
haka naga an rubuta a jikin bangon da muka sha kwanarshi. wani dogon coridor muka shiga
mai d'auke da dakuna, amma kuma abun mamaki d'akunan a bud'e suke ba a kulle kamar
yanda nayi tunaniba. Wasu sai kai kawo su ke yi a zauren, yayin da kuma wasu suke zazzaune
a k'ofar d'akunansu, wasu ma suna zaune akan gadajen kwanansu. "Sannu sir mariya." Shine abunda suke ta ce mata. da fara'a take ta amsawa. Wani d'aki muka
shiga mai d'auke da gadaje shidda sama da k'asa na kwanan mai rai goma sha biyu kenan.
Mata uku muka samu a zaune a d'akin. Biyun suna k'asa a zaune suna cin abinci. D'ayar kuma
tana zaune a bakin gado tana sak'ar hular sanyi na jinjiraye sak'ar kwaraishe na farin k'ulu." "Sir mariya barka da zuwa. Munyi bak'i ne?" A cewar ta zaune a kan gadonta kenan."
"Eh uwatale ga bak'inan Wannan Ramatu wannan Hauwa. Dubanmu tayi tace.
"Hauwa, Ramatu ga abokan zamanku nan, nanne dak'in naku, sai ku kula dan Allah ku saki jiki
kuma"
Hawaye na soma zubarwa, take wata nadama mara amsani da saukarmun. Uwatale ce ta
zaunar dani a bakin wani gado, matan da suke zaune kuma suka kamo hannun Ramatu suka
zaunar da'ita.
Zuchiyata ce ta tsinke sosai.
Yanzu a cikin d'akinnan da gidannan zan k'araci rayuwar duniyata? Uwatale tace.
"Kuka ya zama dole, mu muka k'adartoma kanmu wannan k'addarar, da sannu zaku zama 'yan
gida. Shekarata goma a cikin gidannan, nayi kai harna zama 'yar gari, nice shugabar d'akinnan,
ko wacce anan ta same ni. Hauwa kuyi hak'uri kunji?" Murmushi mai ciwo na sakar mata, wani
irin zazzab'ine ya rufemun ganina da ji na, take na soma rawar sanyi, kankace me sai Amai.
matannan biyu su ka yi tsaye a kaina harda ma mak'otan d'akinmu. Uwatale kuma ta je ta tawo
da Sir mariya.
Jikina ta tab'a taji shi kau da zafi sosai.
"Sannu Hauwa, zaki iya lallab'awa mu je d'akin shan magani?" Na kasa ce mata komai ma, sai
uwatale ce ta taimaka mun na mik'e tsaye. Ahankali nake takawa bana ko iya gani, har muka

isa d'akin shan magani."
"Sister Aisha ga mara lafiya nan ki duba ta, inna maganine sai a bata magani, in kuma na zuwa
asibiti ne sai a kiran danginta." Sir Mariya ce ke magana" Wacce aka kira da sister Aisha ta
soma tambayata bayan taji zafin jikin nawa."
"Yaya kike ji yanzu haka?. Cikin nauyin k'irji nace mata.
K'irjina ne ya ke yi mun kamar an d'auramun garwashi, ga nauyi, sai jijiyar bayan kunnena kuma
da take yi mun ciwo, har wajan ya kumbura."
Sister Aisha tace da Sir Mariya
"Gaskiya sai an fita da'ita zuwa asibiti a waje, sai an hanzarta kuma."
"Okey, Uwatale kuje d'aki ta saka kayanta, sai ku sameni a office bari in je a gama shirya
komai."
Uwatale ta kaini d'akinmu na saka kayan 'yan fursina a jikina, kayan dana jisu tamkar k'aya na
saka.
Kan Kanta muka je, na ba da lambar Aminu, dan a kirashi. Amma bai d'aga ba."
"Hauwa bai d'aga ba, gashi baki da ko kwabo a kanta, saidai akwai d'ankunnen gwal d'inki da
sark'a da zobe." Ni dai na kasa magana, mota aka sani, tare da ankwa a hannuna. Sai Asibitin
malam Aminu kano

Aminu
A bakin kof'ar prison din Adaidaita sahu ya ajjiyesu. Baffa ne ya biya kud'in, domun babu kud'i
su a jikinsu.
Aminu yana biye da su Baffa jiki ba laka, har zuwa kan kanta.
"madam sannu da aiki fa" Jamila ce ke magana da gandirobar da take kanta."
"Yauwa wajan wa kuka zo?" tace
"Wajan Hauwa Sada, wacce aka kammala shariarta yau, ni ƙanwartace uwa ɗaya uba ɗaya,
wannan mijinta ne, wannan kuma Babanmu ne." Dubansu ta yi tace."
"Yanzu kuwa aka fita da ita zuwa Asibitin malam Aminu kano, ba lafiya, ta bamu number Aminu
mun kira bai d'auka ba" Da zafin nama Aminu ya iso gaban kanta bakinshi yana rawa.
"Meke damunta dan Allah? Nine Aminu"
"Gaskiya bamu sani ba, sai dai zaku iya zuwa asibiti ku ganta, dama dole za'a kira ku, sannan
bata da kud'i a kanta, sai dai akwai zinarenta da aka ajjiye mata, bari a baku." wata durowa ta
jawo ta ciro golds d'in a bak'ar leda ta mik'a musu. Jamila ce ta amsa. Nan kuma suka
d'unguma Asibitin Aminu kano."
Hauwa
Muna isa aka shiga dani zuwa ciki, gandirobar da su kai mun raki su biyu, suna tsaye a bakin
k'ofar da aka shiga dani.
ni dai ban sake sanin komai ba daga nan."

Aminu
Da hanzari suka fito a cikin adaidaita sahun zuwa cikin asibitin, sun sha wuya sosai, da
tambaya suka iso har zuwa inda d'akin da aka shigar da Hauwa. Aminu ya isa wajan
gandirobobin dake tsaye a bakin k'ofar d'akin yace."

"Dr ya sanar da ku halin da take ne? Kafin su bashi amsa Dr ya fito a cikin d'akin. Da sauri
Aminu ya mik'a mishi hannu suka yi musabaha.
"Dr ya jikin nata?" Baffa ne ya matso yace.
"Likita a wanne hali take yanzu?" Jamila kuwa tana zaune sai hawaye take zubarwa, koya ta
tuno abunda ya faru sai taji tamkar ta had'iye zuchiyarta ta mutu ta huta. Har ji take yi dama
itace a kaima d'aurin rai_ da rai da taji dad'i. Ta fita daga wata duniyar zuwa wata duniyar."
Likita ya sauke ajjiyar

1 / 14