Author : Hadiza Adamu Shitu Category : Hausa Read
basiru ya yi
murmushi.
“Amina wato k0 ‘yar karar ma babu
kina nufin wajen Amira kike son zuwa.” Abban
Amira hankalina ya kasa
kwanciya ne tun da auren Amira ya mutu.”
Kwalla ta taru a idonta har ta kasa karasa furta
sauran kalamanta. Alhaji basiru ya zauna a
gefenta.
“Amina ki kwantar ‘ da hankalinki
kamar yan da nawa hankalin ya. dan kwanta a
lokacin dana riske labarin ; mutuwar auren Amira
hankalina ya yi mutukar ta shi, na shiga damuwa
wadda ban taba shiga ba, sai dai shigar Alhaji
Musbahu cikin lamarin ya dan kwantar min da
hankali har na yi tawakkali na soma zargin hakan
Alkhairi ne 21 ga Amira amma ina goyon bayan ki
je ki ga Amira yan da ta yi kibarta hankalinta
akwance ke duk kin tsangwami kanki saboda son
‘ya’ya irin naki.”
Ya Karasa maganar da salon zolaya. Ita ma ta yi
murmushi ta ce.
Har na kai ka.? yace waneni ya bata‘amsa hade
da rike haBa. Ta ; fita kawai tana dariyar yanda
ya yi.
’Daren ranar da Amira ta shanye kunun gishirin
da ta damawa kanta dare ne da ya waye mata
batare da ta rintsa idanunta'ba, k0 da na minti
daya saboda wahala da azabar ciwon ciki da
amai da ta dinga _yi har ya zarta na maganin da
tasha a baya.
Ta yi kuka tayi nadamar abin do. take shirin
aikatawa a daren wahalar tunatara da ita mutuwa
da iri makomar wanda ya kashe rai ya kuma
mutu “
'hanyar aikata hakan wahalar duhiya ma ke nan.
tayi Nadama sosai a cikin ranta da alkawarin ba
zata sake yin waniyunkurin zubar da cikin nan ba,
k0 ma dai menene zata jure shi domin iyakarshi
kunyar duniya ce kadai ta yiwa Malam Allah ya
isa sau ba adadi lokutan da numfashin ma ya
soma yi mata wuya. ‘
’ nurkursusu da juye juyen wahala ya kaita har
zuwa wayewar gari a‘ dai dai lokacin'da ta fara
fitar da rai da rayuwa tsananin ya kara tsananta
a gareta barcin' rahma ya kwasheta wan da bata
san ma ya dauke ta ba.
Dai dai lokacin karfe bakWai‘ ne har da rabi na
safiya, bata san‘ ina ta lulaba barci ne? Mutuwa
ne? Suma ne.? Duk bata san me take yiba a cikin
ukun nan ba har; sai data ji muryar Hajiya kaka
na tashin
ashe Ina duniya ta fada a zuciyarta ya yin da
take; nanata salati tsowon rayuwarta ba zata
manta da azabar da ta sha a daren jiya ba. '
Hajiya Kaka ta ce.
‘ “To kasa Sarkin barci _ni zan shiga gidan Uwani
gashi Atine ma bata nan sai ki tashi ki kula mana
da gidan.”
Bata iya cewa komai ba ta dai ta shi ta mike
zaune haka Hajiya Kaka bata‘jira jin ta bakin taba
ta daga ta mike sai ta yi waje.
..Amira ta mike cike da mamakin yan
> da take jin jikinta babu ko burBushin ' ciwon
jiya sai barci kawai da kasala da suka addaBeta
jikinta babu
Tana mikewa ta ji wani abu mai dumi na bin
jikinta gabanta ya yi wata irin faduwa wadda ita
kanta bata san dalilin yin ta ba tun da abin da
take zaton tana nema ne bata tsaya binciken
kanta ba ta shiga toilet cike da tabbacin jini ne
wannan wahala.
Ta fada asarari ta suma bincikar ,
kanta sai dai ba abin da ta yi zato din bane wani
farin ruwa ne jikinta asanyaye ta yi wanka ta fito
ta shirya cikin dinkkin doguwar riga ta fito flour
ta zauna tana karyawa da bakin shayi wanda
yasha kayan kamshin gargajiya zuciyarta cike da
firgicin halin rintsin da take ciki, ita daya jal
bayan mutane da dama da suka yi
sanadiyar shigarta suna cikin kwanciyar
hankali abinsu;
Kalmar da Ummama tasha fada mata ga shi ta
bayyana a kanta; sallamar da ta ji ce ta sata. jin
wani irin gigitaccen faduwar gaba har kofin data
riqe a hannunta ya kusa subuce mata: sai dai bai
fadin ba amma ruwan dake cikinshi ya dan zubo
mata.
Idanunta na ,kallon bakin kofar har. Umman ta
shigo flour.
“ Umman mu sannun kida zuwa
Tana maganar idanunta 'na kan led an dake
hannunta ta yunkura ta mike
‘ ta sake gyarawa Umman darddumar da take
zaune a kai. ‘
Umman tun da ta shig0 binta kawai take da
'kallo faduwar gabanta ne ya kara tsananta har
ta kasa zama Amira ta ce.
“Umma ki zauna mana ga waje kawo Umar don
na san kun sha tafiya.”
Umman ta sauke ajiyar zuciya ‘ta zauna tare da
mikawa Amira Umar kamar
yan da ta bukata.
Amira ta durkusa ta gaisheta ta amsa “ sannan
ta ce “Ina Hajiyar.?’
Amira ta ce.
“bata nan ta fita gidan Uwani ni kadai ce a gidan
bari na kawo miki kofi ki sha tea.”,
. Umman su ta ce.
“A’a Amira bar shi sai da muka karya muka
taho.”
Amira ta zauna tana tambayar kannenta Umar na
kan cinyarta tana bashi shayi.
Sun yi shiru na tsahon minti biyar Umman tace.
“Ammira Hankalina ya kasa kwanciya tun ranar
da naji labarin
mutuwar aurenki shi yasa yau dai nace bari na
daure na zo na ganki domin jikina
yana bani ~ba haka kawai wannan sakin ya faru
ba, kamar yan da ake dorawa matar Alhaji
Saminu' sai kuma dana ganki zargina yake. son
ya zama gaskiya ta Bangaren da ban taba zato
ba daga
gareki.”
ba‘ Tuni murya Maman Amira ta soma sauyawa
zuwa rawa rawa na tashin hankali, ita ma tuni
Amiran kwallar da take makalewa suka soma
zubowa akan fuskarta.
“Amira irin sakayyar da zaki yi min' ke nan duk
irin tarbiyar dana baki ban taba zaton zan sameki
a yanda kike ba, amma shi ke nan na gode da irin
sakayyar da kika yi min.”
Har kwalla sun soma zubo mata bakin ‘ciki ya
hanata karasa maganganun da dama bata yi
niyar furta wa Amira suba kawai ta mike tasa
hannu ta dauki‘Umar’ '
tana laluBan mayafi tana sharar kwallar dake
zubo mata. ‘
Amira ta ce
Bankada
Chapter9
“Mama ban taba canzawa ba daga
yan da kika sanni ba ban kuma taba tunanin
canzawa daga irin tarbiyar da kika baniba.”
’ Maman Amira ta watsa mata wata,. irin harara.
“Zaki rainamin hankali ne kamar ‘ yan da kikewa‘
hajiya kina nufin wannan cikin da kike ‘mikewa da
kyar cikin wata daya ne a jikinki?” ‘
Amira ta girgiza kai.
“Mama bani da‘ abokin shawarar daya wuce ki
tun ina ‘yar Kankanuwata zuciyata bata taba
rikon abin da baki sani ba sai wannan Kaddarar
Boye miki da na yi na yi ne kiyarda da hanzarina,
amma ban taBa yin zina ba da son raina ba,
wannan
kaddara da ta same ni ma fyade aka yimin.”
Tun~ da Amira ta soma magana Mamamta ta ci
gaba da tafiya cikin dacin rai Amira na bin
bayanta bata ‘tsaya Ba Amira ta ce.
“Malam balarabe ne fa Mama ya yi
‘min fyade lokacin dana yi ,zuwa na
qarshe wajen karBar rubutu. Cak maman Amira
ta tsaya daga takun da zai kaita soron‘gidan ta
juyo tana duban
fuskarta Amira Jin ta ambaci ,malam
“Mai kika Ce Amira.” Tana SOn tabbatarwa da
abin da kunnU'wanta suka jiyo mata. Amira ta
ce.
“Mama gon .girman Allah ki tsaya ki saurareni
domin ke kadai ce kika
san halayyata ke kadai nake zaton zaki yar da
dani domin karya k0 kazaf1 ba aikina bane ki
shigo.” "
Maman Amira ta juya floun ta zauna a in da suka
zauna jikin Mama‘ya yi sanyi sosai ita ma ta bita
ta zauna Amira ta soma bata~labarin tun daga
ranar da suka fara zuwa wajen ‘malam har zuwa
ranar da ya' yi mata fyade da kokarin ta na zubar
da cikin tun kafin ta goga musu abin kunya.
(Inna lillahi Wa inna ilaihir raj’un)Maman ta furta
bade da goge zufar data keto mata ta yi ajiyar
zuciya~ sannan ta amsa.
“Amm kin yi kuskure a tun farko da kika'gujewa
Bacin raina kika- Boye min da kin tunasar da ni a
tun ranar da na yi iya
kokari wajen yin wani abu mai amfani da zai
hana k0mai taSiri a rayuwarki amma bawa baya
wucewa kaddararsa kuma kada ki ci gaba da
Boyewa ki bayyana halin da kike ciki domin Boyon
bazaiyi miki amfani ba, ka da ki sake nufin
zubarwa domi; zai iya tafiya da rayuwarki idan
idan kuwa kika dage a hakan zaki iya fadaWa
cikin fushin ubangiji “Allah ya kiyashemu, sannan
kada ki nunawa kowa cewar na san maganar ki
yawaita addu’a da neman ‘ sauki 'ni ,_ ma zan
taya ki Amira ki roki ubangijinki shi kadai domin
bawa bai isa ya bawa bawa abin da Allah bai
bashi ba, kin ji. '
Tun farko zuciyata bata amincewa zuwa wajen.
malam din nan ba" tun da ni
'Ban jefa kafaba sai dai tsoron abin 'Abbanku zai
ceya hanani nahanaki da kuma boye min wasu
abubuwa .dazaki yi tun da . farkon zuwanki
Wanda tun a lokacin ya dace ki gane manufar
Malam a kanki amma baki gaya min ba to
Kaddara dai tariga fata;” Ta mike da hanzari
zuciyarta na"cike da tukukin bakin ciki suka yi
sallama ta’ tafi Amira sai ta wani 'dan‘ sanyi‘ a.
kirjinta ta gyara~- gidan tsaf. Ta dafa masu
abincin rana
. ***
' Alhaji Saminu tun ranar da ya Saki: Amira
zuciyarshi bata' huta mishi da jujjuya. kalamanta‘
ba yadda aka yi aka bata’ rayuwarta a tun
lokacin da take gaya masa harya zargeta da yin
karya ba sai dan ya hangi
zamansu a nan gaba zata iya jefa rayuwarta ga
yin abin da yafi hakan, saboda ta mallake shi yaji
ta fice masa daga ’rai, domin bai ’samu abin 'da
ya zata‘daga gareta ba, kuma ya hangi‘ cikin a
tare da ita ya zama tilas ya rabu da ita dan haka
ya yanke igiyoyin aurenta uku dake kansa, sai
'dai zuciyarshi ta kasa hutawa da abin da
yake'hangen tausayi ne tsantsa ya ji yana
mutukar tausayin - Amira har yana jin da a
lokacin da tausayinnan nata ya ziyarce‘shine
yanzu zai iya hakurin zama tare da ita illa
kawai‘ya
kaita a cire cikin yanzu kuwa da ya saketa babu
wata dama da zata sa yaci gaba da zama da ita
dukkuwa da yanda tunaninta yake kwarzaBar
zuciyarsa.
Ya zama kullum sakawa*da kwancewa kawai
yake yi yana tuna irin dacin da Amira zata shiga
da kuncin rayuwa‘bayan iyayenta sun ‘ gane
ajiyar da take tare da ita me yiwuwa‘ta rasa
ranta wajen circ cikin k0 ta haife shi ta zama
abar nunawa a’bar kyama a idon jama’a. ‘
' Kilama iyayenta su koreta, yarinya karama
yanzu, haka da yawan yaran da suke Batawa
suke tsintar kansu.
Haka iyaycnsu ke nan suke shiga halin da ‘ yakc
ji a cikin ranshi abin ya dame shi bare ace‘yarsa
k0 qanwarka a yi mata' haka lallai ‘
‘rayuwar 'bariki bata da wani amfani sai cutarwa
da “nadamar aikatawa, su yi ta ,kwanciya da
yaran mutane wasu su dau ciki su zubar wasu
kuma su haifa suna tsoron su. ce na kane koma
‘na wata rana su kawo maka 'shi cikin iyalanka
yaya zaka ji, k0 da wanne ido zaka kalle yaran ko
an zubar k0 an haifar maka ba naka ne dai Allah
ya sani. . .
Kuma sai kun yi shari’a da shi _ _ ubangiji ta
yadda aka yi ka Samar dashi ta mummunar
hanYa.
' *****
,’ Amira na zaune a tsakar gida tana gyaran
'wake hajiya kaka na daga cikin kichin tana
~shara suna taBa hira da Amira' Hajiya Atine ne
ta dawo daga tafiyar da ta yi wajen jinyar jikanta
da ya kwanta a' Asabiti tSawon kwana goma ta
yunkura da hanZarinta‘da nufin ‘ tarar hajiya
Atine da‘kayan da take rike da su amma
nandanan cikinta ya hana wannan yunkurin
har sai data'dagora qaga da kyar. - ‘ Hajiya‘
Atine na kallonta ya yin da ita ma hajiya kaka ta
fito tana cewa muryar wa nakeji kamar na atine
Hajiya Atine ido kadai 'ta 'zubawa- Amira
kallonta ’take jikinta a sanyaye harta~ Zauna
Kaka na tambayarta mai jiki da yadda ta' yaji
,sauki.”
idan zata tashi ga shi jikinta ya yi nauyi hajia
kaka ta shiga wani tunani na dabam.”
’ Abubuwan da Hajiya Atine ta hango‘ sai yanzu
ita ma ta kula da hakan tabbas Amira tana
dagawa da kyar ta tashi da kyar.
' Nan da nan sai zuciyarta ta shiga wasu wasi
duk da ba ganita yi cikin ya tasa tayi ba amma
jikinta ya bude sosai kirjinta ya cika ga
mazaunan data sake ajiyewa duk da tana da su,
da ma can.
Hajiya Kaka ta ce “Kada fa na yi girman
dan mutum.
Hajiya Atine ta ce“Haba yarinya tatsitsiya kamar
Amira zata yi, ya dai dace a bincika sosai saboda
yan da lamarin aurenta ya zo da matsala, in ma
cikinne tun yanzu a san da shi da iya kwanakinsa
kinsa Hajiya Kaka ta mike “Haba ni ma
hankalina bai‘ kwanta' ba ‘Atine nakan hasko“
abubuwa da dama game da ita zatonane dai bai
kai na yanzu ba.”
" Ita ma Atine kaucewa kawai take gidan
kada ta tabbatar da mummunan zargi‘.“ Amira
kuwa dake tsakar gida tana jin su zuciyarta nata.
dukan tara tara._ ' Har zuwa lokacin da hajiya
Kaka ta
kwala mata kira ta amsa ta shigo Hajiya’
ta ce“Zauna.” gefenta ta zauna Haj iya kaka tace.
“Wai ni yaushe ne rabonki da al’ada?
Amira na san dai tun zuwanki nan bakiyi
ba.” " Amira ta Ce Wata na biyar
ke nan.”
Ta fada batare da jan dogon nazari ba.
Suka saki salati da tafa hannuwa. Hajiya Kaka
bakinta har rawa yake yi.
Lallai ne ba a banza ba mijinki. ya yi miki saki
irin na kwatance da ban mamaki ban da haka har
yaushe ne rabuwa dake a daren amarcinki ga
shinan kin dauko mana abin kunya cikin zuri’a
zagi da gore gore, da cin mutuncin mahafiyarta.”
' ‘
Hajiya kaka fada takeyi ta na kuka. Hajiya Atine
na bata hakuri tana cewa
“Ai ba ita ce da laifi ba tun da ita ba zata ta so
zubda mutuncinta ba sai dai hali irin na'yaran
zamani da ka haifcsu baka haifi halinsu ba
Amira na zaune tana jinsu ko digon hawaye babu
a fuskarta. ,,
Hajiya kaka ta yi ajiyar zuciya cikin sheshshkar
kuka ta dubi 'Amira “Munafuka‘ kina Wani kallon
mutane ido fiki fiki kin san cikine dake’ tun ‘wuri
baki fada ba har aka daura miki aure to uban
waye ya yi miki cikin sai ki‘ fadamin yanzu nan
tun kafin babanki ya tambayeki dan kin san shi
bada baki zai tambayeki ba meyiwuwa sai ya yi_
sanadin sumar dake idan kin farfado kya bashi
amsa' mutuniyar mutuniyar banza, ba fambayarki
nakeyi.ba ba” Batare da jin fargaba ba Amira ta
ce. ., Malam balarabe nefa kuma ni fyade
yayimin'bada son rainab ba
Kafin' ta Karashe maganar Hajiya kaka ‘
ta dubi Hajiya Atine kamar ,yaya Mallam balarabe
Wanne? "‘ “
Hajiya 'Atine ta ce “Ina na sani tambayeta dai;”
Kafin Hajiya kaka ta soma maganar Amira ta
soma basu labarin abin da ya faru ‘tun ‘ ranar'
da ta kaita wajen Malam Balarabe.” ' ‘ ‘ Hajiya
Kaka 'ta 'mike tsaye cikin hanzari ta ‘dauki wani
murfin faranti ta jefaWa Amira shi a'saman
goshinta.
kinji ‘ min shegiyar ‘yarinya sharri kuma zaki yiwa
malam ‘dan na kai ki wajenshi ya rufa asirin
kamarki me Malam 'Balarabe zai dake mutum
bawan ‘ Allah ne, me riko da bin sunnar ma’aiki
har yaUShe ma kika isa ki yaudare shi bare-har
yai miki fyade saboda dai nina kaiki kawai kike
son shafamin kashin kaza
baki isa ba koda munafukar uwarki baku iSa
hadani da dana ba, da mugun halinku Basai idan
basiru ya ji wannan da wane ido. zan kalle shi‘na
kai ‘yar‘shi anyi lalata da ita lallai yarinYar. nan
kin cuceni. mu .ki sake shiri dan hankali ba zai
dauki wannan ba, tun wuri ki lalubo wanda ya yi
miki ciki.”‘ Ta sake rushewa da kuka. Amira ta
ce. “Hajiya Kaka ai a‘gabanki ya riKe min hannu
kina gani to a wace aya ko hadisin ne aka
halasta mishi ya yi min haka, kuma ai hakan ya
saBawa bin sunnar ma’aiki (S.A.W.) da wacce
hujjar kike bashi kariya ba zai aikata abin da yafi
hakan a kaina ba, _; yanda kika dauke shi ba
haka yake ba lallai a baya daga cikin malamai
masu tsoron Allah kamar yan da kike zargi,
menen ribata da na Bata' rayuwata da wannan
babban abin ' kunyar kawai dan son na Kulla
mishi sharri, haba Hajia
Amira.‘ ma ‘kwallah Suka zubo mata saboda
ciwon yadda,’ aka maids abin kan mahaifiyarta
bayan ta San tafi kowa jin zafin. faruwan abin
' Hajiya Kaka na Kuka tana juya maganganun
Amira a ranta tabbas. mutum mugun icé ne baka
iya gane nagartarshi a fuskar. sa ‘ ‘ ‘
,Dakin ya Yi‘ shiru 'sai sautin‘kukan hajiya kaka
ne kasai ake ji Hajiya Atine tace Ai kuka ba abin
'yi‘ bane...a tsaya a fuskanci abin da ya kamata
a yi kinji dai muganar yarinyar na akwai Kamshin
gaskiya cikinta, kin ga kwanaki' dana raka Habiba
zuwanta' daya bata‘ koma ba dana tambayeta
sai ta ce ita dai ta daina zuwa gurin kowannen
malami domin Malam din
ya gaya mata wata magana da bata yi zaton jinta
daga gareshi ba.
,Na tambayeta amma dai bata gayamin ba ta dai
ce abar maganar shi kawai kin ga da maganar
mai .dadi ce ai da bata Boye min
ba, tun da bata da kamarni, kin ga mu tsofaffine
ba zai nuna mana ba su kuwa yana ganin yarane
musamman da yarinta da ba zasu iya gane in
da ya dosa da wuri ba har sai ta kai yan da ba
za su kwaci kan su ba,
kamar Amira da ya danawa tarko bata ganeba.” ,
.
Hajiya kaka tuni ta shanye kukanta har sai .da
Hajiya Atine ta gama yi mata wannan jawabin
sannan ta ce.
“Yanzu yaya zamuyi wallahi ina kunyar .hada ido
da mahaifin yarinyar nan da wannan maganar.”
Amira idonta a kasa suna digar kwalla ta
baza_kunnuwanta tana saurararsu.
“Yanzu dai‘ abar maganar nan a tsakaninmu mu‘
uku sannan‘muje mu gayawa Malam aika aikar
da ya yi duk yanda yaga za a yi ma sai muji daga
gareshi tun da shi shaidani ne ya san yanda zaiyi
da cikin.
Hajiya Kaka ta zaro idanu. “Yanzu zamu iya cewa
ya yi mata ciki.” ’
Haj iya Atine ta ce.
“Kwarai kuwa ai kunyar mara kunya a sarace idan
muka nuna muna tsoro ai sai ya kawo wasa kin
ga ta shi ma muje da zafi zafi ake dukan Karfe.”
Ta dauki mayafinta dake gefenta ta lulluba.
Hajiya Kaka ma ta yafa nata suka fita tamkar an
zarewa Amira laka ta kasa
motsawa daga in take zaune.
Soron gidan" Malam balarabe-.. a cike yake da
mata su Hajiya suka bi layi har ya zo kansu SuKa
shiga. , .
. yana zaune kan buzunsh1 tun da ya'
hango Hajiya kaka ya ji wani irin nishadi domin
ya san k0 ba maganar Amira ceta kawota
gareshiba Zai sami damar tambayar ta‘ k0da
labarinta ya samu ya zai rage zafin da yake ji
cikin ranshi.
da fara’a gamida da doki ya tarbesu sun gaisa
a takaice Hajiya kaka ta ce
‘ “Malam wata babbar matsalace fa ta taso mu
cikin ranar nan? ' ‘
Ya ce
“Babu damuwa in sha Allah komai zai zo arshc
tun da kun Kara so nan,”
Har ya yunkura da nufin dauko wani
allo ta ce. “Dama Amira ce keda Ciki Wata razana
da ya yi ya koma ya zauna shi kawai ya tabbatar
musu da ceWa ya aikata laifinshi amma sai ya yi
kokarin daidaita nutsuwarshi ya ce"
“Toh masha Allah.”
Ganin Hajiya ta kasa karasa kalaman da suke
bakinta.
Hajiya Atine ta ce.
“Eh Malam Amira na da ciki kuma an same shi ne
kafin aurenta yanzu haka mijin ya sakota tun
ranar' da ta kwana daya a gidansa sai dai da a
ka matsa mata da tambayar wanda ya yi cikin
cewa ta yi kai ne ka yi mata fyade.”
Tun kafin ta gama bayanin cikin Malam ya kada
sai dai ya samu dakeya a fuska har ta kai
karshen maganar ta sannan ya numfaSa hade da
ambaton.
“Inna lillahi wa Inna Ilahirraj’un) wato sharre
sharren da nake ji ana yiwa malamai ni ma ya
zokaina saboda kuna son ku zubar min da kima
da mutuncina shi ne zaku likamin abin da ban ji
ba ban gani ba, idan taimako kuke son ayi muku
a kyauta me zai hana ku fada ‘ ataimaka muku
‘sai kun