Zuma Sai Da Wuta Complete Hausa Novels Pdf by Zahra bukar .pdf

Author :  Zarah Bukar Category :  Tknovels

Chapter   9 / 20

24K to 27K   out of 57.2K words

din.
Gyaran murya yayi, Salma ta dubeshi
Yace "bani labarin samarin ki ?
Dariya tayi
"Banda saurayi, infact ni bana soyayya"
"Miyasa ?
Ajiye pen din hannuta tayi hade da yin tagumi, amaraice tace "Sanadin So Ummata tasha
wahalan rayuwa, daga karshe ma Abbana ya rabu da ita da tsowon ciki, bansan lokacin ba,
bansan anyi ba amma ayadda naji labari yadda komai ya faru yasa kwata kwata na cire so
araina" Kallon tausayi yayi mata, tunda yake gida bai tabaji labarin Ummanta abakin Hajiya ba, saidai
zaiso sani..
Kaman wanda baisan da rasuwan Umman ba yace "ina umman take ?
Kaman zatayi kuka tace "ta rasu, lokacin daban santa ba, i was 3years old tym din".

Maida dubansa Mujahid yayi bisa laptop din yace "bai kamata ki cire so aranki ba, tunda iyayan
ki daban ke daban"
"Hmm, am sacred banso ayi breaking heart dina"
Shuru Mujahid yayi baice komai ba, bayason cikata da surutu, bari yayi sai kuma gobe ya kara
jeho mata wata tambayar.
Cigaba da karatun Salma tayi, lokaci Sallah azahar nayi ya nuna mata toilet dake office din
sannan yafice zuwa masallaci, bayan ya dawo ya tura aka kawo wa salma abincin take away,
godiya tayi.

Karfe bakwai Daddy ya dawo Gida, nan ya tsarawa Mom batun zuwan Jaafar, sosai taji dadi da
batun daddy dan kuwa ta kagara Salma tayi aure ko zata nutsu, nan daddy ya shaida mata
bayan Sallah Isha'i Jaafar zaizo ganin Salma, dadi sosai taji, wayarta tadauka dan kiran Salma.

Bayan Salma ta idar da sallar Magrib, Qur'an dake ajiye a office din tadau ta karanta sannan ta
ijeye ta cigaba da karatunta, lokacin Mujahid yafita masallaci bai dawo ba, kirar Mom tagani tayi
azaman dauka.
Aladab ce ta gaidata, Mom ta amsa sannan tace "Salma kibar duk abunda kike kidawo gidan
yanzu nan, Daddy zai baki wani Surprise"
Farin ciki ne ya kamata, tace "momy miye ne, dan Allah gayamin i cnt wait saina zo"
Dariya momy tayi tace "idan kinason sani kizo maza yanzun nan, kuma kiyi sauri" katse call din
Mom tayi, cike da Murna Salma tahau tattare books dinta ajaka, Mujahid ne ya shigo, ganin
tana hade komai yace "keda kika ce sai 10 zamu tafi, kin fasa ne ?
"Eh nafasa, kaini Gida" cigaba tayi da hade komai zuciyar ta fal murna.

8.20 Jaafar ya iso gate din Gidan Daddy, bai tab'a zuwa gidan ba yasa yakira Daddy awaya dan
tabbar da gidan ne, nan take Daddy ya kira mai gadi aka budewa mai gate ya shigo gidan, cikin
palo gidan Daddy yamai iso, ya shiga yagaida Mom aladabce, sosai mom ta yaba da hankalin
sa, sun gaisa sosai, mai aiki ta kawo mai na shasha baki, shikam Jaafar gaban sane keta
faduwa, har yayi dana sanin kowa kanshi gidan.

Mom kam murmushi kawai take tana saurara isowan Salma....
[9/7, 12:37 AM] Xarah Bukar: Zuma Sai Da Wuta

~na~
©ҳaɾaɧ bųkaɾ
®NWA


43 - 50

Murmusawa Mujahid yayi ganin yadda take cikin walwala. Table dinsa ya k'arasa yadau
wayarsa tare da mukulin mota. Ficewa sukayi daga office suka nufi ma'ajiya motar, Salma na
tafe tana waya da Mom, cikin sauri tayi gaba ta tsaya bakin motar. Wayar sace tayi ruri, ya duba

yaga Junaina da kuma miss call datai mai wanda bai lura ba sai yanzu, tsaye yayi nan inda
yake batare daya karasa inda Salman take ba ya dauka.
"Little sis ya ake ciki ?
Kaman munafuka Junaina tahau duben ko ina a palo gudun kar wani yajita, murya kasa kasa
tace "yayA naga ya jafs ya fita, kuma naji yana waya da wani zaije ganin wata yarinya, i dont
know wace yarinya ce"
"Yaushe ya fita ?..
"Yadan jima kuma bai cewa Hajiya Komai ba"
"Okay Sis, ki cigaba da samai ido, i'll call you later" katse call din yayi ya karasa motan suka
shiga, sai sannan ya tambayi salma dalilin tafiyar ta, bata boye maiba ta fadi mai Mom ke
kiranta kuma it urgent.
Shuru Mujahid yayi yana tunani anya ba gidansu Salma yaje ba, wata zuciyar tace it cnt be
possible, miye zai kaishi gidan, saidai surprise da Mom zata bawa salma ne ya tsaya mai arai,
zuciyar sam bata aminta da hakan ba, kuma baiji yana son tafiyar Salma ayanzuba. Kallonta
yayi da gefe ido yaga tana latsar wayarta fuska ta dauke da murmushi.. Murmushi yayi sannan yaja wani wawan burki da saida ta tsorota, afirgice ta kalle shi, gani
tayi ya daura kansa bisa steering hannusa dafe kan gefen cikinsa, murkutsutsu yahau yi tamkar
wanda zai mutu.
Tsabar gigita bata san sanda takai hanunta bisa bayan saba tanai tambayarsa maike damunsa,
kasa magana yayi banda cije labb'a da yake, fita tayi motan ta zagayo gurin sa. Tambayarsa ta
kuma tayi, murya ciki ciki yace "am sick, can you drive ?
Kai ta gigiza alamun eh, taimaka mai tayi ya koma dayan sit din sannan ta shiga taja motar.
Kaman mai shirin kuka ta kalle shi, "wana asibiti zamu ?
"Kaini gida kawai" ya fada yana lumshe ido, shingidewa yayi akan sit kaman wani marar lapian
gaskia.
Hankali tashe tahau driving ba tare data tuna kiran da Mom ke mata ba, suna isowa gidanshi
ta taimaka mai suka shiga ciki ayayinda sai faman cemai sannu take, shikam dariya ke cinsa
yana gimtsewa. Zaunar dashi tayi kan two sitter sannan ta dube shi, murya cike da tausayi tace
"sannu yaya.." Yi yayi tamkar baiji taba saima rufe ido dayayi, itakam tanason tafiya ga dare yafara lulawa,
gyara zama tayi ta fuskan ceshi tanai karemai kallon aranta tanai kara jin sonshi. Sunkai 20mins
ahaka kafin nan ya bude ido, suna kallan juna, lumshe ido yayi yace hado min tea nasha
magani" Ba musu ta mike ta shiga kitchen ta hado ta kawo mai, k'insha yayi ya ajiye akan yayimai zafi
da yawa, zama tayi tanai jiran tea yayi sanyi tanason tafiya saidai bata iya barin sa cikin larura.


Har kafar Tara su Daddy da jaafar na zauna suna jiran salma, shuru babu labarinta, sau kusan
hudu Daddy na kiran wayarta babu respond, ransa ne ya bacci, nan yahau tambayan Mom,
cemai tayi skull ta shiga karatu saboda exams da zasu fara, jin shaanin karatu yasanya Daddy
yayi calming down, dan yasan lokacin exam Salma bata wasa. shikam Jaafar dadi yaji, amma
aransa mamaki yake ace yarinya har yanzu bata dawo ba, jinjina kai yayi "anya ta arziki ce
kuwa" azuci yayi maganar.

Hira kadan suka tab"a Daddy yace mai yayi hakuri idan ya dawo daga tafiyar sai yadawo kafin
nan diyarshi ta gama exams sai ayi magana, Jaafar kam bai damuba, gaba ta kaishi gobarar titi
a Jos, san samu ma kar Daddy ya kuma mai zancen. Sallama yayi masu yabar gida.

Mujahid kuwa shiriritar da Salma yahau yi, bayan tea yayi sanyi k'insha yayi wai zaiyi amai,
saida ta kuma had'amai Black tea sannan yadan sha kadan da maganin bayan tasha walaha da
lallaba shi sannan ya iya shan pill na magani guda daya, acewarsa daci yayi yawa. Bayan nan
kuma ta tashi da niyya tafiya ya langwabe da ciwon kai, saida ta tayi zaman kusan 30 minti
tanai mai sannu.. Karshe dai saida yaga 11 tayi sannan ya koma normal, tace mai zata tafi dare
yayi, ba kunya yace suje ya kaita gida, itakam mamaki ne ya kamata mutum sai kace mai
aljanu, tunani tayi anya ba raina mata wayo yake ba. Haka dai tabishi suka shiga mota, sai janta
yake da hira, kasa magana tayi tsananin yadda taganshi garau, wayarta ta duba taga miss calls
na Daddy, tsaki tayi aranta tace "Allah yasa banyi ranshi surprise dinnan ba"
Nan baki gate ya sauke ta tamai sallama ta shiga gida, Mom ta tarar zaune palo, dan tuni
Daddy ya shiga ya kwanta, ganin Salma yasa hankalinta ya kwanta, fada tayi mata sosai akan
dawowan dare amatsayin mace bai kamaceta ba, hakuri Salma ta bata, itadai surprise din
takeson sani, tambayar Mom tayi taki fada mata komai sai ce mata tayi bayan exams zataji
komai daga bakin Daddy.

***

Washegari langwabewa Mujahid yayi bayan yayi shirin sa tsaf na fita office, Salma ya kira yace
ta taimaka ta kaishi office dan baya jin dadi, bata kowa mai aranta ba dukda dai zuciyar ta na
kisyasta mata wani abu, kuma jiya taji dadin karatu a office dinsa. Gidan taje ta dauke sa suka
tafi.
Tun ranar abu kaman wasa, kullum Salma na tare da Mujahid iyakacin taje skull tayi exam
tadawo ta koma office dinsa ta zauna karatu, ko shopping zataje saidai ta zauna shi yaje yayi
mata, sam bayaso ta fita ba tare dashi ba gudun kar yan'uwansa su ganta, balle jaafar da har
yanxu neman ta yake. Har azuciya Mujahid yasan ya kamu da son Salma saidai yayi alwashin rama abunda tamai
dan kuwa bazai barta taci bulus ba, ganin yadda ta dukufa da karatu yasa ya bata lokaci dan
gama exams dinta, ita kuwa Salma zuciya daya take zaune dashi, abu daya ke daure mata kai
yadda bai furta yana sonta ba alhalin soyayya kuru kuru yake nuna mata, tanason sani mike
zuciyarsa game da ita.


Ta b'angaran Junaina bata daina cusa kai gurin mujahid ba, ko tusa akai a gida saita buga ta
fadimai, wataran rohoton sumai amfani wataran kuma data fara fadin abunda bai dameshi ba
katse wayan yake. Kullum a rokonshin take ya dawo gida.


Yauce ranar da Salma ta gama Exams, tana fitowa Hall tayi kicibis da Faiza zata shiga next hall

supervision, Hararan juna sukayi kowa ya wuce, kowane da abunda yake zak'awa game da
junan su aranshi, K'wafa Faiza tayi aranta tace "yar banzan yarinya very soon zai jefar dake".
Tuni Salma tabaiwa banza ajiya, kobi takan Faiza bata kuma ba tq fada mota taja zuwa gida,
karfe sha biyu ne lokacin, so take tayi wanka ta huta kafin taje gurin Mujahid tamai albishir din
gama exams danba sani yayi ba.

Tana isa gida parking tayi ta fito, kokarin kulle motar tayi taji muryan Salim abayanta.
"Yau kuma baki je wajan sa karuwan ci ba ? Fuska babu annuri yayi magana.
Mamakine ya kamata, ta juyo tace "yaya karuwan ci, a ina, yaushe, ?
Mugun kallo yakai mata wanda daga gani asama yake, cikin zafin nama ya riko hannuta da
karfin gaske wanda saida tadan tsaki kara, "ni zaki rainawa wayo Salma, gayamin uban mi
kikeyi a office dinsa"
Kokarin kwance hannuta tahau yi takasa, bata rai tayi tace "zan kira Daddy idan baka sake
niba.."
Mugun dariya yayi yace "tunda shine ke dauramiki gindin kina iskancin da kikaga dama ko,
waya sani ma kokin bashi kanki"
Wani mugun girgiza Salma tayi da kalaman sa, cike da tsantsan bacin rai takai mai azababan
mari da dayan hannuta, ba shiri ya saki hannuta yanai mata kallon mamaki lokaci guda kuma
zuciyar sa ke tafasa, afuce ta nuna shi da yatsa "idan kana iskancin ka yakare akaina karka
kuskura kasako min iyaye, banza, dan akuya kawai, kuma kasani i hate you Mujahid nakeso
bakai ba wanda baisan ciwon kansa ba"
Dafe Kunci Salim yayi yana huci, tunanin abunda zai mata kawai yake, Harara ta ballamai,
wucewa zatayi yasa mata kafa tayi wani mugun faduwa kasa wanwas, adan tsorace ta daga kai
ta budeshi, sosai ta tsorata da yanayin, "anya Salim baya da hankali" ta fada aranta.
Nunata yayi da yatsa yace "ni kika mara saboda da wani banza, aikuwa sai kinyi danasani zan
nuna maki ni ba wawan da kike tunani bane" juyawa yayi ya tafi, zuciyarsa na tafasa, shi kadai
yasan makircin da zai shuka mata gurin Mujahid din da take takaman tanaso da kauna.

Salma kam tsoro ne sosai ya kamata, mikewa tayi kokarin yi ta kasa zabar azabar dataji kafar ta
guda nayi, dakyar da azaba ta mike tsaye, kaman tayi ihu dan azaba, awahale ta iya jan dayar
kafar ta karasa cikin gida, bata iya shiga gurin mom ba ta wuce dakinta.

Duk akan Idon Salim, yaji dadin yadda yaga ta kasa takawa, koba komai dole ta hakura da
zuwa gurin Mujahid, murmurshin Mugunta ya saki afili yace "zaki gane kuran ki .............


Ni xarah nace Toh Fah, Salma duk ke daya, enemies ta ko ina.
Allah ya karemu daga sharin masu shairi.
[9/7, 12:37 AM] Xarah Bukar: Zuma Sai Da Wuta

~na~
©ҳaɾaɧ bųkaɾ
(Aunty cute)

®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION...

Wattpad Cutexarah
Blog xarahbukar.wordpress.com

51


Tsabar rad'adin da k'afar take mata dak'yar ta cillara ta fad'a band'aki tayi wanka ta fito ta
kwanta gado, sosai k'afar tayi tsami haka dai ta daure har bacci b'arawo yayi awon gaba da ita.

Mujahid ne zaune office yana danna na'ura mai kwakwalwa dake gabansa, jifa jifa yakan
k'yallarawa agogon tsintsiyar hannusa kallo, guntun tsaki yaja ganin k'arfe daya ta gota bata iso
ba gashi kuma ya k'agara ya ganta.
Mubarak ne ya shigo office din tare da sallama, amsawa yayi ciki ciki ba tare daya dubesa ba,
Dariya Mubarak yayi hade da zama yanai kallon office din tamkar wani sabon bak'on sa, duban
Mujahid yayi, cikin zolaya yace "yau matar ka bata zo ba?
Sai sannan Mujahid ya dubeshi, murmushi yayi.
"Zata zo, na tabbata ma tana hanya"
"taku salon soyayyar daban take, wai ma yaushe zaka rama abunda tama ? Mubarak ya fada
ba tare daya bar kyalkyalewa da dariya ba.
Nisawa Mujahid yayi, yace" abokina ina cikin yanayin, na rasa mai zan mata kuma ma bazan
iya cutar da ita ba, koba komai yar'uwa tace ta jini, na hakura, yanzu so nake na sadata da
Hajiya".
Dakatar da dariyan Mubarak yayi, yace "naji dadi ka gano gaskian zuciyanka, Hajiya kuwa sai
tafi kowa farin ciki da kai, yaushe zamuje mu kai amaryar mu gidan sirika.." Cike da zolaya Ya
karashe maganar, mugun kallo Mujahid yamai yamike ya fice tare kokarin gitmse dariyar data
zomai. Murmushi Mujahid yayi yadau wayarsa dan kiran Hajiya yi mata albishir, dailing nambar zaiyi,
Salim ya fadomai cikin office kamar wani mayunwacin zaki.
Ajiye wayar yayi yabishi da kallon waya baka izinin shigo min office, cikin rashin damuwa da
kallon dayake mai Salim yaja kujerar dake fuskantar sa ya zauna had'e da dora kafa daya kan
daya, sannan cikin karaji yace "Sir ba batun aiki ya kawo ni nan ba."
Ran Mujahid yakai mak'walan baci, shuru yayi yana jiran abunda zaice.
Salim ya cigaba
"Salma tawace, tare ka fara ganin mu, tun kafin ta sanka muke mu'amala, dan Allah karka shiga
tsakanin mu, muna matukar son Juna, adalilin ka yau ta zubar da cikana da take dauke dashi"
Mik'ewa Mujahid yayi, fuska daure, afusace yace "tashi ka fita kafin nasa a cilla ka waje"
"Kayi hakuri sir banxo da fad'a ba" mikewa Salim yayi had'e da risinawa sannan ya fice a office
din.
Tsaki yaja ya koma ya zauna ranshi na k'una, ko kadan bai yadda da abunda Salim yace ba,
yasan kafin su saba da Salma kallon marar kamun kai yake mata yanzu kuwa d'an zaman da
yayi da ita ya tabbatar ba abunda yake tunani bane, kuma ma yasan ba yadda zaai Salma ta

kaiwan shashashan yaron nan kanta, tsaki ya kuma ja yace "Salma tafi karfin ka, baka isa ka
rainamin hankali ba, wawan banza kawai". Wayarsa ya dauka yahau kiran Salma, sau biyar ya
kira tana ruri baaa dauka ba, ajiye wayar yayi zuciyar sa na aiyyana mai abubuwa, saurin
kawarwa yayi ya cigaba da aikin gabansa.
Bayan la'asar Salma ta farka bacci da matsananci ciwon kai, dakyar ta yunkuro zaune taji kafar
tai mata nauyi, wani irin juwa take ji, sauka tayi kan gadon ta rarrafa zuwa bandaki ta dauro
alwala ta fito tayi sallah zaune sannan ta koma gado ta kwanta, daukar wayarta tayi taga kiran
shi, da sauri tayi dailing no dinsa. Kaman jira yake, yayi azaman dauka yace "kina Ina ?
Murya ciki ciki, kaman mai shirin kuka tace "ina gida, tuna dazu nadawo saidai bana jin dadi"
Bata rai yayi.
"Mike damun ki ?
Shuru tayi, tanason cemai kafar ta ke ciwo tana tsoron ya tambayeta sanadi, ga kuma kanta na
ciwo, wahalalliyar ajiyar zuciya ta sauke sannan tace "kaina ke ciwo".
So yage ya gasgata zancen Salim, yace "deme kuma ?
Zuciya daya bakinta ya furta "cikina"
Baice komai ba kuma bai jira abunda zata kuma cewa ba ya katse wayar, bata kawo komai
aranta ba ta ajiye wayar hade da gyara kwanciyar ta.
Kasa gasgata zance Mujahid yayi, yanaso ya yadda da abunda Salim yace ya kasa, kalllon
wayarsa yayi dake rike hannusa jiran ko zata kira shi yaji shuru.. Jiki sanyaye ya ajiye wayar
aranshi yana fadin "Tabbas Biri yayi kama da mutum....




Masu korafin basu san ma'anar zuma sai da wuta, bara na maku bayani dalla dalla.

Shi sak'ar zuma baa iya daukan shi saboda Zuma dake makale jikin sakar, komin yadda
zaki ki kori Zuma bazata koru ba tsananin yadda take da taurin kai da kafiya maganin ta daya
ce wato Wuta...kinasa mata wuta zata saduda ta gudu tabar sak'arta ba tare da bata lokaci ba.

Shiyasa hausawa sukace Zuma Sai da wuta.

Shin acikin
Mujahid
Salma
Salim
Jaafar
Da
Junaina waye Zuman waye wutan ??

Ina jiran Amsar ku....

[9/7, 12:37 AM] Xarah Bukar: Zuma Sai Da Wuta

~na~
©ҳaɾaɧ bųkaɾ
(Aunty

9 / 20