Author : Zarah Bukar Category : Tknovels
tasha kuka harta gaji.
Zama sukayi aka gaisa, Daddy yace "jaafar yanxu nake shirin kiran ka awaya"
Ajiya zuciya ya sauke ya mikawa Daddy wayan Salma, karba yayi, ya labarta masu haduwa su
da Salma da kuma yanxu asibitin da take. Salati Mom tahau yi hade da fashewa da sabon kuka,
Hajiya kam binta kawai tayi da ido, Daddy yace "amma officer in charge of this case sai yaci
uwarsa, saiya fadamin yaushe yaga yata ta kashe wani dahar zaiyi babak'eran aresting one n
only daughter na"
Katse shi Mom tayi da cewa, "Alhaji tashi zakayi muje mu dibo yarta."..
Jaafar yace "baa bari, saidai gobe.."
Sai sannan Mom ta dubi Hajiya dakyau sun danyi yanayi da Salma, sharewa tayi tace
"mungode sosai da temakon yarmu da kukayi, Allah ya saka da alheri"
Ajiyar zuciya Hajiya ta sauke tace "nice da gode maku, Allah kadai yasan dami xai saka maku"
Kallon rashin fahimta Mom tayi mata, hajiya taci gaba "basan ya akayi Salma ta dawo hannunku
ba, saidai kun cancanci riketa yadda naga duk kun damu" k'walla hajiya ta share tacigaba "ni
yayar mahaifiya salma ce, na jima ina neman ta banganta ba"
Ware ido Mom tayi, shikam Dad baiyi mamaki ba, koda ya hadu da Salma daman neman
yan'uwanta taxoyi a garin Abuja, ganinta karama lokacin yasanya ya kawo ta gida yarike ta
tamkar yar cikinsa, saidai yaji dadi ganin Jaafar amatsayin d'an Hajiya, hada aura salam da
Jafar yazo asauki kenan.
Kuka Mom take sosai tana rokan Hajiya karta rabata da Salma, Hajiyan ma kuka take tace
"karki damu Salma takuce halak malak bazan rabaku da ita ba"
Dddy yace "ikon Allah kenan, jaafar Allah yayi bazaku hadu da Salma ba tun shekarun baya
dana ma zancen auran diyata, ashe kai dan'uwan ta nema, faduwa yazo daidai da zama".
Sosa keya jaafar yayi hade dayin murnushi..
Hajiya kam jikinta ne yayi sanyi jin Daddy zai ruguza mata plans, saidai ba yadda ta iya tunda
shiya rike Salma, bata isa tace Mujahid ta kamawa Salma ba, balle yadda taga Daddy yadau
zafi da officer dake kokarin aika salma gidan yari....
Sun dan jima suna magana, daga bisani su Hajiya suka bar gidan bayan sunyi zasu hadu
gobe a asibiti.
****
Washe gari bayan Mujahid yayi Sallar asubah asibitin ya nufa gurin Salma danso yake ta farka
agaban idonsa.
Salma kam Baccinta take, wata nurse ta shigo dakin tacire roban jini sannan ta sa mata na
ruwa, fita nurse din tayi, baiyi awa daya ba Salma ta fara motsi, ahankali ta bude, ganinta cikin
farin daki yasata mikewa azabure, wani kara tasaki jin ta karce hannuta, duban gurin tayi taga
haunta da karfen gadon makale da handcuff, kokarin cixgewa tayi ta kasa, "na shigu uku" ta
fada bayan ta tuna abunda ya faru"
kuka ta soma yi, jin motsin xaa shigo yasata tsayar da kukan hade da kafawa kofar ido.
Mujahid ne ya shigo, jikinsa sanye da dagon jallabiya, tana ganinshi ta hade hade rai, tuna
neman kasheta da yasoyi tayi.
Murmushi yayi mai dauke da ma'ana iri iri sanna ya karasa daf da ita ya tsaya, murya ciki ciki
yace "ya jikin ki ?
Banxa tayi dashi
Yace "hope you're ready to spend 30 years a gidan yari"
Dogon Tsaki taja, tace"am ready, then after 30 years kuma i'll come back to destroy you for
good".
Dariyan rainin hankali yayi yace "kina da guts dayawa" gashin kanta ya damko, saida tayi kara,
daure fuska yayi yace "dan uwarki ni kike yiwa tsaki.."
Dukda ciwon da jikinta yake mai hanata kokarin cizge hannusa daka kanta ba, kaman mai shirin
yi kuka tace "idan banyi tsaki ba mai kakeso nayi, apologise or beg your pardon kake so nayi,
toh kasani, that will never happen, badai so kake ka kaini prison ba, bismillah, kuma point of
correction uwarka badai uwata ba..." Iya k'ulewa Mujahid ya kai, wuyanta ya damko da karfin gaske, yace " uwata kike zagi.."
Tace "uwa batafi uwa ba, idan kana nonsense dinka dont ever include my Mom."
Sakinta yayi yana Huci, juyawa yayi zai fita tace "am hungry, get me sumtin to eat".
Bai iya tanka taba ya fice zuciyarsa na zafi, baiso reaction din Salma haka ba, yaso ace kuka
zatayi ta rokoshi amma dan karfin hali irin nata ba ita tayi kisan ba but she is willing to serve 30
year a prison... Tsaki yaja yana tunanin yadda zaisa a azabtar da ita a prison. Motar sa ya shiga
ya koma gida dan shiryawa zuwa office.
Sai da gari yayi haske Mom da Daddy suka shirya fita asibiti gurin Salma, har sun shiga mota
yan'uwan Baba nayaro suka kira Daddy suka fadimai rasuwar, hankalinsa sosai ya tashi fasa
zuwa asibitin yayi ya nufi Gidan taaziya, Mom kam asibiti ta wuto nan ta iske Hajiya da Jafar na
jiranta a haraban gurin, shiga sukayi wards din, sukayi saan police daya ke gurin wanda ya iso
da safe baisan da order din Mujahid ba yabar Jaafar ya shiga, Mom da Hajiya sun tsaya suna
magana awaje.
Bacci Salma take ya karasa ya zauna kusa da ita, kallonta yake cike da so da kauna, shafan
pretty face dinta yayi har zuwa kan lips dinta yana admiring dinta, dan motsawa tayi yayi sauri
cire hannusa, bude ido tayi ahankalin ta dubesa, atunaninta Mujahid ne, tace "ina abinci ? Can
kasan makoshinta tayi maganar. Murmushi yayi yace "yanxu xaa kawo, how are you feeling ?
Sai sannan tagane ba Mujahid bane, yunkurowa zaune tayi kokarin yi, yayi sauri temaka mata.
Kallan shi tayi ayayinda shima kallon ta yake, murya kasa kasa tace "thank you"
"For what" ya fada hade da rike hannuta mai sakale da handcuff, haushi ne sosai yakama shi
yasan aikin Mujahid ne.
Murmushi tayi, jikin sanyi voice tace "kaman nasanka wani wuri kafin ranar da kayi saving dina?
Dariya yayi wanda ya kara fiddo kyau shi,
aranta tace "so cute dashi, ba kaman banzan nan ba kullum fuska daure"
Magana zaiyi Mom ta shigo dakin, Hajiya abayanta, da sauri Mom ta karasa gurin Jafar ya mike
tsaye ya matsa gefe, kuka Salma ta fashe dashi ganin Mom, nan take ta susuce tahau rarrashi,
dakyar Salma tayi shuru tace "Mom yunwa nakeji, kuma acire min wannan abun" turo baki tayi
tanai mata nuni da cuffs din hannuta. "Mun shige su" Mom ta fada cike da mamaki, kallon Hajiya tayi tace "amma babu azzalimi
kaman Officer nan, ji mugunta dan Allah.."
Sai sannan Salma ta lura da Hajiya dake kallon su jiki sanyaye, shuru Hajiya tayi sanin cewa
d'anta ne azzalimun da Mom ta ambata.
Maida dubanta Salma tayi ga Mom, murya kasa kasa tace "Mom matar nan kaman Hajiyar
Ummata"
"Itace, tare da d'anta daya taimake ki" nuna jaafar Mom tayi,
Farin ciki ne ya mamaye Salma, duk sai taji Jafar ya kara kwanta mata, ashe dai jinin tane
shiyasa ya ceceta.
"Hajiya.." Salma ta fada tana kallon Hajiya, murmushi hajiya tayi ta mike ta karasa gareta tana
fadin "aina dauka bazaki gane niba" rugume juna sukayi, Salma na kukan farin ciki.
Daddy na zuwa gidan Baba nayaro taaziya yayi masu, bai samu janaizar saba, abun tausayi
dayaji sanadin Mutuwarsa, tashin hankali biyu ne suka hade mai, jiki babu kwari ya wuce NPF
(HQ) gurin head of police, sir Ahmad.
Kara tattauna abunda ke faruwa sukayi, Sir Ahmad yace tabbas yasan da case din saidai
baisan diyar shice major suspect ba, atake ya tura department dinsu Mujahid kiran sa, baa
same shiba ya aika a kira mai Mubarak sanin cewa su biyu ne witness aranar da abun yafaru.
Mubarak na zuwa, Sir Ahmad yahau shi da tambayo yi, bai boye komai ba ya zayyane masu
labarin salma da mujahid tun farkon haduwar su har zuwa ranar da abunda ya faru, ya kuma
jajjada wa sir Ahmad lailai Mujahid baya cikin hankalin sa, So da kiyyaya sun rufe mai ido.
Zufa Daddy yahau yi, gano cewa duk case dun revovle around Baba nayaro, "amma yaron
nan ya cika dan iska, yan'uwan marigayi basu pressing charges ba saikai dan kawai wata
manufarka daban zaka tsangwama d'iyata" azuci Daddy yayi maganan.
Sir Ahmad yace "zaancen banza kenan, wato personal feeling dinsa yake hadawa da aikinsa
dan cimma burinsa, dan bashi da kunya kuma harda aika gawa asibiti ayi autopsy alhalin yasa
ko kyankyaso yarinya bata iya kashewa"
"Kaga Mubarak, nemi wani ya amso mana autopsy din mugani"
Ba musu Mubarak ya mike ya fice, police din daya kai gawar asibiti ya tura ya amso, Doctor
kam zuciya daya yabada atunaninsa Mujahid ne ya aiko.
Mujahid na Tuki ya dunga ganin call daga office, asibiti zaije amsan autopsy ya fasa ya wuce
Office, yana isa aka sanar mai Sir Ahmad na kiran shi, hankali kwance ya shiga office din, wani
mugun Harara Daddy yakai mai, shan jinin jikinsa yayi ya dake ya karasa gurin Sir Ahmad.
Sir Ahmad yace "yanxu M. Abdulsalam ka kyauta da abunda kayi, kaida kake daya daga cikin
wanda suka san aikinsu, miyasa kakeso yin injustice ?
Kallon bangane ba Mujahid yamai, police ne ya shigo da autopsy result ya mikawa Sir Ahmad,
Mujahid kaman yayi ihu.
Budewa Sir Ahmad yayi ya karanta sanna ya dubesa yace "the deceased was beating with
severe blows before stab to death, yanxu gayamin ita buduwarta ka da kakejin haushi itace
tamai dukan kafin ta kashe shi ko kuwa she is stupid dazata kashe shi kuma ta tsaya yimai kuka
ba tare data gudu ba" Shuru Mujahid yayi yana kallom Mubarak da wutsiyan ido, sarai yasan shiya tona komai..
Sir Ahmad yace "ka godewa Allah Mahaifin yarinya baiyi pressing charges akan attempting
kashe diyar sa dakayi ba, daga yanxu nayi closing case dinnan, kai kuna you're suspended till
further notice".
Mugun Kallon Mujahid yakaiwa Sir Ahmad, afusace ya ciro bage, Id da bingidar ya zubarsu kan
table dinsa, hade da ficewa afusace yanai huci, mikewa Mubarak yayi yabi bayansa..
Daddy yace "hukuncin yayi tsauri da yawa.
Sir Ahmad yace "Barni dashi, so nake yagano bambancin sentimental feelings dinsa da
aikinsa".
Mubarak na kwalla mai kira ko kallan sa baiyi ba,
Ya shige motarsa yaja afusace, gurin abinci ya nufa ya siya take away sannan yaja zuwa asibiti
gurin Salma..
Tundaga nesa ya hangi babu police gurin, haushi ne yakamasa, yana shiga dakin mutanan
daya gani yasa shi daskarewa gurin, Hajiya da Mom zaune gefe suna hira, Jafar zaune kusa da
Salma yana bata tea abakin tana zuba mai shagwaban ta koshi, sai wani lallabata yake.
"Kai kuma fah, daga ina ? Mom tafada fuska ba annuri ganinsa sanyen da kayan yan sanda.
Afusace Hajiya ta mike ta kwashe shi da marin da saidai Salma ta saki ihu tsabar razana.
Bai damu da marin ba banda jafar dayake watsawa mugun kallo.
"Dan ubanka bani mukullin Handcuffs din.." Hajiya ta fada cikin karaji.
Karamin mukullin ya mikata ta amsa ta jefawa jafar ya cabe yayi sauri bude handcuffs din,
mikewa yayi yabawa hajiya, "ungo tsiyar ka, kuma ka fice anan" hajiya ta fadi hade dajan
haunnsa ta dunkule mai Handcuffs din ciki, Mujahid baice komai ba yayi kokarin ajiye abincin,
tsawa Hajiya tamai tace ya wuce da abinci baa bukata, zuciyarsa na tafasa ya juya ya fice.
Mom tace "dan banxan yaro, waishi police, kinyi maganin shege"
Mugun Kallo Salma takai mata ba tare data lura ba, aranta adduaa take Allah yasa Mujahid ba
d'an Hajiya bane, idan kuwa hakan ya tabbata she won't forgive him da boyemata shi dan uwan
tane da yayi.
Mujahid na Fitowa ya Hadu da Daddy zai wuce ciki, kawar dakai yayi gefe ya wuce ranshi na
kuna.
Dariya Daddy yayi yace "kaji da rashin aikin ka, Salma kuwa tama nisa".
Wayyo su oooo anyi 2 zero í ½í¸‚
[9/7, 12:37 AM] Xarah Bukar: Zuma Sai Da Wuta
~na~
©ҳaɾaɧ bųkaɾ
(Aunty Cute)
55
Daddy na shiga d'akin yayi farin cikin ganin Salma ta warware, nan ya basu albishiri din yadda
komai ta kasance. Mom kam tafi farin cikin rashin aikin mujahid sai d'ura mai zagin Allah tsine
take. Hajiya kuwa murmushin dole kawai take, tana mamakin karfin hali irin na Mom, kodayake
Salma diyar tace duk abunda tace daidai ne. Salma kam tagama gano komai da Reaction din
Hajiya sai fama yiwa Mom ido take akan tayi shuru bata sanma tana yiba. Aunty Bilki ma tazo
dubata, sun dade asibiti kafin daga bisa suka koma gida.
Kwana su Salma biyu a asibiti Likita ya sallame su. Gidan Mom suka wuce wanda ba hakan
Hajiya taso ba. Bayan kwana biyu kuwa Daddy dakan sa yacema Salma ta shirya Jafar ya kaita
gurin Hajiya tayi mata kwana biu, dadi sosai taji dama ta jima dason tambayarsa zataje sai Allah
yasa ya furta mata hakan. Ranar da zasu Jafar na waje parking lot yana jiranta, ita kuma tana tare da Mom a palo suna
Sallama, mik'e mata wayarta Mom tayi tace
"Saura idan kinje ki manta dani"
"Haba Mom taya zamanta dake, kece fah uwa ta" ashagwabe tayi magana.
Kunnan ta Mom tajA, cikin zolaya tace "banda rashin ji, kinga Allah ya kawo maki mijin mai kirki
karna kuskura naji kinma Jafar rashin Mutuncin, nasan halin ki"
Dan k'ara Salma tayi hade da cizge ruk'on da Mom tayi mata, dariya tayi sannan tace "kai Mom
ina laifin wanda ya taimake ka cikin tsaka mai wuya"
Dariya sukayi atare sannan sukayi sallama, har bakin Motar Mom tarakata tanai kara mata fada,
motar zata shiga ta hangi Salim bakin window dakinsa yana kallonta, dauke kai tayi tana
mamaki yadda yake acting crazy kwana biyun nan. Saida Mom taga sunja sannan ta koma ciki.
Shuru sukayi kowa da abunda yake sak'awa aransa, satan kallon ta Jaafar yayi yaga tana juya
wayar dake hannunta, da alamun kuma tunanin take ganin bata cikin hayyacin ta. Cikin cool
voice yace "tunanin mi kenan, ko har yanzu jikin ne ?
Sai sannan ta dawo daga duniyar tunanin inda jakar ta da hoton Mujahid suke, tasan dai tare
suke da wayarta cikin jakar amma Wayar kadai Mom ta bata ba jakar.
Murmushin ta saki hade da dubansa, tace "everytime i close my eye kai nake gani, kana da kirki
sosai"
"Uhmm are you sure, ba wani can daban kike gani ba.." Cikin zolaya ya karashe zancen.
Dariya tayi bata ce komai ba, banda murmusawa da take.
Gabadaya duniyar tama Mujahid zafi, ba aikin fari balle na baki duk zaman kadai ce ya ishe ba,
tun ranar dama bai kuma bi takan Salma ba, mugun haushi da tsanarta yake ji duk asanadin ta
ya rasa komai, one thing dayafi damunsa shine yadda ya kasa yakaceta aransa, wani mugun
Tsaki yaja hade da kaiwa hannusa daya haushi, gidan dayake zaune ma bakin kirin yake ganin
sa tsbar takaici, mikewa tsaye yayi daga kan kujerar palon da yake zaune, kai komo yahau yi
yanai nemawa kansa mafita, karshe dai ya yankewa kansa komawa Gida tunda dama ba
koransa akayi ba shiya kori kasan, duban agogo yayi yaga biyar na yamma ta gota fasa tafiya
yayi ya bari zuwa gobe.
Suna isowa Gidan, Salma ta jinjina kyan da girman gidan, fitowa tayi daga motan tanai karewa
ko ina kallon, kallon Jafar tayi, tsaye yake bakin boot yana ciro trolleys dinta.
Tace "wow yaya this house is beautiful.."
Magana zaiyi sukaga an bude gate motar kirar avensis ta shigo, dauke kai Jafar yayi, salma
kam kallon motar take har tayi parking idan suke tsaye, Junaina ce ta fito amotan hade dakaiwa
Salma wani mugun kallo aranta tana fadin "i cnt believe this devil is my sister" wani mugun
tsanan Salam takaraji tun ranar da Hajiya ta fadi mata ita kanwar tace, dan haushi ma ko asibiti
kasa zuwa dubo ta tayi.
"Ya jafs ina wuni" tafada batare data kalle saba, tayi wucewarta
Bai amsa ba, sai kallon Salma dayayi yaga duk jikinta yayi sanyi, murya maraice tace "i dont
think she will forgive me..
Yace "she is very angry but trust me she will hose down"
"I pray so" Salma ta fada hade da sauke ajiyar heart, ciki suka karasa, Hajiya na zaune palo
tana kallon aljazeera, ladabce Salma ta gaidata, farin ciki mara misaltuwa ne lullube Hajiya,
kasa zaune tayi ta mike tahau nannan da Salma, babban dakin mai kyau anan kasa Hajiya ta
nuna mata amatsayin nata, Salma kam kin zama tayi ta nace lailai ita a dakin Hajiya zata
sauka, hajiya kam taji dadi hakan, ranar kam Salma taga gata gurin Hajiya da Jaafar, sai wani
narke masu take suna biyeta, Junaina kam sai binta da harara da tsaki take, zama tayi dakin
tahau trying namban Mujahid dan kai masa rahota, taji wayarsa kashe.
****
Washe gari Mujahid yayi shirin sa tsaf cikin kananun kaya dayayi matukar fiddo azahirin kansa,
kulle gidan yayi ya fada motarsa yaja yabar Gidan.
Bayan sun kare breakfast, wajen gidan Salma da Jaafar suka fito yanai nuna mata ko ina da
garden dun gidan. Kaman masoyan juna gwanin shaawa suke tafe suna darawa abunsu ba tare
da matsala tattare dasu ba, zayawo sukayi suka tsaya bakin motar sa, da alamun fita zaiyi.
Marairace murya tayi tace "yaya yaushe zaka dawo ?
Folding hands dinsa yayi a kirji hade dakai mata wani killer smile, yace "tun baje gate ba harkin
fara missing dina"
Dariya tayi, sai kuma ta tsayar da dariyan tace
"Yaya you're very special,
Shuru sukayi suna duban juna for some seconds sannan tace "plz karka dade.."
Agogon hanusa ya kalla yace "i promise..
Okay bye" ta fada..
Kashe mata ido yayi, sukai smiling atare sannan ya shiga motar yaja.
Palo ta komo hade da sauke dogon ajiyar zuciya,