Zuma Sai Da Wuta Complete Hausa Novels Pdf by Zahra bukar .pdf

Author :  Zarah Bukar Category :  Tknovels

Chapter   10 / 20

27K to 30K   out of 57.2K words

Cute)
®NWA

Vote me on Wattpad @Cutexarah

xarahbukar.wordpress.com

52


Da Magrib Mom ta lek'a d'akinta kansacewar taji shigowarta tun rana, ganin bata da niyyah
fitowa ya sanya ta bibiyar ta, kwance ta ganta can k'arshe gado akudundune, k'arasa wa gurin
tayi tahau tashin ta, bude ido salma tayi, jikinta gabad'aya k'yamar yake tsabar yadda zazzab'i
mai zafin gaske ya cafketa, hankali mom ne ya tashi ganin yanayi ta, ba tare da b'ata lokaci ba
ta taimaka mata tasa kaya suka fita waje, kiran Salim tayi yaxo yaja su zuwa asibiti, a mota sai
faman yi mata sannu yake tamkar ba shine sanadi ba, bata iya amsa shiba har suka isa asibiti
aka bata gado.
Koda Mujahid ya koma gida kasa zaune yayi, kalaman Salim ke yawo a kwakwalwan kansa.
Kamar wani tab'abb'e yahau girgiza kansa yana fadin it cant be possible, yana son Salma kuma
yayi trusting dinta, ba zai tab'a yadda da zance salim ba" wayarsa dake ajiye kan 3 sitter yadau
hade da mik'ewa tsaya yayi dailing no din Salma, har kusan sau biyar bata dauka ba, nan take
wani mugun haushin ta ya dirar mai, cilla wayar yayi kam kujerar sannan ya zauna kasa hade
da dafe kansa. Atakaice dai ranar dakyar ya iya runtsawa, da safe bayan yayi shirin sa na
office fita yayi, bai zarce ko ina ba sai gidan su Salma, ya jima yana horn daga bisani mai Gadi
ya iske shi ya sanar mai babu kowa agidan sai Salim, hajiya da diyarta kuma suna asibiti, Alhaji
dama baya gari.
Komawa Mota Mujahid yayi ran sa bak'in k'irin, zuciyar sa kuwa ta gama gasgatar mai da
gaskian lamarin, wani irin haushi kanshi yake ji da tun farko yayi sake har Salma ta shigo mai
rayuwa, yana son salma, she's the only gal da yasan he can die for, saidai bazai taba yadda ta
raina mai hankali ba much less tayi deceiving dinsa with her cute innocent face, nambarta dake
wayar sa yayi deleting hade da kunna motan, kallan gate din gidan yayi yace you're dead to me"
afusace yaja motar sa yayi gaba.

"Wai yaushe hakan ta faru bansani ba" acewar Mom, zaune take gefe gadon da Salma ke
kwance, kafar mai targade daure da farin gyalle, Yunkurowa Salma tayi ta jingine jikinta a karfan
gado, Magana zatayi Salim ya shigo rike da flask da Mom ta aikeshi gida ya dauko, Harara
Salma takai mai, yace "sannu sister, ya jikin ? Atakaice tace "lapia" duban Mom tayi tace "ina tafiya nayi missing steps na fadi"
Mom tace "tsautsayi kenan baya wuce ranar sa, Allah ya tsare gaba, ya ciwon Kan ?

Da sauki" Salma ta amsa, tashi Mom tayi ta fita gurin Doctor, kusa da ita Salim ya karaso hade
da marairece fiska yace "sis am sorry, duk nina jaza maki"
Tabe baki tayi
"Ba komai ya wuce, ni yanzu kawai gida nakeson komawa, nabar wayata kan gado" kaman
zatayi kuka ta karashe zance, Mujahid ne aranta, tana son fadimai tana asibiti karya jita
shuru.
Mom ce tadawo dakin tana waya da Daddy ya mike ya fice, mikewa Salma wayan tayi ta amsa
yiwa Daddy magana.

K'ashe gari likita ya sallame su, suna isowa gidan wayarta tadau ka taga miss call dinsa, farin
ciki ne ya ziyar ceta ganin yadda ya damu da ita, kiran sa tahauyi fuskar ta dauke da murmushi.

Alokacin Mujahid zaune yake office yana danna laptop dake gabansa, fuskar sa babu annuri,
shi kadai yasan yadda yake jin zafi azuciyar sa, yana ganin kiran nambarta yaki dauka, har
kusan sau goma takira bai dauka ba, karshen ma wulla nambarta yayi a reject list ya cigaba da
aikin gabansa yana huci.
Mamaki ne yakama Salma alamun da wayarta ya nuna mata nambarta is rejected, zama tayi
tana tunanin lapia kuwa, bata saduda ba daddare tahau kokarin kirasan still abu daya yake
nuna mata, hankalinta ne ya tashi, duk atunaninta ko wani mugun abune ya faru dashi. Kasa
runtsawa tayi har garin Allah ya waye, da safe shiryawa tayi ta shiga motarta taja zuwa office
dinsa, tana isa daga main entrance gate din wasu polisawa suka hanata shiga, mamaki ne
yakamata dan kuwa sun santa duk zuwanta barinta suke, rokon su tahau yi da magiya, fir suka
hanata shiga karshe ma ce mata sukai Ogan su yace karsu barta ta shigo.
Jiki sabule ta koma gida, kwata kwata batama san miya faru hakan ke faruwa ba, batai kasa a
gwiwwaba saida tayi kwana uku tana zuwa basa barinta ta shiga, hankalinta sosai ya tashi, a
kwana na hud'un ne ta kuma komawa, tana cikin rokonsu Mujahid ya iso gurin cikin motarsa zai
shiga, ajiyar zuciya ta sauke ta nufesa da sauri, saidai mi, ko kallanta bai yiba yakara baiwa
motan wuta ya shige ciki yabarta nan tsaye cikin tsananin tashin hankali marar mitsaltuwa, nan
take zuciyar ta ya fadi mata somthing is not right, kai komo tahau yi agurin tana tunanin. Horn
taji bayanta da azama ta juwa, tagane shi, Mubarak ne da take gani office din mujahid, karasa
gurinsa tayi hade da gaidashi, yace "mai kikeyi anan, ki shiga mana".
Kai ta girgiza, tace "Mujahid ya basu order karsu bari na shiga, dan Allah ka taimaka ni, i need
to talk to him".
Tausayi sosai tabashi, saidai yasan Mujahid da kafiya koda ya shigar da Salma bazai yadda ta
shigar mai office ba tunda har yasa doka a entrance kar abari tashigo, ko miya hadusu kuma,
duk axuci yake zancen.
Yace "why not ki hakura da ganinshi ki tafi gida, i dont tink zai kulaki"
Kaman zatayi kuka ta marairace fuska tace "dan Allah ka tamakeni, yaki kulani for d past 4
dayx, i need to talk to him, inason sanin miyasa yake ignoring dina all of a sudden"
Shuru Mubarak yayi yana naiman mafitan yadda hakan zai yuyu, ajiyar zuciya ya sauke yace
"kinga abu daya zan iya maki, ki fadi inda kikeso ku hadu, ni kuma na maki alkwarin kawo maki
Mujahid"

Nisawa Salma ayi, taji dadin abunda yace, hakan kadai zaisa ta hadu da Mujahid harya
saurareta.
Risinawa tayi tace "nagode sosai"
Dariya yayi
"Baki fadi inda zan kawo miki shi ba"
Murmushi tayi tana tunanin peaceful gurin da yakamata su hadu, can ta tuna da plantation
garden na Daddy, gurin nada matikar girma, kyau da shaawa uwa uba akwai flawowi da mayan
bishiyoyi gwanin shawaa.
Tace "kasan A & M gardens na hanyar Dikkoh ?
Yace "uhhm nasan gurin, can kike so ku hadu".
Cike da farin ciki tace eh, dariya yayi yace ba matsala gobe by 4.30 zaki ganmu"
Godiya sosai tamai sannan ya wuce, motarta taja ta wuce Garden din.
Tana isa Baba nayaro ta iske, mai kula da shuke shuke gurin, gaidashi tayi aladabce ya amsa
cike da fara'a, suna shiri sosai da Salma kasancewar yawanci idan damuwa tayi mata yawa
gurin take zuwa shan iska.
Gurin da pink da yellow flowers suka fi yawa nan Salma tacemai ya gyara gurin yayi kyau dan
tana da bako, so take idan yazo duk wata bakin cikin sa ya yaye, shikam Baba nayaro dariya
sosai tabashi yahau zolayan ta yayi sirki.... Sun dan jima suna magana daga bisani Salma
tamai sallama ta koma gida.. Salim ta tadda ya fito daga motar sa, da alamun shigowar sa gidan kenan, "Salma daga ina
kike da yamma haka ? Ya fada cikin salon kulawa kaman gaske, deep down kuma so yake
yasan ina taje dan kwana biyu baya ganin ta a office din Mujahid.
Ganin yadda yake mata kirki kwana biu yasa ta saki fuska tace "ya salim Ogan ka naban
Tough tym, kwata kwata nakasa gane kanshi, yanxu baya kulani"
Murmushi yayi wanda shi kadai yasan maanar sa yace "kin manta The boss is always d boss,
fadin Sakon ki saina kaimai".
Tabe baki tayi "no need gobe zamu hadu a Garden din Daddy by 4pm suprised visit zamu ma
juna.."
Ware ido yayi in shocked, "yasan Garden dinne ?
Dariya tayi, tayi gaba tana fadin "a'a, gobe zai sani" tafiyar ta tayi..
Tsaye Salim yayi zuciyar shi na kuna, aranshi yace "muje zuwa, mahaukaci yahau kura",
naushin iska yayi ya wuce part dinsa.

*****
Washe Gari.

*Kaduna*..

Jaafar ne tsaye bakin motar sa bayan su kammala shari'a da sukai tayi kusan kwanakin da suka
shud'e a Supreme court. Bude motar yayi ya ajiye tilan takardu dake hannunsa sannan ya shiga
motar, yaja komawa Birnin tarayya (Abuja).

*Abuja*

Tun Safe Salma ta birkice kayanta gabayada tanai neman wanda ya dace tasa, karshe dai
white jean da pink top ta ajiye gefe sannan tadau Hoton Mujahid wanda tuni ta wulla a trash can
kwanakin baya saidai daga baya tacire ta adana shi, daukon hoton tayi tana kalla hade da
lumshe ido, daga bisani ta bude pink cluth bag dinta ta ajiye frame din ciki, wanka tayi ta fito ta
sannan ta zauna jiran karfe hudu ta cika.

K'asa Zaune Salim yayi a office, duk mintina kallon agogo yake, yana fitowa sallah azahar, joint
dinsu na yan shaye shaye yaje, saida yayi tatul sannan yahau kuka yana tunanin yadda zai
raba Salma da Mujahid, rasa mafita yayi daga karshe ya yanke shawaran zuwa Garden din
Kidnapping dinta kafin su hadu da Mujahid. Karfe uku da rabi nayi Motar sa ya shiga yaja yanai wani reckless driving har ya isa Garden
din, black Face mask daya siya na musamman yadau ya sanyawa fuskar sa sannan ya shiga
Garden din cikin sadaf ya boye cikin wata bishiya.
Katon Scissors ne Hannu Baba Nayaro, sai gyaran wasu flowers yake cikin sauri yana duba
lokaci kar Salma ta iso ta iske bai gamaba, aiki yake sosai yaji alamun saukar Numfashi daga
ina yake, dakatar da aikin yayi yafara takowa gurin yana fadin "waye anan...?
Tsoro ne ya kama Salim, da sauri ya fito yakama wuyan Baba nayaro, yace "sshh kamin shuru
karka kuskara kayi ihu"
Kokarin kwace kansa Baba nayaro yahau yi, yakasa, iya karfinsa ya take kafar Salim, da sauri
Salim ya sakarmai wuya, Guduwa Baba nayaro zaiyi Salim yayi saurin rikosa hade da kwashe
tsoho da mari, nan take fada ya kicibe tsakanin su, sukahau dambe, duka sosai Salim yama
baba nayaro, ganin yana kokarin guduwa yasa ya dauki scissors din zuciya daya ya caka mai
atsakiya cikinsa, ihu Baba yayi ya fadi kasa bakinsa na ambato kalmar shahada, tsoro da firgice
ne yakama Salim ganin yadda jinin Baba ke bulbula, hankali tashe ya cire mask din fuskarsa
yahau yiwa Baba sannu, nunasa Baba yayi da yatsa yace dama kaina....,
Tsorata Salim ya kuma yi da sauri ya ruga da gudu yabar gurin cike da tsananin fargaba.

Fuska dauke da seriousness Mubarak ya iske Mujahid, yace "Mjay tashi muje na nunama wani
abu"
Dubasan Mujahid yayi kaman bazai kulasaba ganin yadda yaci serious first tym in his life yasa
shi cewa "miya faru ?
Mubarak yace "it urgent, plz tashi muje banaso ka cikani da tambaya"
Kaman bazai tashi ba, daga baya kuma ya mike bayan Mubarak ya fice a office, "this is not
good" Mujahid yafada aransa, atunanin sa ko batun wani crime ne Mubarak yakeso suje sugani,
drawer na table din ya janyo yadau bindigar sa da Handcuffs yasa a ajihunun sannan ya fita,
gurin mota ya iske Mubarak, shiga sukayi Mubarak yaja motar.
Hudu na cika Salma ta kammale shirin ta, jakarta da hoton ke ciki ta dauka sannan ta fita palo,
dakin Mom ta nufa da sauri tai mata sallama akan zataje shopping sannan ta fito, bata dau
motar taba acewarta kar Mujahid yagani bakin garden din yafasa karaso wa ciki, Fita waje tayi
ta Tari Taxi ya kaita Garden din.

Tana shiga Garden din wani irin fresh air taji da farin ciki, fatan ta Allah yasa Mujahid yace yana
sonta da sai tafi ko wace farin ciki.
Taku daya biyu zuwa uku tayi tafara ganin d'ison jini, bin jini tayi har inda Baba nayaro ke
kwance, cike da tashin hankali ta tsugunna gaban sa takiran sunansa, jini sosai ke zuba saman
cikinsa, hannu ta tasa ta tari jinin tana ambatan innalillahi wa inna'ilaihi rajun, jijji gashi tahau yi
ko motsi baya yi, tuni hannuta da farin wandonta suka kwashi jini, ihu take tana kiran sunan
baba.

Parking Mubarak yayi, kallan sa Mujahid yayi yace "wai miye zan gani anan ne, nifa ban ciki da
wasan ka na banza.."
"Fito muje" Mubarak ya fadi, fito wa sukayi suka shiga Garden din, suna tafiya Mujahid yaji ihu,
kallon Mubarak yayi yace "whats going on ?
Kafin Mubarak yayi magana sukaji wani ihu, atake maza suka rafta da gudu inda ihu ke tasowa.

"Na shiga Uku" Salma ta fada, tanai kokarin cire Scissors din dake makale jikin cikin Baba,
kasawa tayi ta mike hade dasa duka hannunta biyu akan scissors din da niyyan cirewa.
"Mi kikeyi anan ?
Muryan Mujahid taji agabanta, sam bata lura da tahowar su da gudu ba, adan tsorace tayi Baya
ganin mugun kallon dayake mata, "ba komaii" ta fada cikin inda inda.
Tsayawa gefe Mubarak yayi, Mujahid ya karasa hade da Taba wuyan Baba, babu alamun rai
tattare dashi, kallon Salma yayi, cikin karaji da zare ido yace "Uban mi kika yimai ?
Kaman zatayi kuka tahau fadin "nima haka naganshi.."
Mujahid ya gama kulewa, ko daya bai yadda da abunda tace ba, yace "ni zaki rainawa wayo,
munafuka, yar daba, karuwa yar iskaaa..."
Katse shi Mubarak yayi da cewa "mjay stop it mana, baka da hankaline kake tunanin karamar
yarinya da kashe tsohon mutum haka..".
Kallon banza yama Mubarak sannan ya dube Salma hade da ciro bindigar da handcuffs, nunata
yayi da bundigar, fuskar ba annuri yace "you're under arrest ..."
Katse shi tayi da cewa "yaya dan Allah kayi hakuri, wlh bani bace, believe me.."
Tsawa ya bugu mata dasaida yan hanjin ta suka kada yace "shut up, you have the right to
remain silent, anything u say can and will be used against you in a court of law..."
Iya kuluwa Mubarak yakai, ganin Mujahid da gaske yake arresting salma zaiyi yasahi, riko
hannusa "Mjay, calm down mana, kar kayi using personal issues dinka da aikin ki, we both
know ba ita ta kashe shiba".
"Karya kake, am sure itace tayi kisan kuma abunda yasa ka kawo ni nan kenan danna gani da
idona"
Kallon Salam Mubarak yayi yamata sign din ta gudu, tagane da sauri ta juya zata gudu, mujahid
yace "don't you dare walk out on mee"
Tsayawa tayi chak, kuka takeson yi dan taji dadi takasa, kwata kwata ba mujahid din data sani
ne wanan ba saidai she isn't stupid dazata tsaya yayi arresting dinta abanza.
Tana jin yafara taku daya biyu a bayanta tayi sauri afkawa da gudu, Tsayawa Mujahid yayi yana
kwalla kiran sunanta, ganin bata da niyyan tsaya wa yasanya shi pulling trigger, daidai kafardar
hannuta Bullet din yabi ya karce ta, ihu tayi sosai, wani mugun jiri yafara daukar ta, bazata iya

tsayawa ba ta cigaba da gudu hade da rike gurin wanda tuni jini yafara zuba.

Ko ajikin Mujahid saima kokarin kara kai mata harbe da yake, wani Mugun Mari Mubarak ya
tsakar mai, suka haure da Dambe...

Hankali tashe Salma ta fice a garden din, kan titi tayo da gudu tana neman madafa, kasancewar
titi high way ce yasanya motoci daidaiku ke wucewa aguje batare da sun lura da ita ba, titin ta
kalla da idanuwan da sukayi dishishi, kallon bayanta tayi taji tsoron kar Mujahid ya kamata, da
sauri ta ruga tsakiyar titin, kafin takai ga gangarawa kasa wata BmW ta kunno kai, kiris ya rage
bai kwashe taba yayi saurin taka burgi, itakam stars tafara gani nan take jira ya kwasheta
kasa...
"Subhanallahi" Jaafar ya fada ganin yadda ta zube kasa, ga jini ta ko ina ajikinta, fitowa yayi
da sauri ya karasa gurinta, kallonta yayi gabansa ya fadi, "Ummi.."
Ya kira sunanta a akideme, daukarta yayi yana jijjiga, yana kiran sunanta, ahankali ta bude ido
ta kalle shi, "Help me..' Ta iya fada, kanta ya fado bisa Kirjinsa alamun babu rai tattare da ita...

Innalilahi wa inna'ilaihi rajun yahau furtawa, Ummi bazaki mutu ba dayardar Ubangiji... Ya kuma
fadi, da sauri ya karasa da ita mota yasata abaya sannan ya shiga gaba motan ya zaune hade
da cire suit jacket dinsa daya shafi jini ya ajiye gefe sannan yaja motar.....
[9/7, 12:37 AM] Xarah Bukar: Zuma Sai Da Wuta

~na~
©ҳaɾaɧ bųkaɾ
(Aunty Cute)

Wattpad @Cutexarah
Blog xarahbukar.wordpress.com

53

Saida Mubarak ya tabbatar Salma ta b'ace agurin sannan ya dakatar da fad'an hade da matsa
wa gefen yana cewa "May calm down plz, ka saurare abunda zan fad'a ma"
Iya k'ulewa Mujahid yakai, nunasa yayi da bindigar cike da fusace yace "enough of your
nonsense, hand over the d damm keys"
"Easy mehh.." Mubarak ya fad'a had'e dayin surrender, key din ya ciro ya wulla mai ya ceb'e.
Fuska ba annuri Mujahid yahau shi da mugun kallo yana cewa "dont you dare interfere, am
warning you, stay out of this"
Kai Mubarak ya daga mai, tausayin Salma sosai yakama shi da takaici duk dalilin sa komai
tsakanin su yakara tabarb'arewa, yana gani Mujahid ya juya da sauri yabar gurin.

Titi ya nufa bai ganta ba sai jinin daya gani kwace gurin, hannu yasa yaji jinin fresh ya tabbatar
ba tayi nisa ba aduk inda take, Wayarsa ya fiddo ya kira duk polisawa dake check point din
hanyoyin fita da

10 / 20