Author : Zarah Bukar Category : Tknovels
faculty dinsu tare dasu shehu da wasu yan ajin su
suna tattaunawa game da wani course da zasu shiga test, wayarta ke kunnata tana waya da
Salim, murya kasa kasa hade da dariya, katse wayan tayi, shehu yace "wannan dariya fah ?.
Tabe baki tayi, tace "yayana ne, lallab'ashi nake yakai min motata gyara ban iya jure shiga taxi"
Yace "kai yaune fah kawai kikazo da taxi, Yayan nan naki kodai dashi zaai ?
Wani mugun kallo takaiwa Shehu, ba shiri yayi azaman kama kanshi, lumshe Ido Salma tayi
hade da kallon wayarta wanda tun ranar take tunanin zai kirata amma shuru, tanason sanin ya
yanayin jikinsa yake, taso zuwa office din Faiza tambayar ta, saidai ta fasa gudun kar girma ya
fadi kasa wanwas.. Karar shigowan sakone ne ya katse mata hanzari, tayi azaman budewa
ganin Mujahid.
"Hi, kwana biyu, dafatan kin isa gida Lapia ?
Murmushi ta saki, aranta tace "sai yau ya tuna dani"
Reply ta rubuta mai, "ya jikin ka, kashe maganin?
Dadine sosai ya kamashi, baiyi expecting tamai reply da wuri haka ba.
"Am okay, when are you less busy nazo na maki special godiya for saving my life..
Gabanta ne yafadi, itakam bataso su kuma haduwa da daddare dan kuwa tsoron shi take,
saidai kuma tana son ganin kyakyawan fuskan sa, tunani ta hauyi can dai tasamo mafita ta turo
mai "ina skull yanxu, zamuyi cA test, kana iya zuwa kasame ni by 4pm"
Yana gani murmushi yayi, Mikewa sukayi suka tafi Hall kasancewar lokacin test din yayi.
***
Hudu nayi Mujahid ya karaso yayi parking can gaba da inda Hall din yake, lumshe idanu yayi
yahau zama jiranta.
Cikin nutsuwa Fa'iza ta kankamce office dinta, sannan tadau jakarta ta fito, yau bata zo da
motar taba kuma batayi tunanin Mujahid ya fito aiki ba saboda condition dinshi, can gaba da
faculty tasamu taxi ta tare shi ta shiga yaja, sun shigo round kenan ta hangi Motarsa, saurin
tsayar da taxi din tayi tahau duban motan, saida ta hango fuskan shi ta tabbatar shine. Murmushi tayi aranta tace "ashe ma yazo daukata" wayarta ta duba bataga call dinsa ba tayi
tunanin ko rashin netwrk. Sauka tayi daga taxi din ta nufo motarsa sa cikin sauri.
Shikam Mujahid kallon saitin gaban shi yake dan ganin tahowar Salma bai ankaraba yaji
anbude kofar gefe an shigo, kallon ta yayi cike da mamaki.
Gyara zama tayi tace, "Mjay aida security ka tura office ya kirani, instead of kayi ta jirana"
Bata rai yayi yace.
"Aiba wajan ki nazo ba, kuma am not your driver..
Dariya tayi, cikin rashin kula da yanayin sa tace "wasa kake, gurina kazo kawai haushi zaman
jiran da kayi kake.."
Mujahid kam bai iya cewa komai ba, hankalinsa tuni ya koma kan Salma dake tahowa tana
duban cikin jarkata tana lulube, komi take nema, oho, yafada aransa, takaici ne ya kama Faiza
ganin inda idanuwan sa ke kalla.
ID card dinta take tunanin kota manta a Hall yasata alube, tana gani ta zuge jakar ta maida
hankalinta kan tafiyar ta, murmushi tahau yi ganin motar sa, kadan ya rage ta isa gurin ta lura
da Faiza dake hakince kan sit tanai kai mata mugun kallo, gaban Salma ne yafadi, saurin
shanye murmushi tayi hade da bata rai, kaman ta fasa karasawa gurin sai kuma ta dake ta
karasa saitin gurin da Mujahid ke zaune, kawar dakai tayi gefe tace "sannu"
Kallon ta yayi tamai kyau, kwana biyu nan ya lura ta daina shigar banxa data saba, jallabiya ce
baka jikinta tayi rolling da veil din, kallon Faiza yayi da gefen Ido kaman yahau ta da duka, yace
"ya test din ?
Haushi ne yakama Salma, "wato bazai ce shigo motar ba nice sanda mai jure tsayuwa, wlh
kunyi kadan" aranta tayi magana, Afili tace "Nina tafi sai anjima" kaman zatayi kuka tayi
maganar, tafiyar ta tayi bata jira cewar saba.
Tsaki Yaja ya kalli Faiza dake cika tana batsewa yace
"Miyasa kike son janyowa kanki raini, gurinta fah nazo bake ba, anjima kuma idan ta hukuntaki
kihau kuka".
Kallon takaici tamai
"Ai tare ta ganmu, kuma ma aina fita matsayi agurinka"
Kasa tankata yayi dan haushi, kunna motar yayi yaga Salma na kokarin Tsayar da Taxi, dasauri
yaja inda take yace "Kizo nayi dropping dinki
Sai sannan ta dubeshi, Murmushi tayi hade da ciro 1k dake jakarta sannan ta nuna mai tace ina
da kudin motar haya basai an lab'a niba" karawa gaba tayi abunta.
Kulewa Faiza tayi tace "kaga ja'ira ni take gayawa maganar banza baka ce komai ba"
Dogon tsaki Mujahid yaja hade da watsa mata Harara, yace "ki tafi da motar gida zanzo na
dauka" bai jira cewarta ba ya bude murfin ya fita, Sakin baki Faiza tayi cike da Mamaki rashin M
irin nasa, k'wafa tayi cikin tsananin haushin Salma sannan ta fito ta zagaya gurinsa ta zauna
hade da data motar.
Salma na shiga taxi data tsayar, taji an bude kofar baya inda take zaune an shigo, adan tsorace
ta kalleshi, magana zatayi taji yacewa mai taxi su tafi, mamaki ne yakamata, "ina ta sa motar" ta
fada aranta, batasan ya fito fili ba..
Lafewa yayi kan sit din hade da fuskan tarta sanan yace "nabarwa Auntyn ki ta tafi gida dashi
tunda kinki shigowa.."
Kunyace ta kamata, aranta taji dadin abunda yayi tasan kam Faiza taji haushi, matsawa kadan
tayi tahau bude wani handout tada ciro ajakar, Murya kasa kasa tace "ya jikin ?
Shuru yayi baice komai ba, dagowa tayi suka hada ido ta wayance da cewa "ba lafi, bruises
dinma sun warke," dauke kai tayi tahau bude pages din handout din.
Dogon ajiyar zuciya ya sauke hade da lumshe ido yace, "Miyasa baki kirani awaya ba ?
"Hmm, nayi bizy ne, soon zamu fara exams"
Magana zaiyi Wayarsa tahau ringing, dubawa yayi yaga hajiya, gabansa ne ya fadi, yaushe
rabo dayaji motsin su Hajiya tun randa yabar gida, gyara zama yayi sannan ya dauka, gaidata
yayi ta amsa ciki ciki, sannan tace "kazo gida kasameni ina da magana da kai ."
Dafe kai yayi kaman yayi ihu, sanin maganarta batada nasaba da wacce take kusa dashi,
murya kasa kasa yace "Hajiya yamma tayi, gobe insha Allahu zan shigo"
"Allah ya kaimu" ta fada hade da katse wayan.
Satar Kallon shi Salma tayi tace "wace ce ?
Yak'e yayi yace "mama nace"
Cike da fara'a ta dubeshi tace "i would like to meet her, wana unguwa take ?
Tashin hankali ne ya diran mai, dakyar yace "ba anan take ba, can Sokoto suke zama"
Harara takai mai cikin salon wasa tace "kodai bakaso nasanta ne, naga ai sister dinka anan
take skull.."
Dariya yayi wanda da gangan ya tsiro shi gudun karta dago shi, yace "Amina wai, ai sunyi hutu
tama koma gida can sokoto.."
Murmushi Salma tayi tace "ayyo" aranta kuma tana tunanin Amina dayace dan kuwa ba Amina
sister dinshi tace sunanta ba, bata damu ba ta kawar da tunanin kasancewar taje gidan shi
kuma bata ga alamu yana da yan'uwa ba.
Shuru ne ya ratsa tsakanin su har taxi ya iso gidan su.
Kallon shi tayi, gabadaya baya cikin hankalinsa, tabosa tayi, adan firgice ya kalleta, murmushi
tayi tace "kana da abun dariya, kodai dukan yafara tab'a kane.."
Murmushin k'asaita yayi, irin wanda yake fizgar zuciyar wanda aka yiwa.
Yace
"Kije ki huta, i'll call you later"
Okay, bye ta fada ta fice a mota.
Gobe Birthday na í ½í±¯í ½í±¯í ½í±¯í ½í±¯í ½í±¯í ½í±¯í ½í²ƒí ¼í¿¿
[9/7, 12:37 AM] Xarah Bukar: : Zuma Sai Da Wuta
~na~
©ҳaɾaɧ bųkar
41- 43
Gidan su fa'iza ya wuce amsan motarsa. Isketa ta yayi tsaye haraban gidan jingine bisa motar.
Da ganin sa tahau cika da batsewa, cikin koya kula da yanayin ta yace tabashin mukullin.
Kaman zatayi kuka tace "Mjay miyasa zaka min haka gaban yarinyar nan, shikenan ta gama
raina ni yanzu gani zatayi daidai nake da ita tunda kana kulata" Kallon takaici yayi mata.
"Keda ita ba d'aya bane, you're my friend ita kuma she is nothing.."
Cikin rashin gamsuwa da kalamansa ta tab'e.
"ban yadda ba saboda dazu kallon da kake mata baiyi kama da babu komai ba, kuma na
tabbata ka fara sonta"
Murmushi gefen baki ya saki wanda shi kadau yasan manufarsa, yace "tabbas na kamu da
sonta saidai son da nake mata baikai na kasance tare da ita ba, kin dauka zan barta taci bulus
ne bayan tamin rashin mutunci "
Nisawa Faiza tayi, aranta batai na"am da koma mai yake niyyan yiba, tunda har ya furta yana
sonta ba lailai ne ya rama abunda zaiyi ba
"What are you planning ?
Girziga kai yayi yace "i dont know yet, ina dai tunani gagarinmin abunda zanyi na koya mata
hankali, so nake tayi kuka da idanta"
"Daganan kuma saika rabu da ita kenan ? Faiza ta fadi.
Tsaki yaja
"Kinga enough of your questions, you're just a friend banaso ki wuce limit dinki" ya fada, amshe
mukulli hannuta yayi ya fada motar yaja ya barta nan tsaye baki sake cike da takaici.
Salma na shiga Gida daki ta wuce ta kwanta, zuciyar ta fal da farin ciki, tunanin Mujahid take
tana tuna farkon haduwa su izuwa yau, kwata kwata takasa gane kanta, shin sonshi take komi,
kullum dashi take kwana ta tashi, girgiza kai tayi, sam babu lissafi soyayya aranta, bata tab'a yi
ba saidai na baya data gani sun wahalu daga karshe ma tsana ce ta biyo baya shiyasa take
bala'in tsoron fadawa soyayyar wani. Tana son Mujahid amma bazata nuna mai komai ba
ayanxu har saida tabbatar he won't break her heart.
****
Tun daga ranar lamari ya canza tsakanin su, soyayya da kulawa sosai Mujahid yake nunawa
Salma saida bai fito yace yana sonta ba, har ilah yau bai kuma canza kudurin sa na koya mata
hankali ba, ta bangaran Salma kuwa zuciya daya take zaune dashi takan yi mamaki sai kace ba
kwanakin baya suke casa juna ba, aranta takanyi tunanin anya kuwa Mujahid baida wani
mugun nufin akanta, saurin kawar da tunanin take saboda tsananin yadda yake damuwa da
lamarinta.
Daddyn Salma ne tare da Ja'afar a office dinsa. ja'afar yana daya daga cikin lauyoyi da Alhaji
Abbas ya aminta saboda tsananin rike gaskia da Tsoron Allah da yake azuciyarsa, sau tari
yawan idan zaiyi harkar canji da dollars ko euro yafi yadda da damk'awa jaafar takardun
shaidan komai dan yasan bazai cucu saba. Zaune suka suna magana akan wani fili daya siya a Kaduna, copy na takardu shaida da komai
ya mikewa Jaafar, karba yayi yana dubansu
Daddy yace "ka adana su da sauran"
Hade takardun jaafar yayi cikin briefcase nasa sannan ya mike da niyan yimai sallama, dakatar
dashi Daddy yayi hade da cewa "ya maganar mu ta kwanaki, naji shuru baka kara waiwayar
zancen ba.."
Zama jaafar yayi had'e da kirkiro murmushi dole, shikam yama manta da zancen, shuru yayi
yana tunanin zancen da neman amsar bawa Daddy, bazai yaudari zuciyan saba dan kuwa yana
son Junaina, saidai kuma ba damuwa tayi dashi ba ga kuma Daddy da yakeson ya hada shi da
Diyar shi dako sanin ta bai yiba balle ma yasota, shi kuma auran bayama cikin lissafinsa yanzu
kokarin Nemo Ummi kawai yake dan farin cikin hajiyarsu kuma baima isa ya tunkareta da sunan
yana son aure ba, ana takai wa yake ta kaya.
Ajiyar zuciya ya sauke yace "Alhaji wani hazari ba gudu ba, maizai hana mu hadu da diyar taka,
idan ta amicin dani saina yadda karya zamana ko tana da wanda takeso"
Farin ciki sosai ya lulube Daddy, kasancewar ta bangaran Salma ba matsala koda batason
Jaafar yasan zata mai biyayyah, kuma ma baiyi tunanin Salma nada wani da takeso ba.
yace "ba matsala, gobe kazo gidana mu kara tattaunawa saika ganta
Yake jaafar yayi aranshi yace "Allah yasa karta aminci, afili yace "saidai yau nazo, saboda gobe
da safe ina da aiki a Kaduna"
"ba damuwa, Allah ya kaimu zuwa dare" acewar Daddy.
Godiya yama Daddy sannan sukai sallama ya fice azama.
Tun ranar da Hajiya ta kira Mujahid tace yazo gida bai samu daman zuwa ba sai rana ta yau
acewarsa aiki yamai yawa bacin kuma da gangan yaki zuwa.
Fuska ba yabo ba fallasa Hajiya ta tarbeshi, nan tahau mai fadan barin sa gida akan abunda
baikai ya kawo ba, Mujahid kam shuru yayi yana sauraran ta dan ya kagara ta gama ya wuce
aikinsa, tace "Bani hotunan Ummi dana baka kwanakin baya"
Sosa keya yayi alamun marar gaskia yace "mi zaai dasu, an ganta ne ?
Hajiya tace " baa ganta ba, kawai hoton zaka bani tunda ba nemo ta zakayi ba, tuni Jaafar ya
dukufa da nemo ta kuma am sure zai samota aduk inda take"
Ware ido Mujahid yayi adan kidime yace "jaafar zaki bawa hoton ?
Mugun kallo takai mai, tace "ko babu hoto Jaafar yasan fuskan ta, kaida ba saninta kayiba yasa
na baka hoton"
Gabansa ne ya fadi, fatan shi Allah yasa kar Jaafar ya hadu da Salma, nisawa yayi yace "Hajiya
basai jaafar ya nemo taba, nida kaina zan kawota gidan nan very soon."
"Ka ganta ne" Acewar ta.
Kai ya girgiza alamun a'a, aranshi yace "ki bani time very soon zaki ganta amma saina koya
mata hankali yadda idan ta shigo gidannan bazata yadda ki had'ata aure da niba".
Tashi yayi ya mata sallman zai wuce office ya fice waje, nan suka hadu da Junaina ta dawo
daga gidan wata kawarta dan tuni sun gama Neco.
"Yaya kyan tafiya dawowa" ta fada tana dariya.
Tabe baki yayi yace, "ce maki akayi nadawo"
"Oh Allah, he will never change, ni ina can ina missing dinshi amma koya kula dani" aranta tayi
maganar, Afili tace "yaya akwai abunda nakeso kasani, sumtin is going on in this house"
Kallon gefe yayi babu mai dubansu sannan ya jata gefe danjin wana abu ke faruwa, sau tari
dama ita ke kaima rohoton abubuwan dake faruwa agidan dan ba zama yake ba.
Murya kasa kasa tace "bansan full story dinba, naji dai Hajiya na Waya da Aunty Bilkisu akan
wani abu, i dunno ko kudi ne ko gida ko kuma ince sumtin is missing i dont really know, naji
Hajiya tace tunda kai kaki nemo wa idan ya jaafar ya nemo shi zata
bawa ta fasa baka"
Hankalin sane ya tashi danya gane inda Zancen ya dosa, saidai bazai bari Jaafar yaga Salma
ba much less ya yadda da auran suba.
Dakewa yayi yace "little sis kinsan mi zakimin"
Kur tayi tana kallon shi, yace "inaso ki sawa Jaafar ido, idan kinji yana waya akan wata mace ko
bincike ki bani feedback kinji"
Kai ta girgiza alamun toh, murmushi ya sakar mata. "yauwa my beautiful sister, you know i like
you alot"
Dariya tayi tace "nidai yaya kadawo gida plz, wlh i missed you alot".
"Karki damu nakusa dawowa"
Dadi sosai taji, sun jima yana biyeta sai shagwaba take zuba mai daga bisani ya lallab'a ta ta
tafi ya koma motarsa yaja yabar gidan.
Tuki yake yana neman mafitan yadda Jaafar bazai hadu da Salma ba, idan yayi sake kuwa
yanaji yana gani zaiga Salma a gidansu, dabara ce ta fadowa mai yadau waya hade da dailing
no din Salma.
Alokacin kuwa had'e book dinta Salma tayi cikin jakarta sannan tabar dakinta, gurin Mom ta
shiga ta mata sallama ta fito cikin sauri, library na skull takesan zuwa karatu saboda jibi ne zasu
fara exams.
Kokarin bude motar tayi taga kiransa, murmushi tayi ta dauka.
Daga can Bangaran cikin sweet voice dinshi yace "Angel of my life, son kowa kin wanda ya
rasa"
Dariya tayi kasa kasa, tace "ka fara koh, how am i even sure am your angel"
Yace "believe me, ba karya nake ba, idan ma baki yadda ba God knows it.
"Kaga ni library zani, inada exam jibi, kana ina?
Yaji dadi abunda tace, aranshi yace "perfect, nasan abunda zanyi"
Afili yace "ina driving, ki jirani nazo nayi picking dinki saimuje inda babu wanda zai dameki dan
kisamu kiyi karatu, nasan ki da tsokana kar kije kiyi dambe da mutane a library" karashe
maganar yayi cikin zolaya.
Shagwabe fuska tayi kaman yana ganinta, tace "nifah bani da tsokana, ko dambe ban taba
yibaaa.."
"Hmm, kedin, ki jirani am coming" katse call din yayi, ta fita can bakin gate jiran shi, baafi 20
mins ya karaso ta shiga motan ya kama hanyar office dinsa, tagane hanyar, tace "lailai ma office
dinka ne bazaa dameni ba?
Wani shumin kallo yayi mata da saida taji shi a kwakwalwar kanta, murya kasa kasa yace "duk
wanda ya dameki cikin cell zan wurga shi..
Ware ido tayi adan tsorace, "cikin cell sai kaca a film"
Dariya yayi bai kuma cewa komai ba ganin yadan tadan tsorata, suna isa parking yayi, suka fito
suka shiga elevator har zuwa cikin office dinsa, ita batama san akwai elevator ba kasancewar ta
stair security yabi da ita kwana kin baya.
Office din babba ne mai shegen kyau can gefe inda Couch da center table yake takarasa ta
zauna shi kuma yA karasa gurin table dinsa ya zauna kan kujerar sa hade da fara aikin danna
laptop din gabansa, sosai yaci serious da abunda yake batare daya dubi Salma ba.
Itakam abunda take so kenan, bude handout dinta tayi ta dukafa da karatun General studies
da suke dashi.
Bayan kaman awanni uku Mubarak ya shigo office din, ganin Salma yasashi dariya, zama
yayi gurin mujahid yana zolayar shi murya kasakasa, b'ata rai Mujahid yayi, yafara magana cikin
fad'a, duk ahankali suke magana, Salma bataji komai ba kuma bata damu dason jiba, sund'an
jima sannan Mubarak ya fice office