Author : Zarah Bukar Category : Tknovels
sauya launi zuwa ja.
"Ya kakeso nayi, dole naje na fahimtar da ita".
Hannu Abdul ya daura bisa kafadar sa.
"ka bari ba yanzu ba, she need some time"
Shuru Mujahid yayi batare daya iya cewa uffan ba, sun d'an jima nan tsaye kaman sanduna
daga bisani suka koma ciki. Wayarsa dake ajiye kan kujerar palon yadauka ya kira Salma,
saidai ba bugun duniyar dabai yiba fir taki dauka.
Akan titi kuwa wuta sosai Salma take bawa motar ayayinda take zubar da hawayan bak'in ciki,
dakyar ta iya karaso da kanta gida, Afusace ta bude motar ta fito batare da ta tsaya bi takan
wayarta ba, wani mugun juwa da azababban ciwon kai ke barazanar barar da gabobin jikinta.
Adaddafe tafara takawa zuwa bangaran Salim wanda ayanzu ta tabbatar shi daya ke mata son
gaskia, sab'anin da datake mai kallon wawa, soko marar hankali, yaudai gashi wanda take ma
kallon zinare yazame mata bak'in gwarwashi.
Kuka take sosai ta k'usa kai cikin palon, kwance ta iske shi bisa doguwar kujera duk jikinsa
mace, da alamun ma cikin zufin tunanin yake, sunansa ta kira cikin sheshek'a tare da fad'awa
jikinsa, Atsorace ya dagota ya yunkuro zaune yana kallon ta, duk ta gama birkice sa da kamshin
jikinta, tunda suke gidan bai taba ganin ta cikin mugun yanayi aka ba. Cike da firgita yahau tambayan ba'isin kukan ta, kasa magana tayi saima sautin kukan ta daya
tsanan ta, hankalin Salim ne yatashi, dakyar ta iya cewa
"Yaya kaina ke ciwo"
Janyota yayi ta kwanta bisa kirjinsa yanai mata sannu hade da bubbuga mata baya cike da
lallami, sosai yaji dadin yadda suke makale da juya, aransa sai aiyanawa yake dama tazo mai
yanzu yakamata ya mayar da Salma tashi ta har abada.
Salma kam kukan ta take, ko tuna abunda ya faru bata sanyi, yadda zata gayawa Daddy ta fasa
auran Mujahid kadai ne matsalan ta, tunda tun farko ita tace tagani tanaso bawai tursasa ta
akayi ba.
Dagota yayi ahankali ya jingine ta jikin kujerar, cikin sanyi murya yace
"bari nadauko miki maganin ciwon kan"
Kai kawai ta daga mai, ya wuce dakin sa, side drawer ya bude ya dauko wani magani dani
kaina bansan na miye ba sannan ya fito yadauki bottle water dake ajiye center table ya karasa
gareta..
Salma kam bata kaunar magani, dakyar da lallami ta yadda tasha pills guda biyu daya dauko,
ubansa tayi ido jajir tace, "nagode"
Aranta kuwa danasani take dama tun farko shi ta baiwa soyayyan ta, koda yake bai baci ba
zata fadi ma Daddy shi takeson aura ba Mujahid ba. Shingid'e kanta tayi kan kujerar, Murmushi
Salim yayi yahau goge mata hawayan fuskar ta, bayan kaman minti biyar tafara ji nauyin jiki da
kasala, mikewa tayi tace "yaya sai da safe"
Yace "Allah ya kaimu" aranshi kuwa yace keda ganin safiya badai a gidan nan ba.
Taku tafarayi ahankali taji mugun hajijiya, abubuwan dake palon biyu uku tafara ganin su, bata
aune ba taji ta ta fadi kasa wanwas.
Farin cike ne yakama Salim, mikewa yayi ya tako inda take ya tsugunna yanai mata shuumin
kallo sannan ya mike ya leka waje ta window, shuru babu kowa, daukar ta yayi suka fito
haraban gidan ya nufi inda motarsa ya bude yasata sannan ya shiga yaja yabar gidan @ 360...
Ba zaice ko ina ba sai Badoo Quarter, agaban wani gidan mai kyau madaidai ci yayi parking ya
fito ya kuma daukar ta suka shiga ciki, palon mai shima mai kyau yasha kayan alatu, dakin ya
bude yashiga ya ajiyeta kan gado sannan ya fito ahankali ya kulle gidan, Ajiyar zuciya ya sauke
ya koma motar sa yaja ya koma gida.
[9/7, 12:38 AM] Xarah Bukar: Zuma Sai Da Wuta
~na~
©ҳaɾaɧ bųkaɾ
(Aunty Cute)
NAGARTA WRITERS ASSOCIATION {NWA}
Allahu akbar kulu'nafsi za'ikatu mauti, Allah yaji kanki da rahma Maman besty Yar ficika. May
jannatul Firdausi be ur final destination.
64
Kuka sosai Salma take yi, duk yadda taso fita gidan kasawa tayi kasancewar duk kofofin tamke
suke da mukulli, ganin ba sarki sai Allah yasa ta lallashi kanta tadau abuncin daya kawo taci ta
kwanta nan kasan dakin cike da tausayin kanta. Salim kuwa ganin yadda Mom bata zarge shi
da komai ba yasashi samun karfin gwiwa, dakinsa ya nufa ya shirya kayansa tsaf cikin akwati
cike da murnan gobe zai fece zuwa kasar Ghana da salma koda kuwa baa fasa daura mata
aure da wanda yafi tsana a duniya ba, shine kawai ya gudu da Salma shine muradin sa.
Gida Mujahid ya nufa duk jiki amace, tunanin yake da amincewar ta tabar gidan tabi salim ko
kuwa dai sacen ta yayi dagaske. Dafe kai yayi cike da tashin hankali kwata kwata yarasa ta
yadda zai bullowa lamarin, wayarsa Da mubarak sunyi dashi cewa karya damu gobe zai baza
yan sanda a gari neman duk inda take, for now ya ya bari ayi daurin auren ba tare da tashin
hankali, dan kuwa muddin hajiya taji labarin abunda ake ciki saidai kuwa afasa auran. Da
wannan shawarar Mujahid yadan samu nutsuwa kadan.
***
Washe gari Mom bata nunawa kowa abunda ake ciki ba, yaken dole kawai take ana buduri, ita
duk atunanin ta ba bata Salma tayi ba aganinta su Hajiya suka dauketa dan su nuna mata
iyakar ta, babu abunda tace da Daddy har aka daura auren su kowanne abisa sadaqi dubu
hamsin, bayan Daddy ya dawo ne yace da ita tama su Hajiya waya yakamata ace Salma ta
dawo, yafiso ya mikata gidan miji dakansa. Toh kawai Mom tace dashi saida taga yabar gurin
tadau wayar Salma kiran nambar Mujahid.
Gidan Mubarak su Mujahid dasu Abdul suka nufa bayan an daura aure, ko wanne su sanye da
tsadadsiyar shadda sunyi kyau barin ma Mujahid dayafi su kyau da kwarjini, da ganin fuskokin
su babu walwala tattare da ita saidai ango duk yafi shiga kidima ganin tun safe samun inda
Salma take yaci tura kasancewar yan sanda kusan ashiri da aka baza nemanta basu ganta ba. Nisawa Mubarak yayi yace "Mjay kasan abunda zamuyi ?"
Kallonsa yayi ido yajir, Mubarak yacigaba "kawo namban ta muyi tracing Gps device din ta dan
sanin exact location nata"
Tsaki Mujahid yaja yace "wannan idea din is of no use, wayarta na gida gurin momcy dinta, nifa
am sure dan Iskan nan yasan inda take y not kayi kama shi kayi torturing dinshi tunda ni am out
of the force"
Dariya Mubarak yayi.
"Taya zan kama Salim without concrete evidence, you're crazy sai kace nina aikeka ka kwafsa"
Abdul ne yace "anyi mai wuyan ai, auran"
Harara Mujahid yakai ma, aranshi yana fadin ina dadi babu matan.
Mubarak yace "kaga there is nothing i can do, addua zamuyi Allah ya bayyana ta, kuma dole su
Hajiya susan abunda ke faruwa"
Magana Mujahid zaiyi wayarsa tahau ruri, dubawa yayi yaga namban salma, da azama ya
dauka, Muryar Mom yaji tace "ina fatan dai ka fito da ita aduk inda kuka boyeta ?
Ruwan ne ya cinyesa, kasa magana yayi sai kuka daya fashe dashi, haushi ne ya kamata ta
katse wayan.
Kallon yayi cike da tausayin kasan, Azabure kuma ya mike daga inda yake zaune ya kalli
Mubarak yace "na tuna akwai agogona na office gurinta saidai bazan iya accessing gps din
device dinba saboda password dinsa na office is blocked, i need your password da tab dinka"
Mamakine ya kama Mubarak, ya zaai yabata agogon shi na office wanda manyan maaikata
kadai ke da acces dashi, kuma ma ai yakamata ace yayi submitting agogon tun randa Sir
Ahmed ya bashi suspension, kodayake yanxu agogon zai iya amfani indai tana tare dashi, tsaki
Mubarak yaja yace kai banza ne wlh, mikewa yayi yadauki tab dinsa dake kan table sannan ya
mika mai yana kaimai harara, su Abdul kam dariya abun ya basu.
Lekowa haraban Gidan Salim yayi, saida ya tabbatar babu kowa sannan yaja akwatin sa ya fito
waje, bakin mota ya tsaya ya karewa gidan kallon karshe, sannan ya bude boot yasa akwatin ya
zagaya yazauna cikin motar, tagumi yayi yahau tuna yadda Daddy ya taimake sa lokacin da
bashi da kowa yq dauko shi daga tsumma ya kawo sa gidan tun yana karami harya girma ya
zama wani abun, Saidai soyayya Salma ta ruguzamai rayuwa kuma baiga zai iya hakura da ita
ba. Hawayene ya zubo mai cike da tausayin kansa, atake yaji wani irin ciwon kai ya tsiga reshi,
da sauri yasa hannu cikin aljihun rigarsa ya ciro wasu jajayan kwayoyi kusan kuda takwas ya
afka abaki hade da hadiye su, wani irin buguwa yaji cikin kwakwalwaraa sannan kuma alokaci
guda yaji sa ya dawo normal, Ajiyar zuciya ya sauke ya kunna motar ya fice daga gidan.
****
Wani dattijo mai kimanin shekaru hamsi da hudu ne zaune cikin motar sa dake fake bakin gate
din gidan Hajiya, yafi minti talatin zaune yana saka da warwaran yadda zai shiga gidan, idan bai
manta ba last haduwan su da Hajiya kusan shekaru goma da suka wuce, rannar da suko
gidanshi a gombe ya masu rashin mutunci akan karsu kara zuwan mai gida yanzu kuwa gashi
ya dawo cikin hayyacin sa yaran kawai yake son gani ya nemi gafarar su, musamman Salma
daya yayi mugun bakan ta mata. Kukan nadama ne ya kufce masa, saida yayi mai isar sa
sannan ya fito ya tunkari gate din gidan, gaisawa sukayi da Mai gadi sannan yace mai yamai iso
gurin Hajiya, maigadi kam ganin mutumin yamai yanayi da yaran gidan yasa shi cemai ya shigo
ciki bara yaje ya kira mai Hajiya.
Hajiya kuwa sai hidima take da bakin da suka zo daurin aure, su Aunty Bilki na daki tare da
Junaina da wasu yan uwa suna ta zolayar ta, ita kuwa sai wani kuka da langwabewar
shagwaba take, Annah ce ta leko dakin jiki ba laka, ganin Hajiya bata ciki yasa ta komo palo ne
manta, jamaa sai janta suke ta hira batako kalle su ba, Bata ganta ba, daga can kitchen ta jiyo muryar ta, da azama ta shiga kitchen taja ta suka fito
waje inda babu jama'a.
"Annah lafiya kuwa ? Hajiya ta fadi tanai mata kallon tababbiya, ta lura jiya zuwa yau Annah
bata cikin wani walwala.
Kuka Annah ta fashe dashi tana fadi mata karyan aikan Salma da tayi da kuma sanarwa mujajid
gaskia da tayi, Salati Hajiya tayi cike da tashin hankali, right under her nose abubuwa sun faru
bata da labari, wayarta da hannuta tahau kiran Mujahid dashi, shuru no amsa. Hakalinta ne ya
kuma tashi, bata sanda tahau Annah da masifa ba tsabar takaici, Annah kam kuka take tana
fadin "wlh duk laifi nane, kila ma yan yanke suka kamata, ashaa tama mutu kila"
Ran hajiya ne ya kuma bashi, magana zatayi taga mai gadi ya kusanta gurun su, da sauri ta
karasa garesa tana tambayar sa ko yaga Mujahid, shikam bai amsa tambayar taba yace "Hajiya
kinyi bako, wai Alhaji babangida daga Gombe ?
Ras gabanta ya fadi, Annah ta gane waye hakan, kallon Hajiya tayi baki wangale.
Daskarewa sukayi gurin ba tare dasun san ya karaso gurin ba, sai jin muryar sukayi cikin
Sallama, atsorace suka kai dubansa garesa nan take annurin fuskan Hajiya ya dauke.
"Babangida ina fatan dai ba daurin aure kazo ba, dan tuni madaurin auren uban yaranka ya
daura"
Jikin sane yayi sanyi, baiyi mamaki ba tunda yasan yammatan sunkai aure, kuka ne yazo mai
ya tsuguna baiwa Hajiya hakuri, bata sauraresa ba ta juya zata koma suka ji muryar Junaina ta
fito da gudu tana kiran Hajiya, da gudu ta karasa gurin cikin haki tana fadin "hajiya kinji su Aunty
biliki wai dole sai anmin kitso kanana nikuma bana so" karshe maganar tayi tanai bin ko wannen
su da kallo ganin bama fahimtar abunda take fadi sukayi ba.
"Yar auta ta haka kika girma" babangida ya fada yana kallonta, kallon shi tayi kaman taso gane
shi a hoto, Annah ce ta katse mata kallon da cewa "ke Abban kune"
"Abban mu" junai ta fada cike da murna, ita kan burinta bai wuce taga Abban taba, da sauri taje
ta rungume shi cike da farin ciki, kuka sosai Abban su yafashi dashi, Shuru Hajiya tayi tana
kallon su idonta cike da hawaye tunanin ina Salma ta shiga take aranta.
Gidan Salim
Salma bata samu runtsawa ba sai bayan sallah Asubah wani mugun bacci ya sace ta, sai after
1 ta tashi da matsanan cin yunwa, ruwa kadai ta iya sha tayi alwala tayi salllah azahar sannan
ta koma kan gadon ta kwanta, wani red light taga yana blinking jikin agogon hannuta bata damu
ba ta share tahau Tunanin Abbanta da gidansu a Gombe da yadda tayi zaman kanta a gudin
tun bayan da abba ya rabu da Amminta sanadin Aunty jamila daya aure ta mallakesa da sai
yadda tace zaiyi karshe ma Abba dakanshi yace mata tabar masa gida taje ta nemi dangin
uwarta, shine ma dalilin zuwan ta Abuja, bata san kowa agarin ba Allah ya hada ta da Daddy ya
taimake ya riketa amatsayin yar cikin sa, Nisawa tayi tace "Allah ya kare ka Abba daga shairin
Aunty, nasan bayin kanka bane" shuru tayi tana ayyana idan tasamu hanyan guduwa Gombe
zata koma gurin Abbanta.
Around 3 taji motsin ana shigowa, mikewa tayi zaune adan tsorace, Salim ne ya shigo, farar
fuskar sa jajir, da ganin sa ba cikin hankalin sa yake ba, cike da karaji yace "ke tashi mu tashi,
flight din 5pm garemu"
Tausayin sane ya kamata ganin yana yinsa, tagane yayi high da yawa, cikin sanyi murya tace
"yaya you need a doctor, na yadda zan bika amma kabari muje aduba ka, you're really sick"
Wani mugun kallo yakai mata da saida taja baya, Bindigarsa dake aljihun bayan rigarsa ya ciro
afusace ya nunata dashi yana dariya yace, "i won't allow you take me for a fool, Get out out.."
Atsawace ya karashe maganar.
Dan ihu tayi ganin dagaske zai iya pulling Tigger, tace "yaya zan bika Ghana, amma dole muje
asibiti"
"Yarinyar nan wasa kike dani" ya fada, deawer ya bude ya ciro wasu drugs daban dake cikin
wani white container ya ciro pills da dayawa ya apka abaki sannan ya kalle yace "Get out,
before i pull d trigger.."
Haushi ne yakamata, dan kuwa tsoron ma ta daina ji, tace "babu idan zani, kuma nasan you
wont try killig me kaida ko kwaro banga ka taba kashe wa ba".
Kecewa yayi da mugun dariya sannan yace "salma it all your fault you made me become a
killer, saboda ke na kashe Babanayaro mistakely, dan haka you wll be stock with me foreva"
hannu yasa ya fizgo ta batare daya damu da state of confusion data shiga ba, innalilahi kadai
Salma ke ambata sai yanxu tagama gane ba sonta yake ba he is only obsessed with her.
Ihu tahau yi yana janya waje, gate din ya bude ya jata bakin mota taki shiga, kokarin turata ciki
yayi ta gantsara mai cizo, wani mugun mari yakai mata saida ta fadi kasa hade da zakin
razanannan ihu, hannusa yasa zai damko wuyanta ya lura da agogon hannunta dake blinking
Red light. Ware ido yayi in shocked, ya daga ta tsaye afusace yana fadin "gidan uban wa kika samu
agogon nan?
Yawu ta fota mai a fuska, tace "you're insane" sannan tayi kokarin warce kanta ta ruga da gudu
zuwa bakin gate din dake hangame, saita ta yayi da bindigar yace "dont you dare leave this
house".
Stand still tayi gabanta na faduwa, takowa ya farayi gurinta suka ga motocin Yan Sanda ya diro
gurin, motar dake biye dasu kuma Mubarak da Mujahid ke ciki, da sauri suka fito daga mota
akidimi.
Salma na gani Mujahid ta rugu ta fada jikinsa tana kuka, shima rungemeta yayi yana kukan
yana kara bata hakuri.
Salim kam is shocked, da abunda idansa yagani, ransa ne yabaci aganinsa Salma ta kara
yaudaran sane ta hanya fada masu inda ya kawota, bai lura da jinin daya fara zubowa daka
hancin saba ya kuma saita bindigar kansu.
Yan sanda dake gurin ne suka ce yayi surrender, ko kallan su baiyi ba balle yayi surrender.
Hankalin Salma ne ya tashi, tayi saurin saki Mujahid, kallon Salim tayi, hanci sa na bleading
sosai tace "ya you need so help, plz stop acting crazing muje asibiti plz..." Kuka ta fashe da
dashi tana rokansa, amma ina shikam bata kansan yake ba, so yake kawai ya harbe Mujahid
dan kishi, takowa Salma zatayi garesa Mujahid yayi saurin rikota yace "he is crazy, dont move
further.."
Kallan sa Salma tayi, murya kasa kasa tace "he is my brother, i dont wanna lose him"
Dariyar dayafi kuka ciwo sukaji Salim yayi yace "indai shi kika zaba na gwammace ki mutu
kowa yayi asara" harba bindigar yayi saitin Salma ayayinda yaji karfin jikinsa ya kare ya fadi nan
kasa, jini ta hanci da kunne, cikin zafin nama Mujahid ya tureta bullet din ya same shi, nan take
ya fadi kasa wanwas babu rai ai jini dake ambaliya ta baki, Ihu Salma tayi, Mubarak yayo kansa
gadangadan, sauran yan sanda kuma sukayi kan Salim.
Ihu Salma take tana kuka tana jijiga Mujahid, amma ina bai ma san tana yiba, halinkali tashe
Mubarak ya ba yan sandan oda aka dauke su biyu cikin Mota, Salma sai kuka take tana rokon
mujahid Gafara, duk itace sanadin komai, kuka sosai take har suka isa asibiti aka wuce dasu
Emergency.
Salma kam kuka jikinta ya gama gayamata Mujahid dinta bazai farfado ba, dakyar Mubarak
yahau Lallaba ta rage kuka, wayar Mujahid dake motarsa yadauka ya kira su Hajiya ya shaida
masu suna asibiti, sannan ya karbi namban mom gurin Salma suma ya sanar dasu abunda ke
faruwa.
Baa fi minti 30 ba kowa family ya hallara agurin, tsabar Kidima Salma bata ma lura da Abbanta
dake tare da