Author : Zarah Bukar Category : Tknovels
ta hango sa dunk'ule tsakiyar gadon
kud'undine cikin bargo kansa kadai ke waje yana baccin sa hankalin kwance, ga wata
sanyayyiyar kamshi dake tashi ta kowana lungu da tsakon d'akin. Karasawa tayi gefe gadon
sannan ta kira Sunan sa ahankali, shuru bai amsa mata ba, tsoro ne yakamata kodai baya da
lafia, rarrafawa tayi har tsakiyan gadon ta tsugunna daidai fuskar sa, hannu takai bisa goshinsa
taji temperature dinsa is normal, ajiyar zuciya ta sauke ta zubawa kyakyawan fuskar sa idanu,
murmushi tayi zata juya taji ya riko hannuta tafado jikinsa, cike da kid'ima ta kallesa, gani tayi
idanuwan sa bude yana mai mata wani irin kallo mai fizgar zuciyar wanda ake ma, Saurin d'ago
da jikinta tayi, suna kallon juna..
Ganin tayi ya mika hannunsa zai taba jikinta tayi saurin rintse idanu, murmushi marar sauti ya
saki, yasa hannu ya gawar da gashin kanta gefe daya zubo ya rufe rabin fuskar ta.
"Kin dauka na mutu ne ?
Ya fada cikin salon da bata taba ji garesa ba.
Bude ido tayi ta dubesa, murya shagwabe tace "naga miss call dinka"
Marairace fuska yayi yace "sanyi nakeji, i need your body to warm me up" karashe maganar
yayi ya kuma janyo ta jikinsa.
Mintsini takai mai, tace "are you crazy ? Cikin salon wasa ta fad'i.
Dariya yayi yace "am crazy about you"
Chakwulkuli yahau yi mata, tahau rokonsa ya bari, wani mugun dariya ke cinta, kasa jure wa
tayi tadau karamin pilo tanai kaimai duka cikin salon kauna, tace "plz stop it..
Ganin ba bari xaiyi ba tahau kokarin sauka kan gadon da ya hargitse gaba daya, kowannan su
dariya yake suka ji an bango kofar dakin da karfin gaske, atare sukayi surrender cike da tsoro.
Tsaye Annah tayi ranta na mugun tafasa da bacin rai, mugun kallon tama Salma tace "Miye
hakan, nonuwa awaje, gashi a hargitse ?
Saurin karasa saukowa Salma tayi cike da kunya, adjusting hannun rigarta data zabulo kasa
tahau yi.
Tsaki Mujahid yaja yace "waike Annah sa idon naki har dare ma kasuwa take ci"
Haushi ya kuma kamata, Salma kam tsuru tsuru tayi.
Annah tace "zakaci uwar kane, yarinyar mutane ka matse a daki, wayasan ma mikai mata, kaga
yarinya shuru shuru".
Dariyar rainin wayo yayi yace "ki tambayeta idan nina ce tazo"
Kallon ta Annah tayi tana jiran amsa, Salma kam ihu yarage bata yiba dan kunya, kuma abun
haushi ma ita takawo kanta....bata ankara ba taji saukar Sandar Annah a ajikinta, kara marar
sauri ta saki zabar azaba, da sauri Mujahid ya sauko kan gado ya amshe Sandar yaja Salma
gefe, yace "Allah kuwa kika kara dukanta awaje zaki kwana". Tafi Annah tayi tace "ubanka ma yayi kadan" nuna Salma tayi da hannu tace "keda nake
yabonki Sallah ashe ko alwalar ma baki iya ba, nasan maganin ku, kafin ku b'arko abun kunya
kwara na aurar daku cikin satin nan yan banza yaran kawai" warce Sandar tayi hannusa ta juya
tafita. Adan kidime ya kalli Salma yace "hope bata ji maki ciwo ba.?
Kai ta girgiza alamun a'a, sai kuma tace "yaya sandar akwai zafi ashe" kaman tayi kuka ta fadi
hakan.
Sosai yaji tausayinta, dan kuwa yasan zafin sandar, zaunar da ita yayi kan gadon yace "am
sorry, duk laifi na ne"
Murmushi tayi batace komai ba, sai kallan juna da suke, Annah ce ta kuma dawowa tana fadin
"kina fitowa ko saina zo na kara maki ?
Da sauri ta mike, tace "Ya good nyt"
Kaman karta tafi yaji, lumshe ido yayi yace "nyt dear, sleep tight"
Ficewa tayi da azama, yabi bayanta da kallo cike da tsatsan sonta, zuciyar sa sai kara tuna mai
yake ya rama abunda tayimai kwanakin baya.
Labb'an sa nakasa ya ciza, sannan yace "i love you so much but dole nayi hurting dinki kema
ki dandani azabar danasha" kwanciya yayi kan gandon yana tunanin hope he isn't making any
mistake.
Saida Annah ta raka Salma har daki sannan takoma Palo tazauna tana huci, wayarta tadauka
ta kira Hajiya, Hajiya kam duk ta tsorata ganin kira alokacin, tana dauka Annah tahau ta da
Masifar akan lailai saita dawo gidan Gobe, dan kuwa cikin wani sati take so ayi aure tun kafin
yaran Gidan su kasheta da bakin ciki. Hajiya kam bata gane inda zance yado sa ba, saida Annah tayi mata bayanin abunda ya faru,
Salati Hajiya tahau yi, tace bataga ta zama ba dawo wa gida yakamata.
[9/7, 12:38 AM] Xarah Bukar: Zuma Sai Da Wuta
~na~
©ҳaɾaɧ bųkaɾ
NAGARTA WRITERS ASSOCIATION {NWA}
Allahu akbar kulu'nafsi za'ikatu mauti, Allah yaji kanki da rahma Maman besty Yar ficika. May
jannatul Firdausi be ur final destination.
61
Har wayewar garin Allah Annah bata bar jinini ba, ganin babu wanda ya tashi bacci a mutanan
gidan yasa ta tusa Salma agaba akan lailai saita koma gidan su kafin ta janyo mata abun
magana, ita kam dariya ma batun ya bata, had'a kayanta tayi cikin akwati ta fito, har waje bakin
mota Annah ta tisa keyarta gaba tana kumfan baki, Salma kam ko ajikinta tafad'a mota Driver
yaja maida ta gidansu. Ajiyar zuciya Annah ta sauke ta koma ciki tana magagganun ita d'aya
kamar tab'abb'iya..
Salma na isa gida Momy taji dadin ganinta, dan kuwa ta jima da son dawowarta alkunya yasa
kawai batai mata batun dawowa ba dan har Daddy taima zancen yace da ita karta manta Salma
gidan yan'uwanta taje ba wani gurin ba.
Ta b'angaran Mujahid kuwa koda ya sauko kasa around 12 baiji duriyar Salma ba, sharewa yayi
atunaninsa abunda ya faru jiya yahanata fitowa. Around 4 bayan ya dawo Masjid ne ya lura
something is not right ganin yadda Annah kemai mugun kallon tana cika tanai batsewa, baibi
takan taba ya leka dakin Hajiya, wayam yagani babu salma balle alamunta, ransa ne yabaci,
atake ya ciro wayarsa daga aljihu ya kira Salma, dariya tayi dataga call din though she was
expecting ya kira ta tun dazu, tana dauka yace kina ina ? Atakaice yayi maganar.
"Gidan mu" ta fada tanai cigaba da dariya, shikam haushi ma tabasa ya katse call din ya fito
palo gurin Annah, fuska ba annuri yace "Annah miyasa Salma tabar gudan nan ba tare da izini
nabaa ?
Harara ta watsa mai sannan ta d'auke kai tana fadin "Zancen kake so, wai ance da gwauro ya
iyali"
Iya k'uluwa Mujahid yakai baima san mai kalamanta suke nufi ba, yace "bar ganin kin koreta
kamar kinci galaba akanmu, ni yanzu gidan su zan nufa ganin ta, sai inga abunda kika isa yi"
cike da karaji yayi maganar.
Dogon Tsaki Annah taja ta tab'e baki had'e da ware hannuwanta biyu, tace "Abu mai sau'ki,
shan koko da matsami, kuje can ku karata badai agidan nan ba, idan kaga kuma ta dawo toh an
shafa fatiha ne, jarababbun yaran kawai"
K'wafa Mujahid yayi ya fice waje afusace.
Salma tare da Momy a d'aki suna hirar su cike da annushuwa, Salma tace "Momy nikam ina ya
Salim tunda na tafi bai kira niba ??
Tab'e baki Mony tayi tace "these dayx bansan maike damun saba, he is always indoors, dukya
rame ba yadda banyi muje yaga Doctor ba yaki acewar sa kalau yake"
Jikin Salma ne yayi sanyi, sosai taji tausayinsa, ada bata da wani aboki sai Salim tanson shi
sosai, halinsa kadai yasa take maintaining distance.
Wayarta ce tayi karar shigowar text, dubawa tayi tare da murmusa, kallon Momy tayi tace
"sweetheart dina ya iso"
Dundu Momy takai mata tana fadin "marar kunya kawai" dariyar sukayi atare ta mike da azama
taje dakin ta tadau veil tayafa akan doguwar rigarta sannan ta fita haraban gidan inda yake
tsaye bakin motar sa, fuska murtuke.
Da fara'a ta karasa garesa, gaidasa tayi ya kuma tamke fuska ya dauke kai.
Rud'ewa Salma tayi, sam batason ganin one love dinta ahaka, kaman zatayi kuka ta shagwab'e
murya da cewa, "yaya am sorry, wlh Annah ta tisa ni gaba shiyasa banma Sallama ba"
Sai sannan yakalle ta, cike da haushi yace "atleast you could have holla me on phone before
leaving, bakiga yadda hankalina ya tashi da rashin ganin kiba"
Hakuri Salma tahau bashi shikam sai wani cin magani yake, dakyar tasamu ta lallaba shi
haryayi dariya, hirar su mai cike da so da kauna suka hauyi daga bisani yaduba agogon hannu
sa ganin lokaci, duban agogon Salma tayi hade da dariya tace "ya agogon nan yan nan ?
Murmushi yayi ya kalle ta yace "babu inda zaije tunda baki sace shiba"
Dariya ta kumayi tuna haduwar su ta biyu a club data zaremai agogon yabiyo ta ya kwace.
"Wlh i was only looking for your trouble ranar, amma yaya do you still smoke ?
Gyara tsayuwar sa yayi yanai kaimata wani shumin kallo sannan yace "har yanxu kina zuwa
Club ?
Harara takai mai cikin salon wasa, bata bashi amsa ba tace "yaya inason agogon nan, ban taba
ganin irin saba"
Kallan sliver agogon yayi yace "ba normal agogo bane, but i cnt tell you kona miye"
Ashagwabe tace "yaya kabani plz, inason agogon"
Dariya tabashi da yadda tayi maganar, zai iya bata amma yana tsoron karta batar mai dashi.
Cire ogogon yayi ya rike hannuta yace "promise baza kibari asace ba"
Kada kai tayi cike dajin dadi, yace "aro nabaki fa"
Kai ta kuma d'agawa cike dajin dadin, sakala mata yayi a hannu tana shakar kamshin sa dake
fita daga agogon, sosai tajita cikin farin ciki sun kara jimawa agurin daga bisani sukayi sallama
yabar gidan.
Bangaran Salim Salma ta nufa ta iske shi yashe kasan tsakiyar palo, da ganin baya cikin
hayyacin sa, karewa ko ina kallo tayi komai kaca kaca, ga uban emty bottles na barasa,
gabadaya ya gama muzanta. Ranta ne ya baci ta tsugunna gabansa inda yake kwance,
afusace tahau kiran sunan sa, bude idanuwasan da suka sauya launi zuja yayi ya sauke su
akanta, adan zabure ya mike zaune atunanin sa ko imagination dayasaba yine.
Fuska daure tace "Ya Salim miye haka, why are you trying to useless your life ?
Sauri riko hannuta yayi tabi gemai hannun da karfin gaske tana hararar sa, murya raunane yace
"Salma yazanyi da sonki, duk yadda kika ganni da kuma duk abunda nake Sonki ne Sanadi
(littafin Jiddah Aliyu) na rasa ya zanyi da rayuwa ta" kuka ne ya kufce masa hade da sauri
rungumarta, Haushi ne ya turnuketa ta turesa daga jikinta ta mike tsaye tanai mai mugun kallo
tace "ya salim kabar bata lokacin ka akaina, cox i dont love you, tayama xaai na soka jibeka so
useless and irresponsible, the only gentleman i love is your Boss, get that in your dummy brain"
ahasale ta karasa maganar, shikam kuka yaci gaba, tsaki taja tahau gyara ko ina na gurin
sannan ta fita ta barshi cike da tausayin so maso wani dayake mata.
*****
Washe gari ne Hajiya ta dawo gida da yan'uwa birjit na fara shirin buki. Annah kam baki har
kunne zata aurar da jikoki, sunyi magana dasu Daddy an tsayar da rana one week kacal.
Su Junaina kam sai sabon iyayi daya karu an kusa shiga daga ciki, sosai take jin dadin yadda
Jafar yake nuna mata so da kulawa, itama baa barta baya ba dama gashi ta iya shishigi da
ladabi a soyayyan shiyasa sukafi dacewa da juna.
Su Oga Mujahid da Salma baa magana soyayyan sosai suke ba kama hannu yaro, wataran har
Mamaki Hajiya take da irin son da Mujahid yakema Salma dan kuwa bata zata ba..
Daddy ne ya amshe zamewa Salma da Junai Uba game da komai na auren, kafin satin auran
sukaje Dubai yin siyayyan abubuwan amfani masu shegu tsada sannan suka dawo.
Satin Buki.
Gidan su Momy ya cika sosai da jamaa, yan'uwanta ma sunyi kara sunzo saboda son datake
ma Salma, wasu yan'uwan Salma na dangin uwa duk can suka sauka, masu gyaran jiki irin irin
kusan goma Hajiya ta aiko suke gyara Salma anan gidan, Junai ma acan gidansu gyara sosai
ake mata, saidai har yanxu ba wani shiri suke da Salma ba.. Event ma da suka hade kin
Amincewa Junai tayi suyi tare cewa tayi kowa yayi nasa daban a inda yakeso, hakan Sosai
yabawa Hajiya haushi sharewa kawai tayi ta barta ahanka, mazan ma baa barsu baya ba sai
nasu shirin suke.
Three Dayx to Daurin aure, kuma gobe ne zaai event din Arabian night.
Su salma ansha murja dakayan Dilka da turaran kamshi, duk inda ta ratsa shining take da
kamshi, tayi kyau sosai, kayan tsumuwa na mata (Aunty Guarantee) ba wanda baa bata tasha
ba, na cushe cushe ne fir taki amincewa dasu dan bata yadda dasu ba majority ma ovary
cancer suke sanyawa.
Around 8 na dare ta fito wanka sai kyalli skin dinta yake, zama tayi gaban mirror ta murje jikinta
da turaruka masu dama sannan ta sanya night wear riga da wando cotton ta kwanta, agogon
mujahid dake kan side drawer tadau tana shakar kamshinsa sannan ta makala a hannuta.
kaman jira take taji wayarta na ringing, da azama tadau ka ganin wanda ke kira. Daga can bangaran yace "Angel am dieing" cikin wata irin salo mai rikitarwa yayi maganar.
Adan rude ta mike zaune "My love you're killing me, plz talk to me, miyasa meka ?
Lumshe ido yayi "am sick, cronic ciwon kai ke damuna"..
"OmG" ta fada adan kidime, ta mike tsaye.
Tace "yaya kana ina
Murya wahale Yace "ina gida, apart din Baki".
Ajiyar zuciya ta sauke tace "yaya plz stay calm, i cnt sleep idan banzo naga condition dinka ba,
am coming right away" katse wayan tayi da sauri ta suri Hijab dinta tadau mukullin mota ta fita
dakin, mutane sosai tagani palo anata hira, ta kitchen tabi ta fita waje batare da kowa yaganta
ba. Mota ta shiga taja tabar gidan at 360.
Dariya sosai Mujahid yayi bayan sun gama wayan, zaune yake shida wasu cousin dinsa guda
biyu a palon bak'i, duk wayar da yayi da Salma a speaker yasan ya suka ji komai.
Dayan mai suna Khaleel yace "Mjay kaci saa yarinyar nan na bala'in sonka, jifa yadda ta rud'e,
dama nice nasamu Babe haka" dariya sosai yake yana maganar.
Murmushi Mujahid yayi yace "nima ina bala'in sonta, i cnt live without her, she is my everything
but some scores have to be settle, Salma ta mugun wahalar dani ba kadan ba"
Harara Dayan mai Suna Abdul yamai yace "miye amfanin settling scores tunda nan da 3 dayx
she is all yours, koma dai miye ka barta kawai"
Mujahid yace "aiko mi nayi mata bazata ji haushi na ba, she is madly inlove with me"
Dariya Khaleel yace "babaa wai wana irin wahala kake nufi tabaka?
Mikewa Mujahid yayi yace ina zuwa" fita yayi can bakin gate yayi magana da mai gadi sannan
kuma ya dawo palon ya zauna. Labarin tun farkon haduwan su da Salma yafara basu, jifa jifa
kuma yakan kalli wayarsa.
Salma na isowa Gidan wani mugun Horn tahau yi, da sauri mai gadi ya bude mata ta cilla motar
ciki da sauri tayi parking ta fito... Sauri sauri, gudu gudu tayi tafara karasawa part din Baki dake
can nesa da main house, takusa daf da gurin taji ana kyalkyalewa da dariya, tsoro ne yakamata
tafara takawa da sauri, daidai bakin Kofar taji Muryar Mujahid na magana cikin dariya, gabanta
ne ya fadi ta daskare gurin ba tare data iya kwakwaran motsi ba.
Cikin dariya Mujahid yace "kasan most funniest part of the story, bayan munyi plan da abokina
nayi kissing dinta still bata bada kai ba, saida nayi fooling dinta na aika wasu Maza sukamin
Duka atiti sannan fah ta waiwayeni"
Khaleel yace "gaskia kayi fooling dinta dayawa, ni yaushe zan yadda nasha duka abanza"
Mujahid yace "bayan ta fara kulani i had to pretend loving her duk dan na shuka mata rashin
mutunci, kuma nasan itace same Ummi da Hajiya ta isheni saina nemo, niku kuwa na share
naki nunawa Hajiya nasan wata Ummi. The next tin kawai naganta a gidan nan, kasan kuma
miya faru ? Haushi ne yakama Abdul, Khaleel kam dama player ne, kuma dadin labarin yake ji yace "what
next ?
Mujahid yace "Could you imagine, yarinyar nan tasamin attarugu a shower gel dina, nikuma
arashin sani nayi using, ranar ko i felt like strangling her to death"
Dariya sosai Khaleel yakeyi, abu sai kace a film, yace "Mjay gaskia ka wahalu, ya kayi kuma?
K'wafa Mujahid yayi yace "ya kuwa nayi, fooling dinta bashi da wuya, tricking dinta nayi into
biliving ina sonta, ita kuma tayi saurin bada kai as usual .."
Khaleel yace "amma fa Salma ta hadu, koba laifi zaka huta da jikinta.."
Kaaa cigaba da Sauraro Salma tayi, hannu tasa kan kunnuwan ta tana fadin "innalillahi wa
Inna'ilaihi rajun" hawayan Bakin Ciki data jima basu zubo mata ba suka hau ambaliya a fuskar
ta, kuka sosai take tafara ja dabaya tayi tuntube tafadi kasa, ihu ta saki cike da tashin hankali.
Jin ihun Salma yasa Mujahid mikewa akidime ya fito waje, ganinta yayi zaune kasa tana rusa
kukan daya jima yanason Ganin hawayanta. Da sauri ya karasa gareta yana fadin "Habibty
yaushe kika zo ?
Wani sabon kuka tafashe dashi, jin sabon yaudarar dayake shirin yi mata, mikewa tayi tsaye
tana kallon yadda duk ya gigice, rikota yayi cike da kulawa, wani irin feeling yaji ya ratsa jikinsa,
ga kamshi jikinta sai ratsa mai gabobin jikinsa yake gabadaya.
Murya kasa kasa yace "sweetheart mi aka mike, plz stop crying, your tears are breaking my
heart" janyota yayi zai rungumeta tasa hannu da karfi ta turesa baya.
Cikin kuka ta nuna shi da yatsa tace "dont you dare lay your filthy hands on my body, banza
macuci, dan iskA, Allah ya isa tsakani na dakai,