Author : Zarah Bukar Category : Tknovels
yadda ranta ke bace, dan kuwa kiris ya rage tayi
kuka.
Hannu motar taja ta rufe ta kunna tayi gaba, sosai Mujahid yaji dadi, koba komai ya ajiyeta in
her place, next tym she will learn to respect herself, saidai rashin kukan ta yabashi haushi.
Dariya yayi ya koma motar sa yaja gidan su Faiza, taji dadin ganinsa, sun jima suna hira kafin
nan ya gangaro mata wata tambaya.
"Faiza ya student dinki, hop dai yanxu bata miki raini...
"Wa kenan" Faiza ta tambaya, dukda tasan wace yake nufi.
Yace "ko Ummi koya take da suna, yarinyar nan mai harka da area boys"
Tsaki tayi tace "Salma xakace, sam bana kaunar yarinyar nan... "Karashe maganar tayi tanai
duban fuskan shi, saidai bata gano komai ba.
Shuru yayi tace "Mjay don't tell me you're fond of that girl ?
Dariya yayi ya share zance yace "ya bazawarai, nifa ke nake jira kiyi aure sai nayi, kinsan
friends dont abandon friends.
Harara takai mai cikin salon wasa, azuciyar ta taji haushi abunda yace.
Tace "kamin adduaa Allah ya kawo na gari"
"Okay tam".
Wata hira suka kama sun jima tare daga bisani ya koma gida.
****
Washe gari..
8am Salma ke da Lecture, 7.30 ta fito fuska ba annuri, zuciyan ta na radadin abunda ya faru
jiya, Daddy da Momy ta iske zaune a dining, Daddy nasha tea, ciki ciki ta gaida su, daga ganin
fuskar ta bata cikin walwala.
Daddy yace "Salma make damun ki ?
Kaman zatayi kuka tace ba komai, juyawa tayi ta fice daga palon, mikewa Mom tayi da sauri
zata nufeta, Dad yayi saurin dakatar da ita
Yace "karki damu, indai Salma ce she will over come any obstacle, mu bata time"
Zama Mom tayi jikin ta duk amace, tana son Salma duk wani damuwa ta Salma bataso.
***
Mujahid na shiri kunna Motarsa yaga Junai ta fito da saurin ta sanye da Uniform, tuna abunda
ya faru jiya yayi, da sauri ya karasa inda take tahowa.
Murmushi ya sakar mata yace "autar mu ya kike..
Bata rai tayi zata wuce ya kuma jan motar gabanta, "Junai am sorry nasan namaki laifi jiya".
Sai sannan ta kalleshi, turo baki tayi tace naji"
"Zona kaiki skull".
"Banso" ta fada.
"Baki hakura ba kenan, toh bara na fito nayi kneel down n seek for your forgiveness" shirin bude
motar yayi tayi saurin dakatar dashi, "yaya unless kai zakazo kayi picking dinta"
Murmushi yayi yace "i promise"
Itama murmushin tayi sannan ta shiga motar yaja.
***
Salma kam tunanin abunda zata wa Mujahid take dan huce haushi, tana isawo Traffic light ta
tsaya jiran Green light, tagumi tayi tahau saka da warwara, kaman ance juya ta juya left hand
side dinta, Mujahid tagani zaune da wata mai Uniform suna hira shi kuma yanai sakar mata
murmushi. Haushi ne yakamata yadda ta ganshi cikin nishadi meanwhile gata nan kaman ta mutu, saidai
tasan abunda xatayi.
Grean light na nunawa Mujahid yaja yayi gaba, lane dinsa ta koma tafara binsa a baya har
suka isa makaranta junaina, tana ganin Junaina tamai nuni da 12 xai dawo daukan ta sannan
yamata bye yaja yabar gurin.
Dariyan Mugunta Salma tayi, tun bata aiwatar da kudirin taba taji farin ciki ya mamaye ta,
reverse tayi ta koma baya inda taga wani Toy Store, shiga tayi ta siyi Bindigar wasa ta yara
wanda idan ka ganta zaka dauka ta gaske ce, can gefe tayi parking zaman jiran 12 yayi.
12 nayi taga anfara fitowa, wasu anxo daukan su, daga can nesa ta hangi Junaina tsaye da
kawayanta, sundan jima tare sannan suka mata bye suka wuce.
Kunna motar Salma tayi ta karasa daidai Inda Junaina take tayi wining glass, Kallon ta Junaina
tayi tana Murmushi.
Murmushi Salma tayi ta fiddo takarda a Jarkata tace "you are...".
Katse ta Junaina tayi tace "am Naina, nyc meeting you" Hannu Junaina ta mika mata zuciya
daya, harga Allah taji Salma ta kwanta mata arai.
"Shigo mu tafi, Officer mujahid ya aikoni kaiki office dinsa daga nan ku tafi gida..". Acewar
Salma batare data mika mata hannu ba.
Junaina baki har kunne ta zagaya ta shiga gaba ta zauna Salma taja motar, adaidai lokaci shi
kuma Mujahid yayo kwanar Makarantar.
Sun glasses dinta Salma tadau ta saka a fuska hade da kara daure fuska tamau, Junai kam
banda murmushi ba abunda take.
Wayar Salma ce tayi ringing, daukar tayi tasa a kunne suka fara magana da wani, can kuma
tace "Tk hop dai kazo da igiyoyin ".
Daga can yace eh.
Tace na kusa karasowa, katse wayan tayi.
Junaina taso tagano wani abu saidai bata fahimci komai ba saida taga sai tafiya suke ba
alamun tsayawa, gabanta ne ya fadi, nan take ta gano sumtin is not right.
"Sister kince office din Yaya zaki kaini" junai ta fadi.
Banxa da ita Salma tayi, kara tambaya Junai tayi, afusace Salma ta fiddo Bindigar, cikin tsawa
tace "zakimin shuru ko saina harbeki...
Jiki na rawa Junai tayi shuru, Suna zuwa Dutsen Alhaji suka doshi wani daji, Salma ta sayar da
motar hade da nuna mata bindigar.
Jiki na rawa Junai ta sauka, ganin maza biyu tayi gabanta rike da igiyoyi, "ku daure ta " Salma
ta fada.
Ihu Junaina tayi cike da tsoro tace "baiwar Allah mina yi miki, wace ce ke?
Dariya Salma tayi tace "Mujahid bai taba baki labari na ba.
Cikin muryan kuka junaina tace "karya kikema yayana nasan baisan ki ba, kuma baya harka da
Karuwai, kidnappers irin ku....
Wani wawan Mari Salma takai mata, nan Take kan Junaina ya juye, star, moon harma da
rainbows ta fara gani saidai ta kasa tantance wanne ne wanne......
Tofah......
Muje zuwa.......
Labari don start ooooo
[9/7, 12:37 AM] Xarah Bukar: Zuma Sai Da Wuta
~na~
©ҳaɾaɧ bųkaɾ
®NWA
27 - 30
Zaman minti biyar Mujahid yayi ba alamun fitowar ta. Wani guard dake guri ya tambaya yacemai
ta jima da tafiyA. Bai damu ba yaja motarsa yayi gaba, atunaninsa tabi motan friends dinta,
office ya wuce abunshi.
Dakyar junaina ta dawo hayyacinta bayan wasu tsuntsaye data ga suna lilo bisa kanta tsabar
rad'ad'in marin, nan take tsoron ta yadawo sabo sai sannan ta ankara da tuni sun daure ta da
igiyar ajiki wata bishiyar kwakwa dake gurin.
"Welcom back" Salma ta fad'a daga inda take hakinci kan dutse dake gurin, maza biyun na
tsaye bayanta rike da hangbag dinta, fuskar ta daure tamau babu annuri.
Kuka sosai Junaina ta fashe dashi, farar fuskar tuni ya sauya launi zuwa ja, ga wata uwar
yunwa dake addabarta ko breakfast batai ba tafita skull..
Gyara zama Salam tayi tace "gwara ma kibar kuka, cox i wont spare you, ina da Unfinished
business da yayan ki"
Cikin shesheka Junaina tace,
"koma miye kuyi settling tsakanin ku, dan Allah ki barni na tafi gida, ina da exam gobe"
"Okay, lemme c if yayanki zai dau call dina" jakar dake hannu guy ta amsa ta ciro wayarta
sannan tahau dailing no din Mujahid.
Yana ganin Call din Salma tsaki yayi, bai dauka ba yacigaba da aikin gabansa, saida ta kira sau
kusan hudu ba respond sannan ta kalli Junaina, dariya tayi tace "it seems today isn't your lucky
day"
Adan tsoro junai ta ware ido, Salma ta cigaba "nan da 3 hours idan baiyi picking call dinaa ba i
won't hesitate blowing your brains out" karashe maganar tayi tanai mata nuni da bindigar.
Junai kam ta gama firgita, kuka sosai take, tashi Salma tayi ta koma mota ta zauna zuciyarta na
radadi, tana ji ajikinta sumtin is not right saidai bata san miye ba, ayanxu burin ta kawai ta rama
abunda Mujahid yayi mata, kwantar da Sit tayi ta kwanta hade da sanya earpiece kunne tahau
sauraran wakar freedom ta Akon.
****
Shuru har karfe hud'u Junaina bata dawo ba, shiga dakin ta Hajiya tayi taga wayam.
"Ikon Allah, har yanxu bata dawo ba" ta fada, nambar junai ta kira taji ta ajiye kan dressing
mirror tanai ringing. Daya daga cikin mai aikknsu kande ta kwalawa kira, tana zuwa tace "kikace
da mujahid junaina ta bar gida da safe"
"Eh" kande tace.
"shuru dai bata dawo ba, bari na kira mujahid"
Kira nambasa tayi, shikam alokacin ma ya fito masallaci sallah la'asar, office xai koma yaga call
din hajiya, dauka yayi tace
"kuna tare da Junaina ?
Cikin rashin fahimta yace
"Yaushe?
Hajiya tace "bata dawo gida ba, tun bayan daka fita da ita"
Bata rai yayi. "nifah dropping dinta kawai nayi a skull...
"Toh kaje ka dauko ta" kaste call din tayi batare data jiran cewar saba.
Guntun tsaki yaja, aransha shi yana fadin yaran biyun nan fitinar su bata karewa, i dont have
time for their nonsense" wucewa office yayi.
Ta bangaran Salma kuwa bata kuma trying no din Mujahid ba, haka tayi ta zamanta a mota
daga bisani ne ta fito gurin Junai, ganin yadda ta galabaita yasa ta tura Tk cikin gari siyo mata
abinci take away da drink, bayan ya dawo ba yadda batayi ta bawa Junaina abincin, fir taki
karba taci banda tsine mata data dunga yi tana kuka. Yammace ta doso, hakalin Salma yafara tashi, tunanin kar dare yayi masu gurin, uwa uban
idan mujahid bai dau call dinta ba batasan ya zatayi da Junaina ba, tsoro ne yakamata kar
yarinyar mutane ta mutu a hannu ta...wayarta ta kalla ta hau turama Mujahid Text msg.
Kaman bazai duba ba sai kuma yafasa ya bude sakon "pick d damm call before i murder
your stupid crying sister".
Gabansa ne ya fadi, hankali tashe ya mike tsaye cikin rawar jiki yafara neman nambar ta, saida
tayi ringing sau biyar sannan ta dauka..
Cikin fusata yace "dont tell me dagaske kike
Tsaki taja.
"do you take me as a joke" kusa da Junai ta karasa hade da riko gashin kanta, ihu junai tayi cike
da azaban rikon da tai mata, wayar Salma ta dasa mata akunne, muryar Mujahid taji akid'ime
yana cewa "Auta ki kwantar da hankalin yanxu zanzo..."..
Maida wayar salma tayi kunnan ta sanna tace "kaji ai da kunnan ka".
Ran sa yagama baci, cikin daga murya yace "What did you want, say your price ?
Harara tayi kaman tana ganinshi, tace
"If you keep yelling at me i wont negotiate, so better calm yourself muyi magana like gentle
people".
Kaman ya shaketa yakeji, kwantar da murya yayi.
"Duk abunda kikeso xan maki kuma zan baki ko miye, but plz leave my sister out of this"
Shuru tayi tana tunanin mai takeso gareshi, can ta tuna da abunda ya faru a Qrand Square,
k'ala mata satan 50k da yayi saita tatikeshi hamsin sau goma.
Murmushi tayi tace "500k nakeso,
Iya k'uluwa yakai yace "aini ba ubanki bane dazan dauki 500k na baki, su kananan kwari da
kike bi miye amfanin su"
Dariya rainin wayo tayi sannan ta bata rai tace "idan banga alert nan da 10 minti ba, forget you i
have a sister" dif ta kashe call din.
Hauka ne kadai yarage Mujahid baiba, kaman wani zaki ya hau huci a office din, yasan Salma is
a bitch saidai bai taba tsammanin she can stoop so low tayi kidnapping Junaina ba much less
tayi demanding makudan kudi haka ba, tsoronsa daya karta gano Gidansu tunda har ta iya sato
Junaina, Allah kadai yasan a ina ta gano shi as yayan Junai. Karar shigowan text msg na account no dinta ne ya katsemai tunani, da sauri yadau ipad dinsa
ya shiga yi mata transfer din kudi, amma a zuciyan shi yayi alwashi karbo kudin sa dan kuwa
bazai bari taci bulus ba.
Salma naji alert tasa Su Tk suka kunce Junai, dakyar ta iya takawa suka karasa mota ta shiga
abun tausayi, kallon su Tk Salma tayi sannan ta zaro 20k ta basu tace "aikkn nan bashi da
amfani ku kama sanaa koda wanki da guga ne".
Sukam godiya sukai sosai cike da murna, dama rashin nasha da ci ke sanya su yin wani abun.
Shiga motar Salma tayi taja, Junai na zaune tana sauke numfashi wahala, hawaye take
zubarwa, kanta dauke gefe tanai kallon waje.
Kiran Mujahid tayi, da azama ya dauka tace "ka fito tsakiyar cikin gari" katse call din tayi,
yakuma kira bata dauka ba, saida ta iso National stadium sannan tayi parking, ta turamai text
din inda take, kallon Junai tayi tace "kina iya sauka"
Kaman jira take ta bude motar, zata sauka taji Salma tace "am sorry idan kinji haushi na"..
Da karfi Junai ta rufe kofar batare data tsaya sauraran taba, saidai kalmar idan kinji haushi da
Salma tace ya mugun kara bata mata rai, "wana kare xaa ma cin kashi haka yak'i jin haushi,
itama dai tasan abunda tayi can never be forgotten or forgive" azuci junai tayi maganar, can
gefe ta zauna akasa jiran Mujahid.
Cikin rashin damuwa Salma taja motarta tayi gaba.
Baafi minti 20 ba Mujahid ya iso gurin hankali tashe, da sauri ya sauka ya riko ta suka shiga
motan yaja, ba abunda bai tambayi Junai ba fir taki magana har suka iso gida, Nan suka iske
Hajiya da Jaafar shima alokacin ya dawo aiki yaga hankalin hajiya tashe, fitowa neman junai
zasuyi sukaga motar Mujahid ya shigo.. Kafin ya tsayar da motar Junaina ta bude kofar ta fito, da gudu ta karasa gurun jafar hade da
fadawa cikin sa tanai kuka mai tsuma zuciya.
Tambayan miyasa meta jaafar yahau yi, bata iya bashi amsa ba sai kuka, yajata suka shiga ciki.
Mugun kallom Hajiya tama Mujahid dake tsaye bayan ya fito motar, kaman marar gaskia haka
ya koma.
Fuskar hajiya ba annuri tace "ina ka kaita, mai kayi mata..".
Shuru yayi baice komai ba, tsoron sa daya kar Junaina tama hajiya Description din Salma,
yasan Hajiya dason bin diddigi.
Wayar hannuta Hajiya ta danna hade da kiran Aunty Bilkisu, fitowan ta kenan daga NNPC clinic
inda take aiki. Hajiya tace da ita ta biyo ta gida Junai ba lapia.
Hararan Mujahid tayi sannan ta kama hanyar komawa ciki.
Zaunar da ita Jafar yayi kan gadonta yanai kara tambayan ta, jikinta gaba daya rawa yake, cikin
muryan tace "wata yar Mafia ce ta saceni, kuma da alamun tana da wani Dirty relationship da
yaya kuma fah her face looks familair i just dont know ina na santa"
Riko hannuta yayi yana lallashinta yace "ko Faizan Umma ce.
Kada kai tayi "Aunty faiza is too naive, ba ita bace wannan fah so pretty gata black beauty
saidai zuciyan ta ba imani, i was so scared, kiris yarage bata harbe ni da bindiga ba" duk cikin
Kuka take maganar, fuskar ta gabadaya ta kumbure.
Hankali jaafar ne yatashi, yau kam sai yayi confronting yayan shi, Hajiya ce ta shigo, ba
tambayar da batai ma Junaina ba, taki gaya mata komai, sai cewa tayi b'ata tayi sunje gidan
kawarta.
Aunty Bilki na karaso wa ta duba Junai hade da bata pain relief, sai sannan hankalin Hajiya ya
kwanta atunanin ta ko wani abu mugun abu Mujahid, dakyar Junai ta iya tashi tayi wanka tayi
alwala sannan ta fito tahau jera salloli.
Rai bace Jaafar ya haura sama, dakin Mujahid ya fada ba tare da Sallama ba, tsakiya dakin
ya iske shi zaune akasa kan center carpet, hannusa rike da Sigari yana busa, daga ninsa cikin
tsananin baccin rai yake.
Yana ganin Jaafar ya dauke kai,
Kansa jaafar ya karaso ya tsaye yace "wace yarinya ce keda guts din kidnapping junaina
sannan kai kuma as a policeman you aint doing anything about it ?
Banza dashi Mujahid yayi, dan kuwa ayadda ranshi ke zafi sai iya haushi da duka.
Kafadar sa Jaafar ya riko yace " stand like a man and talk to me, ko nima tsoro na kakeji kaman
yadda tsoron yar mafia ya hanaka arresting dinta..".
Azabure Mujahid ya mike yana huci, iya karfin sa yasa ya ture Jaafar wanda saida ya bugu da
D mirror dake gurin, glass din ya face, da gudu Hajiya da Aunty b suka hauro sama.
Mugun naushi Mujahid ya kaimai a fuska, nan suka cakwade suka fara dambe, akideme su
Hajiya suka fado dakin, Salati ta saki tahau kokarin rabasu, jaafar ta janye gefe wanda tuni
bakinsa yafara zub da jini, fadi yake "matsoracin kawai, ai fitowa xakayi ka fadi abunda ya faru
bawai kayi shuru" Rufe mai baki Hajiya tayi tana jaafar yi shuru ya isa, mujahid kuwa huci kadai yake, ganin yadda
attention din Hajiya da aunty b na gurin Jaafar yasa shi fara harhada kayan shi cikin akwati,
atsorace Aunty B ta kalle shi Mujahid miye haka, ina zaka.
Baibi takan taba ya hade kayansa a kwati yaja ya raba gefen su ya wuce, Janyo Aunty B hajiya
tayi tace "kyaleshi ya gama fushi, muje ki taimaka wa Jaafar" ba musu Aunty B ta riko jaafar
suka sauka kasa, kallon dakin Hajiya tayi taga sigari dake baje agun, kai ta girgiza tace "Allah
ya shirya min kai Mujahid"
Afusace Mujahid ya fada mota yaja, bai zarce ko ina ba sai Louis House nan inda gidajan
mayan yan sanda Nigeria suke, babban Flat dinsa ya nufa, security dake gurin ya bude mai
gate din gidan, hadaddan gida ne mai dauke da 3bd, 2palo ds kitch sai haraban gida da garden
ta baya, ko dauka akkwati bai ba ya shiga gidan, ciki ma ya hadu ba karya.. Dirshan yayi kan kujera ya dafe kai kaman yayi kuka, shi kadai yasan abunda ke yawan mai
azuciya.
Da nishadi Salma ta karasa gida, dakinta ta fada ta kwanta abunta kasancewar hutun sallah
take, so take