Zuma Sai Da Wuta Complete Hausa Novels Pdf by Zahra bukar .pdf

Author :  Zarah Bukar Category :  Tknovels

Chapter   3 / 20

6K to 9K   out of 57.2K words

dinta. Math textbook dinta ta dauka da biro sannan ta fita zuwa
palon, kusa da Mom ta zauna tana dubu textbook din sannan ta kalli Daddy fuska shagwabe
tace "Daddy nayi misplacing calculator dina gashi kuma ina da assignment dazanyi" Murmushi Daddy yayi jin diyar shi taci serious da karatu, yace
"ki duba dakina cikin drawer bazaa rasa ba"
Mikewa tayi da azama, cikin sauri tace "yauwa Daddy, nagode, Mom gud nyt" ta karasa

maganar hade da sauri fad'awa dakin Daddy.
Dariya Mom tayi suka cigaba da hirar su.

Kaman munafuka tadau calculator din ta fito, sad'af ta wuce hanyar kitchen ba tare da iyayan
sun lura ba, cabinet ta bude ta ajiye textbook da cal din da hijab din jikinta sannan ta bude k'ofar
ahankali ta fice waje bayan ta rufe da mukulli.

Salim dake tsaye yana kallon tahowar ta susucewa yayi, gabadaya ta rikitamai tunani wani abu
yaji yana tsikaran shi da azalzalan zuciyan shi.
Bai ankara ba yaji ta gabansa yana shakar kamshi dake tashi jikinta.
Harara takai mai tace "wannan kallon fah, kasan dai i hate it, ka kama kanka"
Sose keya yayi baice komai ba ya bude mata motar ta shiga sannan shima yaja.

Officers Club...

Sun iso yayi parking, tura kofar Salma tayi ta jita gam...
Bata rai tayi ta dubeshi
"Miye haka".
Kallon ta yayi, gabadaya idanunsa sun sauya launi, hannu yasa ya fizgo ta jikinsa sannan yace
"ki bani chance Salma, ina mutuwar sonki"
Kallonsa tayi cikin ido ba tare da tayi yunkurin dagowa daga jikinsa ba saima murmushi ta sakar
mai hade da kai fuskan ta daidai fuskar shi suna jin numfashin junan su, kallon ta yake yanai
tunanin kota amsa mar soyayyar ganin yadda ta sakar mai jiki, da kuma bakin junan su dake
daf da hadewa, kallon lips din yayi, yana gaf da daura nasa yaji ta bugu uban tsaki hade dakai
hannuta bisa lock tayi unlocking motar, janye jikinta tayi ta bude kofar ta fito ta zagaya bangaran
sa ta window tace "kasan dai halin Daddy, karma ka fara" wuce wa tayi ba tare data jira cewar
saba.
Numfashi ya sauke mai dauke da tari wahala da shaawa data motsomai, kallon joystick dinsa
yayi ya ganta tsaye k'ekam, saidai ba yadda ya iya mafitar sa daya yasa hannu karkashin sit
yadau kwalba mai dauke da barasa (giya) ya fara tuttulawa bakinsa.

Cikin takun isa da takama ta shiga gurin mai dauke da disco light, hadaddan gurine na
watayawa, kowa da abinda ya shafe shi, ba ruwan wani da wani, wasu mazan na gefe suna
rawa da yammata wasu kuma zaune suke gurin wine bar, wasu kuma makale da yammata su
suna shan minti, wasu kuwa chess game sukeyi. Fara taku tayi gurin Wine bar taji wani a bayanta,
"Yammata..
Juyawa tayi
Yace "kin hadu fah, da irinku yadace aje Dubai hutawa.
Yak'e tayi hade da fari da Ido, aranta tace da uwarka zakaje Dubai hutawa badai dani ba, shege
mai kan kwakwa.
Afili tace
"Dagaske" cikin nuna farin ciki, wayarsa ce tayi ringing yadauka hade da jan hannuta suka

karasa gurin hade da zama kan long backless chairs dake gurin...

Daga can Gefe yake zaune, yana kallon abunda ke gudana agurin, agogon hannusa ya duba
yaga goma ta cika, guntun tsaki yaja hade da gyara zama, ya dubi bartender dake guri..
"Bani sigari guda daya".
"Yes sir" bar tender ya fadi hade da mai lightening sannan ya mika mar.
"Sir do you need wine or beer ?
Kallon banxa da Mujahid ya wulla mai yasashi tsuke baki.

Cikin kwarewa ya fara zugarta juyawan da zaiyi ya hangota tanai kokari saka hannu cikin aljihun
wanda suke zaune tare, ware ido yayi yana tuna abunda fa'iza tace mai akan yarinyar
barauniya ce.
Shikam ya shagala da waya, Salma ta ciro wallet dinsa dake ajiye, budewa tayi taciro dari biyar
biu dake wallet din.

Mugun tsananta Mujahid yaji hade da saurin dauke kai gareta.
Tsaki taja tana fadin "matsiyaci ko kudin kirki baya shi" maida kudin tayi cikin wallet din sanan ta
maida mai abarsa ta mike tsaye, saurin riko hannuta yayi yanai mata nuni da karta tafi, harara
takaima sannan ta fizge hannun tayi gaba.

Cike tsananin bacin rai Mujahid ya gama yiwa sigarin zukan Allah tsine uwar hegu, sannan ya
mika hannu gurin bartender yana fadin karomin daya"
Mikomai bartender yayi, hannusa yasa zai amsa yaji hannu wata bisa nashi tanai shirin amsan
sigarin saidai kafin yakai ga amsa ta rigashi amshewa.
Saurin Duban ta yayi dan ganin wace yar iskan ce da karfin halin shiga tsabgarsa.
"Kallamu ka gama kallo..." Ta fada cikin salo rainin wayo, kallon ta yayi saidai mamakin ganin
tasa sigarin abakinta yasa shi sank'amewa gurin...
Dariya tayi ta cire sigari daga bakin ta
tace "i never knew the decent and useful policemen smoke, much less a indoors inda babu
wanda zai gansu"
Shikam ya gama kulewa da ita, tashi yayi ya canza guri dan bazai iya tanka taba yadda yake
mugun jin tsananta da haushinta.
Matsawa tayi inda ya canxa tanai kuma darawa, tace "karka damu your secret is save with me,
am sure irinku ke claming goods guys a gida"
Tsaki yaja aranshi yace "shameless bitch"
Karaf a kunnan ta baisan ma ya fada fili ba.
Ranta yadan sosu, sai yanxu ta gane kallon dayake mata, murmushin dole tayi tabar gurin. Fita
tayi ta wurgar da sigarin sannan tahau goge bakinta, abunda bata tama yiba asalima taimakon
shi tajeyi, saidai inya san wata bai san wata ba, hannuta dake dunkele ta bude kallon agogonsa
data zare ba tare da sanin saba, murmushi tayi ta cusa a bra dinta sannan tahau nema Salim
su koma gida. Can lungu daga baya taganshi da azama ta karasa gareshi ganin baya cikin
hayyacin shi banda barasa dayake ta kokarin sha, idon ji jajir.
"Na shiga uku, yaya miye haka" ta fada cikin tsoro, rikoshi tayi da niyya dagoshi suka fadi kasa

tare ayayinda yake ta suburbuda surututai game da yadda yake sonta.
Tsaki taja, duk ya shafa mata giya ajiki, barin gurin tayi neman temako.

Mikewa tsaye yayi ya kai ido kan hannusa dan duba tym saidai wayam yagani ba agogo, k'asan
gurin yahau dubawa saidai wayan, mamaki yayi dan daxu ma ya duba agogon,
"Kodai.. Ya fadi aransa, ba tantama itace amma how cms, can ya tuna daxu hannusa da nata
sun hade.
"Yarinyan nan wasa take dani" ya fada, fitowa yayi waje, kicibis sukayi xata shiga yayi saurin
finciko ta hade da manne ta jikin bango, hannusa daya shake bisa wuyanta.
Zare ido tayi tanai kallon yadda ya koma mata kamar zagi, murya sheke tace "sake min wuya...
Kara shaketa yayi, ya matse ta tsam har suna shakan numfashin juna, cikin zare ido "dan
ubanki, idan kina karuwancin ki, sata da rashin kunyar ki, ki tsayar can gurin k'ananan k'wari da
kika saba yi suna kyale ki, dont you dare ki kusanto gareni, am not one of those useless men
da kike toying around dasu, Understand? Harara takai mai ta kuma cewa "kasakeni ?
Sakinta yayi, yana kara kallon shegen kayan jikinta, sannan yace "ina agogona ?
"Ka bani ajiye ne"
Kara daure fuska yayi
"Tunda kinyi shaye shayan da kika saba ai dole kice haka" kara matseta
Yayi, jikinsu na gogan juna ya kuma tambayanta.
Wani irin yanayi taji da tunda taxo duniya bata taba jinsa ba, d'an matsar da jikinta daga nashi
tayi ya kara matseta, daurewa tayi ta kallesa cikin dakewa gudin karya gano komai tace
"bansani ba" hade da daure fuska, jikinta yahau dubawa baiga komai ba, can idanuwasa sukayi
caraf akan boobs dinta, kallon su yahau yi, xaikai hannu tayi sauri sa hannunta ta tokare shi,
bige hannu yayi yanai mata mugun kallo yace "Worthless prostitute kin dauka dason raina jikina
ke goguwa da naki, banxa marar tabiyya" bai jira cewarta ba ya tumbula hannu cikin yar top din
jikinta yafara laluban agogon shi, sai gashi ya dauko.
"Banxa barauniya" ya fada hade da tureta gefe.
Ranta ya gama bacci, saidai bazata bari yaci galaba akan taba, dariya tayi tace "ai ban cika
barauniya ba tunda baka da guts din arresting dina, dan iska kawai"
Murmushin da shika d'ai yasan manufarshi yayi yace,
"We will see about that, useless girl, bani da lokacin ki" tafiyarsa yayi yabarta nan tsaye.

"Salma karki ma banxan nan kuka, you're strong" ta fada aranta, jiki sabule ta juya ciki takira
maza biyu sukasa Salim a mota taja su sukayi gida zuciyar ta dauke da tunani iri irin. Tana isa
gida dakyar tasamu ta rike Salim zuwa part dinsa danta lura sam baya cikin hankalinshi sannan
tabi ta kitchen ta shiga part dinsu cikin sand'a ta gudun cikin dakinta.
Hankali kwace yasa mukulli ya bude palon gidan ya shiga, jin shuru yasa shi sauke ajiyar zuciya
tare da kokarin haurawa sama.
"Mujahid.... "
Yaji kiran sunan sa tamkar saukar aradu, gabansa ne ya fadi ya juyo, Hajiya yagani sanye fuska
babu annuri.

"Daga ina kake, wato ni mahaifiyar kake wasan buya da ita, ko kuwa dai ni saar kace ??
Cikin fusata ta jeromai tambayan tare da karasa wa gabansa suna facing juna.
D'aure fuska yayi yace "aiyuka sukamin yawa"
"Aiyukan banxa da haryau ka kasayin simple aiki dana saka"..
Kallan mamaki yay mata, "wai simple aiki, nemo mutum daya bata for 7 years ne simple, kuma
ma just 3 month back aka san she is missing"
Afili yace "hajiya sorry to say, ya kamata ki manta da so called yarinyan nan, cox nayi iya
kokarina ban ganta ba.."
Wani mugun mari Hajiya ta watsa mai kafin ya ida magana, cikin huci tace "diyar kanwar tawace
so called, Mujahid ni kake gayawa maganan nan, yarinya da uwarta taci kashinka da fitsari kake
kira da so called, atleast idan baka nemo ta dan niba ko adan yadda uwarta ta raineka ai ka
nemo ta" Idon shi sosai ya canxa launi, yace "shikenan Hajiya zan ajiye aikin, sai anemi wanda xai
nemota amma bani ba, tunda duk kokarin da nake baa gani, narasa miyasa bakya kaunata
acikin gidan nan, kowa zaiyi abunda yake so amma banda ni kuma tunba yauba kike treating
dina haka" kaman xaiyi kuka yayi maganar, wuce warsa yayi ba tare daya jira cewar taba. Jikin hajiya sosai yayi sanyi, tasan Majahid da taurin kai, tunda ya furta bazai nemo taba toh
kuwa bazai ba, tsoro ne ya kamata kar ya ajiye aikin.
Zancen Abban su Mujahid ta tuna.
"Salamatu ki rage daukan zafi akan Mujahid, shi yaro idan yayi laifi baa mai duka ko zagi dan
kuwa zai iya zama tsegararre, hakan da kikeyi yasa yazama mai mugun taurin kai acikin
yan'uwan sa" abunda mijinta ke yawan fada mata kenan aduk randa Mujahid yayi mata laifi,
Ajiyar zuciya ta sauke tana kara tuno wasu abubuwan da Abban yaranta ya fadi mata kafin
rasuwar sa.

Cikin kunci ya karasa dakinsa, ya jima yana saka da warwaran neman mafita dan kuwa bazai
yadda kudurin Hajiya ya tabbata akan shi na auramai ummi ba, ga kuma wata can Salma tanai
daura mai zafi, tunowa yayi sanda ya matseta jikin sa dawani yanayi daya shiga, saidai abun
daya lura ita ko ajikinta da alamun shi kadai ya shiga yanayin, tsaki yaja yace "ta saba da maza
no wonder she wont feel anything...
Dogon Ajiyar Zuciya ya sauke, aranshi sunan Ummi Salma ke yawo a kwakwalwan kanshi.



***
Bayan kwana biu...
Mujahid bai kuma fita office ba, kullum yana makale a daki, ko kiran shi akai a office saidai ya
dauka yace baya da lapia, hankali Hajiya yayi matuka tashi sosai, saida taje dakanta ta
lallabashi bayan tace mai ta hakura da neman Ummi harsai randa Allah ya bayyanata sannan
ya saki ranshi. Ta bangaran Salim ma kusan hakane, mugun Haushi salma yakeji saidai sonta na nan daram
aranshi.

Kasancewar yau suke da lectures masu yawa, tun 10 Salma ta shiga skull. Karfe hudu bayan
an fito sallah, sukaje faculty ita da abokanta Shehu da Habib submitting wani assignment da
aka basu kwanaki baya kowa yayi submitting banda ita.
Zama sukayi kan dakali suna hira da musun Ball, dan kuwa Salma akwai son Ball, Suna cikin yi
Malama Faiza taxo da motar ta kirar Civic tayi parking gurin ta fito rike da takardu hannuta,
dawowar ta kenan daga lecture data dauki yan level 2.
Dariya Salma tayi ta kalli Habibu tace ka kalli wani film the sugar Mummy.
Shikam Habib ya dauka da gaske take, yace "miya faru, halan film din ya hadu...
"Ina fa ya hadu, wata tsohuwar matace ta auri Yaro koma ince sa'an ta, kaga couple din, ko
dacewa basuyi ba, i dunno y old hags dinnan basa respecting kansu su nemi daidai dasu".
Dariya Habib da shehu suka kwashe dashi, tsaf Faiza ta gane da ita Salma take, dakewa tayi ta
tsaya duban takardun hannunta duk dan taji karshe cin fuska da Salma ke mata.
Habib yace "indai akwai love ai shikenan"
Tsaki salma taja, "love my foot, kaga kamin submitting din nizan shiga Auditorium nasha Ac,
kasan ban saba da zafi ba"
Shehu yace "Salma akwai fa Math 101 yanxu, kodayake Mutumin bai shigowa da wuri"
Yatsine fuska tayi tace "nikam sai 5.30 xan shigo hall, nasan Shirgegen gardin nan ba zuwa xai
ba" juyawa tayi ta kara gaba.
Sai sannan su habib suka lura da Faiza dake kallon su, cikin rawar jiki suka gaidata hade barin
gurin.
Ran Faiza ya gama baci, tana shiga office dinta tahau tunanin yadda zataci uban Salma.
Salam dai akwai kwakwala balle tabata F a course dinta, tunanin take can dabara ta fado mata,
timetable tadau ta duban sunan wanda ke masu Math 102, Malam Dauda ne kuma suna
gaisawa, mikewa tayi ta iske shi office zaune baya da shirin fita lectures, rokosan tayi akan ya
bata aran space din, ba masu yabata dan kuwa bashi da niyya zuwa. Office ta koma da azama tadau Test Question papers daya kamata ta masu test next week ta
fita dashi.
Securities shida ta kira suka rakata Hall din, dalibai kam tsorata sukai ganin test zaai tuni wasu
suka tsure, shehu kam kokarin kiran Salma yahau bata dauka ba, gashi kuma itace mai kokarin,
nata suke kwashe idan zaai test.

Da sauri Faiza tahau raba papers sannan kowa ya fara, hankalinta kwance Salma bata hall din.
Sai 5.30 Salma ta fito daga Auditorium, miss call din shehu tagani, bata damu ba ta karasa
gaban hall, jin shuru gabanta ya fadi, tana shiga taga kowa yayi wiri wiri da ido, kafin ta ankara
taji Faiza tace "Hey Get out"
Tsaye Salma tayi, tsoro yakamata ana test, Daddy kadai take tunawa zaici ubanta idan yaji
labarin batai test ba.
"Kumin waje da ita" Faiza ta fadi ma securities din.
Dakewa Salma tayi hade da watsa mata harara sanan ta fita bakin Hall ta tsaya kaman xatayi
kuka.
"Zakisan dawa kike" Faiza ta fadi a aranta hade da dailling numban Mjay, yana gida zaune
gaban laptop yana dannawa saidai mintuna kadan yakan tuna haduwarsa da Salma.
Daukan wayan yayi, ta fito waje gaban Salma cikoin yauki da kwarkwasa tace

"Mjay ya jikin ka
"Am alright, ya skull ko kin dawo gida ?
"Ina skull dai, hope dai kasha magani... Ta fadi murya a shagwabe
Salma kam kallonta take aranta tana fadi "zaki gane kuran kine"
"Faiza miya faru .. Mujahid ya tambayeta cikin rashin fahimtar yadda cikin sakon daya ta canza
salon maganarta a shagwab'e.
"Ba komai" tace
Katse wayan yayi, kunya ta kamata,
Mugun kallo tama salma sannan tace "okay, i love you tooo, bye" cike rangwada ta koma ajin.
Salma kaman ta hadiyi yawu ta mutu, tunowa tayi da worthless prostitute da Mujahid ya kirata
dashi, shine ba kunya yake cewa tsohuwar nan i love you.
Haushi ne ya kuma kamata, afusace tabar gurin ta shiga motar ta taja.. Gurin wasu kawayanta
area boys ta nufa, sun jima suna magana daga bisani tabar wajan zuxiyar ta fari tas.
[9/7, 12:37 AM] Xarah Bukar: *Zuma Sai Da Wuta*

~na~
©ҳaɾaɧ bųkar



21__23


Ana gama Test Faiza ta tattare script din gurin daya, zuciyarta fayau dauke da farin ciki, mota ta
shiga ta ajiye su gefe sanna taja, ganin hadarin dake garin kuma magrib ta kusanto ya sanyata
wucewa gida ba tare data koma office ba.

Wani Mugun Dariya Salma ta face dashi ayayinta take kokari kunna motar ta dake parke gefen
titi, kunnawa tayi taja ta at 360 tanai bin motar Faiza abaya, can kuma tafara slowing down kafin
daga bisani ta tsaya da motar tana dariya.

Parking Faiza tayi ta fito tanai kallon samari hudu rike da Adda dasuma kallon ta suke fuske
babu annuri, da ganin su yan tasha ne.
"Lafiya ?
Ta fada cikin karfin hali nuna rashin tsoho.
Basu tanka taba saima dayan su dayace bude motar duk abunda kuka gani ku kwasa, kaman
jira suke suka bude kofar test script din suka dauka hade da handbag dinta dake ciki, budewa
sukai babu komai sai gayyar pen da kayan shafa.
Hankalinta ne yatashi tace "dan Allah kuyi hakuri, banda ko sisi takardun nan kuma ba nawa
bane".
Dariya sukayi.
"ba matsala, wanan takardar ai kudi ci, muna bawa mai kosai zata siyosu naira hamsi"
Kaman tayi kuka take kallon su, test din da taci buri shine zasu saida hamsin, bata gama

tsorata ba taga sun soka kusa a tire motar ta, dariya sosai suka kwashe dashi sannan suka hau
mashi dinsu suka bar gurin.

Salma kam baki har kunne dan dariya, kallon Faiza take yadda gaba daya ta susuce, next plan
dinta tayi shirin yi, tayar da motan zatayi ta lura faiza na waya bayan ta gaba kuma ta shiga

3 / 20