Zuma Sai Da Wuta Complete Hausa Novels Pdf by Zahra bukar .pdf

Author :  Zarah Bukar Category :  Tknovels

Chapter   13 / 20

36K to 39K   out of 57.2K words

sai sannan ta tsaya karewa ko ina na palon
kallo kasancewar babu kowa..
Palon ya hadu, idanuwan ta suka sauka kan Katunan frames mai step guda biyar manne jikin
bangon palan, wata farar kyakyawan Tsoyuwar mai glass ce a babban frame din, "ko wace ce
wannan" ta fada.
Mai bi masa ta kalla Hajiya da late Abban su Jaafar wanda sanye yake da kayan Sojoji, sai
saura kuma hoton jaafar, junaina da Mujahid, sun mata kyau sosai, kallon na Mujahid tayi ta
buga uban tsaki aranta tace "to hell with you".
Afusace ta juya zata bar gurin tagan shi Tsaye bakin kofar shigowa, kusan minti daya yayi
tsaye ganin ta tsaye gaban Hotonsa, baisan wace ce ba, yadai tsaya jiran ta juyo.
Harga Allah ta tsorata da ganinsa, ihu yarage batayi ba ta maze ta tsayaa mayar mai da
mugun kallon dayake wurgo mata.
Magana zai yi Hajiya ta fito daga daki tanai kiran Ummi, "naam Hajiya" Salma ta amsa
aladabce, ganin Mujahid yasata daure fuska tace "kai kuma daga ina ?
Sosa keya yayi ya gaidata, tabe baki tayi

Da sauri Salma ta risina tace "yaya ina wuni, sannu da zuwa" fuskar ta daure da fara'a..
Kallon mamaki yabita dashi..
Hajiya tace "bada kai take ba, mugun banxa, Allah yasa dai zuciyarta a tsarkake take shiyasa
bata nufeka da shairi ba upon all abun dakai mata, idan baka sani ba toh yar'uwarka ce"
Ware ido yayi in shock.
Hajiya tacigaba "iskancin banxa au dama baka sani ba ?
"Bansanta ba, yama sunanta ? In serious tone yayi maganar
Kallon Banxa Hajiya tamai sannan ta kalli Salma tace "kiyi hakuri da abunda ya maki, Mujahid
sunan sa, daga shi sai jaafar a haife.."
Shuru Salma tayi, ta mugun kuluwa da denying dinta da yayi, sai yanxu ta kara tabbata wa
dagangan yaki nuna cewa yasanta tun farkon haduwan su..
Dakyar tace "ba komai hajiya ya wuce" wuce wa tayi daki, hajiya tabita abaya..
Tsaye Mujahid yayi gun hade da daura hannu akai, "yaushe tazo gidan nan ? Ya tambayi
kansa..
Tifowa Salma tayi rike da Plate a hannu, ko kallan shi batayi ba ta wuce ta gabansa, fizgo
hannuta yayi da karfi, ihu tasoyi yayi sauri rufe mata baki da hannusa yaja ta suka shiga
kitchen, can karshe bango ya turata hade da matse ta da jikinsa har suna juwo numfashin Juna,
tsuro tayi da ido, fuska ba annuri yace "What are you doing here, evil tramp from hell.. Alamun tamai da bakinta is close, cire hannu yayi daga bakinta, harara takai mai tace "the evil
tramp is you, you kept me away from knowing my family and the worst part of the story you try
putting me behind bars, why, do you hate me that much ?"
Cikin rashin damuwa da abunda tace yace "datx your story not mine, i need to know uban miya
kawo ki gidan nan ? Cikin zare ido yayi maganar.
Dariyar takaici tayi tace "the only reason y am here, its because of your brother, he is such an
Angel, so sweet, i cnt wait to be in his arms..".
Murde hannuta yayi, yanai mata mugun kallo da idanuwa sa da suka sauya launi zuwa ja, ko
ajikinta saima kokarin gyara gashin kanta daya bazu gefe, hannu ya nunata dashi, "badai
karuwan ci ya kawoki cikin gidan nanba, we shall cee about that.."
Tsaki taja ta kalli hannuta dayake rike dashi tace "M.u ka saki hannu karuwa mana, ko ka fara
shiga tarko ne.." Cikin salon rainin wayo tayi maganar.
Haushi biyu ne ya kamashi, "wai M.u, amma yarinyar nan ta raina ni, kodan Yaya bamu"
aransa yayi magana.
Rai bace yayi wurgi da Hannuta sannan ya juwa zai fita sukayi kicibis da Junaina zata shigo,
"yaya yaushe ka dawo" ta fada da murnan ta, ko kallanta baiyi ba yayi gaba abunsa.
Tabe baki tayi, ganin Salma Mak'ale gurin kaman mai shirin kuka, karasawa gurinta tayi tanai
kai mata kallon banxa sann tace "bawai kinzo gidan nan ba, better stay away from my
boyfriend, Mujahid nawane nikadai, kodayake y am i wasting tym talking to you, very soon zaiyi
kicking dinki out of this house cox he hate you so much Big sister" tsaki taja ta juya ta bude
fridge tadau drink sannan ta fita tabar Salma daskare tanai kallon ta.
"Oh ma God, little sis you're too good ki falling wa M. U, na shiga uku" ta fada hade da zamewa
kasa ta zauna.
Kanta ta daura kan kafafunta tahau yin kuka dani bansan dalili ba.
[9/7, 12:37 AM] Xarah Bukar: Zuma Sai Da Wuta

~na~
©ҳaɾaɧ bųkaɾ
(Aunty Cute)


56

Ido jajir ta mike ta k'arasa bakin sink ta wanke fuskarta sannan ta fita zuwa palo, Junaina ta iske
zaune tana kallon cartoon, kallon banza suka aikama juna sannan ta wuce dakin Hajiya. Kallon
daya Hajiya tayi mata tagano kuka tayi batace mata komai ta mike ta fita a dakin. Jiki ba kwari
ta fada gado ta kwanta, lumshe ido tayi hade da girgiza kanta tana fadin kanwata da Mujahid,
no no it wont happen gaskia, mutumin nan mugune, i wont allow him hurt my little sis"
maganganu tahau yi tamkar tababbiya daga bisani kuma shuru tayi tanai neman mafita.

Karfe takwas na dare Jafar ya dawo gidan, baiyi mamakin ganin Mujahid ba, ko takansa biya ba
ya karasa kitchen inda yajiyo muryar Hajiya tanai bawa masu aikin ordern su tsaftace ko ina.
"Sweetheart da kanki, yau kece a kitchen" ya fada yanai karasa shiga kitchen din.
Dariya tayi ta rufe kofar fridge datake rike dashi tana duban yadda yake kyalli, "Son kansan dole
saida sa ido, maid dinnan sumtymz basu sanin aikin su"
Sosa keya yayi yace "naga Mujahid ya dawo, why ?
Tabe baki tayi,
"Wayasan mai, ni tunda yaxo baice min komai ba"
Nisawa Jafar yayi.
"Ummi fah, tana ina ?
Kwatar da Murya Hajiya tayi, tace "tana daki, i dunno watx wrong with her amma dagani she is
depressed"
"bari naje naganta" ya fada da azama hade da juyawa.

Zaune take bisa praying mat tayi tagumi bayan ta idar da sallar ishaai. Shigowa yayi hade da
Sallama, amsawa tayi tare da saurin gyara zama tanai sakar mai murmushi, kusa da ita ya
zauna yanai kare mata kallo, yace "meke damunki ?
"Maika gani, ba abunda ke damuna..
Hannuta ya riko, tadan razana, ya lura da hakan ya share yace "you're lieing, nasan akwai
abunda ke damunki i can feel it"
Kallon shi tayi ido cike da tear, ahankali ta zame hannuta daka nasa, cikin sanyi murya tace
"you're a good man, i dont tink you will be happy with me"
"Miyasa kikace haka, Don't you love me ?
Kuka ta fashe dashi hade da kawar da fuska tana shesheka, hannu yakai bisa fuskar ya juyo da
ita sunai fuskan ta juna, murumshi ya sakar mata yace "bana son kuka tashi muje muyi Dinner"
Atare suka mike, ya goge mata hawaye yace ta shiga toilet ta wanke fuska, ba musu taje ta
wanko ta fito, cikin zolaya yace "to miye kuma na b'ata rai, sai kinmin murmushi zamu fita".
Dariya tayi bata ce komai ba suka fita tare zuwa palo.

Dining area suka nufa, Mujahid na zaune shida Junaina tanai mai magana kasa kasa, shikuma
yayi kicin kicin da Fuska, ganin Salma da Jafar yaka daure fuska. Hajiya kuwa tana palo zaune,
bata fiya cin abincin dare ba.

Zama Salma tayi ba tare data kalle saba, gefenta Jafar ya zauna.
Hararar iska Junaina tayi sannan tace ya jafs kaifah muke jira tun dazu"
Dariya yayi
"Ai gani nazo you can served us.."
Cikin zumudi dajin dadi yay mata dariya unlike kwanaki dayake daure mata fuska, hannu takai
kan serving spoon zata dauka Salma ta rigata dauka, tsaki taja ta janye hannuta. Murmushi
Salma tayi ta bude warmers din, ganish macroni ne da pepper chiken, plate din gaban Jafar ta
zuba abinci sannan ta ijiye serving spoon din. Kallon ta Jaafar yayi yace "bazaki zubawa kanki ba"
Spoon tadauka tace "habibty tare zan ci dakai" ashagwabe tayi maganar.
Mugun kallo Mujahid yakai mata, so yake su hada ido amma taki kallon shi, saima faran cin
abincin sukayi tana zuba mai yauki da yanga.
Junaina kuwa tafi shi k'ulewa yadda Salma ta nuna halin kota kula da serving dinsu, kallon
Mujahid tayi, tanaso tasama masu abinci tare tana tsoron ya dizga ta, mazewa tayi ta zuba mai
da niyyan suci tare taga ya mike yadau plate din abinci ya koma kujerar dake fuskantar Salma
ya zauna.. Kuka ne kadai ya rage Junaina batayi ba, akule ta dibi nata abinci tanai kaiwa su Salma Harara.

Ajiye Spoon din Salma tayi, murya kasa kasa tace
"Yaya feed me Hannu na ciwo"
Murmushi Jafar yayi, ya fara feeding dinta, fork ya dauka ya yanki kazar xai bata abaki, da sauri
ta girgiza kai tare da turo mouth "no yaya hakorina ke ciwo, bazan iya ci ba ka faraci abakin ka
idan yayi laushi saika ban"
Dariya sosai tabashi, ya dake yasa naman abakinsa yafara ci, sai kallon shi take tana lumshe
ido.

Dogon Tsaki Junaina taja jin abunda Salma tace, aranta tace "so disgusting"mikewa tayi hade
da daukan abincinta ta koma palo.

Duk yadda Mujahid yaso su hada ido da Salma ki tayi, iya kuluwa yakai da rainin hankali da
suke agabansa, saidai bazai bari ta amshin Kazar bakin k'anin saba. kafarsa yakai daidai kan
nata hade da murjesu da karfin gaske.
Dan karamin kara ta tsaki takai dubanta kan Mujahid,
"habibty miya faru ? Jafar ya fada, duk ta kidime zabar yadda Mujahid ke cigaba da take mata
kafa.
Cikin inda inda tace "yaya hakorina xai cire.."
"This is serious" jafar ya fada hade da mikewa yace bari nakawo maki warm water" da sauri
yabi hanyar kitchen.

Matso da Fuskan sa Mujahid yayi kusa da fuskanta, sannan ya kalli palo dan tabbar da babu
wanda ke ganin su, Duban ta yayi fuskar daure, yace "what do you think you're doing ?"
Ahankali yayi maganar.
Harara takai mai, ta matso da fuskan ta tsatin kunnansa tace "Datx non of your bizness, kuma
kabar taka min kafa"
"You're trying to seduce hime right ?
Bitting lower lips dinta tayi tare da kashe mai daradara eyes dinta yace "kwarai kuwa, are you
jealous ?
Dariya yayi yakai mata cixo a kumatu sannan yace
"Dont even tink about it"
kallon banxa tamai, ta shafa inda ya cixa tace "dan iska kawai" mikewa tayi afusace zata koma
palo yasa mata kafa tafadi tim akasa.
"Subhanallahi" Hajiya da Jafar suka fada tare, fitowan shi daga kitchen yaga duk abunda ya
faru, sharewa yayi ya karasa gurinta, "sorry Habibty" ya fada yanai kokarin taimaka mata,
Mikewa tayi batare data bari ya tab'a taba, yaken dole tayi tace "yaya ba komai fah, faduwa
kawai nayi"
Sannu yahau cemata suka zauna a kujera 3 sitter, Hajiya ma sannu tai mata, junai kuwa sai
dariya take kyalkyalewa.. Oga Mujahid baima san suna yiba, banda abincisa da yakeci ko
ajikinsa.

Warm water din Jafar yabata, kin sha tayi tace hakorin yadaina ciwo, shuru tayi bata kuma cewa
uffan fa tsananin yadda Mujahid ya bata mata rai, tunanin yadda zata rama kawai take. Duk
yadda Jafar yaso suyi hira kin kulashi tayi daga bisani ta koma
daki ta kwanta........

Typing din yau sai Ahankali wollah....
Kuyi maneji
[9/7, 12:37 AM] Xarah Bukar: Zuma Sai Da Wuta

~na~
©ҳaɾaɧ bųkaɾ
(Aunty Cute)
®NWA


Allahu akbar kulu'nafsi za'ikatu mauti, Allah yaji kanki da rahma Maman besty Yar ficika. May
jannatul Firdausi be ur final destination.



57

Barin palon sukayi yarage Hajiya da Mujahid. Mik'ewa yayi kamar marar gaskia zai haura sama
tace "koma ka zauna" fuska ba wahala ta fad'i hakan.
Komawa yayi ya zauna ba tare dayace uffan ba.
Hajiya tace "miya dawo dakai gidan nan ?
Nisawa yayi.
"Ba komai, kawai naga banda aikin yi ne"
Mugun kallo ta aika mai.
"Mujahid ka fita ido na, ka dauna banga sanda kasa mata kafa ta fadi ba, kuma nasan sarai
saboda ita ka dawo gidan nan".
Sose k'eya yayi, murya kasa kasa yace "nifa ba ruwana da ita bamma san da zaman taba,
infact ko ak'afa aka d'auramim ita bazan jaba"
K'wafa Hajiya tayi, ta shak'e abunda yace ba kad'an ba.
"Tashi ka bani guri kafin na kwashe ka da mari"
Dariya yayi ahankali ya mike hade da mata asubah ta gari ya haura Sama.
Washe gari yakama weekend, kowa sai sanda yaga dama yake tashi bacci, around 10 Salma ta
tashi tayi wanka ta shirya cikin dogowar riga atamfa, fitowa tayi daka d'akin ahankali gudun
karta tashi Hajiya, kitchen ta shiga had'a tea ta hango shi ta window yana playing basket ball,
Murmushi tayi tace "perfect timing, yanzu miya kamata nayi mai" tunani tahau yi, can dabara ta
fado mata, fridge ta bude ta dibi atarugu da yawa tasa a bowl ta jika da ruwa zafi Sannan ta
sane ruwan a bowl, daukan ruwan tayi ta haurawa Sama da sauri. Dakuna Hudu tagani mai
dauke da parlour, shiga na farko tayi babu alumun da wani ciki, tana leka na biyu ta hangi Jafar
zaune gaban laptop yana dannawa, saurin komawa baya tayi, next dakin data shiga ya tabbar
mata da dakinsane, daddadan kamshi da sanyi ke tashi ta ko wana lungu da sakon d'akin.
Dariya tayi ta shige Toilet tadau shower gel dinsa ta bude ta zuba ruwan taragun sannan tafito
da sauri tafara saukowa, kafin ta ida sauka Junaina ta fito daki wucewa kitchen, hada ido
sukayi Junaina tayi saurin dauke kai bayan ta maka mata uwar harara. Salma kam bata damu
ba, palo ta zauna hade da kunna Tv.
Kusan rabin awa Mujahid yayi yana playing b-b kanan ya koma cikin gidan, jikin sa sharkaf da
zufa, so yake kadai yayi freshen up dan samun dadi jikinsa, Salma naji shigowarsa ta maida
dubanta garesa, dogon tsaki taja ta hararesa hade da dauke kanta, bai ce mata uffan ba ya
haye sama, aranshi yana fadin "bari nayi wanka na sauko zakici ubanki ne" Toilet ya fad'a ya sakarwa kanshi ruwan shower mai dumi, shower gel din yadau ya matso hade
da shafawa a fuska daidai kan idanunwa sa, runtse ido yayi sakamakan azaban daya ziyar ci
idon, "wanna yajin daga ina kuma" yafa d'a aranshi, kara tasar gel din yayi yakuma shafawa
dan wanke idon da kyau, raradi ya kuma ji yayi azama kashe warm water aganinsa yajin daga
ruwan dumin ne, ruwan sanyi ya kunna ya kuma murza gel din a ido, azabar tafi ta daxu, wulli
yayi da shower gel din yahau murza ido da ruwan sanyi saidai ina ko alamun sauki baiji ba
banda radadi da idon suke, sosai suka sauya launi zuwa jajir. Ganin ba madafa yasa ya dau
sabulun dake gurin yayi wanka adaddafa idanu a kulle.

Murumshi kawai Salma keyi ita daya, jira take taji ihun sa shuru bataji ba, jin taku ana saukowa
yasata azama mik'ewa tsaye hade da kallon gurin. Jaafar tagani, laptop rike hannusa yanai

sakar mata murmushi.
Yace "har kin tashi ?
Risina tayi
"Yaya ina kwana ?
Lapia" ya amsa, aranshi yana mamakin bata kirashi da Habibi ba.
"Yaya fita zakayi"
Kai ya girgiza, "garden zan futa na zauna, akwai aikin da nakeyi nagaji da zaman d'aka"
"Muje na tayaka zama" Ta fada hade da daukar wayarta dake ajiye kan kujera.
Murmushi yay yayi gaba ta mara mai baya.

Duk akan Idon Junaina dake makale bakin kofa kitchen, haushi ne yakamata.
"matar nan sai shishigin tsiya wlh, da farar safiya ko miye nabinsa waje" ta fadi, tsaki taja wata
zuciya tace kema kije gurin masoyinki Mujahid mana, kai ta girgiza tace aikuwa dai kila ma
bacci yake bara naje na tasoshi muje waje. Da sauri ta haura saman.

Dakyar Mujahid ya iya bude ido, sosai sukayi Jajir, ko lotion bai iya shafawa ba ya shirya cikin
kananun kaya, black shade yasanya a fuska ya koma toilet yadau shower gel din yana kalla
cike da mamakin sabon al'amari.

Ahankali Junaina ta turo kofar dakin ta shigo, babu kowa ciki tayi tunanin koya fita, wayarsa
data gani kan gado yasa ta karasa ciki hade da daukar wayar, camera ta shiga zata dauki kanta
Selfi ya fito daga toilet. A tsorace ta dire wayar, cikin inda inda tace "Good morning".
Mamaki ne yakama shi, yaushe Junaina ta renashi haka harda shigomai daki batare da izinin
saba.
Fuska ya murtuke "ke!!! Miya shigo dake nan..
Kaman marar gaskiya ta ware idanu, "dama wai kiran ka zan..."
Katse ta yayi da cewa "wato bincike kika zo yimin ad'aki harda daukan wayata, gayamin waya
aikoki ?
Yadda yake magana yasa ta tsorota, bata ga alamun wasa tattare dashi ba, kaman zatayi kuka
tace "wallahi yaya ba bincike nazo yi ba ?..
Cikin tsawa yace "karya kike, ni nasan halin ki am sure kuma rahoto kikazo samu dan kaiwa
gaba".
Kasa magana Junaina tayi, gabanta na dukan uku uku, ga kuma haushi kalamansa daya
turnuk'e ta, koda take nemo rahoto aishi take kawo wa shine kuma yau zaiyi turning tables
around.
"Get down on your kneels" ya fada cikin harsh voice.
Kuka ta fashe dashi "yaya dan Allah kayi hakuri"
Rab'awa yayi ta gefenta ya wuce yana cewa "bari na dauko belt, yau sai kin gayamin ubanwa
ya aiko ki"
Da sauri tayi kneel down tana rokansa, belt ya dauko ya tsula mata daya abaya, ihu tayi tace
"na shiga uku, yaya wlh da akwai zafi"
Jinjina kai yayi yana tunanin

13 / 20