Author : Zarah Bukar Category : Tknovels
hade da dauke kansan, he cnt believe abunda ke faruwa, amma yarinyar ta
gaba dashi da irin insult data mai.
Tana ganin Motar Salim ya iso ta sauke numfashi, fitowa yayi tayi sauri karasawa gareshi, hade
da kaimai hug
"Thank God yaya ka iso on tym" ta fade cike da murna.
Janyeta yayi yace "keda waye, miya faru ?
Hannu tasa natai nuna mai motar tana tab'e baki.
Duban motan yayi, atake yasha jinin jikinsan ganin motan Ogan sane.
"La'ilah mai salma ta tsokano mai yanxu" ya fadi aranshi.
Shikam Mujahid ganinsu ta side mirrow yasa shi kara daure fuska hade da fitowa yana masu
mugun kalloi, hararar sa Salma tahauyi sai sannan tagano Guy din cikin frame din ne, mijin
tsohuwa Fa'iza atunanin ta, saidai dalilin dayasa yake binta shine bata sani ba, kallon Salim tayi
da tuni yayi tsuru tsuru tace "what are you waiting for, kayi arresting dinshi mana"
Karasa wa gurinsa Salim yayi, hade da risinawa yace
"Sir kayi hakuri, kanwa tace ay mata uxuri"
Girgiza kai Mujahid yayi yace,
"atunanin you are d useless person a family dinku ashe dai kana da kanwa data fita zama
useless and shameless"
Shuru Salim yayi yasan hakan zata kasance.
Salma kam tagama fusata da abunda yace, tace "i tink you're d shamless person here, jibeka
sanye da suit kaman mutum arziki,
Sauri rufe mata baki salim yayi
"Plz salma kiyi shuru
Cire hannusa tayi cikin masifa tace "haba yaya kanaji yana xagin mu, who the hell is he, dan
kawai shida matarsa suna aiki saisu nemin raina mutane, or do they tink d world revolve around
them"
Janye ta salim yayi sauri yi, yanai bawa mujahid hakuri, saidai kasan zuciyan shi yaji dadi
yadda Salma ta mayar mai magana, suna cikin haka Fa'iza ta karaso
"Mjay make faruwane"
Nuni yay mata da hannu ta shiga motar sannan shima ya shiga, ran shi ya gaba bacci.
"Ban taba sani apart from student akwai dabbobi anan ba"
Kallon Salma tayi dake tsaye gefe Salim na bata baki,
tace "miya faru"
Yace "stupid gal din ta dauka sonta nake, dan kawai munyi crossing path daxu da yanxu"
Tsaki faiza taja tace "Salma Abbas maccido, ai sam yarinyar bata da kunya ga bin maza, ina
zargin ma barauniya ce
Tayar da motar yayi yace "mita sace maki"
Shuru Fa'iza tayi dan kuwa bata da evidence tunda bata ganta ba, amma tana zargin itace.
Tace "haka naji wasu student na fadi.
Tsaki yaja ya figi motar hade da buda masu kura ya wuci, rikota Salim yayi yace "salma cool
down mana, so kike yasaki a prison, babban police nefa".
Kaman xatayi kuka tace "and so, wana law ne yace yamin rashin Mutunci".
Masifa sosai salma tahau dakyar Salim ya lallbata ta shiga motar ta taja yanai biye da ita a tasa
motar har suka isa gida hadaddan gidansu dake Asokoro.
Suna isa momy ta iske zaune a palo, da gudu ta karasa gurinta fuska ba walwala.
"Yau kuma wace tsokana kika iyo"
Gunguni tahau yi
Salim yay mata bayani.
Haushi ne ya kama Mom tahau ta da fada, "nikam nagaji da fitinar ku, yau salim kaine gobe
kuma itace, bari dai Daddy yadawo".
Hankalin Salma ne ya tashi tana mugun tsoro fadan Daddy, shiyasa akodayaushe take kaffa
kaffa, hakuri tahau ba Momy kamn xatayi kuka, dakyar mom tA hakuri tanai tsokanan ta
maganinta Daddy.
Banda Zagin salma ba abunda Fa'iza take a motar har suka isa gidansu dake Garki 2,
ya ajiyeta
Yace ki tabbata motar ki an gyara nagaji da zama driver dinki".
Murmushi tayi tace "ba damuwa sai munyi waya"
Bye tamai sannan yaja ya koma office shidai Gida nedai bazai jeba.,( ni xarah nace xaka hadu
da Hajiya)
Tana shiga Gida, Umma ta fake ta da Ido alamun tuhuma, sanna tace
"Faiza idan yaron nan sonki yake ya turo ayi magana, nagaji da wannan dangantakar taku,
kusan shekaru ashiri kuna tare kinyi aure harkin fito kuma still kuna tare idan sonki yake ya turo.
Shuru Fa"iza tayi, ita kanta tarasa meke cikin zuciyar Mujahid, tun suna secondary skul suke
tare as friends har yau kuma banda wanan bataga alamu love ba, tace
"Umma bafa saurayina bane abokina ne, kuma ma shifa babu so aranshi"
Kwafa umma tayi
"Karyan banza, duba fah yadda yake ji dake, ko gidansu ansanku tare, wa zaku rainawa
hankali"
Faiza kam bata iya cewa komai ba ta wuce ciki, Allah yaga zuciyanta tun kafin auranta na farko
takeso mujahid ganin bashi da niyya yasa tayi auranta gashi ta fito ba abunda ya canxa.
***
[9/7, 12:37 AM] Xarah Bukar: *Zuma sai da wuta*
~na~
©ҳaɾaɧ bųkaɾ
Happy birthday *Billy Galadanci*, Wishing you more perfect years ahead, its you day Have fun
*Wannan shafin naku ne, Hauwa shehu, maman safara da Aisha ture nagode matika da
soyayyar ku gareni*
Wishing you safe trip to Birnin shehu, Feedoh Deedoh (Aunty yar ficika ), kina isa kuma ki
aikomin da Matata gimbiyata, Sannan ki biyo ta gida Muci Rengem
11 - 14
**
Cikin kayan yan sanda yayi shirin sa tsaf sannan ya sauk'o k'asa, jin shuru a palon yasanya shi
ficewa waje da azama gudun kar hajiya tasan da fitar sa dan kuwa wasan b'uya yake da ita,
adaran jiya ma cikin tsadaf ya shigo gidan yaci sa'an Hajiya ta jima da bacci.
Duk akan Idon Junaina dake tsaye ta window kitchen tana kurban tea, jikin ta tsaye da uniform
na makaranta. Ajiye mug din tayi tama mai aikin su Lami sallama sannan ta fito waje haraban
gidan inda motar ta ke ajiye, shi kuma alokacin yake kokarin tayar da tasa.
Murmushi yayi ya dubeta.
"idan bazaki damu ba kizo nayi dropping dinki"
Kallon gefen ta tayi dan kuwa batai tunanin da ita yake ba, ganin ita dayace yasa ta gano da ita
yake.
Farin cikine ya cikata.
"Da gaske yaya.."
Kai ya d'aga mata, da sauri ta zagaya ta shiga ta zauna fuskar ta dauke da murmushi.
"Yaya ina kwana"
Ta fad'i.
Bai amsa ba yace,
"Hajiya bata ce maki komai jiya ba"
Kallon rashin fahimta tamai.
"wana abu kenan"
Daure fuska yayi yace ba komai sannan yaja motar.
Tace,
"ya Mjay zaka dawo daukana kenan
"A'a"
Ya fad'i atakaice.
Kallon shi tayi kaman zatayi kuka, aranta tanai takaicin gwanintarsa na kaita skull alhalin ba
dawowa daukar ta zaiyi ba, kodayake ta riga ta gano shi, bata da wani amfani agurin sa sai
yana neman information gurinta yake bata fuska.
Basu kara magana ba har suka isa premier Academy babu wanda yace uffan.
Sauka tayi motan, kafin takai ga mai magana yaja motar yayi gaba.
Guntun tsaki taja.
"Baima damu da yadda zan koma gida ba" aranta tayi maganar.
Murya k'awayanta taji abaya sunai kiranta, sauri sakin fuska tayi hade da sakin murmushi ta
juya kallon su, kawarta Hameeda tace
"wow badai shine sweetheart dinki ba, gaskia ya hadu acikin uniform".
Dariya Junanai tayi aranta tana tunanin yadda zaici ubanta idan yasan da sunan sweetheart
dinta kawayanta ke mai nuni.
Share zancen tayi taja hannusu suka shiga ciki.
Yana isa NPF (Nigeria police force Q), parking yayi ya fito k'arasawa dept dinsu ya hadu da
abokin sa kuma abokin aikinsa Mubarak. Gaisawa sukayi har zai wuce ya tsaya yace.
"Mubarak nasan kasan manyan mutane agarin nan".
Dariya Mubarak yayi yace "ka shirya aure kenan, diyar wace ce yanzu nama hanya"..
Tsaki Mujahid yayi.
"Kaima kasan babu wanan a lissafina, kasan wani babban mutum Alhaji Abbas Maccido a
agarin nan ? Ya fada, dukda baisan waye Alhajin ba yasan mai kudi ne ganin motar da
shameless daughter dinsa ke driving.
K'ad'a kai Mubarak yayi yace
"nasan shi, babban dan canji ne (Burea de change) mai kudin gaske wanda anjima ana
damawa dashi"
Numfashi Mujahid ya sauke.
"Good, inason details din komai game da family members dinsa, And plz make it Quick".
Cigaba yayi da tafiyan sa batare daya jira cewar Mubarak ba.
Dariya Mubarak yayi ya wuce, aranshi yana adduan ko abokinshi ya fara sanya So aranshi.
***
Yau lecture free day, ko wanka batayi ba ta fita palo yin breakfast, wanda k'idar gidan ne dole by
8am a hadu dining yin breakfast kafin nan kowa ya wuce zabgogin sa.
Kayan bacci ne jikinta riga da wando cotten, gashin kanta baje babu kallabi, Su biyu ta tarar
zaune kan dinning taja kujera ta zauna hade da yin mik'a da salati sannan ta kalli iyayan hade
da k'ok'arin fara had'a tea.
"Dad n mom good morning"
Kunnan ta Mom ta rik'o tace,
"Salma bana hanaki fitowa da Nyt wear ba, idan Salim ko wani ya ganki haka fah".
"Kai mom bacci fah xan koma idan na gama"
Katse su Daddy yayi da cewa, "yau baki da lectures ne ko wani bak'in halin kikayi aka koroki "
fuska daure yayi maganan.
Shagwabe Fuska Salma tayi, aranta tanai fadi "Daddy dai zancen shi kullum makaranta, kuma
ma babu wanda ya isa ya koreni, i can defend myself".
Afili tace "Daddy bamu da lec yau, sai gobe muke da Math 105"
Yace "Good, make sure kiyi revising kafin kiyi bacci".
"Yes, Daddy" ta fada tanai dariya kasa kasa.
Mik'ewa Daddy yayi sannan ya kalle ta yace "ki zauna a gida, banso na dawo daga office naji
labarinki in some kind of trouble"
"Okay Dad, Allah ya dawo dakai lafiya"
Ta amsa.
Murmushi yayi sannan ya wuce, mik'ewa Mom tayi hade da kai mata duka tace "kin daiji abunda
yace wlh Salma ki kiyaye ni"
Dariya tayi.
"Momy mi nayi kuma".
Harara mom takai mata sannan ta juya da azama tabi bayan Daddy rakashi bakin mota.
Kad'an ta iya cin abinci ta tashi ta koma Daki, jakarta ta jiya ta fiddo daukan handout dinta taga
frame din hoton sa, Dogon tsaki taja, harga Allah ta manta da hotonsa a jarkarta, wani mugun
haushin sa taji tunawa da yadda ya zage su jiya. Daukan Frame din tayi ta ajiye shi kan
Console daidai inda hotonta dana Momy ke ajiye, harara hoton tahau yi taji an turo kofar dakin
an shigo, da sauri ta kife frame din sannan ta juyo adan tsorace, ganin wanda ya shigo yasa ta
daure fuska.
"Ya Salim miye haka, jifa yadda ka tsorata ni ko sallama babu ka fadomin daki"
Karasawa yayi ya tsaya gabanta hade da kai hannu bisa gashin kanta yanai shafawa.
Yace "ai nanma dakina na, yaushe kuma kika tsiro da sai nayi sallama zan shigo"
Hannu yakai kan habarta hade da dago fuskan ta sunai fuskanta juna, yacigaba "Miye kike
boyewa bakya so nagani, kinsan dai no Secret tsakanin mu"
Janyota yayi jikinsa yanai kokarin hade bakinsa da nata, tayi sauri matsawa gefe hade da kara
tamke fuska
"Oh yaya plz stop it, you're getting too close"
Hannu ta ya riko yace
"Just a kiss saina tafi, kinga babu wanda ya ganmu".
Takaici ne ya kamata
"Why cnt you understand, i don't have any feelings for you, tayama zan yadda kayi kissing dina
cikin gidan iyayena adakina for dat matter"
Idon shine ya fara sauya launi, yace "karya kike salma, duk yadda kike hugging dina muke
holding hands sannan kice baki da feelings, i know you love me kawai bakya son nuna wane".
Dafe kai tayi cike da takaicin abunda yace.
"I swear i dont love you kaman yadda kake tunani, d only people i love sune Daddy, mom n you,
plz ka bini ahankali kar love din yan'uwantaka da nake ma ta koma Hatred"
Kaman zaiyi kuka yake kallan ta, yace "Salma ina sonki"
Dauke kai tayi gefe, yayi gaba zai wuce tayi saurin rikon hannu shi ya juyo suna fuskanta juna.
Tace "yaya am sorry, babu so araina dan Allah karka ji haushi na"
Murmushi dabai kai zuciya ba ya kirkiro yace "ba komai, i hope randa kikasa so aranki ni zaki
so".
Dariya tayi, dan abune ne mai wuya, tace "yaya by 9pm idan ka dawo aiki, zamuje Officers club
chiiling, zaman gida ba dadi"
Ware ido yayi, yace "ba ruwana, kinsan dai Daddy ya hanaki fitan dare"
Shagwabe fuska tayi tace "don't worry satar fita zanyi yadda bazai gane ba, ko kuma nazo part
dinka na boye idan yayi bacci sai muje"
Dariya yayi yace "nice idea, nizan wuce office, am getting late"
Hannu shi ta saki tace okay bye"
Sannan ya fita sukayi kicibis da momy a palo, kallon tuhuma tamai dan tuni ya riga kowa
breakfast yace ya tafi ashe yana nan.
"Mom agogona dana bata ajiye naje karb'a" ya fadi cikin muryan marasa gaskia.
K"wafa Mom tayi batace komai ma ya fice cikin sauri.
****
Bayan Magrib Mubarak yasamu daman harharda Details din, zaune yake a office din yana
dannan laptop din gabansa saidai rabin hankalinsa yayi gida, sarai yasan yama Hajiya laifi
amma taurin kai bazai barshi yaje ya fuskan ceta ba.
Knocking Mubarak yayi ya shigo bayan anmai izini, zama yayi kujeran bak'i yana murmushi
ayayinda Mujahid ya daure fuska yanai mai kallon dami kazo.
"Kwantar da hankalin ka nasamo ma komai akan Family din Alhaji Abbas Maccido"
Gyara zama Mujahid yayi yanai duban sa.
Mubarak yace "Alhaji Abbas matar sa daya Hajiya Zaituna da kuma diyar su tilo Salma, da wani
saurayi da suke rike dashi a gidan tun yana yaro Salim ne sunan shi"
Anzo gurin, k'ad'a kai Mujahid yayi, sai yanxu yagane ashe Salma da Salim ba siblings bane,
saidai akwai wani abun dake tsakanin su ganin yadda sukai ta mannewa juna jiya.
Duban Mubarak yayi yace "baka da komai akan Salma".
Kashe mai ido Mubarak yayi yace "kodai kana ciki ne, kaga yar kyakyawa ka susuce"
Tsaki yaja, aranshi yanai mai zaiyi da Bak'ar karuwa.
Afili yace,
"baka amsamin tambaya taba"
Nisawa Mubarak yayi "Ba wani abu akanta, tayi secondary skull dinta a London, uban nata
yaso tayi jamiar acan taki zama fir ta gudo Nigeria, uban nata sam baya wasa da karatun ta,
yanxu dai nan gwagwalada take 100 level"
Jinjina kai Mujahid, yayi yanai zancan zuci.
"Tabbas biri yayi kama da mutum, sam yarinyar batta da tarbiyya amma yayi alkawari koya
mata hankali da samun tarbiyyan da ubanta bai bata ba"
Sun jima suna magana daga bisani Mubarak ya fice daga office din.
Mikewa Mujahid yayi ya tattare komai gefe sannan ya fito, parking lot ya nufa ya hadu da Salim
shima zai shiga motarsa, wani kallon suka aikawa juna dani kaina ban tantance kallon miye ba
sannan kowanne su ya shiga motar sa yaja.
Tuk'i Mujahid yayi yana tunanin yadda xai rama wulakanci da Salma tamai, danya lura ma
kallon banxa Salim yamai daxu duk akan rainin da salma tamai agabansa.
Sallah ishai da yaji ake kira yasa yayi parking a gefe hanya ya shiga masallacin dake gurin,
bayan ya fito ne ya tuna da Junaina, wayarsa ya fiddo ya kirata, alokacin kuwa tanai zaune tare
da Hajiya a Palo suna hira taji kirar sa.
Dauka tayi ta mike hade da matsawa can gefe da ita
"Yaya kana ina, daxu naji Hajiya da Aunty Bilkisu suna waya, kuma kaman zancen kane, hajiya
nata fada.
Dafe kai yayi, yace "kin dawo gida ne "
Haushi ne yakamata, sai yanxu ya tuna da ita, tace "eh nadawo".
Katse call din yayi ba tare dayace komai ba, kallon wayar tayi kaman tayi ihu, jiki sabule ta
koma ta zauna.
Tsaki yaja hade da kallon agogon sa, takwas da rabi na dare, muddin yaje gida yanxu xai hadu
da Hajiyarsa, shawara ya yanke na zuwa Officers Club kafin sha daya ya koma gida, yasan by
dat tym tuni Hajiya tayi Bacci.
Nima xarah nace na tayi yin wanka kafin mu hadu Officers Club♀♀♀
[9/7, 12:37 AM] Xarah Bukar: *Zuma Sai Da Wuta*
~na~
©ҳaɾaɧ bųkaɾ
®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION
Fatan Alheri gare ku Nagartattu.
Benaxir Omar
Lubie maitafsir
M jabo
Futha lurv
Biebee Isa
Queen miemee
Jeedah Aliyu
Fiddausi Sodangi
Miemee bee
Mom Fatee
Khadeeja Candy
Pharty BB
Mr umar
Mamu
Deeja Abdul
Asee B Aliyu
4 Stars
Raz
Safha
Da duka wanda ban ambata ba.
*Jinjina Ga kawata Zuwairat (Umm Maryam) Allah ya kara basira da kaifin Ido*.
*Ayusher*
*Sumayya Salees Sadeeq*
*Billyn Abdul*
*#Ana tare*
*Wannan Shafin naki ne Shuwah Darling, ilysm* ❤❤
15 - 20
Tafi mintuna ashiri da shiryawa cikin fitinannan matsatsan english wears riga da wando da
sukayi mutukar fiddo da azahirin shape din jikinta, kai komo take a tsakar dakin tanai saka da
warwaran neman hanya fecewa. Lek'awa tayi ta k'ofa ta hange Daddy da mom zaune parlour
suna hira, susucewa tayi ta koma ta zauna hade da latsar nambar Salim. Yana tsaye bakin mota yanai jiranta ganin call dinta yasashi azaman dauka.
"Kayan da kika shanya sun bushe" Ya fad'a cike da takaici zaman jiranta da yake.
"Ya salim am sorry kaban tym kadan, narasa yadd zan fito, su Daddy sun babbake apalo"
"Minti biyar nabaki idan baki fitowa zan koma daki na kwanta"
Tsaki tayi ta kashe wayan.
"harshi zai bata minti biyar waye shi" Aranta ta fad'i.
Wardrope ta bude tadau dogon hijab dinta mai hannu ta sanya sannan tadau wipes to goge red
lipstick dake shafe bisa sexy lips