Author : Zarah Bukar Category : Tknovels
anya ba ita tasamai abu mai yaji a shower gel dinsa ba, dan kuwa
kafin yafita playing b-b yayi wanka da gel din baiji yaji ba.
Fuska ba annuri yace "wato daxun kin shigomin daki ko ?.
Ware ido tayi cikin rashin fahimta, yace "badake nake ba" daka belt yayi zai tsula mata.
Tace "yaya wlh yanxu nashigo, daxu dai naga Adda Ummi ta sauko daga stairs bansani ba
konan ta shigo" kuka sosai ta fashe dashi
Cize Lab'a Mujahid yayi aranshi yace "lailai yarinyar nan ta cika yar daba" kallon Junaina yayi
yace "b4 d count of three tashi ki bace anan"
Mikewa tayi ta fita da gudu tana sosa baya.
Nisawa Mujahid yayi yakarasa bakin mirror, cire glass dun fuskar sa yayi yanai kallon idonsa
dayai jajir ya duru da ruwa, wani irin raradi da azaba yake ji.
Sunan Salma kadai yake ambata aranshi, shi kadai yasan rashin mutumcin dazai mata.
A can Garden kuma.....
To be continued......
[9/7, 12:37 AM] Xarah Bukar: Zuma Sai Da Wuta
~na~
©ҳaɾaɧ bųkaɾ
(Aunty Cute)
NAGARTA WRITERS ASSOCIATION...
Allahu akbar kulu'nafsi za'ikatu mauti, Allah yaji kanki da rahma Maman besty Yar ficika. May
jannatul Firdausi be ur final destination.
58
Acan Garden kuwa zaune suke kan d'aya daga cikin kujerun, Jafar kam duk'ufa yayi da danna
laptop dinsa kasancewar wani babban aiki dayasa agaba, Salma kuwa wayarta kadai take
latsawa, so take ta kira Mujahid amma tafasa gudun karya dago abun data mai, ajiye wayar tayi
a cinye hade da sauke ajiyar zuciya. "Kin gaji ne ? Jafar ya fad'a yana cigaba da aikin sa ba tare daya dube taba.
Dubansa tayi.
"Bakai ka shareni ba" ashagwabe tayi maganar.
Dariya yayi
"Kinga wani case nake bincike akai, mayb zuwa next week zanje Kaduna"
Dadi Salma taji aranta, idan ya tafi zata samu sararin yiwa Mujahid rashin mutunci.
"Murna kike zan tafi ko ? Ya jeho mata tambaya.
Kunya ce takamata, ta dake tace "yazaka ce hakan bayan kai yayana abun alfahari nane, ni wlh
banso ka tafi kaine kaidai good abu arayuwa ta"
Murumshi yayi, ciki ciki yace "naga alama kam".
Bataji abun da yace ba, zatayi magana suka ji ana rangad'a uban horn daga can bakin gate,
maida dubansu sukayi b'angaran, wata mota jeep ce ta shigo ta karasa maajiyar motoci ta
tsaya.
Salma tace "suwaye ne..
Mikewa tsaye yayi itama ta mike suka fara tawaka gurin....
Wata kyakyawar tsohuwar matar ce ta zuro kafa daga motan ta fito, da ganinta kasan ta hada
alak'a da masu gidan, da azama driver ya zagawo gurin ta hade da risinawa ya mika mata wani
sliver walking stick, amsa tayi tanai karewa gidan kallon hade da sauke sanyayyiyar ajiyar
zuciya. Gaban Salma ne yafadi, tagane matar data gani a hoto ce, murya jafar taj yace "Granny dinmu
ce, mahaifiyar Daddyn mu"
Yaken dole Salma tayi, kwakwata bataga alamun annuri a fuskar taba, shuru tayi suka cigaba
da takawa gurin da take tsaye tana shakar sanyayyar iskar gurin.
Daga inda suke tagowa Jafar yace "wa nake gani kaman Annah." Karashe maganar yayi cikin
zolaya.
Dariya Annah tayi har hakoranta suka bayyana.
Ga mamakin Salma taga Annah ta juya wani bangaran tana lalube, cewa take "Jafar kaine ko
kuwa kunne na ne ?
Karasawa yayi ya rikon ta, yana dariya gani tanan".
Tace mikomin gilashi na yana mota, dauko mata yayi ta amsa tasa sannan ta kallesa "wato kun
gurma ko ganin ku baa yi, tunda baku iya zuwa gurina gani zo gurinku"..
Dariya yayi.
"Kai Annah daga zuwa sai neman sababi ?
"Kaga ni bani guri" ta fada, wucewa zatayi Salma tace "Annah ina wuni ?
Kallon Salma tayi, bata amsa ba sai tab'e baki datayi ta wuce.
Jiki sanyaye Salma ta dubi shi.
"Bata gani ne ?
Alamun tayi shuru yayi mata, saida Annah ta masu tazara yace "zaki sha duka idan taji kinci
mata bata gani, tana gani amma sai da glasses,
Ware ido salma tayi.
"Miya sameta halan
"Bakomai, ciwon idon gada sukayi gurin babansu, sai dai nata yayi worst, sau biyu ana mata
operation"
"Allah sarki, amma naga ku yaran Hajiya baku gada ba"
Dariya jafar yayi, yace "inji wa, koda yake niban da matsalan ido, Aunty Bilki da Mujahid suka
gado ta"
Mamaki ne yakama Salma bata ga alamun ciwon ido ga mujahid ba, dama ma Aunty Bilki
tanasa glass.
Shuru tayi suka cigaba da tafiya ciki.
Side drawer Mujahid ya bude yadauko wani magana a tube ya diga a idon, wani mugun azaba
yaji, maida black shade yayi ya fice daga d'akin.
Ta bangaran Junai kuwa kitchen ta shiga ta zauna matsar kwalla, koda Hajiya ta fito ta isketa a
hakan ba tambayar da batai mata ba taki fad'a mata komai sai cewa tayi cikinta ke ciwo, Palo
hajiya ta riko ta suka dawo tanai mata sannu.
Banko kofar Palo Annah tayi batare da Sallama ba ta kutsa kai ciki ta fadin "ba kowa agidan ne
?
Adan tsorace su Hajiya suka juya kallanta jin yadda aka banko kofar, bata yi samma nin ganin
taba ba dan kuwa sunyi waya jiya bata ce mata tana tafe ba.
Dakyar Hajiya ta iya hadiyan yawu tace "Annah sannu da zuwa, aibansan kina tafe ba"
Tabe baki tayi ta kalli yadda palon ke haskawa da kayan alatu, tace "yanzu kin ganni ai
Shuru Hajiya tayi, Junaina ta gaidata, nunata tayi da walking stick din tace "kece haka kika
girma ?
Magana Junai zatayi Salma da Jaafar suka shigo palon adaidai lokacin da Mujahid ya sauko
daga stairs.
Zubamai ido sukayi, ko kallonsu bayi ba, fuska daure ya kama hanyar ficewa, dakatar dashi
Hajiya tayi da cewa "bakaga Annah ba zaka wuce ?
Tsaye yayi chak yanai ma wani Annah mugun kallo ta Black shade din fuskar sa, aranshi yace
"uhnm sai yadda ta yuyu kenan, nakuda ad'aki mayya"
Afili yace "mai makauniyar nan tazoyi agidan nan ?
B'ata rai Annah tayi ta k'arasa kusa dashi, bai ankara ba yaji ta fara kaimai Duka da Sandar
hannu ta tana fadin "uwar ka nazo, dan tselan uwa kawai" ta ko ina tahau kaimai bugu, ihu
kadai yarage baiyi ba tsabar yadda sandar keda zafi, Salma kam dariya tahau babbaka wa,
ayayinda saura kuma suke kallon Annah cike da takaicin abunda take, Mujahid kam ganin ba
bari zatayi ba yasa yayi hanyar waje da sauri, baima lura ba yaji ya buge kai da bango, da
azama ya fice waje.
"Ni zai nunawa duniyan ci kamar wace ya samu sa'ar sa" Annah ta fada Masifa sosai tahau yi,
Salma kam kasa daina dariya tayi, da sauri tabi bayan sa waje, Mugun kallo Annah takai masu,
tace da Hajiya ke kuma muje ciki ina da magana dake, haushi biu ne yakama hajiya ba yadda
ta iya ta marawa Annah baya suka shiga daki.
Ajiyar Zuciya Junaina ta sauke ta kalli Jafar dake tsaye yana jin haushin fitar Salma, tace "yaya
Alhakina ya kaima ya Mujahid, dazu bakaga dukan da yayi min ba
Da mamaki ya kalle ta, "duka kuma, mi kikayi ?
"Daga daukar wayarsa, wai bincike zan mar, yahau ni da zagi da duka"
Dariya zancenta yabashi, yace "yayi maganin ki kenan ?
Turo baki tayi "aini yanxu ba ruwana dashi, he is so mean".
Murmushi yayi, Baice komai ba ya wuce ya haura sama, turo baki tayi ta tahau gungunin baice
mata sannu ba.
Haraban Gidan Salma ta fito waigen inda Mujahid yake, daga can nesa ta ganshi gurin parking
motaci zaune kan boot din motarsa, kansa daure bisa cinyar sa.
Karasawa tayi gurin tana mamakin miyake yi gurin. Yana jin tsayuwar ta gurin yaki d'ago wa,
hannu tasa ta d'ago da fuskar sa tana fadin "yaya badai dukan nan yasaka kuka ba" cike da
zolaya tayi maganar, saidai ganin shatin dukan da yadda fuskarsa ta kumbura yasata ta shan
jinin jikinta.
Hawaye taga ya fara gangarowa bisa kunci sa, yace "hankalin ki ya kwanta koh tunda kinga
karshe na?
Cike da kidima da tsoro take kallan sa, gabanta sai faduwa yake..
Murmushin takaici yayi yace
"Am sorry nasan nayi hurting dinki, plz forgive me".
Tausayin sane ya kamata saidai bazata bari ya raina mata wayo ba, tace "miyasa sai yanzu
zaka nemi afuwata ?
Ahankali ya zamo daga kan motar, suna fuskan tar juna, cikin sanyi murya yace "Salma i love
you alot, dou nasan ba lailai ne ki yadda ba but tun ranar dana fara ganinki nakasa samin
nutsuwa, kawai karfin hali da ego irin nawa yasa ban taba fahimtar hakan ba sai yau"
Kur Salma tayi mai da idanu, danson tantance gaskiar maganar sa ko kadan bata yadda dashi
ba, saidai taji dadi i love you daya ce mata, kalamar data jima take son ji garesa, koda ace
karya yake itadai taji dadi.
Dariyar rainin wayo ta saki sannan kuma ta daure fuska tace "do you tink am stupid, if i could
recall, kwanakin baya haka kazo kace you liked me, ka bukaci friendship dina nikuma i was
dumb nayi accepting, at last miya biyo baya, you wanted killing me, tnkx to Allah nayi surviving
but still saida kaso ka kaini prison, gayamin wannan so ne ko kiyyaya or is it part of your
egotistical behaviour ?
Hannuta ya riko, yace "nasan baza ki yadda ba, kin tsane ni, but plz find a place in your heart ki
yafemin"
Dogon Tsaki Salma taja.
"You're not serious" ta fada hade da kawar da kanta gefen, sam ta kasa fahimtar inda ya dosa.
Gani tayi yayi kneeling down, da sauri ta kalle shi hade da ware idano.
Black shade din fuskar sa yacire yace " ciwon ido zai zama ajalina, i dont tink zan iya kaiwa jibi
da irin azabar da nakeji, bazaki bani tym ko kadan ba ?
Tsoro da firgice ne suka kamata ganin yadda idonsa yayi jajir suna zubo ruwa, runtse ido yayi
da sauri dan bazai iya barin su bude ba.
Tsugunna wa tayi gabansa,
Cikin rawar Murya tace "yaya miyasa me ka haka?
Kuka ya fashe dashi "i dont know, mayb kuma shower gel dina yayi expire nikuma nayi using
yayi affecting dina, koma. dai miye ne ya illatani dayawa coz i cnt see clearly".
Na shiga uku na kasheshi, Salma ta fada aranta, sai yanxu tagane dalilin buguwarsa a bango
daxu. Kaman zatayi kuka tace "plz yaya tashi muje asibiti, i cnt see you liked this"
Kai ya girgiza.
"karki damu nariga nayi using wani magani na, kuma banaso Hajiya tasan ina cikin matsala
zata iya shiga tashin hankali"
Hannuta ya riko gabaya, "just tell me kin yafemin ko zanji dadi araina"
Sosai yabata Tausayi, wani irin haushin kanta take ji da muguntar da tamai, tace "yaya na yafe
maka dukdai ban rikeka araina ba, but plz kadaina cewa xaka mutu, you cnt leave me"
Ajiyar zuciya ya sauke, ya zauna akasa had'e da zaunar da ita yace "kinga no secret between
us, nafada mike zuciyata, do you have something to confess ?.
Shuru tayi, gabanta na faduwa, tanason gayamai itace silan komai tana tsoro.
Ji tayi yace taimaka min mu shiga ciki, kinsan yanxu na zama makaho.
Mikewa tayi jiki sanyaye suka fara takawa ciki, sun kusa shiga Palo Salma ta tsaya tace "yaya
karsu Hajiya su ganmu tare, miza muce masu ?
Yace "hakane ga wayata ki kira Faiza tazo, tunda na makance bakya so aganmu tare, nasan ita
komin rintsi she wil stand by me"
Cire wayar yayi aljihu ya mike mata, kin karba tayi tace "wasa nake fah"
Aranta kuwa tace "wana hauka ya kaini kirama wannan bazawarar"
Ciki suka shiga suka ci saa ba kowa a palon sai junai da hankalinta gabadaya yana kan Tv,
ahankali ta taimaka mai suka haura sama.
Masifa Annah tahau yiwa Hajiya adaki, akan yara sun girma har zasu tsofe taki aurar dasu
alhalin ga yammata har biyu a gida, Hakuri Hajiya tahau bata tace "Annah so nake Mujahid da
ita Ummi su shirya kansu sai ayi auran, nafison su tare akan da Jafar, da dukkan alamu kuma
suna son juna" Tasaki Annah taja tace "zancen banxa kenan, ina ruwan wani da shirin su ko boyayyar soyayyar
su, ni Ummi tafi kwanta min da Jafar, baki gansu dazun ba gwanin shaawa sun dace sosai,
kuma da bakinki kika cemin Marikin Ummi yafi son ta auri Jafar".
"Annah gaskia hakan baiyi daidai ba"
Ware ido Anna tayi tace "toh uwata saiki dakeni ai, kinsan dai na fiki iko da yaran nan tunda ni
uwar uban suce".
Hajiya tace "hakane, duk yadda kikayi daidai ne"
Washe baki Annah tayi tace "Dadina dake saurin fahimta, tunda yanzu nazo gidan yaushe zaki
tafi Maiduguri yi masu albishir din bayyanar Ummi da kuma batun auran, bana so adau lokaci,
gwara ayi buki tunda karfi na ".
Mamaki ne yakama Hajiya, sai kace tace mata zataje Maiduguri, kodayake dama tana da
niyyan zuwa.
Tace "sai wani watan na shirya zuwa"
Ware ido Annah tayi, tace "nan da wata daya, lailai salamatu bakya so naga auran nan, tab
aikuwa hakan bazai yuyuba gobe zaki tafi Maiduguri, dan kuwa ba zama nazoyi a garin nan ba,
Buki ya kawoni, ki shirya gobe ki wuce kafin ki dawo kuma zan nemi Daddyn Ummi mu tsayar
da rana" Hajiya kam bata iya cewa komai ba tsabar takaici, tasan zaman Annah gidan husuma kawai
zata hada ta tsangwamawa yaran gidan.
Allah ya kaimu gobe" hajiya ta fada, barin daki tayi ta koma dakinta tahau shirya kaya a akwati.
Daki Salma ta shigar da Mujahid, zama yayi gefe godon yace "i really need some sleep"
Jiki na rawa ta yaye comforter dake gado, kwaciya yayi ta rufa mai comfortee din sannan ta
zauna gefe sa tana kallon kyakyawan fuskar sa, idonsa rufe, yana fidda numfashi ahankali.
Ta jima zaune harta lura bacci yayi gaba dashi, da sauri ta mike tsadaf ta shiga bandakin sa,
showee gel din tadauka ta fito ahankali ta fice daga dakin, duk akan idonsa, abun da yakeson
Tabbatar wa kenan wato itace tamai mugun tar nan, yunkurowa yayi zaune hade da wrugi da
pilo, dafe kai yayi yace "what should i do na huce abunda kika min, most annoying part shine ko
kuka batayi minba ayadda taga condition dina"
Dogon Tsaki yaja, jin motsi kofa yasashi komawa ya kwanta hade da runtse ido, Salma ce ta
shigo ta karaso da sauri ta zauna gefen sa, pilo data gani akasa tadauka ta runguma tanai aika
mai kallon mai cike da so da kauna, batasan sanda bakinta ya furta I love you..., shuru tayi
saurin yi hade da kama bakinta, Allah yasa bai jita ba tafadi aranta. Tafin hannuta tasa ta rufe
fuskan ta.
Bude ido yayi ya kalleta hade da sakin Wani irin shuumin Murmushi wanda dashi kadai yasan
maanar sa, lumshe ido yayi cikin jin dadin kamshi jikinta dayake shaka.
[9/7, 12:38 AM] Xarah Bukar: Zuma Sai Da Wuta
~na~
©ҳaɾaɧ bųkaɾ
(Aunty Cute)
NAGARTA WRITERS ASSOCIATION
Allahu akbar kulu'nafsi za'ikatu mauti, Allah yaji kanki da rahma Maman besty Yar ficika. May
jannatul Firdausi be ur final destination.
59
Gidan shuru kowa lafe cikin turak'arsa, zuwan Annah sam bai d'ad'ara suba, ganin kowa ya
batsar da ita yasa ta dunga saka da warwara rashin nasiha da zata shukawa yaran gidan.
Ta b'angaran Salam kuwa yuni ranar ita ta funte hajun Mujahid.
Washegari da safe yakama ranar da Hajiya zata tafi Maiduguri, zuge zip din akwatinta tayi
sannan ta kalli Salma dake gyara gadon, kiran sunan ta tayi cikin wata murya bai abar tausayi,
dubanta Salma tayi had'e da amsawa.
Hajiya tace.
"Mujahid ya tashi daga bacci ?
Kunya ce takama Salma, duk'ar dakai tayi k'asa sanna tace "bangan shi a palo ba, k'ila bai tashi
ba"
Nisawa Hajiya tayi, ta karasa kusa gareta had'e da zaunar da ita kan gadon suna fuskan tar
juna, tace,
"Salma burina bai wuce na had'aki aure da mujahid ba, dan Allah kiyi hakuri kuyi sorting
difference dinku kafin nadawo, nasan kuna san junanku, i just dont know miyasa kuke nunawa
juna k'iyayya"
Shuru Salma tayi tana wasa dayan yatsun hannayan ta.
Hajiya tacigaba.
"wani abu daya da mujahid ko yanasan abu hardly yake nunawa, saboda yadda ya d'auki
kanshi yafi karfi ko wana abu, amma deep down he really carez, sometimes saiki kiga dan
hakkin daya raina yana neman tsone mai ido"
Murmurshi kawai Salma tayi, ganin haka yasa Hajiya tadan ji sanyi aranta, fitowa sukayi Salma
biye da akwatin suka shiga dakin Annah, sallama Hajiya tayi mata suka fita haraban gidan.
Jafar da Junai tsaye bakin motar suna jiran Hajiyan, da ganinta Junai tahau kukan zata bita,
dakyar dai Hajiya ta lallab'ata tayi shuru sannan ta shiga motar, Driver dake zaune ciki yajata
suka wuce.
Sabon kuka junai tahau yi ayayinda Jafar sai bata baki yake tana k'ara tunzura da kuka
shagwab'a, Salma kam murmushi tayi ta juya ciki ta barsu nan ganin abun nasu bana karewa
bane.
Kitchen ta nufa tadau Breakfast din Mujahid tahaura sama dashi cikin sauri gudun kar Annah ta
cafketa, ahankali ta tura kofar Palon ta hange shi can nesa kwance kan 3 sitter yana kallon nta
news. Mamakine ya kamata, mai ciwon ido da kallan Tv, Sallama tayi ta tsaya nan inda take.
Mikewa zaune yayi ya kalleta sannan ya amsa sallaman, takowa tayi ciki tana kallon idonsa,
ba laifi idon ya koma normal said'an kumburi dabaza arasa ba.
Murmushi tace "yaya harka tashi ? Karashe maganar tayi tani kai mazauninta kan kujerar
dayake zaune sannan ta ajiye abinci kan side table din gurin.
Murmushin kasaita ya sakar mata, irin murmushin nan dake fizgar zuciyan wanda akayi wa,
kallon juna sukayi for some seconds zuciyoyin ko wanansu harbawa yake, kowa da abunda