Author : Zarah Bukar Category : Tknovels
[9/7, 12:35 AM] Xarah Bukar: *Zυмa*
ѕaι da wυтa
na
©хaraн вυĸar
®Nagarтa Wrιтerѕ Aѕѕocιaтιon {NWA)
ѕpecιal тнanĸѕ тo ѕa'eed вeвejι
ѕpecιal greeтιngѕ тo мy вeloved ѕιѕтo Samrah (ĸιna raιna ĸυllυм, ιlyѕм❤)
ғanѕ ĸυyι нaĸυrι da gajerυn pageѕ da zagυ ganι.
(01)
Su hud'u ne zaune cikin had'add'an office dinsa. Ko wanne sanye da kayan yan sanda, saishi
na biyar dinsu dake sanye cikin Charcoal Gray and navy blue suit, kakkyawa ne mai cikar zati,
kalan fatar sa wankan tarwad'a, ak'alla zai kai kimanin shekaru talatin da bakwai a shekaru.
Tattauna issues suke game da ta'addanci da satan mutane dake addaban kasar gabadaya. Sun jima suna tattaunawa, daga bisani mik'ewa sukai had'e damai sallama suka bar office din.
Guntun Tsaki yaja hade da kallon wayarsa dake ruri kusan awanni da suka shud'e, hannu yakai
kan desk din yadau wayar hade da dubawa, miss call biyar yagani na Aunty B da na Hajiyar su.
Dafe kai yayi cike da tsananin takaicin sanin dalilin kiran. Tsaki ya saki had'e da janyo side
drawer na desk din ya fiddo file mai rubuce da sunan Ummi ajiki da stamp din missing daga
sama, bud'e file din yayi yanai dubawa yaji an turo kofar office d'in, bai dago ba yacigaba da
zabgarsa.
Kyakyawan saurayine mai kimanin shekaru talatin da uku ya shigo, bai karasa ciki ba ya tsaye
bakin k'ofar, fuskar sa ba walwala.
"Morning sir"
Ya furta atakaice.
Ba tare daya dago ba.
"Salim Abbas right ?
"Yes sir"
Salim ya amsa cike da haushin yadda ya ambaci sunanshi cikin salon rainin wayo.
Saida ya jima sannan ya Dago ya kallesa, wani mugun kallo ya aikawa mai.
"hope you're clean, kasan i dislike working with drunkard"
Kasa magana Salim yayi zuciyar sa na tafasa, ya mugun tsanan Ogan shi ba kad'an ba, banda
3 weeks suspension daya bashi ya dawo kuma yana neman wulakantashi.
Bai hankalta ba yaji ya cigaba da magana. "kana iya komawa position dinka, amma kasani next
time it won't be 3 weeks but a whole life time".
Juyawa Salim yayi ya fice daga office d'in batare dayace kanzil ba banda tafarfasa da zuciyar
sa yake.
Shi kam gogan cigaba yayi da duba file din, hotunan Ummi dake ciki yad'au yanai dubawa,
kallon k'urilla yakema hoton da tunanin ina zai nemota, asalima she is 10 years a hoton. Acewar
hajiya kuma zatakai 19 by now. Saidai babban takaicin sa bai wuce ta ina xan fara binciko taba,
a iya sanin sa a Gombe ta b'ata ba Abuja inda yake aiki ba. Rufe file din yayi hade da maida ta
cikin drawan sannan ya mike ya fice daga office din. Inda maajiyar motarsa kirar formatic 350 ya
nufa ya shiga sannan yama Aunty B text msg na gayanan zuwa. Jan motar yayi bai zarce ko ina
ba sai gidan su dake Asokoro na cikin garin Abuja.
***
Shingid'e dattijuwa Hajiya Laurat take bisa lausassiyar doguwar kujeran palon, hannuta rike da
waya tana sauraran kiran d'anta da tun daxu take danna mai kira baya picking. Babbar diyarta
Aunty Bilkisu ta fito daga kitchen hannunta rike da mug tanai kurban shayin dake ciki, karasa
shiga palon tayi tanai kara duban agogon hannuta hade da takaicin rashin karasowa Mujahid,
gashi kuma tana da patience dake jiranta a asibiti.
Zama tayi kusa da Hajiya hade da kwantar da murya tace,
"Hajiya a hakura kawai, wanan wahala ce kawai zaki d'aurawa Mujahid, yarinyar nan fah
dakanta tabar gidan Ubanta, babu wanda ya koreta, gaskia nidai banga amfanin nemo taba.."
Mugun kallo da Hajiya ta watsa mata yasa tayi azaman tsuke kalamanta.
"Bilkisu ki kiyayeni, na dauka kece babban mai hankali ashe baki da hankali, shiyasa duk cikin
ku Jafar yafi yemin, shine kadai ke fahimta ta"
Shuru Aunty B tayi ba tare da tace kanzil ba, saima tsumu tsumu da tayi kamar wace aka tsamo
cikin ruwa. tasan halin tsohuwar su yanzu saita dau zancen da zafi ta inda take shiga ba tanan
zata fita ba.
Daidai bakin k'ofar palon ya tsaya chak sakamakon kalaman Hajiya na karshe daya tsinkawo a
kunnuwansa, sallamar daya ke kokarin yi kasawa yayi jin tanai magana cikin daga murya da
fusata.
"Muddin bai nemo Ummi ba saina mugun b'ata masa rai, tun yaushe mukai zancen dashi amma
har yau babu feedback kuma lokaci na tafiya burina kawai ta bayyana na hadashi aure da ita"
Tashin hankali da firgici ne suka bayyana a fuskarsa, ji yayi gabadaya jikin ya sank'ame kamar
jini bai zagayawa cikin jijiyoyin jikinsa. Dakyar samu karfin motsawa,
ahankali ya fara taku baya sannan ya juya da azama ya koma inda yayi parking motarsa ya
tsaya hade da dafe kanshi.
Ruwane ya cinye Aunty B da mamakin kalaman Hajiya, Ummi data baiwa iskanci baya shine
Hajiya take kokarin kakkab'awa kaninta, duban hajiya tayi, ganin lailai ba wasa take ba yasata
fara kirkiro murmushin dole.
Dafe yake da kanshi kaman xaiyi kuka, gabad'aya Hajiya ta daura mai zafi, bai taba yadda
Hajiya batason shi ba sai yau dayaji abunda take shirin aikatawa. Sai dai yayi alwashin hakan
bazai faru dashi ba, harga Allah yana da niyya nemo Ummi saidai kudirin Hajiya yasanya bazai
nemo taba saidai ma yayi fatan duk inda take a dosar kasar kar ta bayyana. Hannayan sa biyu
ya hada had'e dakaiwa glass din motar noushi cikin fusata yanai huci. Horn din mota dayaji
yasanya shi waigawa kallon motar data danno kai cikin gidan.
"Ya salam, from one Problem to another" ya fadi aranshi hade da saurin kawar dakai gefe
tamkar bai ganta ba, cikin ranshi addu'a yake Allah yasa karta iso garesa.
[9/7, 12:37 AM] Xarah Bukar: *Zuma*
ѕaι da wυтa
na
©хaraн вυĸar
{02}
Murmushin jin dad'i ta saki sakamakon ganin shi da tayi, taso su hadu da safe kafin ta tafi skull
saidai tuni ya rigata sammako.
Gefen motarsa tayi parking motar ta kirar corolla xL sanna ta fito, jikin ta sanye da uniform din
Premiere acedemy, short gray skirt da white long sleeve mai hade da maroon necktie.
Da murmushi ta doso shi, ganin ba fuska ya sanya ta shan jinin jikinta, gabanta na dukan uku
uku.
"Ina kwana ya Mjay
Mugun kallo ya aikamata tare da kara shan magani.
"Da ban kwana ba zaki ganni anan"
Tsura mata idanu yayi jiran amsarta.
Kai ta girgiza.
"Naga kaman ranka abace.." Tayi shuru idonta ya ciko da kwallah
Gyara tsayuwar sa yayi hade da kokarin bude kofar motar yana fadin.
"bana hanaki shiga hurumi naba, waiku matan nan miye matsalan kune".
Guntun saki yaja cike da takaici yadda mata ke bada kansu, balle yar karamar yarinyar dake
tsaye gaban sa, shiyasa har ilah baiga perfect woman data dace dashi ba.
Marairace murya tayi tace "yaya kayi hakuri, am not happy da yadda na ganka ne.
Tsaki yaja, tsayawa mata magana bata lokaci ne, shigewa yayi motar hade da janta yabar ta
nan tsaye jiran tsammani.
Sakin baki tayi tanai kallon motar harta fice daga gidan, Kaman zatayi kuka ta wuce Jiki
sanyaye ta fara takawa cikin gida. Duk a gaban ido Jafar, daga windon saman dakinsa ya
hango draman su, tabe baki yayi, aranshi yanai fadin duk shishigi da takemai bashi zai hana ya
gwasaleta taba, cusa kai ba kwarjini. Daukar wayar sa yayi ya fito daga dakin hannusa rike da
briefcase da suit jacket, cikin sauri ya sauko daga stair din, inda Hajiya take ya nufa hade da
mata sallama daman tuni tasan da tafiyar sa kaduna akan wani case dinsu can na kare hakkin
mutane, addu'ar saukar lafiya da fatan alkhairi tahau zuba mai, Aunty B kuwa shuru tayi gudu
kartace wani abun tasha fada.
"Aunty kina nan ashe baki wuce ba" Jafar ya fadi.
"Yayanka ya shanyamu, nima tashi xan na wuce" Mikewai tayi tana ci gaba da fadin "hajiya
nikam na wuce aiki, sai wani zuwan"
"A sauka kalau, ina gaida yaran" acewar hajiya cikin kota kula da yanayinta.
Daidai Bakin kofar sukayi kicibis da ita zata shigo, ganin aunty B yasata sakin fara'a hade da
gaidata.
Cike da faraa ta amsa mata hade dacewa "Junaina harkun tashi so early"
"Aunty yau bamu da exam, chilling da friends ya kaini skull, gajiya nayi na dawo, mun kusa ma
gama Waec din"
Aunty B tace "Allah ya baku saa.." Cikin saurin tayi maganar sakamakon wayarta data shiga
ruri, hannu ta daga mata hade da ficewa tanai kokar daukan call din, Sai sannan ta lura da Jafar
dake tsaye yanai kallonta, da alamun bashi da shirin yi mata magana.
"ya Jafs sai ina haka rike da briefcase" ta fadi hade da karasawa ciki, zama tayi kusa da hajiya
cikin salon yauki da shagwabe fuska..
Yace "idan kinason sani ki kirani awaya" ficewa yayi batare daya jira cewar taba.
Kaman xatayi kuka ta kalli Hajiya tace "Hajiyata waini miyasa su yaya keson kwasaleni, ya jaf
da mukafi shiri saikiga wataran ya canxa min".
Dariya hajiya tayi.
"banda ke Auta idan sun kwasaleki, saiki fita batun sun kema ki sharesu"
Kai ta girgiza.
"Gaskia bazan iya share Ya mjay ba koda ma ace zaiina dukana kullum"
K'ura mata ido Hajiya tayi cike da mamakin abunda Junaina ta fad'a.
Aranta tace "Auta mujahid ya miki nisa, wannan yarinta gwara ki ajiyeshi gefe".
Afili tace "bansan shirme tashi maza kije ki cire uniform" shagwabe fuska tayi hade da turo baki.
"Kai hajiyata daga magana sai korata awayance"
Harara hajiya takai mata ba shiri ta mike ta wuce dakinta dake nan kasa.
****
Reckless driving da take bisa titin ya sanya mutane da dama da suka san ciwon kansu
matsawa gefe sunai bata guri. Gudu take shantakawa iya san ranta hade da kyalkyale dariya
ganin yadda kowa ya bata sarari, daidai data karaso traffic light ya nuna red, dogon tsaki taja
tayi gaba ba tare data tsayar da motar ba. Bata ankara ba kiris ya rage ta bugi motar data
danno, cikin kota kula da abunda ya faru ta fizgi motar at 360. Gudu take sosai can ta lura da
motar data kusan bigewa na biye da ita, tsoro ne ya kamata kasancewar last week kadai Daddy
ya gargadeta da reckless driving, bata daddara ba kuma takeyi, fatan ta Allah yasa ba yan road
safety bane, dan dakyar daddy ya amso mata motar ta da sukayi seizing kwanakin baya.
Yadda take sharara gudu haka yake binta a baya, baisan waye acikin motar ba amma yayi
alwashi koyawa koma waye lesson, dama ranshi a bace yake yasamu scape goat dazai huce
haushi akanshi. Ringing din wayarsa ce ta katse mai hanzari, murmushi ya saki ganin wacce
take kira, dauka yayi hade da sakawa a speaker. "Fa'iza am driving, zan kira ki later.
Tace "Mjay karka manta by 2pm zaka zo dauka na".
Bata rai yayi yace "you know am not your driving, kuma am not a jobless man, bazan iya zuwa
ba ki shiga cab" katse call din yayi but deep down yasan dole yaje yayi picking dinta bayason
tana shiga motar haya. Kaman kiftawar ido yaga wayam babu motar dayake bi, dukan sitiring
yayi hade dayin U turn ya kama hanyar komawa office.
Ajiyar zuciya ta sauk'e ganin motar dake binta tayi gaba, ahankali tayi reverse ta fito daga
supermarket inda ta shiga tayi parking, da gudu ta kuma fizgar motar, Karar shigowan msg
wayarta tayi, da azama ta duba.
"Salma kiyi sauri, Malama Fa'iza ta karaso, da alamun zata dau Attendance"
Dogon Tsaki taja hade da duba tym, 12 to 2 suke da lecture dinta, amma dan maita stupid
malamar harta shiga hall just 12.05, koda yake daidai take da ita. Wani mugun wuta ta baiwa
motar, bata zarce ko ina sai gwagwalada Abuja.
Cute xara'u
[9/7, 12:37 AM] Xarah Bukar: [18/07 12:25 PM] aυnтy cute хaraн :
*Zuma sai da wuta*
~na~
©ҳaɾaɧ bųkaɾ
Masu k'orafin pages sunyi kadan kumin uxuri, kuyi manaji da iya abunda xan iya baku. Idan
nasamu lokaci zan kara hannu.
*Wannan shafin Naku ne House of novella da dandalin makaranta, Nagode matika da kaunar
ku, ILYA*❤
3 - 10
Parking tayi daidai multi purpose hall inda suke da lecture. jakar ta dake ajiye gefe ta dau ta
fiddo kayan kwalliya ta kara gyare fusk'ar ta dashi sannan ta bud'e kofar ta fito, cikin tsadaf ta
fada ajin gudun kar Malama Fa'iza taji shigowarta kasancewar gabad'aya hankalin ta na bisa
allon datake rubutu, kallon banza yan matan ajin suka bita dashi, bata damu ba ta karasa inda
maza sukafi yawa ta zauna a sit dinta da tuni sun kama mata.
Murya kasa kasa, abokinta na gefen ta yace
"Salma yau mutumiyar ki rashin kirki take ji, ta hana kowa rubutawa wani attendance"
Ajiyar zuciya ta sauke, zatayi magana kenan, Fa'iza ta juya tanai fadin sunan topic dinsu na
yau, hada ido sukai tayi saurin mazewa kaman ta jima da shigowa ajin.
Cikin rashin damuwa da ganinta Fa'iza ta cigaba da lectures dinta, tana gamawa tahau kiran
attendance d'aya bayan d'aya bayan ta gargardi kar wata shegia ko shege ya bita office k'orofi,
tana gamawa ta fice daga ajin.
Dariyan takaici Salma tayi, sam bataji haushi ba saidai shegia data ambata yay mugun b'ata
mata rai tasan kuma babu tantama da ita take, tunda kowa was present banda ita.
Ko hira bata tsaya yi da abokanta ba, ta koma motarta taja ta at 360, department dinsu ta zarce
ta fito tashiga ta tsaya bakin kofar office dinta. Hannu takai bisa kofar taji ta a bude, tsulem ta
fada tanai karewa ko ina kallo sannan ta zauna tanai kallon hoton wani guy dage jikin frame
akan table din. Hannu takai zata dauka taji motsi mukuli a kofar, adan tsorace ta duka kasa
hade da boyewa under table.
Tsaki fa'iza tayi
"garin sauri ashe ban rufe kofar ba" ta fadi.
Turo kofar tayi ta shigo ta ajiye jakarta sannan ta shiga toilet dauro alwala.
Mik'ewa tsaye salma tayi cikin sauri tadau biro dake gurin ta rubuta "ba wani shege kowa da
uban" ajikin wata takarda dake gurin sannan ta sure frame din hoton tayi waje ahankali, da gudu
ta karasa cikin motar ta hade da sauke numfashi tanai kallon hoton, guy din bai wuce 36 ba,
saidai kuma yayi wa Fa'iza yaro idan ma ya girme ta kadan ne "Shi kuma wanan ya rasa waxai aura sai tsohuwar nan, lailai malama dole kanki yayi hayaki"
Surutai tahau yi ita daya.
Bangaran fa'iza kuwa, tana fitowa sallaya ta shimfud'a tahau sallahn azahar bayan ta idarne ta
koma kujera ta zauna saidai wayam babu hoton data saba kalla akullum idan ta zauna, baza
ido tayi tana nema taci karaf da abunda ke rebuce, mamaki sosai ya kamata tahau cigaba da
duban hoton, zuciyarta na zargi wani abu rashin tabbatar wa yasa ta kawar da tunanin.
Karfe 2 da minti goma ya karasa makarantar, parking yayi a gaban department dinta sannan
yadau waya kokarin kiranta.
Jakarta ta zuge ta cilla frame din ciki, sannan ta juya yin reverse, Motar dazu dake binta tagani
ya rufe mata baya, guntun tsaki taja hagonsa zaune cikin suit batare da jacket dinsa ba, kansa
sunkuye yanai duban wayarsa.
"kut ashe ma ba officer bane, naketa kokarin boye kaina, am sure sona yake datx y yaketa bina,
aikuwa xan koyamai hankali"
Dogin tsaki taja had"e da bud'e kofar afusace.
Yana zanune yaji ana buga mai glass, bai dagoba sai wining glass kasa da yayi dan gabadaya
hankalinsa nakan nambar Faiza dayake kokarin turama sakon ya iso.
"Uban wayace ga dinga bina duk inda na ratsa, ko an gayama so dolene, ko kuma ma dai ince
Saceni kekeson yi dan kasamu kudi"
Ta fada cikin karaji da zare idanu,
Chak yayi da wayan ahannu, bai iya dagowa ba saboda kalamanta dayaji bambara kwai wai
So, shi idan akwai abunda ya tsana bai wuce kalmar so va balle soyayya, who d hell is she
dazai ma sota balle ya bibayeta, bai gaba zancen zuci ba yaji tana fadin.
"Kodayake nasan maganin ka, am calling the police saina ga ubanwa ya tsaya ma" wayarta
dake aljihun wandon ta tadauka tafara dailing namba.
Shikam gabadaya ya gaba fusata, ba namijin daya taba mai cin zarafi irin haka balle mace,
mata daya daukesu kanana k'wari wanda daga kuka banza sai shagwaba suka iya, murmushin
dayasan munafarsa ya saki, sannan ya turawa faiza sakon ta fito nan da 30 min, dan kuwa
zaman jiran dan sanda da zaizo arresting dinsa xaiyi.
Matsawa gefe Salma tayi tana wayan.
"Ya salim dan Allah karka jima, kayi sauri ka karaso kafin ya gudu.
Yace "Pretty karki damu, yanxu zaki ganni, make sure kiyi keeping dinshi bizi kafin naxo".
"I'll' tafadi.
ta katse wayan.
Maida dubanta tayi garesa, saidai har yanxu ta kasa tantance fuskasa dake duk'e, kuma
window ma yayi wining dinta sama.
"Laila ma mutumin nan, mugun nan rainin wayo ne, tayama xanyi keeping dinsa busy alhalin
baima kallo ni" tsaki taja tahau safa da marwa a gurin.
"Bari ma dai na kalli useless girl dinnan"
ya fadi aransa, juyawa yayi ya kalle ta, yarinya ce da iyakacinta 18 to 19, kyakyawa black
beauty, jikinta sanye da white pencil jean da red top, da rad hulan yemi alade daure bisa kanta,
kai komo take tanai duban agogon hannuta.
Mugun tsaki yaja