Author : Zahra Muhammad Surbajo Category : Taskar Novels
da ƙuna,bana baƙin cikin fareeda ta samu cikiba,na gorin da labeeb ɗin yay mata da kanshi.
Kashe wayarshi yayi be jira tayi maganaba ya koma ɗakin ransa fess matarsa nada ciki.
Fadeela ranar yadda taga rana haka taga dare bacci ya ƙauracewa idanunta,kuka take tana kaiwa Allah kokenta.
*********
Sai washegari aka sallamosu,inda uwar siyayyar kayan haihuwa da akayi zaku ɗauka yanzu zata haihu.
Haka gidan suka cikashi maƙil anata murnar,haihuwar da zaayi nan da watanni tara tara masu zuwa.
A sanyaye fadeela ta shiga part ɗin na fareeda san mata sannu su kuma gaisa da hajiya.
Tunda ta shiga danginsa ke binta da kallon banza sabida kawai bata haihuba.
"sannu fareeda ya jikin Allah ya baki lfy"cewar fadeela asanyaye.
.Wata uwar shewa suka ɗauka sauran pan uwan labeeb ɗin sannan sukace"ay ciwone da akeso wannan bana fatan asamu sauƙi bane na fatan Allah ta inganta ya raba lafiyane muzo musha suna gidan ɗan uwanmu muzo da motar kwasar kashi akwashe kashin da akai shekara da shekaru anyi,dan yanzu permpers ɗin babybzamu dinga cika sokawen dashi."ayko watacshewar suka sake sawa suna dariya gamida tafawa.
Bata kulasu ba ta gaida hajiya,da ƙyar ta amsa mata,sannan tace"ji yarda ta wani marairaice kamar wata ta kirki,kai kace itace me cikin".
"yimata uzuri hajiya maybe kashi takeji kinsan nan tafi ƙwarewa"cewar ɗaya daga cikinsu.
Hawayen datake ɓoyewa ne suka shiga biyo idanunta da gudu tabar sashin tana kuka kamar ranta ze fita,uwa uba gashi agaban labeeb aka mata wulaƙancin amma be uya cewa komaiba se wasa take da hannun matarsa fareeda.
Kumude je zuwa.
*bana adding a group dan haka kar atambayeni,in so kike in saki to ki biya 300*
*masu son zama cikin group ɗina suna karanta paid book ɗina,tsawon shekara guda to ku biya 1500 insaku a group ɗin da bazaki sake siyan littafina ba se kin shekara.*
FREE NE HAR ƘARSHE
07044600044
[12/9, 14:53] zahrasurbajo1: https://chat.whatsapp.com/I5Nm6R0rL6nIwqbk8MmK1u
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*MAI MAGANIN MATA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*FREE BOOK FROM 1 TO END*
*Zahra Surbajo*
*ME BUƘATAR COMPLETE DOCUMENT ƊIN SHAAWARSHI NAKE 500 NE KITURO KUƊINKI ABAKI*
*HARIJA CE,sabon littafine dazan yishi akan kuɗi 500 kacal,karku bari abaku labari,yazo da salo na musamman shima meso ze iya turo kuɗinshi yanzu ta acct kawai*
*zahra muhammed nasir 2084024749 UBA*
*07044600044*
*24*
Ranar fadeela tayi kuka gamida danasanin shan magungunan mata marasa amfani data dingayi abaya da har ya janyo mata matsala gagaruma a mahaifarta.
ta miƙawa Allah lamarinta san shine maganin kowacce irin damuwa.
*******
Wasa wasa saida labeeb ya kwashe sati biyu curr tare da fareeda yana bata kulawa ba tare da ya bibiyi fadeela ba.
Itako fareeda abun nema ya samu,haka ta miƙe ƙafa yau tace wannan gobe tace wannan shi da ƴan uwa da mahaifiyarsa suna biye mata.
Zaune take duk ta rame tayi baƙi a ƴan kwanakin tayi zurfi cikin tunani ya buɗo ƙofar ya shigo.
Firgigit ta ɗago kanta dan taga ko waye me shigowar,ganin labeeb ne jikinta har ɓari yake ta durƙusa kan guiwowinta tana masa sannu da zuwa.
Ba yabo ba fallasa ya amsa mata,sannan yace"ki yiwa fareeda faten tsaki yanzunan shi takeso ita kuma bata iya ba zan dawo in ɗaukar mata."ya faɗi cikin tsare gida.
Fadeela wacce yanzu labeeb ɗin tsoro yake bata da sauri ta amsa masa da "to zanyi yanzu insha Allahu,saidai tsakin senaje can unguwarmu zan samo kuma motata babu mai aciki ko zaka tura megadi?"ta faɗi kanta aƙasa.
"lallai baki da hankali,watakan intura megadi inbar uwar ƴaƴan nawa agidan ba me gadi ko,to inke bakisan darajar haihuwaba to mu munsani,ki hau napep kije ki dawo ba dole se amota ba"yana kaiwa nan ya fice abinsa.
Wayyo jikinta har ɓari yake ta faɗa ɗaki ra ɗauko hijabinta da kuɗin mota dana siyan tsakin ta fice daga gidan.
Koda taje unguwarsu ba wanda ya ganeta sabida fuskarta arufe take da facemarsk har ta siyo ta dawo.
Tana girkin jikinta na rawa gudun kar yace ta ɓata lokaci.
Ta kammala ko se ƙamshin daɗi yake yi,ta juye a cooler sannan ta ɗauka ta kai.
A falo ta samesu fareeda na zaune kan cinyarshi,daga ita se ɗan threequater wando ,babu bra ajikinta labeeb na surcking boobs ɗin nata tana mai ƴan koke koke.
Fadeela wacce tayi mmkin ganinnhakan dan tayi sallama before tashigo kuma su suka bata damat shigar.
Ƙasa tai da kanta taje ta ajiye tace asanyaye"ga faten"
"To tashi kisha baby dan babyna yasamu shima kinsan namiji nakeson ki haifamin me kama dani"
Noƙe kafaɗa tayi tace tana ruƙoshi"muje ku fara gaisawa da babyn tunda ka tsokanoni"
Fadeela,miƙewa tayi tana haɗa hanya zata fice daga falon,daka mata tsawar da labeeb yayine yasa ta tsaya ta juyo,ɗaike yake da fareedar a hannunshi,yace"ki zuba mata ki fifita mata zamu shiga ciki mu fito"
Ba musu tayi kamar yadda yace su kuma suka wuce ɗaki.
Tana jiyo kukansu inda tasa aranta ba macen da zaawa cin mutunci irin wannan,tayi kuka tayi kuka ba adadi.
Tana gama fifitawar ta fice daga falom tana kuka.
Tana shiga falonta taci karo da murja wacce shigowarta kenan tana ta sallama.
Da gudu ta faɗa jikin murjar tana kuka,kamar ranta ze fita,bata hanata ba saida tayi me isarta sannan tayi shuru tana sauke ajiyar zuciya.
Ƙare mata kallo murja tayi sannan tacs"fadeela baki da lfy ne?"
"Lafiyata lau murja,saidai bani da kwanciyar hankaline"daga haka ta kwashe duk abinda ake mata tin farko ta faɗa mata har zuwa yanzu data ganta tana kuka.
Tun kan ta ƙarasa murjar ke kukan tausayinta,da ƙyar ta rarrashi kanta race a raunane"fadeela a farko de ina me baki haƙuri bisa wannan cin mutunci da ake miki,kiyi haƙuri jarabawace komai ze wuce"
"murja na fara tunanin ince ya sawwaƙemin dan na gaji da zama dashi wlh wulaƙancin yayi yawa murja"ta faɗi tana kuka.
"ko nice ke hakan zanyi amma dan Allah kiyi haƙuri ki jure,komai ze wuce ina baki tabbaci shi kuma labeeb beyi halacciba wlh."
"Ki samu lokaci fadeela ki shirya muje wani asibitin aƙara dubaki tunda yanzu kin dena shan tarkacen ko Allah zesa adace".
murmushin ƙarfin hali tayi tacr"to murja amma ni na jima da fidda rai wlh"
"Rahamar Allah yawa gareta bata ƙarewa fadeela"
Sum jima tana kwatar mata da hankali kamin su sa ranar zuwa asibitin tai mata sallama ta tafi.
********
Koda sukaje asibitin aka sake gwadata dsame problem de sannam kuma har da ƙarin mahaifa take dashi inda likitan ya ƙara da cewa"haihuwa yake aciki,kuyi ƙoƙari ay mata cs acireshi,wataƙila im an cire zata iya haihuwa,amma inba haka ba girma zetayi acikinta wanda ƙarshe se anci wiya sosai"
Fadeela rushewa tayi da kuka tana faɗin"Nasan nayi laifi Allah abaya amma yanzu na tuba Allah ka yafemin Allah karka ƙaddara ranar da zaa yanka cikina kabani lfy Allah na tuba"ta faɗi cikin matsanancin kuka.
"likita zamuje mu shawarci mijinta abinda yace to dashi zaayi amfani,zuwa sati na sama semu dawo"cewar murja.
Hankali atashe suka baro asibitin inda direct gidan iyayen fadeelar suka zarce.
Mamanta ta tsorata dajin matsalar ƴarta amma saita danne dan ta ƙarfafa mata guiwa,tacs "kidaure fadeela aljanna bata samuwa da sauƙi dole se an wahala a n daure."
"Mama kisani a addua dan Allah"ta faɗi cikinnkuka"
"Ina miki fadeela kuma insha Allahu gaba zakiyi dariya"
Sun jima agidan kamin fadeela ta sauke murja agidanta ita kuma ta wuce nata gidan.
********
Saida cikin fareeda yakai wata huɗu sannan labeeb ya dawo yana kwana a ɓangaren fadeela.
Shima sai yakai shabiyun dare acan kuma daga masallacin asuba yake wucewa can ɗin.
Koda tai masa maganar hakkinta na kwanciyar aure amsa ya bata da cewa.
"likita yace anaso a yawaita kwanciya dame ciki dan ɗan cikin yafi lagiya,to bazan iya dinga asarar sperm agunki ba,kiyi haƙuri zuwa ta haihu se ɓuci gaba amma hankalina mi yana kansune."
Shuru tayi bata ce komaiba.
Haka zancan asibiti ma cewa yayi ta bari in fareeda ta haihu ajr ayi batun aykin.
******
Cikin fareeda se ƙara tsufa yake tayinda baiwar Allah fadeela ƙarin mahaifa keta ci gaba ajikinta,gashi duk alamomin da likitan ya faɗi na in ciwon ya girma ajikinta duk tana jinsu,kullum kukanta take kaiwa Allah.
.
Kumude je zuwa.
*bana adding a group dan haka kar atambayeni,in so kike in saki to ki biya 300*
*masu son zama cikin group ɗina suna karanta paid book ɗina,tsawon shekara guda to ku biya 1500 insaku a group ɗin da bazaki sake siyan littafina ba se kin shekara.*
FREE NE HAR ƘARSHE
07044600044
[12/9, 14:53] zahrasurbajo1: https://chat.whatsapp.com/I5Nm6R0rL6nIwqbk8MmK1u
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*MAI MAGANIN MATA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*FREE BOOK FROM 1 TO END*
*Zahra Surbajo*
*HARIJA CE, Na sauya masa suna zuwa AJI DOWN
sabon littafine dazan yishi akan kuɗi 300 kacal, Amma karku bari abaku labari,yazo da salo na musamman shima meso ze iya turo kuɗinshi yanzu ta acct kawai,300 ne yanzu zuwa ranar goma ga wata ya koma 500*
*zahra muhammed nasir 2084024749 UBA*
*07044600044*
*25*
Yauma kamar kullum ta sake samunshi akan batun ciwonta.
"kataimaka muje asibitinnan aduba aga awanne mataki ciwon nan yake wlh bacci bana iyawa sabida yadda nakejin ciwon"ta faɗi hawaye na biyo idonta
Gyara zama yayi sannan yace"to ko fareeda me ciki tsoho tana iya bacci bare ke,nifa fadeela na fara gajiya gaskiya,tunda kikaga matata nada ciki kika ɗauki tsangwama kika sa aranki da baƙin kishi kuma wallahi sede ki mutu,ni nace kidena min mgnr ciwo kijira fareeda ta haihu"
Ɗago ido tayi ta dubeshi hawaye na fita a idanunta tace murya na rawa akaro na farko "labeeb!ni kake wulaƙantawa sabida zaka haihu,?ni fadeela?"
Tsaki yayi sannan yace"an wulaƙantaki ɗin haihuwa ƙaryace in banzace ke kiyi mana,look fadeela nifa bisa lalura nake zaune dake wlh kuma in kika cika takurawa wlh sakinki zanyi na gaji da mugun halinki"ya faɗi yana nunata da yatsa.
Kukan da take riƙewane ya ƙwace tako fashe da kuka tana faɗin "Allah kaine gatana"
Miƙewa yayi yabar mata falon zuwa na gimbiyar gidan,dan sati me zuwa zasu wuce canada acan zata haihu shi da ita da hajiya,to shirye shiryen tafiyar suke.
**********
Tunda yabarta be sake bibiyarta ba,sai ranar da zasu tafi,ya shigo falon ya sameta,cikin matsanancin ciwo dan jiya ko bacci batayiba sabida ciwon da ƙafarta ke mata,ga jini da yake zubo mata.
Da kyar ta amsa sallamarsa tace tana haki,"ka taimakeni labeeb ka kaini asibiti,wlh likita yace matuƙar na fara zubar da jini abu yayi tsamari kataimakeni"
Kauda kai gefe yayi,yace"ki kai kanki,danni yanzu ƙasar zan bari,ga wannan zasu amfaneki bayan baninan."yana kaiwa nan ya ajiye mata envlop kan kujera ya juya yayi tafiyarsa tana kwala masa kira wanda su hajiya dake waje sunnjiyoshi amma be waiga ba.
Koda ya ƙarasa gun su hajiya tambayarshi tayi"wai waccan karyar kiran me take maka?"
Ruƙo hannun fareeda yayi yace"hajiya nifa na gaji da ita wlh shiyasa na sawwaƙe mata,dan banso indawo ma in tadda ita agidana"
"Gwanda dakai wannan tunani da kanka dan zaku fi sakewa kaida matarka uwar ƴaƴanka"cewar hajiya tana murmushi.
Itako fareeda dan daɗi ji tayi kamar tai ihu,dan dama ƴar chadi ta bata wani haɗi,tace dazaran tayi amfani dashi labeeb zeji duk duniya tafiye mishi komai,kuma kanta ze iya komai,uwa uba zeji beson kowacce mace in ba ita ba.
Haka suka rankaya zuwa airport dan jirginsu ya kusa tashi.
********
Fadeela najin fitarsu ta kife agun tana kuka kamar ranta ze fita.
Amai ne yataso mata kan tayi wani yunƙuri tuni ta fara kelayashi a falon.
Tana yunƙurin aman taji wani irin kartawa a cikinta,zuwa can taji nishi na taso mata da ƙarfi,kukan jinjirin da taji ya karaɗe kunnuwanta ne yasata tsorata,wani nishin ta ƙaraji,ay setaji kuka yazama biyu,se kuma ta nemi kowanne irin ciwo ta rasa,
Allah kenan me maida abinda baze yiwuba ya yiwu,ubangiji kafi ƙarfin kowa.
Ido fadeela tabi jariran dashi tana kallonsu hawaye na biyo idanunta, tsananin mamaki yasa tama rasa abun cewa se kuka da kirari da takewa ubangiji....
Wayartace ta shiga ruri,da ƙyar ta matsa ta ɗauka,murjace,tun kan tai mgn murja tace"gani ƙofar gidanku kinanan in shigo"?
"Eh "kawai tace mata.ta ajiye wayar.
Murja na shigowa falon na fadeela ta dafe ƙirji tace tana ware ido"fadeela haihuwa kikayi,dama cikine dake,Allahu akbar!!"""ta faɗi cikin tsananin murna.
Zuwa tayi ta taimaka mata ta miƙe sannan ta shiga ɗakin fadeelar ta samo reza da zare,tazo ta yankewa yaran cibiya se alokacin ta lura ashe duka mazane masu kama da ubansu.
Rungumesu murja tayi tana kuka ta miƙawa fadeela wacce tun ɗazun kuka take ta rasa abun cewa.
Kallon yaran take kamar a mafarki tace "murja ki mareni dan Allah mafarkin dana saba yine "
Ayko marin nata tayi tace"gaskiyace wannan fadeela baƙarya bane haihuwa kikayi ƴan tagwayenki gasu nan masu kama da labeeb ashe ba ciwo bane fadeela Allah ne ya ɓoye abunsa"
Rungume juna sukayi suna kujan farin ciki.
Toilet ta rakata bayan ta tara mata ruwan wanka.
Kamin magriba murja ta gyare mejego da yaranta,gida se ƙamshi yake kamar baayi haihuwa acikiba.
Mahaifiyar fadeela murja ta kira taiwa albishir inda ta fashe da kukan murna
tana godiya ga Allah wanda ta jima kan ta yarda fadeelar ta haihu.
"wai labeeb ɗin bazaki kirashiba?"cewar murja tana murmushi.
"bani envlop ɗin bayanki induba saƙon dayabarmin daze fita ɗazu"
Miƙa mata murja tayi baki buɗe,
Kuɗine aciki dubu ɗari biyu se ƙaramar takarda wacce ta buɗe dan ganin meye aciki.
"ni labeeb na saki mata ta fadeela saki ɗaya in tasamu miji tayi aure"
Hawayen dake biyo idontane yasa murja amsar takardar da sauri,abinda tagani ya gigita.
Haka de sukaci kukansu suka ƴoshi daga ƙarshe suka tattara abinda zasu iya ɗauka murja tajasu a motar fadeelar takaisu ga ummanta ɗauke da saƙonni biyu fari da baƙi.
Comments shike bada ƙwarin guiwar yi
Kumude je zuwa.
*bana adding a group dan haka kar atambayeni,in so kike in saki to ki biya 300*
*masu son zama cikin group ɗina suna karanta paid book ɗina,tsawon shekara guda to ku biya 1500 insaku a group ɗin da bazaki sake siyan littafina ba se kin shekara.*
FREE NE HAR ƘARSHE
07044600044
[12/9, 14:53] zahrasurbajo1: https://chat.whatsapp.com/I5Nm6R0rL6nIwqbk8MmK1u
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*MAI MAGANIN MATA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*FREE BOOK FROM 1 TO END*
*Zahra Surbajo*
*HARIJA CE, Na sauya masa suna zuwa AJI DOWN
sabon littafine dazan yishi akan kuɗi 300 kacal, Amma karku bari abaku labari,yazo da salo na musamman shima meso ze iya turo kuɗinshi yanzu ta acct kawai,300 ne yanzu zuwa ranar goma ga wata ya koma 500*
*zahra muhammed nasir 2084024749 UBA*
*07044600044*
*26*
"wallahi mama ina faɗamiki ya saketa kamin muzo nan"cewar fareeda lokacin data shiga ɗaki bayan sun sauka a canada ta kira ƴar chadi.
Wata guda ƴar chadi ta rangaɗa sannan tace "ay na faɗa miki shifa laƙanin anyi amfani da mahaifar jaɓa ne ta yadda bazata haihuba kuma laƙanin baya karyewa inde ba haihuwa tayiba,toko kinga itako da haihuwa ay sede taga anayi"ta faɗi cike da jin daɗi.
"hmmm bari kedai mama ay wani abun semun dawo tukunna da magajin gidan,gani nake tun anan ze mallaka masa kusan rabin dukiyarsa"cewar farida cike da jin daɗi.
"Allah amin ƴata da munsha budiri"
Jin zaa shigone yasa fareeda kashe wayar,ta shige toilet dama wanka zatayi.
******
Ummar fadeela tayi kuka tayi kuka har saida ya koma na zuci ga farin ciki ga baƙin ciki at dsame time.
Murja tai ta bata baki har ta haƙura,
Ayko kulawa ta shiga basu bayan ta faɗawa ƴan uwanta batun haihuwar ta fadeela.
Washe gari gidan yacika fam da ƴan uwa fa ƙawayenta dan tayata murnar haihuwar da akayi,kowa se jajen rabuwa da mijinta yake mata.
*******
Yau fareeda ta tashi da ciwon naƙuda dan haka daga hajiya har labeeb aruɗe suke,
Motar asibitice tazo har gida ta kwashesu zuwa asibitin.
Nanfa aka shiga bata kulawar data dace,abunka da ƙasashen da suka ci gaba nan fa aka shiga taimakonta.
Hajiya na waje yayinda labeeb ke cikin ɗakin haihuwar yana riƙe da hannun fareeda yana mata sannu.
Duk iya bakin ƙoƙarinsu wajen ganin ta haihu amma abu yaci tura hakanne yasa suka buƙaci yasa musu hannu zasuyi mata cs.
Hankalin labeeb inyayi dubu ya tashi haka hajiya ma,itako farredar bata ma san sunayiba dan ta fara fita hayyacinta.
Haka jiki na rawa yasa hannun aka shiga da ita tiyatar.
Sun jima a ɗakin tiyatar kamin ɗaya daga cikin likitocin ya fito yana share gumi.
Da sauri labeeb yayi kanshi yana tambayar halin da ake ciki.
Riga ya miƙa masa da face marsk sannan yace masa yasa ya biyoshi ciki.
Ba musu yay sauri yasaks sannan ya marawa likitan baya.
bayan sun shigane ya hangi fareeda kwance rai a hannun Allah.
Ɗaya daga cikin likitocinne yace da labeeb"bamu da isasshen lokaci amma yazama wajibi mukira ka zuwa nan,dan abin ya tsoratamu,cikin dake jikin matarka batu na gaskiya ba ciki bane,fibrot ne,kuma anyi sakacin daya girma har ya tsaga mata mahaifa,dan haka mahaifarta ta lalace barinta ajikinta ma ze iya haifar mata da cancer mahaifa,to ashawarce akwai buƙatar inzamu ciro ciwon mu haɗo da mahaifarta,"
tunda likitan ke bayani labeeb ke masa kallon banza,alamun be gamsu ba hakanne yasa likitan kama hannunshi yakaishi inda fareedar ke kwance yasa aka buɗe inda ake aykin ya nuna masa ƙatotuwar halittar dake cikin se nishi yake abun ya riƙa sosai se feshin jini yake.
Yanke jiki labeeb ɗin yayi agurin ya sume.
Fitar dashi akayi su kuma suka ci gaba da aykinsu dan rayuwarta na cikin hatsari.
Suna kammalawa suka sa a bokiti,ciwon da mahaifar gaba ɗayansu.
Koda aka fito da fareeda da gudu hajiya tabi bayansu tana faɗin "kumim bayani me yasamu jikan nawa naga anfito da ɗana a sume?
Basu kulata ba sabida basajin hausa,har suka kai fareedar ɗakin hutu,dan ta samu ta huta.
Hmmmmm Allah kenan.
Comments shike bada ƙwarin guiwar yi
Kumude je zuwa.
*bana adding a group dan haka kar atambayeni,in so kike in saki to ki biya 300*
*masu son zama cikin group ɗina suna karanta paid book ɗina,tsawon shekara guda to ku biya 1500 insaku a group ɗin da bazaki sake siyan littafina ba se kin shekara.*
FREE NE HAR ƘARSHE
07044600044
[12/9, 14:53] zahrasurbajo1: https://chat.whatsapp.com/I5Nm6R0rL6nIwqbk8MmK1u
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*MAI MAGANIN MATA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*FREE BOOK FROM 1 TO END*
*Zahra Surbajo*
*HARIJA CE, Na sauya masa suna zuwa AJI DOWN
sabon littafine dazan yishi akan kuɗi 300 kacal, Amma karku bari abaku labari,yazo da salo na musamman shima meso ze iya turo kuɗinshi yanzu ta acct kawai,300 ne yanzu zuwa ranar goma ga wata ya koma 500*
*zahra muhammed nasir 2084024749 UBA*
*07044600044*
*27*
Se washe gari labeeb ya farka,kansa ke masa wani irin mugun ciwo da ƙyar yake ɗaga idanunsa.
Hajiya dake gefe da sauri ta ƙarasa kusa dashi tana kuka ta kamo hannunsa,dan tun jiya