Author : Zahra Muhammad Surbajo Category : Taskar Novels
ma kuwa baby,Allah miki albarka"
"Amin the priceless prince"
Daga haka taimaka masa tayi yayi wanka ya kimtsa sannan suka nufi dinning dancin abinci.
Canma santi kawai yake mata,tana masa dariya har suka kammala.
*******
A can kano ko Ƴar chadi tayi iya yinta dan ganin ta sakko da fareeda amma hakan yaci tura,shiyasa ta buɗe mata wuta.
Ayko da ike tana tsoronta da gudu tazo ta buɗe ƙofar ta fita tsakar gidan.
Ay kamar jiranta take tako fara faɗa"shashasha wacce batasan me takeyiba,nice fa na haifeki da kaina taya kike tsammanin zan cutar dake,koda ace duk abinda nayi ɗin laifine ay dan de kisamu kwanciyar hankali nayi,amma da ike baki da hankali agaban kishiyarki da mijinki kika yace min baya, dan haka dole yanzu muyi shiri na musamman tunda kinga ay ta kama gida,tunda tunda muka taho ay be nemekiba"
Itade shuru tayi batace komai ba dan zuwa yanzu ta fahimci dan ita tayi komai dan haka zata bi umarnin mahaifiyarta inde tanason tsira da mutuncinta.
Kumude je zuwa.
*bana adding a group dan haka kar atambayeni,in so kike in saki to ki biya 300*
*masu son zama cikin group ɗina suna karanta paid book ɗina,tsawon shekara guda to ku biya 1500 insaku a group ɗin da bazaki sake siyan littafina ba se kin shekara.*
FREE NE HAR ƘARSHE
07044600044
[12/9, 14:53] zahrasurbajo1: https://chat.whatsapp.com/I5Nm6R0rL6nIwqbk8MmK1u
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*MAI MAGANIN MATA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*FREE BOOK FROM 1 TO END*
*Zahra Surbajo*
Bisimillahirrahmanirrahim.
**
*ME BUƘATAR COMPLETE DOCUMENT ƊIN SHAAWARSHI NAKE 500 NE KITURO KUƊINKI ABAKI*
*HARIJA CE,sabon littafine dazan yishi akan kuɗi 500 kacal,karku bari abaku labari,yazo da salo na musamman shima meso ze iya turo kuɗinshi yanzu ta acct kawai*
*zahra muhammed nasir 2084024749 UBA*
*07044600044*
*19*
Saida fareeda ta kwashe kwanaki bakwai da tafiya,labeeb be nemeta ba,dan gaba ɗaya fadeela ta gama cikashi da soyayyarta,ko kaɗan beson rabuwa da ita,ko office a dole yake zuwa.
Fadeela yanzu ba faɗa ba hayaniya ta riƙe mijinta kam a hannuntw yadda takeso yake mata,ba tare datasha maganin mata ba.
Wanda hakan sosai yasa ta tunanin ajiye shan magani na har abada akaro na biyu.
******
Anata ɓangaren fareeda tun bataso mahaifiyarta tasata dole ta dawo tana so,shan magunguna kamar hauka,sabida ƴar chadi tayi imani da magungunanta fadeela kesha yasa be biyo sawunsu ba.
"fareeda zaman nan haka baze yiwu,dole musan abunyi,kina kallo yanzu da biyu ake shigowa gidannan dan aganki aga zaman me kikeyi to ni nagaji number mahaifiyarshi zaki bani"cewar ƴar chadi cikin damuwa.
"mama kar yaga kamar an haɗashi da itane aje baa gyara biyar ba a ɓata goma"ta faɗi a sanyaye.
"shashasha a haka aka ƙwace miki miji,ke komai baki iyaba se ankoya miki"
Number fareeda tabata ba dan ranta yasoba,se dan bata da yadda zatayi.
Bugu ɗaya ana biyu hajiyar labeeb ta ɗauka,bayan sun gaisane ƴar chadi tace"hajiya mahaifiyar fareeda matar ɗanki labeeb ce"
Ayko cike da faraa hajiya ta ƙara gaidata samnan tace"wlh munata ƙoƙarin zuwa Allah be nufa ba tunda abun na sauri akayi,gashi lokacin data tare nan naje yola bana nan,basuzo guna ba banje ba gunsu nima,suna lfy deko?"cewar gajiya tana murna .
"Allah sarki,yanzuma hajiya wata ƴar matsalace ta faru tsakaninta dashi,to tazo gida yau kwana takwas be zoba be kiraba shine yasa nace duk yadda akayi bakusan da maganarba"cewar ƴar chadi.
"amaryar labeeb ɗince har tayi yaji,me akayimata agidan to wlh bazan ɗaukaba,barni dasu zani gidan anjima gobe yana nan zuwa wlh kuma aba yarinyar haƙuri kuma kuyi haƙurin"cewar hajiya cikin faɗa
suna sallama ƴar chadi ta dubeta tace "to da kince kar akira yanzu ba gashi kiram yayi anfaniba"ta faɗi tana murmyshi.
Itade fareeeda ba baka sai kunne burinta be wuce taga mijinnata.
Itako hajiya suna gama wayar tasa driver yakaita gidan nasu labeeb kasancewar week end ce tasan zata sameshi agida.
Kumude je zuwa.
*bana adding a group dan haka kar atambayeni,in so kike in saki to ki biya 300*
*masu son zama cikin group ɗina suna karanta paid book ɗina,tsawon shekara guda to ku biya 1500 insaku a group ɗin da bazaki sake siyan littafina ba se kin shekara.*
FREE NE HAR ƘARSHE
07044600044
[12/9, 14:53] zahrasurbajo1: https://chat.whatsapp.com/I5Nm6R0rL6nIwqbk8MmK1u
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*MAI MAGANIN MATA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*FREE BOOK FROM 1 TO END*
*Zahra Surbajo*
Bisimillahirrahmanirrahim.
**
*ME BUƘATAR COMPLETE DOCUMENT ƊIN SHAAWARSHI NAKE 500 NE KITURO KUƊINKI ABAKI*
*HARIJA CE,sabon littafine dazan yishi akan kuɗi 500 kacal,karku bari abaku labari,yazo da salo na musamman shima meso ze iya turo kuɗinshi yanzu ta acct kawai*
*zahra muhammed nasir 2084024749 UBA*
*07044600044*
*20*
A falo suke fadeela tayi ɗaiɗai akan carpet shikuma yana mata tausa hajiya ta turo ƙofar falon ta shigo.
Da sauri suka waiga dan ganin waye yay musu wannan karan tsaye,ganin hajiyace da sauri dukansu suka miƙe,kowa na ɗan gyara suturar jikinshi
"kade yi asara wallahi labeeb,kadiba kaga yadda yarinyar nan ta maisheka wani soko wanda besan me yakeyiba kazauna kana ta mata tausa"cewar hajiya cikin fushi.
Ɗan rusunawa fadeela tayi tana sosa ƙeya tace"hajiya kiyi haƙuri bazaa sake ba"
"Dalla yimin shuru munafuka,kin kori yarinyar mutane, kin vaje agida ke game miji to wlh makircinki kankai ze ƙare,baki isa ki hanamin ɗa ƙara aureba wlh"
"Dan Allah hajiya kiyi haƙuri dan Allah fadeela ba saar kibace ki dena zantuka nan da ita,"cewar labeeb a sanyaye.
"yimun shuru shanyayyaye kawai ay dole kace haka,to ni ba zama yakawoni gidan ku ba wlh tun muna shaida juna ka kama hanyar kano kaje kazo da matarka banason iskancin banza"ta faɗi kamar zata dakeshi.
"hajiya dama bani na koreta ba dakanta ta tafi,dan haka hajiya dan ta gane tayi kuskure kibarta ta dawo ita kaɗai base najeba,dan tsawon satin nan guda inada meating wlh hajiya."Ya faɗi ba tare da yaji tsoron komai ba.
Shuru hajiya tayi na ƴan daƙiƙu,sannan ta dubeshi tace" kuma bazata ƙara sati agidan nasuba zansa mahaifiyarta ta dawo da ita tunda an zama ɗaya kai kuma ka turamusu kuɗi wadatacce daze kawosu gida."
"Duk yadda kikace hajiya"ya faɗi yana sosa kai.
Tsaki tayi ta juya ta fice daga gidan ba tare data kalli inda suke ba.
Tana fita labeeb ya kamo fadeela wacce tun ɗazu take ɓoye hawaye,ayko yana ruƙota ta faɗa jikinshi tana kuka take faɗin"prince bansan me yasa hajiya bata sona ba haihuwa bani na hana kaina ba,prince kaimata bayani wlh ni ina sonta tunda ta haifamin kai ka bata haƙuri komai ikon Allah ne"ta faɗi cikin matsanancin kuka.
rarrashinta yayi sosai sannan ta saki ranta suke fige furan ƙauna.
Kumude je zuwa.
*bana adding a group dan haka kar atambayeni,in so kike in saki to ki biya 300*
*masu son zama cikin group ɗina suna karanta paid book ɗina,tsawon shekara guda to ku biya 1500 insaku a group ɗin da bazaki sake siyan littafina ba se kin shekara.*
FREE NE HAR ƘARSHE
07044600044
[12/9, 14:53] zahrasurbajo1: https://chat.whatsapp.com/I5Nm6R0rL6nIwqbk8MmK1u
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*MAI MAGANIN MATA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*FREE BOOK FROM 1 TO END*
*Zahra Surbajo*
Bisimillahirrahmanirrahim.
*IN KINSAN A KADUNA KIKE KUMA KE BAZAWARACE MIJINKI YA MUTU KO AURENKINE YA MUTU,KO KE BUDURWACE DA KIKA GIRMA BAKIYI AUREBA DA KIKESO DOGARO DA KANKI,IYA ƘWARYAR BIRNIN KADUNA KAWAI,KUMIN MAGANA A 07044600044*
*ME BUƘATAR COMPLETE DOCUMENT ƊIN SHAAWARSHI NAKE 500 NE KITURO KUƊINKI ABAKI*
*HARIJA CE,sabon littafine dazan yishi akan kuɗi 500 kacal,karku bari abaku labari,yazo da salo na musamman shima meso ze iya turo kuɗinshi yanzu ta acct kawai*
*zahra muhammed nasir 2084024749 UBA*
*07044600044*
*21*
"Haba mama ay ba mutunci aciki ace na koma kuma da kaina ni kaɗai bezoba gaskiya nide bazan iyaba"cewar fareeda lokacin da hajiya ta kira ƴarchadi ta sanar da ita buƙatarta na adawo da ita.
"fareeda inaso kigane wani abu guda ɗaya shifa wannan auren baki kafu agidanba wanda ni kuma shi nake miki fata kisamu ki kafu ta haka zaki gagari kowa ciki harda shi kanshi bare wata mahaifiyarshi ki fahimta mana"
Shuru fareeda tayi tana juya abun aranta,daga ƙarshe de ta amince da buƙatar mahaifiyar tata.
50k labeeb ya turawa fareeda koda taga alert ɗin tayi mamaki,amma seta share bata ko kira ko sms tai masa ba.
Gyara na sosai ƴar chadi taiwa ƴartata duk azuwan seta sace zuciyar kowa acikin su.
Koda ƴarchadi tace zata rakata hanata tayi inda tace"mama inaso karki kuma shigowa gidana a yanxu kibari inkama ƙasa da kyau ta yadda intai miki zansashi ya ɗauki mataki,dan bazan jure rashin kunyar datake mikiba"crwar fareeda.
"To Fareeda na Allah tabbatar da alkhairi"cewar ƴar chadi tana rungumota.
Mota drop ta ɗauka har gida,inda ta shige part ɗinta,batare data ko kalli sashin fadeela ba.
Ɓangarenta ta gyara sosai,da sosai,sannan tai wanka da turarukan maganin mallaka da ƴar chadi ta haɗota dasu.
Abinda zataci ta samawa kanta,sannan ta ɗora girkin tarbar megida.
*******
Gidan wani abokinshi sukaje shida fadeela basu dawo gidanba se gab da magriba,inda me gadi yasanar dashi hajiya amarya ta dawo.
Ko kaɗan fadeela bata nuna tajima me akace ba bare ta ɓata ranta
Shiko tsalatu ya shiga,dan besan yazeyi dasuba,tunda fadeela besanar da ita amarya zata dawo ba,duk da ba laifinshi bane tunda shima basu sanar dashiba.
A ɓangaren fadeela yayi wanka yayi sallahyaci abinci amma be cika cikinshi sosai ba,sannan suka koma falo inda rabin hankalinshi nakan fareeda,dan be kyautaba dan yasan taji dawowarshi.
Ƙarfin hali yayi yace"baby ƙanwarkifa ta dawo ɗazu"
Gyara zamanta tayi sannan tace"barkanta da dawowa an barosu lfy ko?"ta faɗi ba tare data kalleshiba bare yaga wani fushi atattare da ita.
"Bari inje mu gaisa in na dawo to in kuma saida safe to aymim afuwa,"ya faɗi kamar yaron dake tsoron uwarshi.
Murmushi tayi ta shafo gefen fuskarshi tace"karka wani ji ka damu prince jeka kanka tsaye,Allah tashemu lafiya.kaga yau na huta da sukuwarka"ta faɗi tana shafo dick ɗin.
Dariya yayi ya riƙe hannunta yace "ay zan dawo baby bazan miki da wasa ba kuma"ya faɗi yana kashe mata ido.
Rakoshi tayi har bakin ƙofa,ya rungumeta sannan ya lalubi bakinta ya manna mata kiss,sun jima ahaka kamin ta ƙwace kanta ta koma ciki shi kuma ya wuce yana ɗaga mata hannu.
Da sallamarshi ya tura ƙofar falon ya shiga,inda be ga kowa a cikiba hakanne yasa yabi hanyar dazata kaishi ɗakinta inda can ya sameta kwance kan kujera tana latsa waya,
Da ƙyar ta amsa sallamarsa ya shiga yanemi gefen gado ya zauna,yana kallonta.
Ɗauke kai tayi bata kulashiba ita ala dole fushi take,be bi ta kanta ba,ya miƙe ya fice daga ɗakin ransa na masa zafi danshi bega abinda yay mata da zesa tai fushi dashiba.
Ɗakinshi yawuce yayi alwala yayi sallar ishai,sannan ya sauya kayansa zuwa na bacci yabi lafiyar gadonshi ya kawanta,ya janyo wayarshi ya kira fadeela.
Bata jima tana ringing va ta ɗauka tunkan yace komai ta rigashi da cewa,"prince mantuwa kayine zaa miƙo maka?"
"Ko ɗaya baby pls haw online muyi mgn a whatsapp"yana kaiwa nan ya kashe wayarshi.
Ayko ta hau dan tunaninta wani abunne se kawai yace hira zata tayashi kan yayi bacci.
Bata bincikaba amma ay tasan va lau ba haka ta biye mishi sukai ta hira har wajen ƙarfe biyu na dare.
Shigowar fareeda ɗakinne yasa shi yiwa fadeela voics da cewa "nagode baby da ɗebe kewa,seda safe kikwanta haka"
"To prince mukwana lfy agaida amarya"itama tayo mishi voice ɗin,ya kunna yaji sannan ya kashe ya ajiye wayar, ya ɗago ya dubi fareeda wacce wutar kishi keci a fyskar tata.yace
"baki iya sallama bane?"
Shuru tayi batace komai ba,shima bin ta yayi ido.
Kumude je zuwa.
*bana adding a group dan haka kar atambayeni,in so kike in saki to ki biya 300*
*masu son zama cikin group ɗina suna karanta paid book ɗina,tsawon shekara guda to ku biya 1500 insaku a group ɗin da bazaki sake siyan littafina ba se kin shekara.*
FREE NE HAR ƘARSHE
07044600044
[12/9, 14:53] zahrasurbajo1: https://chat.whatsapp.com/I5Nm6R0rL6nIwqbk8MmK1u
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*MAI MAGANIN MATA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*FREE BOOK FROM 1 TO END*
*Zahra Surbajo*
*ME BUƘATAR COMPLETE DOCUMENT ƊIN SHAAWARSHI NAKE 500 NE KITURO KUƊINKI ABAKI*
*HARIJA CE,sabon littafine dazan yishi akan kuɗi 500 kacal,karku bari abaku labari,yazo da salo na musamman shima meso ze iya turo kuɗinshi yanzu ta acct kawai*
*zahra muhammed nasir 2084024749 UBA*
*07044600044*
*22*
"na tafi gida baka biyoniba baka kiraniba,na dawo tun rana naji kadawo bakazo inda nakeba se yanzu,kuma kazo kaci gaba da chatting da matarka wannan adalcine?"cewar fareeda tana cika tana batsewa.
"dakata fareeda,ni ba yaronki bane da zakisani agaba kina min duk wannan,na farkode da kika tafi bada yawuna kika tafiba,kinga ko bazan biki ba,na biyu nazo gareki kin wulaƙantani kuma ni ba bacci nakejiba da inyi chatting da matan waje shiyasa naga dacewar yi da matata,banason hayaniya pls"ya faɗi batare daya kalleta ba.
Durƙushewa tayi agurin ta sa masa kuka,tana faɗin"da kasan baka sona da baka auroni dan ka wulaƙantaniba"
A rayuwar labeeb beson kuka musamman na mace,yanzu xe kiɗime,hakanne yasa ya sakko akan gadon ya rungumota jikinshi,yana shafa bayanta.
"Fareeda duk ranar da kika kuma cemin bana sonki na auroki aranar zan kawo ƙarshen zaman mu tare.na faɗi miki sone yasa na aureki amma kinƙi yarda"
Shuru tayi batace komai ba,miƙewa yayi da ita ajikinshi suka ƙarasa bakin gado ya ci gaba da rarrashinta.
Sun jima kan ya shawo kanta ta dena kukan tsakanin mata da miji se Allah can na hango fareeda ƙafa sama labeeb na miƙa gaisuwar girma a head quater.
Ba ƙaramin tsumashi tayiba da zaƙin data ƙara dan santi ya dinga har saida ta rufe masa baki.
********
Koda gari ya waye ya dawo daga masallaci gudun yim laifi daga masaɗlacin part ɗin fadeela ya wuce,dan su gaisa kar yayi rana.
Yasha mamakin ganin komai tsaf ita kanta zaune yasameta tana shan tea,wanda da yasanta da shegen son jiki amma kwana biyu ya lura ta sauya.
"ranka ya daɗe mijina kaine tafe da sanyin safiyarnan,haka,?"ta faɗi tana rangajin ɗaukar hankali ta ƙarasa inda yake tsaye yana mata murmushi.
tana zuwa jikinshi ta shige,ya rungumeta,sannan ya sumbaci goshinta yace"nine gimbiyata,kin tashi lafiya,?"ya faɗi lokacin daya zauna kan kujera.
Zama tayi akan cinyarshi sannan tace"na kwana prince amma ba lau ba,dan duk kwanan da zanyi baa jikinka ba prince ay bana daɗi bane"ta ƙarasa maganar tana kwantar da kanta a kafaɗarshi.
Sosai yaji daɗin batun nata,dan haka amsa ya bata da cewa"bansan daliliba fadeela yanzu ji nake nafi da sonki,jinake inbabu ke kamar ban kammalaba"ya faɗi yana hure mata idanu.
Lumshe idon tayi cikin salo tabuɗesu sannan tace"yanzu mun ƙara hankali da sanin darajar junanmune mijina."
"Gaskiyane wannan zancan naki babyta"
Sun ɗan jima suna hira cike da so da ƙaunar juna sannan ta rakashi ya tafi dan yaje ya kimtsa,
Cikin dabara tai masa kiss acikin rigarshi farar jallabiyya,ta yadda jambakinta ya fito raɗau.
Fareeda tunda tajishi shuru tasan yanacan gun fadeela,sosai ranta be mata daɗiba amma haka ta cije.
Tana gaban tv zatasa wayarta caji yashigo falon,kai tsaye yaje ya rungumeta ta baya,yace yana shinshina wiyanta"tuba nake baby,naje gun yayarki mu gaisane dan kar in shigo kuma in ƙara fita dan yau ɗin gaba ɗayana nakine"ya faɗi yana shafa boobs ɗinta da mararta.
Murmushi tayi dan taji daɗin kalaman nasa.Sannan tace"bakai laifiba angona,hakanma daidai ne"
Juyo da ita yayi suka fuskanci juna ayko carab idonta ya sauka akan jambakin rigarshi.
Duk wata faraa dake kan fuskarta saida ta kau,sannan tace cikin faɗa"wannan ay be usa ba,inso ake anunamin kun kasance tare,ruwan maniyin zata shafama afuska ingani ba canbaki ba"ta faɗi tana nuna gurin .
Da sauri yakai dubansa gun,yayi mamakin ganin jambakin,wanda yasan ɗaya daga cikin makircin mata kenan.
.
Murmushi yayi ya kamota tana ƙwacewa yacs"makircin matane baby kemw in nazo seki min ba shikenan ba"ya faɗi yana rungumota dannya fahimci tana da saurin fushi.
Kumude je zuwa.
*bana adding a group dan haka kar atambayeni,in so kike in saki to ki biya 300*
*masu son zama cikin group ɗina suna karanta paid book ɗina,tsawon shekara guda to ku biya 1500 insaku a group ɗin da bazaki sake siyan littafina ba se kin shekara.*
FREE NE HAR ƘARSHE
07044600044
[12/9, 14:53] zahrasurbajo1: https://chat.whatsapp.com/I5Nm6R0rL6nIwqbk8MmK1u
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*MAI MAGANIN MATA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*FREE BOOK FROM 1 TO END*
*Zahra Surbajo*
*ME BUƘATAR COMPLETE DOCUMENT ƊIN SHAAWARSHI NAKE 500 NE KITURO KUƊINKI ABAKI*
*HARIJA CE,sabon littafine dazan yishi akan kuɗi 500 kacal,karku bari abaku labari,yazo da salo na musamman shima meso ze iya turo kuɗinshi yanzu ta acct kawai*
*zahra muhammed nasir 2084024749 UBA*
*07044600044*
*23*
To rayuwa taci gaba da garawa,yana iya bakin ƙoƙarinshi wajan ganin ya musu adalci tsakaninsu.
Fadeela ta sauke komai yanzu mijinta takebi sau da ƙafa dan murja tasata ta dawo daga rakiyar magungunan matan datake bankawa cikinta.
Yayinda ita kuma fareeda ƴar chadi ta ɗorata akan shan magungunan harda na masifa,azatonsu fadeelat yanzu ta dace,
.
Hajiya mahaifiyar labeeb sosai take nuna musu banbanci tafison fareeda,danko gidan taje part ɗin fareedar take sauka saidai ita fadeela tabita can su gaisa duk da itace babba.
**********
Yau tun safe fareeda ke fama da ciwon mata ga tashin zuciya komai taci sai ta dawo.
Sosai hankalin labeeb ya tashi,ya ɗauketa suka nufi asibiti dan duk ta galabaita.
Cikin gaggawa aka amsheta aka shiga bata taimakon gaggawa.bayan ta dawo hayyacinta suka fara gudanar da bincike inda gwajin farko suka ga tana ɗauke da ciki dan wata guda.
Lokacin da albishir ɗin ya isa ga kunnuwan labeeb kuka ya fashe dashi na farinciki ya rungumeta yanata sa mata albarka.
Itako wani irin farinciki take mara adadi dan tasan yanzu gida yagama zama nata tunda gashi itace zata fara haifar masa ɗa agidan.
Wayarshi ya zaro ya kira hajiyarshi,vata jima tana ringing ba ta ɗauka,kamar wanda zaa rigashi yace cikin muryar kuka.
"hajiya fareeda na ɗauke da juna biyu yanzu haka muna asibiti"
Wata kabbara hajiya tayi sannan ta rangaɗa guɗa,tace"nayi farinciki labeeb ashe inada rabon ganin ƙwanka aduniya,Allah na gode maka,labeeb ya jikin nata?"
"Da sauƙi hajiya,"ya bata amsa yana kallon fareeda dake ta faman sinne kai wai ita kunya.
"Gani nan zuwa asibitin yanzu,ka kira driver ka faɗa mishi inda kuken"tace lokacin data miƙe ta nufi cikin ɗakinta danta shirya.
*******
Ranar girkin fadeela ne kuma taji shuru be dawo ba,dan tana bacci yazo daga office ya ɗauki fareedar zuwa asibiti dan haka ita batasan wainar da ake toyawaba
Saida tags anyi sallar ishai be dawo bane yasa ta kira wayarshi dan be kai haka awaje.
Ya jima kan yaji ƙarar kiran dan tuni asibitin ya cika da ƴan uwa da abokan arziƙi anzo tayashi murna,kowa senan nan yake da fareeda kamar kwai.
Fita yayi daga ɗakin ya ɗaga kiran.
"prince lafiya kake ko najika shuru baka dawo gida ba"cewar fadeela cike da kulawa.
"ina asibiti tare da fareeda,batajin daɗi shiyasa ban dawo ba"ya bata amsa agajarce danshi beso ta kirashiba yana kusa da uwar ƴaƴanshi.
"me yasameta prince shine baa daɗamin bacin ciwon ƴa mace na ƴamace ne?"ta daɗi cike da kulawa.
"wani ciwon de,amma ita da take ɗauke da cikina fadeela taya zakisan kalar ciwon bayan ke baki taɓa ɗaukar cikin nawa ba"ta bata amsa batare da tunanin komai ba.
Wasu hawayene suka zubo mata,madu tsananin zafi