MAI MAGANIN MATA COMPLETE HAUSA NOVELS BY ZAHRA MUHAMMAD SURBAJO.txt

Author :  Zahra Muhammad Surbajo Category :  Taskar Novels

Chapter   12 / 12

33K to 35.2K   out of 35.2K words

fadeela kan zata bisu amma ya hana sabida twins.





*Littafin AJI DOWN 500 NE KU HANZARTA SIYA DAGAJIN SUNAN KUNSAN ZE BADA CITTA,500 KACAL.*

Comments shike bada ƙwarin guiwar yi

Kumude je zuwa.

*bana adding a group dan haka kar atambayeni,in so kike in saki to ki biya 300*

*masu son zama cikin group ɗina suna karanta paid book ɗina,tsawon shekara guda to ku biya 1500 insaku a group ɗin da bazaki sake siyan littafina ba se kin shekara.*

FREE NE HAR ƘARSHE

07044600044
[12/9, 14:57] zahrasurbajo1: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/G6BmHCxso0rDZyWVQGgYYj



🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*MAI MAGANIN MATA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*FREE BOOK FROM 1 TO END*

*Zahra Surbajo*

*AJEE DOWN an fara posting jiya 500 ne game buƙata,karku bari abaku labari ta hanyar siyan littafina ne kawai zaki nunamin ƙauna ba ki maƙale ki jira asato abaki ki karanta ba*

*zahra muhammed nasir 2084024749 UBA*

*07044600044*


*48*



Fareeda tayi kuka tayi kuka ganin halin da mahaifiyarta take ciki adalilin sama mata farinciki.

Itama ƴarchadi kukan take,dan se yanzu take danasanin duk abinda take aykatawa,wanda yazame mata dole ta nemi yafiya kan ta koma ga Allah,ita bama wannanba,zinar da bokan yadinga yi da ita kamin yahaɗa mata maganin shiyafi komai tsaya mata arai.

Labeeb kwananshi biyu ya shaidawa fareeda zekoma sabida office.

Ayko kamar jira take ta fara faɗa"uwar tawa ba lafiya shine zakai kwana biyu kace zaka tafi?"

Hannunta yakamo yace a tausashe"kiyi haƙuri fareeda na miki alƙawari duk bayan sati guda zan dawo,dubaku,ki natsu kinkula da mama kinji ko ga wannan ki riƙe ki zaa buƙaci wani abu yanzu de na biya duk abinda ake buƙata a asibitin har asallameta"ya miƙa mata miliyan biyu akuɗin dalar amurka.

ƙwace hannunta tayi tace agadarance tana jijjiga kuɗin "da ike wannan ba bikin gidansu fadeela bane shiyasa kaban 2m mahaifiyata ba lafiya,wallahi ka guji raahin adalci"ta faɗi tana watsa masa harara.

Ranshi in yayi dubu ya ɓaci,dan haka ya dubeta afusace yace"to ay uwarkice batawaba,sannan nayi iya yadda nake ganin zan iya,amma ban burgekiba,to inaso kisani fadeela da duk wani abu daya shafeta,nada muhimmanci agurina,kuma inbanda abunki fareeda dukiyata ko inba fadeela ko kar inbata at last de tatace,sabida ta ƴaƴantace,shiyasa nake batan,inaso kisani rashin mutuncinki yafara yawa wanda bazan iya ɗauka ba,dan haka kizauna agidanku sena nemeki"yana kaiwanan ya wuce abinshi yaja motarshi yabarta tsaye baki buɗe da kuɗi a hannu.

Koda yadawo gida be nunawa fadeela akwai matsala tsakaninshi da fareeda ba,koda ta tambayeshi yajikin ƴarchadin cewa yayi kawai da sauƙi.

Lura datayi bayason maganar mahaifiyar fareeda da ita fareedar yasa tadena yimasa Tadeyi fatan alkhairi azuciyarta.



************

Fareeda wata biyu suka share a asibitin malam aminu kano,kamin asallamesu.

Keken guragu tasiyawa ƴarchadi, dan ba ƙafafuwa,koda suka koma gida,nanma de ba labarin labeeb kuma kota kira wayarshi bata shiga,dan yayi blocking ɗinta.

Tun tanasa ran ganinshi harta cire,kullum cikin kuka take tana faɗawa Allah,ta zubar da komai,dan se yanzune imaninta na farko yadawo mata,da itace ke hana mahaifitarta yin abinda take,segashi son zuciya yasa ita da kanta take umartar mahaifiyartata taimata.

Haka ta duƙufa neman yafiyar Allah da azumi dayin sadaka.


Ƙarshede fadeela takira awaya,tana kuka ta roƙeta yafiyar duk abinda taimata,kuma tayafe mata dan fadeela bata da ruƙo.


"to amma fareeda zaman me kike agida wajan wata biyar baki dawoba?"cewar fadeela cike da kulawa.

"rashin kunya naimasa aunty shine yace inzauna sai yanemeni,dan Allah aunty kitaimakamin banason aurena ya mutu"ta faɗi cikin matsanancin kukan dake nuna tsantsar nadamarta.


Sosai fadeela taji tausayinta,tace"ki kwantar da hankalinki ƙanwata namiki alƙawari gobe ko jibi zamuzo infa jikun mama ke kuma mudawo gida tare ki natsu kije maza kisha ƙunshi da kitso kar yazo yaganki ba agyareba"ta ƙarasa maganar cikin raha.

Ayko sosai fareeda taji daɗi dan tasan tunda taimata alƙawari zata cikashi,

Kamar yadda taje hakan tayi takira ƴat maƙwabtansu tasa taimata kitso da ƙunshin.ƴarchadi itama taji daɗin zuwan dazatayi kova komai tanemeta tafiya.

********

"Abban Fareed duk da na lura bakason maganar amma kayi haƙuri na gaza jurewa yau de zanyi maka"


Ko bata faɗaba yasan metake nufi hakanne yasa ya miƙe ze fice daga falon,

"wallahi matuƙar bakaje ka ɗauko matarkaba labeeb bazaka dawo kasameni agidannan ba"fadeela ta faɗi da kakkausar murya.

A firgice ya waigo yana dubanta yace"fadeela kan fareeda zaki barni?"

"Kwarai kuwa matuƙar kazo da son zuciya,yin hakan bakomai bane agurinaba,inasonka ina kishinka amma hakan be rufemin idoba wajan ganin aybinka ba,nasama ido ina kallonkane kawai,amma nasan komai,dan fareeda ra sanar dani kuma ta roƙeni inyafe mata kuma nayi hakan akan me zakabar ƴar mutane agida da auranka akanta,kai in akayiwa naka haka zakaji daɗine"


Shuru yayi yana kallonta cike da alfaharin samunta a mazaunin mata,yasan ba duk maceba fadeelarsa..

Ƙarasawa yayi inda take tsaye,rungumota yayi jikinshi yana faɗin "a huce sarauniyata jar fada tasamu matsala,zaayi yadda kikeso shikenan?"

Rungumeshi tayi itama tana dariya tace"amin afuwar ɗaga sauti"

ɗaukarta yayi cak suka wuce ɗaki yana faɗin"wani laifin akan gado kawai ake gyarashi".


*Littafin AJI DOWN 500 NE KU HANZARTA SIYA DAGAJIN SUNAN KUNSAN ZE BADA CITTA,500 KACAL.*

Comments shike bada ƙwarin guiwar yi

Kumude je zuwa.

*bana adding a group dan haka kar atambayeni,in so kike in saki to ki biya 300*

*masu son zama cikin group ɗina suna karanta paid book ɗina,tsawon shekara guda to ku biya 1500 insaku a group ɗin da bazaki sake siyan littafina ba se kin shekara.*

FREE NE HAR ƘARSHE

07044600044
[12/9, 14:57] zahrasurbajo1: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/G6BmHCxso0rDZyWVQGgYYj



🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*MAI MAGANIN MATA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*FREE BOOK FROM 1 TO END*

*Zahra Surbajo*

*AJEE DOWN an fara posting jiya 500 ne game buƙata,karku bari abaku labari ta hanyar siyan littafina ne kawai zaki nunamin ƙauna ba ki maƙale ki jira asato abaki ki karanta ba*

*zahra muhammed nasir 2084024749 UBA*

*07044600044*


*49*




Kamar yadda Fadeela taima fareeda alƙawari hakance ta faru,suka shirya dasu twins,aka kaisu gun umma dan acewarshi haramunne tafiya duka gida,tunda ba kwana zasuyiba abarsu gun umma.

Sun kama hanyar kano cike da so da ƙaunar juna.

Da azahar suka isa inda fareeda koda tagansu kuja tasa taje da gudu ta rungume fadeela,tana faɗin"nagode auntyna ke ƴar aljannace,samun irinki se antona"tana kaiwa nan tai ƙasa ta kama ƙafafunta,tana faɗin"kiyafemun auntyna natuba bazan kuma ba,"

Ɗagota fadeela tayi ta rungumeta tana faɗin "ya wuce ƙanwata maza jeki gurin mijinki ki tarboshi bakiga sarauta yakejiba"

A hankali takai dubanta gun labeeb wanda tsabar farincikin ganin su atare yasa yake murmushi besan yanayiba.

A hankali tanufeshi aɗan tsorace dan tana gudun ya yarfata.

"zaki ɗago ƙafa koko senazo na cimmiki anan"cewar labeeb lokacin daya buɗe mata hannayensa alamun ta isa gareshi ayko da gudu taƙarasa jikinshi ya rungumeta tasa kuka.

Kishi kumallon mata,da sauri fadeela ta ƙarasa shigewa ɗakin da ƴarchadi take ciki tana mata sannu da zuwa.

Gaisawa sukayi amutunce,sannan taimata ya jikin,ƴarchadi tasa kuka tana neman yafiyar fadeela,inda tace ta jima dayafesu ita,dan haka ta dena kuka.

A can kuwa fareeda na jikin labeeb anata zuba masa shagwaɓa yana rarraashi harde tai shuru,ya kamo hannunta suka isa inda su fadeela suke.

Suna shiga ta ƙwace hannunta anashi dan tasha alwashin kiyaye duk wani abu da in idon fadeela ya gani ranta ze ɓaci


nande aka shiga hirar yaushe gamo,inda yara suka shigo da kayayyakin dasukazowa ƴarchadi dashi.

basu baro kanoba segefin magriba,shima saida labeebvyatakura suzo su tafi dan twins na gida.

fareeda farincikin da take ciki baya misaltuwa,fadeela na gaban mota ita tana baya,koya suka haɗa ido ta mirror yana sakar mata murmushi me sanyaya mata rai,yayinda hannayesu ke sarƙe cikin na juna shida fadeela.

sai tara nadare suka shigo,ba yadda fadeela bataiba kan su wuce gida da safe azo aɗauko su twins ɗin fafur yaƙi,

ayko suna zuwa gidan umma ta sauka amotar tace"Ku wuce kawai prince da safe zamu taho dannasan sunyi bacci kuma kasan de insukayi bacci aka tashesu kuka sukeyi"

Shuru yayi bece komaiba dan yafi kowa sanin fadeela,yasan tayi hakane dan yasamu lokacin fareeda sosai,sabida inde yasannita da twins na gidan vaze natsu guri gudaba .

Murmushi yayi dake nuna ya fahimceta yace" to uwargida sarautar mata,zamu tafi amma de kinsan baki ktautaminba ko?"

Murmushi tayi ta buɗewa fareeda ƙofar motar ta fito,sannan ta buɗe mata gidan gaban ta shiga tasa hannu ta shafo fuskarta tace"ni ban kyautawa babynki ba,ƙanwata gashinan ahannunki kitabbatar da kin kyautata masa kamin in dawo inga yayi ƙiba"

Murmushi fareeda tayi tai ƙasa dakai,dan nauyin fadeelar takeji,dan tasan tayi hakanne dan tabata damar sakewa da mijinta.

"nagode auntyna Allah saka miki da alkhairi na aramin mijinki da kikayi"cewar fadeela akunyace

Dukan wasa fadeela takai mata tana dariya tace "kajini da yarinya wai aramata miji,wlh kinci abinci akaina fareeda"

Sun jima ƙofar gidan kamin tai musu sallama dan ta fahimci inde ba ita ta fara tafiyaba labeeb baze tafiba.

Koda ta shiga samu tayi su twins ɗin na barci,ƴar hira sukayi da umma sannan tai wanka tai sallah tabi lafiyar gado dan duk agajiye take.

********

Ango da amaryarsa ko suna isa gida wanka suka shiga atare,tun atoilet ɗin suke kamar zasu cinye junansu,da ƙyar de aka gama aka fito sukai sallah,ayko takan abinci basubiba suka faɗa gado.


Ranar saida suka raya wannan dare rayuwa bata wasaba,anjida juna daɗi,kowa maida numfashi kawai yakeyi.

******


Saida fadeela tai kwana biyu agidansu dan dayazo ɗaukarsu langaɓewa tayi tacs bata da lafiya,haka yabarta yatafi shikaɗai badan yasoba.

Yasamu isasshen lokacin fareeda wacce har ya gundureta dan ita bata da haɗama😂koya yabata saurin ƙoshi gareta.







************



".


*Littafin AJI DOWN 500 NE KU HANZARTA SIYA DAGAJIN SUNAN KUNSAN ZE BADA CITTA,500 KACAL.*

Comments shike bada ƙwarin guiwar yi

Kumude je zuwa.

*bana adding a group dan haka kar atambayeni,in so kike in saki to ki biya 300*

*masu son zama cikin group ɗina suna karanta paid book ɗina,tsawon shekara guda to ku biya 1500 insaku a group ɗin da bazaki sake siyan littafina ba se kin shekara.*

FREE NE HAR ƘARSHE

07044600044
[12/9, 14:57] zahrasurbajo1: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/G6BmHCxso0rDZyWVQGgYYj



🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*MAI MAGANIN MATA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*FREE BOOK FROM 1 TO END*

*Zahra Surbajo*

*AJEE DOWN an fara posting jiya 500 ne game buƙata,karku bari abaku labari ta hanyar siyan littafina ne kawai zaki nunamin ƙauna ba ki maƙale ki jira asato abaki ki karanta ba*

*zahra muhammed nasir 2084024749 UBA*

*07044600044*


*50*



To Alhamdulillahi rayuwa taci gaba da garawa,inda labeeb ke iya bakin ƙoƙarinshi wajan ganin yayi adalci atsakaninsu.

Fadeela taja fareeda ajiki sosai ta yadda munafukan ƙawayen fareedar insukazo sukaga shaƙuwarsu basa dawowa.

Duk wata ƙofa dazata kawo musu saɓani sun tosheta.

Fareeda yanzu itace me renon su twins,dan fadeela akwai saurin duka ita kuma vata dukansu hakanne yasa sukafi son zama gun auntynsu kan gun fadeela.

Suna da shekara ɗaya da rabi fadeela ta ƙara samun wani cikin,wanda kaf gidan ba wanda yakai fareeda murnar cikin dan tasan in fadeela ra haihu zata ƙara bar mata su twins tunda tasamu sabo,

Labeeb shima yayi murna bada wasa ba,ayko cikin ƙanƙanin lokaci labarin yazagaye dangi kowa se murna ake tayasu.

Cikin na wata biyar labeeb ya kwashesu duka zuwa ƙasa me tsarki harda su twins.

Satinsu biyu suna bauta,daganan suka wuce dubai sukai sati biyu sannan suka dawo.


Duk abinda Fadeela takeso shi fareeda ke mata,ko kaɗan basa son ɓacin ran juna,hakan sosai ya ƙarawa labeeb natsuwa da kwanciyar hankali.

******

Wannan karonma cikin sauƙi fadeela ta haihu a asibiti inda ta haifo ƴarta kyakkyawa me kama da ita.

Kowa se murna yake mata,tun a asibitin ta miƙawa fareeda ƴar tace "gatanan fareeda na haifo miki duniya da lahira banaso tasan ba kece mahaifiyartaba"

Ba fareedaba hatta sauran mutanen dake gurin kyautar ta girgizasu,ayko fareeda kuka tasa ta rungume fadeela tana godiya.

Koda suka dawo gida fafur taƙi ba yarinyar nono acewarta ƴar fareedace.

Ba shiri labeeb ya kwashi fareeda zuwa asibiti dan abata maganin da nono zezo mata,dan fadeela tayi rantsuwa bazata shayar da jinjirarba.

Cikin taimakon Allah nono ya kawo ruwa bayan kwana uku da haihuwar se madara akeba ƴar.

Haka fareeda taita wankan jego dan ruwan nonon yazo sosai.

Fadeela haka taita jego ba jinjira wacce ramar suna haka fadeela tasa fareeda dole tazauna mazaunin mejego.

In banda ƴan uwa na kusa ba wanda besan ba fareeda bace aynihin mejegonba.

**********

Yanzu sunfi ƙarfin akirasu kishiyoyi sede ƴan uwa,dan alaƙarsu tazarce tunanin me tunani.

Zamane na tsakani da Allah sukeyi cike da so da ƙaunar juna,

Fareeda bata da ayki sena nasreen wacce taci sunan hajiya suke kiranta da nasreen.

Iyayen fadeela koda sukaji ta bada ƴa basu mata faɗaba dan sunsan kyawawan halayenta zata iya abinda yafi hakama.

Fatan alkhairi sukayiwa abun,dan shine kawai mafita.

Gidan labeeb zaune ake lafiya,dukansu sun watsar da maganin mata sun kama Allah da manzonsa dan shine kawai ze taimakesu,

Magani ko da kansu duke haɗawa wanda baze cutar dasuba,gashi suna yawan cin ƴaƴan itatuwa watakan fruit dan ƙarin niima da lafiyar jikinsu.

Sun fahimci maganin mata baya riƙe aure ladabi da biyayya da tsabta da iya girkine kawai maganin matan sake riƙe aure.

ALHAMDULILLAHI


anan nakawo ƙarshen wannan labari,ladanvsake ciki Allah bamu duka,inda akau kyskure Allah yafe mana amin.

Darasin dake ciki Allah yasa muyi amfani dashi,maganin mata baya riƙe aure ƴar uwa,ladabi da biyayya,tsabta,haƙuri,girki,kula da ibada shike riƙe aure


kutara cikin tagwayen littafina *AJI DOWN DA KAWALINE*Akan kuɗi 500 karku bari abaku labari akwai karatu namusamnan aciki






Comments shike bada ƙwarin guiwar yi

Kumude je zuwa.

*bana adding a group dan haka kar atambayeni,in so kike in saki to ki biya 300*

*masu son zama cikin group ɗina suna karanta paid book ɗina,tsawon shekara guda to ku biya 1500 insaku a group ɗin da bazaki sake siyan littafina ba se kin shekara.*

FREE NE HAR ƘARSHE

07044600044

12 / 12