Author : Sadiya Kaoje Category : Read Hausa Novels
tsoro bakinta na fitar da wani irin hayaƙi baƙi ƙirin tana kallon Aliyu ilahirin jikinsa karkarwa yake gumi da ya wonke masa jiki gaba ki ɗaya magana ya ke son yi amma ya kasa saboda tsoro da zaran sun haɗa ido da ita sai jikinsa ya ɗau rawa, ta nuna shi da zara zara yatsunta masu kama da lauje a razane ya matso kusa da ita yana zaro idanu kaman zasu faɗi Cak ta ɗaya shi sama kaman wadda ta dauki ɗan jinjiri ta kalleshi da firgitattun idanuwanta ta sheƙe da dariya tana magana cikin wani irin sautin da ya mame gabaki ɗayan dajin.
"Aliyu Usman Marafa....! Ma yau dari Azzalumi da rashin imani yau karshen zalunci ka yazo, ka cucu yan mata bayin Allah ƴaƴan latakawa ka saka iyayensu ciki baƙin ciki da bazasu taɓa mantawa da kai ba duk dalilin son zuciya irin naka da mahaifinka, ka zata Nima irin sauran matan nan ne shine kazo ka yaudare ni ka gudu ko? Na shigo rayuwar ke domin na rama ma sauran mata da ka zalunta zaluncin da kayi musu kamar yadda ka saba zuwa ta sigar yaudara ka yau da re su shi yasa ni ma na shigo yaruwarka..
ta sake sheƙewa da dariya tana faɗin Yau karshen ka yazo Aliyu zan ƙunsa ma baƙin ciki da har ka mutu ba zaka taɓa manta da ni ba da dengin ka, sai nayi kama illar da ba zaka taɓa sha'awa ƴa macce ba
Wannan ma baka komi ba akan azabar da na tanadar maka, da karfi ta yadda shi ƙasa tana dariya ta fara rikiɗa zuwa bakin hayaƙi sai kuma ta ɓace ɓat kaman walƙiya...
"A....li....ya...." Don Allah ki yi haƙuri ki min Afuwa wallahi bazan sake ba na tuba tuba tun ba yau ba wallahi son tsakini da Allah na ke miki zan aure ki ne saboda Allah". Yana magana jikinsa na rawa yana ja da baya cikin Zuciyarsa yana karanta duk Addu'a da ta zo mishi ya rasa wacce Zaiyi, tun da yake aikata abin da yake so ake cewa yaje zai ga sakomakonsa bai taɓa damuwa ba balle ya yi tunanin sakamakon zai riske shi a haka don yana samun daurin gindin Daddnsa da ke ƙara tunzura shi yake aikata abin da ransa ke so, ashe sakamakon gaskiya ne ya zo masa ranar nadama da ake ta kira, Aliya ta shigo rayuwar a dai dai lokacin da yake buƙatar gyara kuskuren da aikata a baya, tun da yake a rayuwarsa bai taɓa ganin Aljani ba sai da ya ji labarin su, yau gashi a gaban Aljana, a take tsanar Daddy ta cika masa Zuciya shi ne silar komi ya cuceshi ya lalata mishi rayuwa yau gashi cikin bala'i da Masifar da Daddy ba zai iya fidda a ciki ba gatan da yake nuna mishi bai mishi rana ba,
"Na shi ga Ukku ni Aliyu, Allah ka yafemin kuskure na na tuba Allah ka fitar da ni cikin wannan hali Allah kana gani da kyakkyawar Zuciya na zo gareta Allah ka kareni daga Sherrinta".
Zantuka yake a firgice tamkar sabon mahaukaci cikin fitar haiyaci ganin abin yake tamkar a mafarki amma idon ya runtse ido ya buɗe sai ga Aliya a gabansa cikin mummunar siffarta mai ban tsoro sai kuma ta ɓace ɓat......
*JUNAINAH*
"Alhamdulillah na gode maka da nuna min wannan ranar, yau rana ce mai cike da farinciki a gurina, ban tsammaci zuwanta a lokacin da na ke raye ba, kuma ban tsammanin zuwanta a nan kusa ba, amman sai ga shi komai ya zo ta yadda ban yi zato ba, na gode Allah da yasa ina da rai akai auren nan"
Dagowa tai ta kalleta sai ta ga hawaye a idon Amma murmushi kuma a fuskarsa. Sake maida kanta tai kasa domin har lokacin kunya ta ke ji ni irin kunyar da ta ke daga lokacin da aka daura auren nan zuwa yau har mamaki take ba ita ba ce domin bata taɓa sanin tana da ita ba sai a yanzu. Bayan sallah isha'i Hajiya Farida ta shigo Bq da ita da Ummy suka gaisa da Amma sai Ummy ta ce mata ta tashi ta je part dinta za tai magana da Amma. Ita kuma ta tashi ta fice ban je part din nata ba na zauna a gurin da ake aje motoci ta zauna ta na tunani ita kadai. Haka tai ta kawo wacan ture wannan har na soma jin bacci a gurin, can kuma Ummy su ka fito daga bq din Ummy na takawa a hankali tare da kawarta har suka iso gurin motar kawar tata, a lokacin ita kuma ta mike tsaye da zimmar komawa Bq din sai Hajiya Farida ta rike baki.
"Junainah yanzu a nan kika zauna? Ba ki je falon Ummy ba?”
"Kunya ta ke ji daman na lura da takunta ai"
Wucewa tai bata ce komai ba sai watsa ta ke da yan yatsunta lokacin da ta shiga bq ta yi zaton Amma zata fada mata wani abun akan zuwan Ummy gurinta amman bata ce mata komai ba sai dai tana ta kallonta tana murmushi. tare suka Kwanta kamar yadda suka saba sai dai jin kunyarta be hanata shigewa bayanta tai bachina ba har gari ya waye. Misalin takwas da yan mintuna Ummy ta aiko Afra tana kiranta, bata jira sun tafi tare ba ta juya ta fice. Ita kuma ta mike tsaye ta dauki Hijab dinta Amma ta ce,", Junainah kin yi dacen suraka indai abun ya bi haka za ki jidadin zama da ita sosai"
Ta kalleta sai kuma na sauke ido kasa, kamar ta tambaya abunda ya Ummy ta zo yi jiya a nan sai kuma ta dauke kaina ta fice daga Bq din, kamar jiya yau ma da kunya ta shiga part dinta sai na samu tana zaune falo ita kadai tana fere dandalin turawa. Har kasa ta ta durƙusa ta gaisheta ta amsa mata da murmushi a fuskarta kamar ko yaushe.
"Ki je Kicin ki gyara min kayan miya ki markaɗa su".
"Toh Ummy"
Kana ta wuce cikin ɗin,
Tsns wuce sun Afreen suka fito ko wacce su riƙe da littafai.
"Ummy zamu wuce School".
"Okay Allah ya tsare".
"Amin"
Sai da suka shiga cikin suka gaisa da Nainah sannan suka wuce".
Tana tsaye ta ji an rige kunkurunta an doro mata kai a wuya
"Good Morning Angel.."
Saurin janye jikinta tai ta juyi tana kyarma irin na tsoro.
"Sannu da zuwa"
"Ina kwana?"
Ya fada yana jan kumatunta tai kasa da kanta Waiga yai ya kalli kofar kitchen din sannan ya saka hannunsa biyu ya rika fuskarta ya yi mata kissing saman lips ɗinta Sai yai saurin juyawa ya fice yana murmush. Hijab ɗin ta ta sa ta goge bakinta tana dagowa sai ta ganshi yana kallonta sai kuma kunyarsa ta rufe ta, murmushi yai ya karaso kusa da ita ya sake rika fuskarta ji kamar ta masa magana ko tai ihu sai kuma ta kasa yi sai kunya ta ke ji wannan karon ta iya saman bakina ya sumbarta ba, bakinsa ya saka cikin nata ya rika jan yawu bakinta yana hadewa 🤮🤮yana ta wasa da halshensa a cikin bakinta sai da ya yi mai isarsa sannan ya wuce pali, "aashe Asad kazami ta musamman duk tsabbatarsa ta banza ce". A faɗa a ranta.
Saida ta gama gyara kayan miya sannan ta fito falo
"Junainah kun gaisa da mai gidan ki?...".
Ummy ta kirata sannan ta fada kamin ta amsa ya dago kansa ya kalleta.
"A'a...."
"To idan kika ganshi ki rika gaishe kin ji".
"To Ummy"
"ina kwana"
"Lafiya lau"
Ya amsa mata fuskarsa babu murmushi ko wasa kamar ba shi ba. Sannan ta wuce Ɓangarensu tare da Breakfast ɗinsu.
*ASAD*
Sai da ta wuce sannan ya mike ya nufi dinning yana fadin.
"Ina Daddy?".
"Ya fita"
Yayi shiru be ce komai ba har ya zauna ya bude abinci ya zubawa kansa ya soma ci yana ta tunanin abunda yai ma Nainah a dazu sai murmushi yake a zuciyarsa.
"yarinyarnan tana son karatu sosai".
Ya dago ya kalli Ummy
"Na sani shiyasa na shigar da ita islamiya ai, kuma bokon ma zan saka nan gaba in sha Allahu".
"Ina jin tsoro kar aurenku ya saka karatunta ya tsaya, tana da ƙoƙari sosai ba ka yadda take maida hankali ba idon su Afreen na mata lessons kuma tana ganewa sosai".
"Ummy As long as zatai zaman aure ai zan barta tai karatunta, ba ni da matsala da wannan amman".
Sai kuma yai shiru ya kasa karasawa. Ummy ta shiga zuba abinci tana tambayarsa.
"Amman me?"
"Tsawon wane lokaci zata dauka a gida tana karatun?"
"Karatu yana da lokaci ne?"
"Na yi magana da Daddynka jiya saboda Hajiya Farida ta kawo wata shawara har ta saka ni dole sai da naje bq nai magana da Amma ita kuma ta amince ta ce mana ba matsala, da na fadawa Dr sai yace shi babu ruwanshi shawara ta mu ce, kuma na kira Anty Umman Deedat na fada mata komai ita ta bani shawara irin wacce Hajiya Farida ta ba ni"
Ya dago tana ta kallonta, gabansa na dan faduwa irin na tsoron nan idan ba wani abun za a bullo da shi ba, wata kila ace ya kai Nainah Bording school ko kasar waje ko kuma ya barta gida har nan da wani lokaci mai tsawo wanda yake jin cewar ba zai iya haka ba.
“Wani abun ne?”
ta ce. " Mun yanke shawarar Junainah ta tare dakinta next week".
Wani irin dadi da mamaki da ya ji lokaci daya, amman yai kokarin dannewa saboda kar Ummy ta ga haukarsa ko rashin kunyarsa, yayi murmushin dake nuna jindadinsa amman ya boye duk wani jindadin a cikin Zuciyarsa...
"Ummy ita Junainah ta yadda zata tare?"
Junainah bata da matsala duk inda aka bi da ita bi za tai, mahaifiyar kuma amince har ma godiya tai mana jin cewar an dauke mata komai"
" Allah ya tabbatar da alheri"
"Amin sai ka fara shirye shirye tun a yanzu"
"In Sha Allahu Ummy"
Tun daga lokacin ya fara shirye shirye kamar yadda Ummy ta fada masa, kudi ya cire mai yawa ya bawa Ummy ta siyoma Junainah kaya da tsarkoki masu kyau da tsada da takalma, kusan kala Hamsim aka mata na sakawa yanzu da kuma na kwaliyar amarci kamin a gama haɗa mata lefenta idan komai ya lafa hankali ya kwanta zai mata cikakken lefe domin yana son ya mayarda ita mutum ita ta zama tana fita da shiga irin ta mayan mata. gidansa mai kyau da tsari Sabon fenti aka yi ma gidan duk kuwa da kasancewar ba a taba shigarsa ba, saka kara kawata shi aka gyara wasu abubuwan, sannan Ummy tai order wasu furnitures daga Abuja masu Kyau da aka kawo aka zuba gaba daya.
*AMMA*
"Junainah mahaifiyar Asad ta nemi Alfarma ki tare nan da sati ɗaya".
"Tarewa ta sati mai zuwa?"
"Ehhh haka ta roka ita da matar da suka zo jiya, kuma ta ce idan na amince zata fadawa Mahaifin Asad sun fada min sun dauke nauyin komai, za su yi duk abunda ya dace, kuma za a hada miki kayan sakawarki wasu tun a nan wasu kuma sai kinje can Saboda kurewar lokaci, tace ba za ayi wani hidima ba amman tana son ta shirya yar walima saboda addu'a"
Nan take ta fashe da kuka.
"Karatuna fa? Yanzu kenan? Barin zuwa makarantar zan yi? Kuma bokan ma ba za a a saka ni ba?"
"Aa zancen karatunki tace yana nan za ki cigaba da karatunki ko bayan aure"
"Amma ni ban yarda ba Wallahi bana so, ma fasa auren gaba daya Wallahi ba zan yarda ba, ni ba zan iya zaman da shi ba, dan Allah karki bari na tare yanzu...."
Shine abunda ta ke fada ta rikon hannunta domin har ga Allah ta tsorota da wani zaman aure a yanzu, Me ake cewa ya tsare tsaren suke ita ba zata iya ba, ga wannan kazantar da yake mata ta san idan can sai ya sake mata ita, karatuna ma lalacewa zai yi. Babu abunda Amma take sai kallo da fuskar tausayi domin kukan ba na wasa ta ke ba.
"Na riga na amince mata ba zan iya canjawa a yanzu ba, Allah yasa hakan shi ya fi alheri"
Kara fashewa fashe da kuka tai , bata ce mata komai ba bayan hawayen da take har tai kuka ta gama na tashi dan kanta ta shiga bandakin ta wanke fuskarta na saka uniform dina ta tafi makarantar islamiya . Sai dai bata sake da kowa ba duk wanda ya kalleta ya san tana cikin damuwa domin har ga Allah bata son tarewar gaba daya ma sai ta ji auren ya fita a ranta
Ƙarfe shidda aka tashe su ta dawo gida kamar wata marar lafiya.............✍️
💋𝐁𝐈𝐍 𝐌𝐀𝐑𝐘𝐀𝐌💋
𝑵𝒂
𝑺𝒂𝒅𝒆𝒆𝒚𝒂 𝑲𝒂'𝒐𝒋𝒆
08149979652
*Book 2*
*JUNAINAH*
Bata kara tabbatar da cewar da gaske ne ba, sai da taga ana ta hidimar bikin, tun ranar laraba aka saka tai wa ka da ruwan lalle mai ja sosai, ranar da ta kama jumma aka zo aka kara gyara mata gashinta har gida, ba kitso aka mata ba sai dai an gyara mata shi gyara na musamman . Lallen ma dan ubansu aka mata mai kyau gaske, tun da take a rayuwata ban taba yin lallae ba sai yau ashe haka yake kyau a fata farin kafata dana hannunta ya fito fes lallen mai ja da baƙi ya fito fes, jikint ya sha dilka ta ko'ina kyali take.
idan dare yayi sai Ummy ta aiko matada fruits ta sha, bayan kwana uku a gidan ta mayar da ita gurin wata kawarta, a can akai ta cusa mata wasu abubuwa da ta ke hadewa daker idan na gama ta shiga bandaki tai kuka son ranta ta fito, duk ta kasa sakewa a gidan lokaci zuwa lokaci Afreen da Afra da Baby suke zuwa su dubata, da dare fruit ake ta kamar yadda Ummy take mata da safe kuma ba a bari ta karya daabu mai nauyi da ta ci kadan sai ace ta bari haka nan bata kaza mai magani da daci ta ci, gashi tsoron matar ta ke domin na lura ita ba kamar Hajjiya Farida ba ce sam bata wasa da yara balle ta sake da su,
yanzu tana jin dadin jikinta domin fatar jikin har wani sheki take tayi laushi sosai fiye da da, gashin kanta kuwa kamar ba nata ba, domin kullum cikin shafa masa mai take tana gyara shi, ita kanta yabon kyaunta take gaba daya ta koma kamar ba ita ba, domin kuwa ta fi da kyau da haske duk wani datti na fuskata da jikina sai da aka kawarda shi. Wata tela ce ta zo ta auna ti ko'ina na jikiñta sai da ta auna ta sannan ta tafi, haka ta rika kwana a gidan kullum idan na yi marmarin ganin Anma sai da a kira mata ita a waya shi ma kuma idan Afreen ko Afra sun zo, sai dai kullum sai ta sha kukan dare ni kadai ba tare da kowa ya sani ba.
Kayan kitchen kuma Hajjiya Farida Ummy ta ba kwangilar sayen komi ta shirya komai ran Friday aka saka.
Kamar yadda Ummy ta tsara ranar Saturday akai walima, ba a yi wani taro ba domin ba kowa da kowa Ummy ta gayyato ba iya na kusa da ita kwai, saboda kurewar lokaci wasu ma jin abun na Momy ne yasa suka zo ba tare da an gayyoto su ba
Da yamma aka sake saka tai wani wankan wata mai kwaliyar ta zo ta shirya ta tai mata makeup nan na kanti sai na fito kamar ba ita ba, dogon hancin nan nata sai ya kara fitowa kowa cewar yake ta yi kyau
Afree ta kama hannunta har falon Dr Kamal fuskarta a rufe da farin mayafi mai kyau sai kyalli yake,
Asad ya mike tsaye ya fuskance ya kama hannayenta masu taushi yana murzawa a hankali.
Ya hade goshinsa da nata yana kallon kwayar idon da ta rufe saboda tsananin kunyarsa da take ji a yanzu. Shi ma rufe idon yayi suna shakar Numfashin juna, a hankali ya saki hannunta ya saka hannayensa ya zagaye kwankwasonta. ya kwantar da ita a kirjinsa dake cike da babbar riga.
Ta yi shiru ya tana shaka fitinannen kamshin dake tashi a jikinsa yana ratsa hancinta
"Soulmate....."
Ya furta mata yana kwanto da kansa kusa da saitin kunnensa. Ta kara lafewa a jikinsa,
Wani shauki na angonci da farinciki yake jin kansa a ciki, tun da aka daura auren be taba jin nauyin ya hau kansa ba sai a yau. Dagota yayi daga jikinsa ya daga mayafinta ya sauke shi a bayanta yana kallonta. Ya sumbanci goshinsa irin sumbantar da sai da tsigar jikinta tashi, ya sumbanci gefen fuskaerta hagu da dama sannan ya kwantar da kansa a wuyanta hancinsa ya shakar kamshin dake tashi a gurin, har lumshe ido yake yana jan numfashi a hankali a hankali.
Ya bude idon ya kama fuskarta yana yawo da idonsa, ya sumbancin hancinta.
Ya hade bakinsu na wasu dakikun da suka suka kusa hada mintuna daya. Yadda jikinta yake rawa ya kara tabbatar masa da ita din sabo shiga ce da bata saba da irin abubuwan ba.
"A falon Daddy mu ke kar wani ya shigo ya ganmu".
"Ni mijinki ne Junainah, daga ranar da aka daura mana aure aka