Bin Maryam Book 2 Complete Sadiya Kaoje

Author :  Sadiya Kaoje Category :  Read Hausa Novels

Chapter   19 / 20

54K to 57K   out of 59.4K words

sabon Aliyu ne nan ba wanda ka sani a baya ba, Kamal Allah ya shirye ni ka ya femin akan irin baƙaƙen magganu da nayi ta faɗa a baya Kamal kai ɗan uwana ne a wajen kuma babban abokina wanda bani da kamar a duniya ka daɗe kana gayamin gaskiya akan abin da nake aikatawa ba bu kyau amma a lokacin sheɗan na kaɗamin ganga ban yadda da abin da ka ke faɗa min na biyema son Zuciyata har ta kaini ga halaka don Allah ka yafe min.....!"

Dr Kamal ya damƙe Hannayensa ciki tausayawa domin duk wanda ya ga Aliyu a halin yanzu ya san ya yi nadama sosai, "Babu komi Aliyu ya wuce ni ban taɓa riƙe ka a ba babban fata na shi ne Allah ya shirye ka ka gane gaskiya kuma Alhamdulillah yau ka gane".

"Na gode sosai da ka fahimce ni Allah bar zumunci, kuma in sha Allahu zan ki ya ye zuwa gidan nan domin gudun zargi".

"No! Aliyu karmuyi haka da kai, kar macce ta haɗa mu abin bai kai ga haka ba, zumunci kam ai yanzu muka fara kasa a ranka komi ya wuce, bana kallonka a matsayin tsohon mijin Maryam ina kallonka a matsayin ɗan uwana uban ƴaƴana kuma, domin Asad ma ɗanane ko bayan raina zai gajeni".

Aliyu ya yi Murmushi mai dauke da zallar farin ciki.

"Mu dawo kan maganar mu me zai hana ka auri sake auren Murjanatu kaɗon zumuncin dake tsakanin a yanzu, kwana kin baya mukayi maganar da Balaraba har ta ce in dai har ka yadda ita ma zata yi ƙoƙarin wajen shawo kan Murjanatu domin ta yadda".

Wani irin daɗi da farin ciki suka lulluɓe sa lokaci ɗaya, daman abin da yake buri ke nan in fact ma yana ɗaya daga cikin abin da ke kawo sa gidan, sai dai yana tunanin yiwuwar hakan ta faru yana jin kunyar Murjanatu idon ya tuno abin da ya yi mata a baya, cikin sanyi Murya ya ce,"Na daɗe ina wannan tunanin sai dai ina jin kunyar Murjanatu da kyar za ta amince ta sake Aure na".

"Ku fa yanzu ba yara ba ne a yanzu ba wanda ta dace da kai kaman Murjanatu haka ita ba wanda ya dace da ita sai kai, don haka ka bar komi a hannuna komi zai so da sauƙi in sha Allahu".

"Allah ya sa".

"Amin".

Sun jima suna hira Sanan Aliyu ya yi masa Sallama ya wuce gida cike da kwarin gwiwa amincewar Murjanatu, yana isa gida gida ya Labartawa mama yadda sukayi da Dr Kamal, Mama ta yi farin ciki sosai tare da fatan Alheri, daga nan kuma ya gayama Daddy da Umma da sauran yan gidan kowa ya yi farin ciki da zanje suna da addu'a Allah yasa ta amince cikin sauƙi.

Dr Kamal na shigowa cikin gida ya zayyana ma Ummy yadda su ka yi da Aliyu, Ummy ta yi farin ciki sosai tare da fatan Alheri, cikin sauri ta nufi Bq, Amma ta jinjina abin cikin ranta bayan gama zayyana mata da abin da Ummy ta zo mata da shi,

Sai ta girgiza kai ta ce,"Ba mai yiwuwa ba ce ni kuma a wajen aure zanyi yi ai sai dai zaman ibada da jiran lokacin mutuwa....!"

Ummy ta katseta da sauri tana faɗin ,"Don Allah ki yi haƙuri na san har yanzu kina jin zafin abin da Aliyu ya yi miki a baya, kada ki duba wannan domin ke ganau ce ba jiyau ba, kin ga yadda rayuwa ta yi da Aliyu da mahaifinsa ki duba Kinga yadda suka canza halayensu na sanki da haƙuri da ya fiya don Allah ki manta da abin da ya wuce ko don ƴaƴanmu".

Amma ta ce,", wallahi ko kaɗan ba na duban wannan, domin tuni na yafe masa ke ma sheda ce....!"

A sanyaye Ummy ta ce,"Idon har zancen ibada ki ke ai shima aure ibada ne duk girman macce darajjarta gidan mijinta ki na so a ce kin mutu babu aure a kanki? bai da ce ba, don Allah ki yi haƙuri ki amince da auren Aliyu, wallahi Aliyu ya yi nadama sosai tsananin kunyarki da yake ji shi ya sa ta kasa tunkararki kai tsaye da maganar Dr ma yace don girman Allah ki yi haƙuri ki amince da Aliyu, da kyar Ummy ta shawo kanta ta amince.

cikin ƙanƙanen lokaci kowa ya ji labarin Amma ta amince da zancen Auren Aliyu. Kowa ya yi farin ciki sosai musamman Asad Nainah ma tayi farin sosai sai dai kuma tana ɗan jin kunya. tuni Ummy ta sanar da yan Sokoto suma sunyi murna sosai musamman Jumayma don har kiran Amma tayi tana zolayarta kaman ba Mahaifiyarta ba.

cikin wata ɗaya aka yi komi aka gama Aliyu ya zo gurin Amma suka gana suka sake fahimtar juna sosai Asad ya ba su gida mai kyau makon wanda Amma zata zauna a da, an gyara ko'ina tsab aka zuba sabbin kayan daki masu kyau da tsada Asad ya haɗa ma Amma lefe kaman wata budurwa Aliyu haka kaya masu yawa da tsada ya ɗunka masa da duk wani abin kalliya irin na maza sai da ya haɗa masa. Bayan sati biyu aka ɗaura Aure Amarya tare a ɗakinta. Bayan kwana biyu su Jumayma suka koma Sokoto.



Bayan wata ɗaya rayuwa ta yi daɗi ta konne ɓangare, ranar Laraba da Daddare Asad da Nainah suke wuce gidan Mama suka yi masu Sallama daga gidan kai tsaye gidan Iya suka wuce suma sukai musu Sallama sannan suka wuce gidan Amma sun tarar da Amarya da ango zauna a falo suna hira gwanin burgewa Amma ta saki jiki sosai suna hira da Asad ta tamkar ba surinkin ta ba, shina zuwa yanzu ya cire duk wata kunya da yake mata a da ya ɗauke ta tamkar mafaiyarsa, shi kuma Aliyu ya ja Nainah da hira tun tana ɗan jin kunya har ta sake sosai tana hira da shi, sun jima sosai a gidan sanan suka yi masu Sallama daga nan gidan Ummy ya nufa a nan ma sai da suka sha hira sosai suka wuce gida.

Washegari wuraren ƙarfe goma na safe jirginsu ya ɗaya zuwa Abuja 12:30 suka isa kai tsaye suka wuce gidan Asad dake Abuja, an gyara ko'ina na gidan kamar mutane na rayuwa a ciki.

"Yaya waya gyara gidan naga ko'ina fes..."

"Gyarawa ake"

"Wa ke gyarawa?"

"Aljanu"

Ya fada yana kashe mata ido kamin ya fada mata cewar akwai masu aiki dake kuka da gidan duk lokaci da zai zo yakan kiransu su gyara ko'ina.

BAYAN SATI BIYU

Kamar yadda Asad yai mata alkawarin saka ta a makarantar be saba alkawarinsa ba, duk kuwa da kasancewar cikin nata wata huɗu ne ya lokacin har da yan kwanaki a kai, amman a haka ya aminta ya saka ta wata makarantar kudi ce da ke nan Abuja ta masu koyon karatu da rubutu da kuma wayenda ba su samu damar kare karatunsu ba.

Karfe 8 ake zuwa a taso sha biyu ga irin su ƴan jss2 Gaba daya makarantar da turancin ake magana tambaya da kuma bada amsa ko da kuwa tsakanin dalibi da dalibi ne, ta ji tsoro sosai ganin irin ka'idar makarantar sai dai hakan ya saka ta kara dagewa da maida hankalin wajen ganin itama ta iya turancin kamar sauran, ba musulmai kadai ba ne a makarantar akwai kistoci, har da matan aure da yan mata a ciki akwai maza akwai mata sai dai bangaren mazan dabam matan ma bangarensu dabam, hijabi har ƙasa take sawa da ñiƙaf da safar hannu da ta ƙafa, Asad Shi yake kai ta ya dauko ita idan sun tashi, idan ma ba shi da time sai dai ya ce ta jira shi idan ya gama ya zo ya dauke ta wani lokacin da yar  kula ta abinci take zuwa kamar wata karamar yarinyar, domin kuwa cikin nata na kara girma cin abincin ta ya karuwa abun har mamaki yake ba ta. zuwa yanzu cikin nata har ya fara tasowa............✍️

💋𝐁𝐈𝐍 𝐌𝐀𝐑𝐘𝐀𝐌💋

𝑵𝒂

𝑺𝒂𝒅𝒆𝒆𝒚𝒂 𝑲𝒂'𝒐𝒋𝒆

08149979652

*Book 2*

_______Karatun da ta ke a yanzu ya fara zame mata da wahala saboda Islamiyya da take zuwa da yamma makaranta ta matan aure wacce ake zuwa karfe uku a taso biyar, Ga kuma cikinta da shiga wata bakwai da shi a yanzu, ba wata wahalar ta ke ba bayan nauyin da cikin ke mata sai kuma yawan zazzabin da saurin fushi, sai dai bata nunawa a gaban Asad saboda ta san halinsa yana ganin wani abun zai iya hana ta karatun ko yanzu da be ga wani abun ba yana fadar wahalar tana ma cikin yawa balle kuma ya gono ai a take zai hanata zuwa makarantar.

  cikin ikon Allah tana gane karatun sosai na bokon da na Islamiyya sannan kullum dare sai Asad ya yi mata bitar karatu na Boko da na Islamiyya hakan yasa abubuwan ke zuwa mata cikin sauƙi domin sai ta ce ma tafi gane karatun Asad akan wanda aka mata a makaranta,

Wata biyu kenan da kawo lefensu Afreen, haka Jumayma da Baby

Duk lokaci ɗaya aka kai musu lefe. An saka buki nan na wata ukku tun da suka zo Abuja bata koma birnin Kebbi ba da dai shi Asad ya je ya yi yan kwanaki ya dawo.

tun daga lokacin kuma aka soma shirye shiryen ta kowanne bangare, tun saura sati biyu aka gama gyaran gidan Amare Afra da Afreen dake Sokoto kasance a gida ɗaya zasu zaune kayan ɗaki iri ɗaya aka musu color ce kawai ta babbanta hatta kayan cikin duk iri ɗaya ne, haka Baby ma komai iri ɗaya aka musu, Asad manya kuɗaɗe ya fitar domin hidimar bukin ya so ya yi ma Jumayma kayan ɗaki kaman na sauran ƙannensa sai dai su Bappa ba su amince saboda hakkinsu na, tun ba su samu damar yima

Nainah ba, dole ne su yi ma Jumayma, duk da hakan Asad bai bar Amma haka ba kuɗi masu yawan gaske yaba Amma ta sai kayan Kicin a matsayin na Uwa, kuma tayi farin ciki sosai da hakan a ɓangaren Aliyu ma ya bata gudunmawarsa kai da yan gidansu ma kowa ya yi iya kacin ƙoƙarin sa, Aure saura sati ɗaya su Ammi suka dawo birnin nan gidan Amma suka sauka hakan zaifi musu sauƙi kuma Amma zata ji daɗin hakan sosai.

Amare hudu duk kansu a nan gidan Ummy suka dawo taci gaba da gyara su, cikin kanƙanen lokaci suka sauya kaman ba su ba, sunyi kyau har sun gaji.

 

Ranar Alhamis su Nainah suka iso.

Washe garin ranar Jumma'a akai Walima akai Dinner, sai da kowa ya halarta sannan daga baya Nainah da Asad suka iso, ta sha kyau abunta ita kanta ta san ta yi kyau domin wani tsadadden lace din ne mai fitar da farin mutum ta saka , ga kuma kitson da aka mata suka sauko har gadon bayanta, kuma tai sa'a Asad ya bar ta ta fidda gashin sai dai be barta ta yafa karamin gyale kamar yadda kowa ke yafawa ba nata babba ne hakan be hana ta yin kyau ba, An zubar da kudi sosai a gurin karin har take ganin kamar hakan be dace ba, angwaye da Amare sun sha kyau sosai, duk inda Asad yai yana rike da Hannunta karin ma bayan yayi musu sai ya dawo gurinta yana ta mata karin ita ko har kunya ta ke ji saboda cikin dake jikinta, bata taɓa daukar cewar Asad zai iya rawa kamar haka a gaban mutane ba, ba wani rawa yai can sosai ba amman yana takawa a hankali yana wasa da Hannunta ta suna tsaye da Amrat yar Hannatu ta zo tai masa kari ta dauki hoto da shi, na ji zafi sosai shi kansa sai da ya lura da hakan har yai murmushi.  An yi dinner lafiya washegari ya kama Assabar sai aka rabu wasu suka tafi gidan Iya wasu kuma suka tsaya a nan gidan Ummy a inda akai na su Afreen da da Afra da Jumayma.

A daren aka tafi da su Afreen da Afra zuwa Sokoto tare da Nainah da duk kuwa da kasancewar Asad be so haka ba, ita kuma lake sai ta tafi kuma Ummy ta saka baki a dole ya kyale ta ta bisa sharadin kwana biyu zata dawo. Jumaymah da baby ko waccensu ta tare a ɗakinta.

Kwana nan ta biyu a Sokoto ta dawo kaman yadda Asad ya ce, an gama buki da sati biyu suka koma Abuja.

Asibitin da ta ke awa likitar ta fada mata Edd ta, tun daga ranar Asad be sake ba ri ta tafi makaranta ba fita ma baya bari tai kullum tana gida idan yana gurin aiki kuma yana yawan kiranta wai ai wani lokacin ba a lokacin da suke fada mutum ke kaiwa ba wani sai yafi wani kuma ba zai kai ba, siyayya kayan sakawa ta babu abunda be siya mata ba, na jariri ne kawai be yi ba wai ba zai siya na mata a haifa masa namiji ba ba kuma zai siya kayan maza a haifa masa mace ba dan haka sai idan ta haihuwa zai hada komai na jariri sai dai ya siya wasu kadan da maza ko mata duka za a iya saka musu. fargabar yadda zata haihu ya hanata sukuni tana jin tsoro ta yadda da ko ya za su fito cikinta duk girman cikina a ce ta nan da zai fito a duk lokacin da ta tuna sai hankalinta ya tashi, ita da ko motsi cikin yai sai ta ji tsoro balle kuma ace haihuwa, wannan yasa na matsawa Asad akan ya mayar da ita gida gurin Amma ta haihu a can, cewa yake wai ko haihuwa tai a gurin Ummy zata zauna.

"Mai ciki..... Mai ciki...."

Tana kokarin zama yake ce mata haka yana mata gwalo kamar wani karamin yaro, fillon kujerar ta dauka na jefa masa tana dariya sai ya shi ma yasa dariya yana zolayarta.

" idan fa zaki haihu ni zan miki nakuda"

"A ina a taba ganin namiji yayi nakuda?"

"Za'a fara aka kaina".

Ya fada yana daga mata gira daya sai kace wani tsoron dan iska.

"Ni dai dan Allah ka daina jana ka bar ni na ji da cikin nan"

Ta fada ta a nishi daker daman haka take idan suka motsa sai su haye mata zuciya daker take numfashi, taso yai ya dawo inda take zaune ya duka gabana ya bude cikin yana kallon yadda yake motsi sai kuma ya dora kansa sama ya lumshe ido yana murmushi, kamin ya ciro wayarsa ya fara daukata video

Ko da na shiga watan haihuwa ta zama wata abar tausayi, domin zama da kyar ta shi da kyar

Ana sauran sati Edd na ya cika ta je asibiti sai suka rike ta bayan sun mata hoto sun duba.abunda suka fada mata wai ba zata iya haihuwa da kanta ba, taga cikin tashin hankali marar misaltuwa, ba ita kadai ba har da yan gidansu da kuma Ummy da Asad sai a lokacin ne na san cewa abunda ke cikinta hudu ne ba biyu ba kamar yadda Asad ya boye mata,

yana gurin aiki ta kira shi a waya ta fada masa bata jindadi tana jin cikin yana mata motsi sosai kuma tana jin ana sukanta baya, da sauri ya zo ya dauke ta suka tafi asibitin, sai aka ce musu ba haihuwar ba ce haihuwar dai tana kusa amman ba ita ce, haka suka kwaso suka dawo gida tare da maganunguna da suka rubuto mata. Sai gani washe gari kamar ba ita bana yi kwaliyata na chakire kamar ba ita ba ga wani uban turaren data zuba ta sha doguwar rigar Atamfa ta na yi daurin dankwalina ture ka ga tsiya. Sannan na shiga kitchen ta girka musu jalof din taliya da vegetables, ta jera saman Dirning ta dawo falo na zauna rike da wayata tana duba Grp WhatsApp dinsu na family.

Tana jin lokacin da Asad ya faka motarsa ya fito ya murdo kofar falon ya shigo hannunsa da leda.

"Sannu da zuwa"

" Baby wannan kwaliya fa? Acancan ai wannan kwaliyar kamata yai ace tukuici za a baki, kuma ba abun a baki tukuici ba ga ki da tulelen ciki, da na taba ki kadan ki fara kuka kina cewa bani da tausayi"

Dariya tai ta yunkura ta mike tsaye ta mika masa bakinta sukai wa juna kiss kamar yadda suka saba sannan ta karbi ledar hannunsa.

"Gaskiya kin yi kyau babyna"

" Thank you"ta faɗa tana kanenn masa ido kamar yadda yake mata sai ya kyalkyale da dariya ya rikota ya zagaye hannayensa da cikinta

"I love you, sarkin raki"

"Aiko ina da kokari"

"Za mu gani idan za ki haihu"

"Ai ba zaka gani ba, idan zan haihu sai dai na baka labari"

"No ba zan yarda ba, ba za ki haihu hannun namiji ba kuma a gabana za ki haihu da ni za a shiga, kin san fa ance akwai likitocin da suke ketawa mace haddi idan za ta haihu kuma ni ba zan yarda wani ya ganki ba, sai dai mace yar'uwarki".

Murmushi nai daman ta san za a rina yadda yake yawan nuna kishinsa ba zai iya yarda wani mijin ya karbi haihuwar ta ba, ko jiya da muka je asibitin sai da ya saka aka nemo masa mace ta duba

19 / 20