Bin Maryam Book 2 Complete Sadiya Kaoje

Author :  Sadiya Kaoje Category :  Read Hausa Novels

Chapter   16 / 20

45K to 48K   out of 59.4K words

ya zama da shi mijinki zai gane ki, ko wane guri ya tafi idan ya ji kamshin turaren ke zaki fado masa a rai, turare yana da fa'ida sosai a gurin ma'aurata, ko da yaushe ki kasance a cikin tsafta da kamshi"

"To Mommy"

Mommy ta hada wasu turarunka ta bata tace tai amfanin da su, sannan sukayi mata Sallama suka wuce..............✍️

💋𝐁𝐈𝐍 𝐌𝐀𝐑𝐘𝐀𝐌💋

𝑵𝒂

𝑺𝒂𝒅𝒆𝒆𝒚𝒂 𝑲𝒂'𝒐𝒋𝒆

08149979652

*Book 2*

_______Naina ta samu tarba ta Mummunan a wajen Ummy abinci kala ta girka mata na zamani da na gargajiya, abin ka da mai ciki duk yawan Abin sai da ta ko wanne kaɗan don duk sun burgeta.

Nan yan uwanta suka rika kiranta suna mata Allah hutar da gajiya ciki har da Mommy anan ana sai da taƙa yi mata na shiha mai shiga jiki.

Godiya ta ƙara yi mata, har ga Allah matar tana burgeta sosai.

Kowa sai da ya kira a gidan har da Amma.

Bayan sun ɗan huta Ummy ta kira Nainah a ɗakinta,

"Junainah Ke yarinya ce na sani, amman daga lokacin da kikai aure zancen yarinta ya kare sai dai a kira ki yarinya saboda shekaru ko kuma wani abun da za ki na shirme ko rashin tunani, ballantana yanzu da kike dauke da juna biyu,

Mijinki na bukatar kulawarki a yanzu fiye da ko yaushe, na san ba ki san wata dawainiyar ba, amman kula da abincinsa ya ci ko be ci ba yana wuyanki a yanzu, karki zamana shi kadai zai dinga damuwa da ke, ki shimfida masa mkalar rayuwar da kike son yai saboda yana tsananin son ki ni na sani, na san ke ma kuma kin san da haka, ki rika yi masa abunda zai kwantar masa da hankali da saka shi natsuwa, hakan ba karamin kara mishi son ki zai yi, a yadda yake damuwa da ke kuma yake son ki idan kina nuna masa damuwarki akan rashin cin abincinsa tun ya dawo daga Sokoto baya cin Abinci yadda ya kamata, amma kin ga yanzu zai ci saboda gudun damuwarki, sannan ki rika yi ma mijinki addu'a a duk sallah musamman a sujadar karshe da kuma bayan tahiya kamin ki sallame, mace mai aure ma ba akarbar addu'arta har sai idan tana yi ma mijinta da kuma iyayenta.

"Na gode Ummy kuma ina sha Allahu zan kiyaye".

"Sannan ke ma ki kula da kanki, wani abun ba sai ance ki yi ba, ya kamata ace kin san aure kike a yanzu, kuma ke ce kadai a gurin mijinki, mijinki na bukatarki a yanzu fiye da ko yaushe, ina fada miki wannan ne saboda na san zaki iya kuma ke kadai na ke da tabbacin za ki saka shi cikin walwala a yanzu, mijinki be iya so ba, be iya ki ba, ba kuma iya sakawa rai abu ba, idan yana so gaba daya yake so baya ganin aibun abun har sai yayi zurfi a ciki, idan kuma ya tsane abu gaba daya yake tsanarsa baya iya ganin kyaun abu har sai yayi nisa a tsanarsa, idan kuma ya sakawa rai abu yana sakawa sosai ta yadda rashin abun nan zai yi ta damunsa yana cinsa a rai, daga ke har shi ni duk kallon yara na ke muku wani abu dole sai an nuna muku, saboda mun fi ku tunani da hangen nesa, na san ba ki yawance a komai ba, sai dai ke din jajirtacciya ce saboda gwargwarmayar rayuwa da kika sha, da kurciyarki kin fuskanci kalubale kala kala na rayuwa kamin yanzu, kuma da Allah ya tashi miki sakamako sai yai miki duka a lokacin da kike bukatar hakan, hakuri yana da kyau kuma yana da riba sosai duk wanda yai hakuri be ga riba ba to kadan yayi"

Sosai ta jidadin magangannun Ummy, a natse ta fada mata komai kuma ta fahimci manufar da nufi, daga lokacin ta sakawa kanta zata iya, kuma ta fara jinta a matsayin mace mai aure mai daraja wacce zata iya kula gidanta da mijinta da kuma yayanta duk kuwa da irin karancin shekarunta waiwaya baya kadan ta tuna abunda ya faru da ita irin halin rayuwar da suka shiga da fadi tashi da tai sai ta ga wacan rayuwar kamar labari aka ba ta ba ita ce ba.

"Tashi ki bi mijinki".

Maganar Ummy ta katse mata tunanin da take.

"Ba ki bukatar komai dai ko?"

"A'a Ummy"

Ta fada tana mikewa tsaye ta dauki Hijabinta ta saka, sannan ta fara takawa a hankali har ta fito falo.

  A hanya ya rika tambaya ko tana son wani abu, sai ta ce masa bata bukatar komai, amman duk da haka sai da ya tsaya ya siya mata gassashiyar kaza da kayan marmari.

"Bana jin yunwa fa"

"Za ki iya bukata da dare ai, kuma ba dan ke kadai na siya ba"

"Ni da wa?."

"Unborn..!"

Ya fada fuskarsa cike da walwala. Har suka isa gida bata sake ce masa komai ba shi ma kuma be ce mata ba, har sai da ya faka motar ta kai hannu zata bude.

"Tsaya ba ri na bude miki"

Fita yai ya zagayo gefenta ya bude mata motar ta fito sannan ya rufe, tana gaba yana bayanta har suka shiga cikin falon, sai ya zauna saman sopa yana kallonta

"Na hada maka ruwan wanka?"

"Zo nan Baby nayi Missing dinku"

Zuwa tai na zauna saman kafafuwansa kamar yadda ya bukata sai ya rumgumeta yana sauke ajiyar zuciya a hankali sai dai hakan be hana ta jin saukarta. Sun dade a haka kamin ya barta ta daga jikinsa Su shiga daki, rumguma da kiss na cikin abunda Asad ya ke so kuma ita ma take so domin yana jin natsuwa sosai idan ya rumgumeta hakan kuma yana kara mata jin son kusanci da shi sosai. Cikin jikinsa ta kwana kamar kullum, A lokacin da suka gama sallah asuba kuma sai ta nufi kitchen ta barshi a dakin yana karatun Alqur'ani ita kuma ta shiga ta kunna gas din ta sarrafa dan abunda ta iya na ruwan zafin tea da suya kwai da dankali.

"Eyye! da kanki kike girki, na fada miki bana son wahalar nan da kike miyasa ba ki jin magana? Baby?".

"Dan na yi aiki ba komai cikin zai yi ba, kuma ni bana son abincin waje"

"To amman sai ki bari idan na gama karatu na hada ko?"

"Bana son girki na namiji"

“Kin taba jin inda da zai ce baya son abincin babansa”

"Haka dai yace wai babansa be iya girki ba, idan ma yayi babu dadi shiyasa nake turo min shi nai amai"

Ta fada tana yatsina fuska, sai ya kara matsowa kusa da ita ya rika hannayena.

“Karki masa karya, na san ba zai ce haka ba, ta ina ma kika ji ya ce haka? Yaushe kika iya karya”

"Uhmm!"

Ta fada da cike da kunya, sai yai murmushim gefen fuska yana aje numfashi. Shi ya taimaka mata ta karasa hada komai, sannan suka karya, be wani ci da yawa ba shi ma kuma dan na matsa masa ne, ita kan ta ci abincin sosai kamar wacce ta kwana da yunwa, ita kanta har mamakin yadda ta ke cin abinci sosai a yanzu

***** *****.

Kaman yadda Bappa ya faɗa bayan sun dawo Asad ya nemi mutumen da ke kula da gidajen gadon su Junainah, da yamma suka wuce can tare Junainah sai da suka zagaye gidajen gabaki ɗaya taga yadda tsarinsu yake anan ta zaɓi wayan da take son mutumen ya damƙa mata keys ɗin da takardun sanan suka wuce, kai tsaye gidan Zaliha cikin Sa'a ko suka tarar da ita, Zaliha sai da tayi gaske sanan ta gane Junainah suka rungume juna suna kukan farin ciki, "Junainah a she zan sake ganin ki a rayuwata? ba in da banyi nemanki ba har gidan su Jamila ne je neman ki, suka ce min ba su san in da ki ke ba, ya jikin Mahaifiyarki?".

A jere Zaliha take mata tambayoyin.

"Amma taji sauƙi Anty Zaliha".

"Allah sarki, wallahi ba in da banyi neman ki ba, har matar da ta nema Miki aiki ta tuntuɓeta ko ta sanan inda ki ke".

"Ya bayan rabuwa Anty Zaliha?".

"Mun gode Allah Junainah".

"Wanan fa Junainah?". Zaliha ta tambaya tana kallon Asad.

Nainah ta sunkuyar da kai tana Murmushi,

"Bakwa kama balle nace yayan ki ne, ta yi Murmushi a karo nan biyu,

"Kinyi Aure ne Nainah?".

"A hankali ta gyaɗa mata kai".

"Allahu Akbar!, Nainah yanzu wannan shine mijin ki? bayan wuya sai daɗi lallai Allah ya yi gaskiya mai haƙuri yana tare da nasara, Allah ya baku zaman lafiya mai ɗorewa da zuri'a mai Albarka".

Tace Amin a hankali.

"Ranka ya dare ina tayaka samun mata tagari irin Junainah".

Asad ya yi Murmushi.

"Nayi farin cikin sake haɗuwa dake Junainah da kin ƙara kwana biyu zuwa ukku da baki sameni ba a gidan nan".

"Lafiya?".

"Kuɗin haya na ne ya ƙare kusan wata biyu shine mai gidan ya ce na bashi gidansa yanzu haka shirye shiryen ta shi nake, abincin da dake seyarwa komi tsaya cak labarin ƙasar sai Addu'a".

Ki Kwantar da hankalin ki Anty Zaliha in sha ba ke ba gidan haya har abada."

Ta ƙarasa maganar tana miƙa ma Zaliha makullin gida tare takardun tana faɗin, "ga wannan".

cikin feshin fahimta Zaliha tasa hannu ta karɓi key ɗin gidan tana kallon Junainah.

"Wannan kuma na mike Junainah?".

"Takardun gida ne kuma mallakin ki".

Zaliha ta miƙe tsaye da saurin tana kallon Junainah,

Junainah ma tamiƙe tsaye a hankali tana Kallonta, "don Allah kar abin ya baki mamaki Anty Zaliha bazan taɓa biyanki a bin da ki kayi min".

Ta duƙa a hankali ta ɗauki ɓakar ledar da suka shigo da ita ga wannan ki ƙara jari".

Jikin Zaliha na rawa ta karɓi ledar tana buɗewa kuɗi ne cike a cikin da sauri ta saki ledar tana ja da baya,

"Anty Zaliha na san kina cikin ruɗi bana son ki min mummunan fahimta duk abin ki ke gani a nan halattacciyar dukiya ce, a baya baki san ko ni wace, daga nan ta soma bata labarin komi daki daki, nan take jikin Zaliha yai sanni ta rungume Junainah tana kuka mai tsuma Zuciya.

"Na gode sosai Junainah da halaccin Allah ya jiƙan Mahaifinki da rahama Allah ya kai ladan a kabarinsa, haƙiƙa basan da wane baki san gode Miki ba! Ina godiya sosai".

"Tsakanin da ke ba godiya Anty Zaliha, har yau ban biya da abin da ki ka min ba, kin taimake ni a lokacin da nake buƙatar taimako, kin tsayamin a lokacin da na rasa bangon jingina".

"Duk abin nayi Miki domin Allah na yi banyi don wata rana nace sai kin biyani",

"Na sani Anty Zaliha duk abin da ki yi domin Allah ki kayi, Shiyassa Allah ya kawo miji mafita a lokacin da ki ke buƙatar ta".

Zaliha ta duƙusa har ƙasa cikin ladabi tayi Asad godiya,

"Sanyi sai ki taso muje a nuna Miki gidan, tare suka wuce gidan mai kyau da tsari daƙi ukku da falo da Kicin tayi farin ciki sosai da garin gidan ko'ina na gidan sai da ta duba sanan suka maida ta gida, Asad ya faɗa mata zai aiko da mota a kwashe kayanta zuwa sabon gida, tayi Mishi godiya sanan Nainah ta karɓi Number suka wuce.

Daga gidan Zaliha kai tsaye suka wuce gidan Baban Jamila gidan duk ya hargitse, ɗakin da sukayi rayuwa a ciki ra tsurama ido komi na dawo mata tiryan tiryan, wasu zafafan hawaye suka zubo mata tasa hannu ta share kwallon tana ci gaba da kallon gidan,..

"Baƙi mukayi a gidan?."

Cewar Innar Jamila sam bata gane Junainah ba, Junainah ta finu wajenta da ɗan sauri sauri ta rungumeta tana faɗin ,"Inna ina wuni?".

"Muryar wa nake ji kaman ta Nainah?".

"Ni ce Inna."

"Allahu Akbar! Junainah daman kuna raye?"

"Muna raye inna, Ina Jamila da Baba?".

"Jamila ai tayi Aure kusan wata huɗu kenan tana kalgo yauma tace zata shigo, Baba Kuma ga shi can ɗaki a kwance kusan wata biyu kenan yana jinya".

"Subuhalillahi me ya same shi?".

"Mashin ya buge shi ya ƙare a kafa amman da sauki sosai don har ya fara takawa".

"Allah ya ba shi lafiya ya tsaye gaba kuma,

"Amin, Ya jikin Murjanatu?".

"Yaji sauƙi sosai".

Suna tsaye a wajen wani mai mashin roba roba ya yi fakin a ƙofar gidan Jamila ta shigo cikin gidan, tayi kyau Abin kaman ba ita,

"Inna Baƙi mukayi?".

Jamila ta faɗa tana kallon Inna.

"Ba baƙi bane Nainah ce".

Jamila ta saki jikarta ta nufi wajen da Nainah take tsaye ta rungumeta cike da farin ciki murna marar misaltuwa.

"Nayi kewarki Sosai Junainah ina Amma?".

"Nima nayi kewarki sosai Jamila, Amma tana nan lafiya lau take".

"Ɗauko ta barma ta zauna mun barta a tsaye tun ɗazu".

Jamila ta shiga ɗakin da saurin ta fito rike da tabarma ta shimfiɗa musu suka zauna,

Bayan sun gama gaisawa Nainah ta shiga ɗakin ta gaida Baban Jamila dake kwance ƙafarshi daure da kara irin ɗaurin nan gargajiya. Ya jima bai gane Nainah ba har sai da Jamila ta yi mishi bayani.

"Allah Sarki Junainah ke ce?".

"Ni ce Baba, ya jikin naka?".

"Jiki Alhamdulillah, ya Mahaifiyar taki?".

"Taji sauƙi".

"Ina muke da zama a yanzu?".

"Garin nan Baba".

"Allah Sarki".

"Daman Baba wajen ka nazo".

"Allah dai yasa Lafiya?".

"Lafiya lau Baba". A hankali tasa hannunta ta buɗe hand bag ɗin ta ta fito da takardun gida da key ta miƙa masa daga kwance da yake, a hankali ya mike zaune.

"Allah dai yasa ba takar da sammaci ba ce?".

"A'a kam Baba".

A nan tayi masu bayanin komi kaman yadda tayi ma Zaliha, Baban Jamila ya fashe da kuka mai tsuma Zuciya kunya duk ta rufe shi bako ba ne ya tuna da shi sai irin walaƙanci da ya yi masu a baya,

"Kaico na! nayi da nasanin abin da na aika musu a baya Junainah don Allah ki yafe min da a bin da yai muku".

"Ba komi Baba ya riga da wuce, fata dai shine ku karɓi kyautar da naso musu da ita da hannu bibbiyu".

Maman Jamila da ita kanta Jamila kukan farin ciki suke,

"Yanzu yar uwarki Jumayma tana raye?".

"Tana raye Baba ta wajen yayan Baban mu a Sokoto".

"Allah mai iko". Cewar Baban Jamila.

"Allah ya jiƙan Mahaifinki da rahama Allah yasa ya huta".

"Amin Inna"

Haka suka rika yi mata godiya suna sa mata Albarka...

Bayan ta ba Baba kudin nera miyan biyu, ta sake dauki wasu 50k ta ba Jamila, Jamila ta rungumeta tana mata godiya sosai, tare da Inna da Jamila suka tafi ta nuna musu gidan suka ga ko'ina sanan suka dawo Inna tayi ma Asad godiya sosai, basu bar gidan ba har sai Asad tabbatar musu da cewa zai aiko da moto a ƙashe kayan su zuwa sabon gida, Jamila ta karɓi number Nainah tare da yi mata alƙawarin kawo mata ziyara wata rana. Da wannan sukayi sallama.....

Cikin kwana biyu Zaliha ta tare a sabon gidanta, haka Baban Jamila ma cikin sati ɗaya suka tare a sabon gidansu.

Ranar Alhamis Zaliha da Jamila suka je gidan Nainah abu kaman haɗin baki, isowar Jamila bada jimawa Zaliha ta iso, haka suka hini a gidan cikin farin ciki Nainah sai nan nan take su, sai da yamma sukayi mata Sallama zasu wuce gida bayan ta cika su da Alheri mai tarin yawa,

**** *****

*JUMAYMAH*

Tana zaune a falo waya na manne a kunnenta,

"Jumaymah..!"

"Na'am"

Ta amsa a hankali, ya ci gaba da magana cikin sanyi murna," ina son mu mufara maganar Auranmu saboda ina son naje na ga magabatanki domin babu maganar wasa , idon zai yuwu sai ciki gaba da karatu a gidana, Amman ya kika gani?".

tayi murmushi kaman tana a gaba shi,

"Hakan yana da matukar amfani musamman yadda muke matukar kyaunar junanmu yin Aurenmu shine yafi da cewa".

"Na gode sosai da kika bani wannan dama kuma in sha Allahu zan yi ƙoƙarin faranta Miki rai, haka dai sukaci gaba da bayyana ma junansu kalaman soyayya..

kamar yadda Ummy ta fada mata tana iya ƙoƙarin wajen ba Asad kulawa, sannan kullum tana waya da yan gidansu.

idan suna gida a jikinsa ta ke wuni idan kuma sun taho gidan Ummy idonsa na kanta da ta yi wani abun da ba daidai ba sai yi mata alama da ido. Ummy ma tana kula da ita har zaman da ke kusa da kofa sai ta fada mata wai mai ciko bata zama a bakin kofar dakin ko kusa da kofa aaboda aljanu, ita dai abun har dariya ya ke bata sai dai bata yi a gabanta Ummy, abun har mamaki yake bata wata kila kuma saboda suna son cikin ne suke ganin komai be dace tai yi ba. Shi kanshi Asad da safe sai ya mata addu'a har a cikin haka ma da dare idan zata kwanta. A ranar da suka wuni gidan Ummy take masa maganar karatunta sai ya nuna mata baya so.

"Ummy ga ciki kuma ace tai karatu? Haba abun ai sai yai dawo, da karatunta zan ji ko cikin dake jikiñta"

"Wai a kanku aka fara ciki ne? Karatu ko na islamiya sai ta fara da shi a yanzu, saboda kula da kanta da addu'oi, ai ilmin mace yana da muhimmanci ba wai ko dan aiki ba, saboda kula da yayanka ma ta koya mu su, kuma

16 / 20