Bin Maryam Book 2 Complete Sadiya Kaoje

Author :  Sadiya Kaoje Category :  Read Hausa Novels

Chapter   12 / 20

33K to 36K   out of 59.4K words

ga Mahaifiyarta da yar Uwar ba".

"Okey, yanzu yaushe ya kamata muyi tafiyar?".

"Nan da kwana biyu zuwa Ukku".

"Okay Allah ya Kaimu".

"Amin".

"Bari na saya muna tiket".

"A'a da mota zamuyi tafiya nan tun da ba wani nisa".

*BAYAN KWANA UKKU*

Bappa bincike sosai ya yi akan gidan su Asad daga ƙarshe ya gano ashe ma sun san juna shida Dr Kamal shine likitan da lula da maifinsu kafin Allah ya yi mishi rasuwa, hakan yasa ya sanar da shi zuwan da Zaiyi gidansa sai dai bai faɗa masa abin zai kawo su ba. Dr Kamal sosai ya yi mamaki zuwan da Bappa Zaiyi gidansa. A ranar ya sanar da Ummy zuwan na su.

Abinci kusan kala Ukku Ummy ta shirya musu ko da goma na safe tai gaba dayansu sun shirya Afra da Afreen sukai wanka . Sai misalin sha daya Bappa ya kira Daddy ya sanar dashi sun shigo gari

sannan ne Ummy ta saka su Afreen suka kwashi kulolin abincin suka jera part din Daddy, ita kuma ta kuna turaren wuta irin mai kamshin nan sosai n ta kara kunna dayan ac sannan ya dawo part dinta, Wani dadi ne ya lullube ta ganin duka yayan nata sun fito fes gwanin sha'awa. Suna jin tsayawar mota sukai hanzari yafa gyalensu suka jiyo bayan Ummy.

Kusan mota biyu Masu Kyau da tsada, sai motar sojoji a baya.

Suna fitowa daga motar Ummy na fitowa ita da su Afreen suna musu sannu da zuwa Junaid da Jamil ne suka fara fitowa sanye suke da shaddar irin ɗaya, sai Sadiya, ɗayan motar kuma Ammi ce da Bappa sai Jumayma dake sanye cikin baƙar Abaya ta rufe fuskarta da niƙab...

"Sannun ku da zuwa".

Ummy ta fada tana kokarin sauka daga balcony din ta nufi inda suke, sai duk suka saki murmushi suna kallonta.

"Sannu da zuwa"

Daddy ya faɗa cikin girmamawa

Sannan yai gaba zuwa part dinsa yana musu iso sai suka bishi a baya..........✍️

💋𝐁𝐈𝐍 𝐌𝐀𝐑𝐘𝐀𝐌💋

𝑵𝒂

𝑺𝒂𝒅𝒆𝒆𝒚𝒂 𝑲𝒂'𝒐𝒋𝒆

08149979652

*Book 2*

______Sosai suka ci dadin yadda aka tarbesu a gidan, bayan sun gama cikin abinci Ummy ta dawo falon domin tambatayar su ko suna buƙatar wani abu, karab idanuwanta suka sauka kan Jumayma dake zaune kasan cewar Daddy ma baya cikin falon cirko cirko sukayi suna kallon ikon Allah da badon a gaban su suka ga isowarsu da zasu dauka Junainah ce,

Mamaki ƙarara a fuska Ummy ta nufi cikin falon hankalin ta da tunanin duk suna wajen Jumaimah.

"Uhh.. na ce ba ko akwai abin da kuke buƙata?".

Ta faɗa Murya na rawa".

"A'a wallahi mun gode sosai da karramawa". Ammi ta faɗa tana Murmushi. Ummy ma ta saki murmushi karfin hali.

"Dr idon ba damuwa ina son zakuyi magana". Bappa ya faɗa yana kallon Dr Kamal.

Daddy ya nemi wuri ya zauna yana kallon Jumayma.

"Toh bari na ɗan baku wajen har ku gama maganar". Cewar Ummy tana ƙoƙarin barin falon.

"Ai da kin zauna Kema".

Ummy ta nemi wuri ta zauna.

Bappa ya yi gyaran Murya sanan ya ce,"Dr mun zo ne akan maganar wata yarinya da kwanaki aka saki video a social media, bayan binciken da nayi na gane yarinyar a gidanka take".

"Junainah kenan?".

"Ehh ita,Yar wajen ƙanena ne Yusuf wannan kuma da kuke gani Twins sister ta ce, sunanta Jumayma". Daddy ya kalli Jumayma cike da mamaki.

"Nasan zakuyi mamaki".

"Gaskiya ne, sosai, Ya kamata murjanatu na kasance a wajen nan domin maganar ta shafeta". Ummy ta faɗa tana kallon Daddy.

"Wacce Murjanatu?".

"Mahaifiyarsu". Ummy ta ba Bappa amsa kai tsaye.

Ummy ta mike zuwa Bq ta kira Amma.

"Ammi zan bita". Jumayma ta faɗa cikin zumuɗi

"A'a ki bari tun da ba jimawa Zatayi ba".dole ta dawo ta zauna.

*AMMA*

Tun wayewar gari take jin faɗuwar gaba jikinta duk a sanyaye ya ke, takanji faɗuwar gaba ta wani ɓangare kuma takanji sanyi a zuciyarta saboda rayama ta da Zuciyarta take na muradin ganin abin da ta jima bata gani ba, ko da Ummy ta shigo zaune take ta tabka tagumi, cikin wannan yanayi Ummy ta ta sameta

"Assalamu alaikum!"

Ummy ta yi sallama har sau uku amma bata ji ba saboda ta yi nisa a duniyar tunani, Sai da Ummy ta tafata saurin sauri juyowa tana kallon Ummy ita ta sakar mata murmushi.



"Lafiya mi ke damunki?".

"Ba komi".

"Daman baƙi mukayi shine nace bari na kiraki ku gaisa".

A sanyaye Amma ta baro Bq ɗin bugun Zuciyarta na tsananta cikin daurin suka ƙara falon Ummy ce a gaba Amma na biye da ita a baya, Jumaimah na ganin Amma ta mike tsaye da gudu ta iso wajenta ta rungumeta tana kukan farin ciki, wani irin shock ya kama Amma jikiñta ya yi wani irin sanyi kaman wanda aka tsoma cikin ƙanƙara.

"Ma..ma...na...! nayi kewarki sosai Jumayma ta faɗa tana kuka, Amma ko tuni tayi mutuwar tsaye tun lokacin da tai Arba da Bappa,

"Innalillahi wa'inna Ilaihir raji'un! Yusuf....!" ta faɗa a hankali a tashe tana ƙoƙarin faɗuwa ƙasa da saurin Ummy da Jumayma sukayi saurin riƙe ta ta faɗa jikin Ummy,

"Ma...ma...! Don Allah ki dena kuka yau ranar farin ciki ce a garemu Mama na jima ina kwaɗarin zuwan wannan rana mai cike da ɗinbin tarihi a rayuwata Mama Ina yar Uwata Junainah?".

Amma ta fashe da kuka, Ummy ta riƙa shafa bayanta tana lallashinta cikin wani irin yanayi mai tsuma gangar jiki Amma ta ƙarasa cikin falon Jumayma na riƙe da hannunta kaman makaho da ɗan jagora, hankali Amma gabaki ɗaya baya wajen Bappa, Murya na rawa ta ce,"Yusuf daman kana raye ba ka mutu ba? Me yasa ka tafi ka barmu cikin ƙunci da wahala Yusuf da kasan halin da zamu shiga da baka tafi ka barmu ba....!". Magana take tana kuka mai taɓa Zuciya.

Ammi ta taso tazo kusa da ita ta dafata tana faɗin ,"Wannan ba Hamma Yusuf ba ne,Yayansa ne Uwa ɗaya uba ɗaya".

"Amma ta ɗago da sauri tana kallonsa sai yanzu ta fahimci ba Yusuf ɗin ta ba ne, koda yana raye ba zai tsufan wannan ba, duk da shina wannan ba wani tsufa ya yi ba sosai saboda hutu.

Share hawayenta ta yi sannan ta bisu ɗaya bayan ɗaya tana kallonsu cike da matsanancin mamaki, Jumayma ta Kwantar da kanta jikin mahaifiyarta tana jin ɗuninta da rasa shekaru masu yawa.

Bappa ya ce,"Abin da Bahijja (Ammi) ta faɗa miki gaskiya ne ni yayan Yusuf ne, wannan ita ce matata Sunanta Bahijja, sai Ƴaƴana Jamil, da Junaid, sai Sadiya.Wannan kuma dake kusa da ke yarki ce Jumayma".

Amma ta kalli Jumayma dake kwance a jikiñta da saurin tana ɗago da fuskantar domin ta tabbatar.

"Tabbas wannan ƴata ce Jumayma koda shekaru sun ja zan ganeta saboda kamannita da yar Uwarta Junainah.... Daman ina ji a jikina kina raye ƴata Allah na gode maka da kanuna min wannan rana... Allah Alhamdulillah!..." Ta faɗa tana kuka tana ƙara rungume Jumaimah a jikiñta kyaunar da kewarta na shiga ruhinta.

"Ya akai Jumayma ta taso hannunku?".

"Labarin mai tsawo ne". Bappa ya bata amsa yana kallonta.

"Hassan Abubakar Saraki shine sunan mahaifinmu Babban Attajiri ne kuma sanannen mu huɗe ne a wajen maifinmu Abubakar (Bappa) Jannat, Yusuf da Yasir yan biyu ne Amma Allah ya yi ma Yasir rasuwa tun suna yara, mu ukku mun taso cikin so da kyaunar junanmu, a ƙa'idar familyn mu Auren farko Bama Auren Bare sai dan zuri'armu , hakan ya samo Asali ne tun kan Hussaini ƙanen Mahaifinmu da ya yi Auren nesa wanda tun daga lokacin da yai Auren ba'a sake jin ɗuriyarsa ba daga shi har matar ya aure sai bayan shekaru sunja sosai aka labarin rasuwarsa har yau ba wanda yasan inda zuri'arsa ta ke ba , ba labarin matar da ya'yan da ta haifa, wannan dalilin yasa Kakanmu Abubakar Saraki ya bar wasiyyar ko bayan ransa bai yafe ba wani Yai Auren farko da ba'a cikin family ba, saboda duk lalaewar idon har mutum ya yi Auren a family ba yadda za'ayi zuri'arsa ta ɓace koda ko sauran sun kasance bare, ana cikin haka Yusuf ya haɗu da wata yarinya har soyayya mai ƙarfi ta shiga tsakanin su, a lokacin da Yusuf ya gabatar da ita a matsayin wanda zai Aure Mahaifinmu da Kakanmu basu amince da ƙudurinsa ba, hankalin sa ya tashi sosai, ganin abin nashi da gaskene Mahaifinmu yasa akayi abincike akan yarinyar a nan ne aka gane ashe bata hanyar Aure aka sameta ba, Yusuf ya shiga damuwa sosai har ta kaishi ga reshin lafiya kaman zai rasa ransa, Yusuf kuma ya kafe ko a haka ya amince zai Aureta tunda ba laifinta bane laifin iyayenta ne Mahaifinmu ya ce bai amince ba, daman yarinya akwai wanda ke son ta, da wannan damar Mahaifinmu ya yi amfani wajen ba iyayen yarinyar kuɗaɗen masu yawa suyi gaggawar Auren da ita, kwatsam Yusuf yaji labarin Aureta daga sama, a lokacin ya yi wata irin muguwar jinya kaman zai rasa ransa, bayan ya samu sauƙi sannu a hankali ya fara mantawa da yarinyar ya dawo yana Rayuwarsa normal, bayan wasu watanni masu yawa ya sake haɗuwa da wata yarinya itama Allah bai kaddari Aurensu ba saboda Mahaifinmu bai amince ba, ko san sau ukku Yusuf na faɗa wa soyayya Amman Mahaifinmu yaƙi amince masa, ranar kwai muka wayi gari ba Yusuf a gidan mu Hankalin ya tashi sosai ba irin nemansa da bamu ba daga nan gida Najeriya har ƙasashen wajen amma ba Labarinsa, shekaru sun ja sosai lokacin nayi Aure har na haifi su Hassan da Hussaini (Junaid da Jamil) Mahaifinmu ya bani wani fili da zamu gida Kamfani, wata rana naje ziyara a kamfanin na duba aikin da ake anan naga Yusuf cikin yan aiki masu kwasar ƙasa duk irin yanayin da yake ciki bai haka na gane shi ba, Bayan na gama yi masa faɗa na barin gida na rungumeshi ina kuka shima yana kuka a lokacin naso na sanarda iyayenmu amma ya hanani saboda kuskuren da ya aikata nan yake faɗa min bayan ya baro gida ya yi Aure harda ƴaƴa biyu mata yan biyu, ya ke cemin yasan iyayenmu ba zasu yafe mishi ba na karya Al'ƙawarin iyaye da kakanni, a nan take na sanarda iyayenmu naga Yusuf nan take Mahaifinmu ya ce yana buƙatar ganinmu, muka wuce gida tare shi bayan mun iso gidan Iyayenmu suka rufe shi da faɗa kaman zasu da keshi yana kuka ya nemin yafiyarsu nan take suka yafe mishi, sai da ya roƙi alfarma da barshi yaci gaba da zama da matarsa kaman yadda ya saba, saboda bata san waje shi ba, in don har yace zai nuna mata matsayin wannan lokaci ba lalle bane ta fahimce shi, wata ƙila reshin yadda zai biyo a baya saboda halin rayuwa da muke ciki. Sosai suka gamsu da bayaninsa, tun daga lokacin, lokaci lokacin kayan kawo muna ziyara, kuma bai fasa aikin lebaranci da yake ba a cewarsa yafi son ya ciyar da iyalinsa da guminsa, duk lokacin da zano kamfani na kalli ɗan uwana yana aiki lebaranci nakayi kuka sosai, duk halin da Yusuf yake ciki muna sane saboda muna bibiyar rayuwarsa duk wani motsinsa akan idon mu yake, a karo na biyu iyayenmu suka sake rokonsa alfarma bakan ya dawo da iyalansa cikin family kuma muyima matar bayanin komi yadda zata fahimta ba tare da ta zarge shi ba, ya nuna muna mu barshi kawai yaci gaba da rayuwarsa aka saboda yana jin daɗin haka. Ya ce muna baya son ya yi wani abu da zai tada hankalin matarsa saboda tana fama da matsalar ƙwaƙwalwa abun kaɗan zai sa ta rasa tunanin kuma Amana ce a gurinsa bata da kowa sai shi. Saboda farin cikinsa muka amince da uzurinsa na Amman don Allah ya amince ya dawo da aikinsa da yake kafin yabar gida, saboda idon ya fara aiki sannu a hankali dukiyar zata dawo ta sanadiyyar haka ya dawo cikin denginsa nan ma bai amince ba ya ce muna,ai ya nunama matar baima yi karatun boko ba, duk wata hanya da zamu bi wajen dawo da martabar Yusuf bai bamu dama ba, naso na ɗauki nauhin karatun yayansa Allah bai kaddara ba saboda ƙin amince da ya yi. Lokaci lokacin nakan je har ƙofar gidansu ina kaimishi alheri a matsayin mai gidansa na wajen aiki, sannu a hankali na fara sabawa da su Jumayma a lokacin basu wuce shekara huɗu ba a duniya Allah ya sanya min sonsu sosai, wani lokaci idon sunzo wajena sukan ce min ina kama da mahaifinsu sai dai nayi murmushi na ce musu Nima ai babansu ne, shakuwarmu dasu a kullum ƙara ƙarfi take har wani daɗi nake ji a raina ina ganin wata ƙila ta sanadiyyar yaran Yusuf dawo cikin familynsa, duk lokacin da na kawo musu ziyara sukan roƙeni akan na sanya su makaranta Musamman Junainah saboda tafiye surutu tana faɗa min tana son karatu sosai babansu yace Baida kudin sasu har roƙona take akan don Allah na sasu a makaranta tun da babansu bai da kuɗi, a lokaci na ƙuduri cewa ko ta halin ƙaƙa sai nasa su makaranta ko Yusuf ya Amince ko kar ya amince, saboda a lokacin nafi son gaskiyar ta baiyana har ga Allah ina jin zafin yadda ɗan uwana ke rayuwa a cikin ƙunci da wahala saboda kawai farin cikin matarsa, bayan na dawo gida na sanarda iyaye abin da ke faruwa da hukncin da nayenke sunyi farin cikin sosai kuma sun goyi bayana dari bisa ɗari. Sai dai abin da ban sani ba Yusuf ya na sane da komi, ranar wata jumma'a ina office a same a office ransa a bace yake roƙona Alfarma bakan don Allah na dena bibiyar rayuwarsa yanzu harta kai ga Matarsa ta fara zarginsa saboda labarina da su Junainah ke bata sannan mutanen unguwa suna faɗa mata suna ganin mai kama shi, tare da su Jumayma, a lokacin nake faɗa masa in dai har yana son na dena bibiyarsa sai dai ya bani Jumaymah ko Junainah na riƙe,a lokacin su Jamil nada shekara goma a duniya bani da wani buri da ya wuce na haifi ɗaya macce, nayi hakan ne saboda nasan ba lalle bane ya amince idon ko bai amince zan sanar mutane waye shi, da mamaki sai nayi yace ya amince in dai haka zaisa na dena bibiyarsa, naji daɗi sosai a lokacin saboda wannan ma yana cikin matakin narasa bai bar Office ɗina Saida muka tsara yadda za'ayi na dauke ɗaya daga cikinsu.

Bayan sati ɗaya da faruwar haka ranar Jumma'a na shiyar daga Sokoto zuwa birnin Kebbi da yamma lis kaman yadda na saba na nufi gidan Yusuf nayi parking a inda na saba yin parking bayan yan mintuna goma sai ga ɗaya daga cikinsu ta fito ƙofar gida yana ganin motata ta nufo inda nake da saurin na buɗe mata mota ta shiga Saida na faki idon mutane sanan na bar unguwar zuwa Sokoto, a lokacin bansan wace na ɗauko a cikinsu ba saboda kammani duk ɗaya na tambayeta sunanta ta faɗamin Jumaimah na gane yar shuru shirun ce ashe, mun ɗan yi nisa da tafiya ta fara yin kuka na maidata gida wajen mamanta da yar Uwarta ita baza bini ba, da kyar nasamu na lallasheta har muka isa Sokoto da ita, kai tsaye na fara wuce da ita gidan Iyayenmu suka ganta sunata farin ciki sannan na wuce da ita gidana,.Saida na shafe tsawon wata daya ina fama da rigimar Jumaymah akan sai na maida gida kullum cikin kuka take ranar da ta cika wata biyu a gida Yusuf ya kawo muna ziyara a ranar Jumayma ta saki jiki sosai tana ta farin ciki har tana tambatayar mahaifiyarta da yar uwarta a lokacin har nasata makarantar boko da islamiyya, lokacin da Yusuf zai tafiya ta riƙa kuka, Saida ya ce mata zaije gida yazo ya yar Uwarta da mahaifiyarsu sanan ta dena kuka, tun daga lokacin Yusuf sai ya rage kawo min ziyara sai dai muna waya da shi sosai, sannu a hankali Jumaymah ta fara sakin jiki damu sosai musamman ma su Jamil saboda duk ranar da babu islamiyya sukan fita da ita wajen shaƙatawa. Shekarar Jumaimah biyu a gidana Allah ya yi ma Mahaifinmu rasuwa,wata ukku cib da rasuwar Mahaifinmu, mahaifiyarmu ma tace ga garinku.bayan an gama zaman makoki na roƙi Yusuf da ya dawo gidan da zama tun ba koma kanwarmu macce ta yi aure. Har ya amince da niyar zai dawo da wannan shawara mukayi Sallama dashi, tun daga lokacin ban ƙara jin ɗuriyar Yusuf naje har gidan da yake Amman ban same ba, haka na shafe tsawon lokaci ina nemansa Amman ban gansa ba har aka haifi Halimatu Sadiya wannan taci sunan mahaifiyarmu. sai daga baya na samu labarin rasuwarsa ta hanyar abokon aikinsa da sukayi aiki a kamfanin mu....".

Bappa ya karasa maganar yana kuka mai tsuma Zuciya, kuka yake kaman wani karamin yaro, Bama shi kadai ba duk mutanen dake zaune a falon Saida sukayi kwalla.

Amma tana kuka ta ce,"Haƙiƙa mun shiga tashin hankali sosai da ni da Mahaifinsu, ranar juma'a da yamma na aiki Jumaymah shago ta karɓo min a shana, kamar wasa jar maggariba Jumaymah bata dawo ba saboda nasa bata da wasa kaman Junainah saboda idon har isa son aiki mai sauri Saida na aiki Jumaymah duk nasa wasa ba ɗabiyarta ba ne sai nayi mata uzuri saboda yarince wata ƙila wasa ya ɗauke mata Hankali, na tafi maƙota sa samo ashana na hasa tura har na kammala girki na Jumaimah bata dawo ba, na

12 / 20