Author : Sadiya Kaoje Category : Read Hausa Novels
tana ta Nam nam da Nainah . Sai da suka yi wanka suka huta sannan suka ci abinci,
warin miyar sakata jin tashi zuciya da sauri ya kawar da fuska yana yunkurin amai. A take ta ji amai ya cika mata baki da sauri tai baya tana kokarin mikewa ta nufi toilte da sauri sai dai kamin na kai tuni aman ya cika mata baki.
"Subhanallahi"
Ummy ta fada tana nufo inda take kamin ta kawo tuni Asad ya zo ya rike ta, ta fara sheka amai kamar zata amayarda duka hanjinta ba taba amai mai wahala irin wannan ba. tana gamawa Asad ya zaunar da ita Afreen ta dauko ruwan gora ta miko masa ya wanke mata fuskarta ya zuba mata a hannunsa ya dura mata a baki ta kuskure
"Sannu"
Ya fada cike da tausayawa, sai ta gyada masa kai tana jin wani irin jiri na ɗibarta,
"Bari na janyo mota sai muje asibiti".
"Aa bana so dan Allah"
Ta fada da saurin domin har ga Allah bana son zuwa asibitin, daman can ita asbiti ba burgeta yake ba,
"Baby Amman jikinki ya yi zafi sosai kuma...."
" idan bata son asibitin ka barta tasha magani sai ta kwanta idan idan ta farka abun be sauka ba, sai a tafi asibitin ko Adnan ya duba ta".
Ummy ta fada ganin zata saka kuka saboda kawai ance aje asibitin.
"Zanje wajen Amma".
"A'a ba dai a haka ba".
"TOH"
sannan suka dawo falo Afra da Afreen suka fara mata sannu na amsa musu tana Murmushi.
"Anty Nainah mun yi missing dinki sosai wallahi".
Bata ce musu komai ba bayan murmushin karfin hali da tai mata, sai Asad ya kalli Afra ya ce.
"kwantawa za tai a dakinki kar motsi ko wani hayani ya tashe ta dan Allah"
"Okay yahya"
Da hannu yai mata alama da ta wuce Ɗakinsa.dake.ciki falo sai ya bi bayanta, har suka shiga dakin saman gado ta haye ta kwanta ya dauko filo ya dora mata a gurin kafafuwana sukai sama.
"Sannu"
Ya fada yana taba kanta.
"Yauwa".
Ta fada tana kallonsa da fafaren idanuwana.
"lafiyarki ta fi muhimmancin a gareni, runtse idonki ki ja numfashi da karfi ki sauke a hankali ki saki tunaninki za ki samu bacci yanzu nan"
Yadda ya fada mata haka tai a take kuwa bacci yai gaba da ita.
yana ganin ta yi bachi ya taso ta baro mata dakin tare da jan kofar a hankali ya kulle, kai tsaye ya wuce Bq ya gaida Amma a tsanake bayan sun gaisa ya wuce gidan Iya ya gaishesu suma....
*JUNAINAH*
Bacci sosai ta yi sai gab da maggariba ta farka cike da son ganin Amma.
"Ya jikin?"
"Na ji sauki"
Ta amsa har lokacin hawaye na sauko mata.
"Ya Asad ya ce na tashe ki ki yi sallah magariba ki ci abinci idan zazzabi be sauka ba za ku je asibiti"
"Ki fada masa na ji sauki"
Ta amsa ta a nufi bandaki don yin alwala so ta ke nai sallah sannan ta wuce wajen Amma A gagauce tai alwalar ta fitowa sai ta samu Asad zaune a kasa Afreen na jera musu abinci shi kuma idonsa na kanta.
"Ya jikinki?"
"Na ji sauki, zanje wajen Amma".
" sai mun cin abinci tukuna"
hijab din Afreen ta saka tai sallah har tai ta gama ta yi addu'a idon Asad na kanta, kamin ta juyo har ya bude fular Abinci ya soma zubawa wa a plate, taba juyowa ya saka spoon ya fara diban abincin ya bata kadan kadan ta ke ci saboda warin miyar nake ji daker ma ta ke iya hadewa a take warin miyar ya daki hancinta sai ta ji kamar zata yi ama da sauri ta rufe bakinta ta nufi bandaki, shi kuma ya taso ya biyota ta sheka aman yana shafa bayanta yana mata sannu cike da kulawa,
Sai da tai aman ta gama sannan ya zuba mata ruwa ta wanke bakinta ya fito daga bandakin. Inda ta aje Hijab dinta da tagama Salla ya nufa ya dauko ya zo kusa da ita yana kokarin saka mata
"Saka muje asibiti"
Ta bata fuska domin har ga Allah bata jin komai a yanzu, bata jin wani ciwon kai ko wani jiri da zafi jikin kamar ɗazun.
" bana jin komai , aman ne kawai kuma shi ma saboda miyar ne'
"Wani abu kika gani a ciki?"
"Warin miyar nake ji".
Da mamaki yake Kallonta,
"Ba komai yanzu ai na daina jinsa, kuma ya daina”
Ta nufi gurin kular abinci na zauna ta saka hannu tana ci ahankali.
"Na ƙoshi tea nake son sha".
"Okay"
Ya tashi ya fice rike da wayarsa, yana fita tai saurin nufar bandaki ta amayarda da dan abunda ta ci na tuwon ta wanke bakinta ta dawo, jinginawa tai da gadon, tana tunanin Amma,
Bai wani jima ba ya shigo dauke da mug ya zauna kusa da ita ya kai mata tea a baki, kadan ta kurba shi ma ta ji bata sonsa kuma bata son ta nuna masa kar yace dole sai sunje asibiti, a dole ta daure ta hanye rabin.tea din sannan ta kawar da kai sai ya aje kofin ya janyo ta jikinsa ya kwatar ita yana shafa bayanta.
Bayan mintuna goma lokacin ta samu sauƙin abin da take ji Asad ya rakata Bq wajen Amma hira sosai sukayi sai kusan shaɗai saura suka musu Sallama suka wuce gidan su anan Ummy take sanar da Asad nan da kwana biyu Dr Kamal zai dawo daga Umura....
tun kan ta karaso ya janyo motarsa ya bude mata ta shiga ta zauna ya ya rufe ganbun motar sannan ya zagaya ya shiga ya yi mata key suka dauki hanyar gida. Sai da ya biya ta wani shago ya siya musu tsire da kaza sannan suka isa gida. Da kansa ya fita ta zagoyo inda ta ke ya bude mata mota tana saukowa ya saka hannunsa ya rumgumeta kamar wata yar baby ko kunyar mai gadinsa da ke hangen baya ji, ita kuwa duk kunyarsa ta rufe ta.
"Mai gadi na kallon mu".
“Sai me dan ya ganmu? Be san na aure ki ba ni ko kuma be san namiji na taba matarsa ba? Is normal ma ai ba waji abun nai miki ba dafaki kawai nai".
Ya fada yana bude gidan baya ya dauko siyayyar da yai musu da dayan hannunsa yayinda dayan hannun yake makalle da ita kamar . Da hannu daya ya rufe motar suka nufi cikin gida
Tsire kawai taci kaɗan,sai da su kai wanka a tare kamar yadda ya saba mata sannan suka saka kayan bacci iri ɗaya suka kwanta. Misalin biyu da wani abu ta dare yunwa ta tasheni a dole na bar jikinsa ta sauka daga kan gadon ta nufi wutar dakin na kunna ko da na juyo sai na ga mutun yana kallonta
"Yunwa na ke ji".
"Okey zauna bari na haɗo Miki tea"
Ya fada yana saukowa daga kan gadon ya fita daga dakin, ita kuma ta zauna saman kujerar sai gashi ya dawo da mug da plate da Dan karamin tebur ya janyo ya dora plate din sannan ya miko mata hannu ta taso sai ya nufi bandaki da ita, wani lokacin yadda yake mata abu kamar wata yar baby abun har mamaki yake bata, wata kila saboda wani lokacin baya son yawan magana ne shiyasa ya son ya yi maka abu kawai ba sai ya furta ya ce kai ba wata kila kuma kuanar ce kaiwai yake nuna mata. Saida ta wanke bakinta sannan suka fito ta dawo inda ta zauna dazun ta zauna yawuna har tsinkewa suke kamin ta ci ragiwar tsiren da ta rage . Kusa da itaya zauna ya saka hannunsa yana bata a baki tana ci sai da koshi sannan. Ya bata ruwan sanyi ta sha ya maida kayan cikin,
ya kwanta saman gado ya janyo ta ta ta kwanta a kirjinsa, har safe yana rumgume da ita sosai a kirjinsa. Bayan sun yi sallah ya kwantar da kanta. jikinsa yana karatun kur'anin daya saba, ba dade yana karatun ba ta tashi daga kwancen da ta ke a cinyarsa ta sauko falo ta nufi kitchen domin samun abunda zaci sakawa cikinta saboda wata azzababbar yunwa da ta ke ji. cikin sauri ta haɗa tea ta sha.
Misalin tara da rabi Ummy ta aiko musu Breakfast bayan sunci sukayi Wonka., ta fito ta shirya cikin wando da riga English wears, kayan su karbe ta sosai dan man leben da ta shafa ya kara mata kyau ta saka ma gashinta ribbom sai ta fito kamar wata balaraba.
"Wow you look so beautiful".
Ta yi murmushi tana kallonsa ta cikin madubi har ya karaso kusa da ita ya rumgumeta ta baya yai kissing dinta.
"Kin yi kyau"
"Na gode"
Ta fada tana dariya.
"Ya jikin naki?"
"Da sauƙi".
"Allah ya ƙara sauƙi".
"Amin, ni Aban san mi ke damu Na ba haka"
"Ko?".
"Uhmm"
" na yi ajiya a cikinki"
Ta dan wara ido domin bata fahimta ba.
"Ajiya kuma?"
Yayi dariya ya sumbanci kumatunta tare da kai hannu ya shafa cikin.
“I mean kina da juna biyu".
Ta ji wani shock da sauri ta juyo ta kalleshi.
"Ba da gaske ba"
"Gaskiya Zatayi halinta very soon"
Ya kai ka sani?"
Ya kai goshinta kan nata yana goga mata hancinsa.
"ki daina son wasu abubuwan da kike so ba? Tun da kika zo gidan nan kin yi period? ni kuma a san ciki ne".
"Miye period?".
"Al'ada, ko haila".
Ya fada mata cikin rada sannan ya mikar da ita tsaye ya duka ya bude cikin yai sumbance a cikin.
sannan ya murza yatsun hannunta ya fice yana mata murmushi, juyawa tai ta kalli madubin dake bayanta ta bude cikin tana kallo ta madubi.
"Kenan yanzu dandan yana ciki?"
Ta shafa cikin tana ta mamaki, sai kuma tai murmushi tana jin mugun dadi. Tana tsaye a gaban madubin tana kallon cikin har ya sake dawowa dakin, zuwa yai bayanta ya tsaya yana kallonta ta cikin madubin ya saka hannunsa yana zirya da shi a fuskarta.
"Allah ya saukeki lafiya".
Sai ra rufe ido tana dariya ta juyo ta saka kanta cikin kirjinsa.
" Allah yasa yan biyu ne ko yan Ukku"
Ta dago ta kalleshi.
"Kai har uku? Akwai wuya ai"
"Allah zai kawo miki sauƙi".
Ya sumbance ta sannan ya kama hannunta suka fito falo ranar a gida suka yini.
Washe gari ta farka da wuri ta shiga kitchen tana kokarin kunna gas , ya shigo ya same ta sai ya karba ya dora ruwa ya sa ta fasa kwai ta kwada shi kuma ya hada komai ba karyarwa.
Da rana ma haka ya girka musu jalof taliya.
Washe gari Daddy ya da dawo kaman yadda Ummy ta faɗa.
A lokacin da ya shiga wanka ta dauko tsintsiya ta share dakin lokacin da ya fito da sharar a falo sai gashi ya fito daure da tawul a jikinsa ya tsaya bakin kofar dakin yana kallonta. ganin be ce komai ba yasa ta ce.
"Har ka gama wanka ne?"
Be ce mata komai ba sai ma kara hade fuska da yai, tunani na tsaya ta san dai kamin ya shiga wanka bata masa wani abun ba, kusan ma tun da aka daura mana aure Asad be taba yin fushi da ita ba amman yadda na ga ya hade rai na san ba lafiya ba. Kallon jikinta tai duk da nasan ba a jikinta ba ne matsalar domin ita kadai ce a falon ba tare da kowa ba balle har ya ce wani ya gannta babu Hijabi.
"Lafiya?".
Ta tambaya tanaturo baki
"Yanzu fisabidillahi dan neman magana ba, miye na wani daukar tsintsiya ki yi shara daga nan sai kice mopping za ki yi ki yi wankewanke da wasu abubuwa ko? Na san halinki ai, kuma can da da kike ke kadai ba ki yi ba sai yanzu da kuka zama ku biyu?".
"Na ga gidan yayi datti".
"Ina ruwanki".
Ta rausayarda kai.
“Wuce ki yi wanka za mu je mu gaida Daddy, daga can za muce asibitin gurin likitan”
"Mi zai min?"
“Zan siyo magani a can kuma ina bukatar ganinsa dan ya fada miki irin abubuwan da zaki rika ci da yi da kunnenki kiji domin ni kin raina ni idan na ce ki daina sai kokarin yi za ki yi”
"Aa ban fa raina ka ba"
"Zamu gani ai"
Ya fada yana jam kumatuna ba tare da ya mata murmushi ba, a dole ta koma ciki tai wanka ta shirya kamar yadda ya bukata, a tare muka fito da shi yana kallon yadda yake kallon tafiyata wata kila so yake yai sauri ko ta taka ba daidai ba yace da gangan na ke yi saboda ciki. Shi ya bude mata motar ta shiga sannan shi ma ya shiga ya zauna, sai ya kai hannunsa a bakinsa yana karanta Addu'a sannan ya saka dayan hannunsa ya daga Hijab ɗinta ya bude rigar zanen da ke jikina ya shafa mata addu'ar a ciki. Sannan yai ma motar key daman tuni mai gadin ya bude musu gate, a hankali ya fara tukin har suka fito daga cikin gidan.
Ta yi zaton gidan za su fara zuwa sannan su wuce asibitin sai ya fara zuwa asibiti File aka fara bude mata sannan ya sake tambaya ko tana jin wani abun.
"Bana jin komai"
A nan ya sake rubuta wani abun a farar takadar ya mikawa Asad
"Ka kara mata da wannan,
Asad yayi murmushi yana kallonta kunya ce ta rufe ta tai kasa da kanta tana watsa da yan yatsunta cikin Hijab.
"Doc ka fada mata abunda ya kamata tai da wanda be kamata ba da abubuwan da zata ci wanda zai amfaneta"
a take likita ya fara lissafa mata irin abubuwan da zata rika ci da kuma aikin da zati yi wanda ba mai wahalarwa ba.
“Aa no doctor ni bana son ta yi aiki komi".
" ai aikin yana da kyau amman banda na wahala".
"Aiki komi bazata yi ba".
ya fada , shi kuwa likitan sai dariya yake, ita dai gaba daya kunya ta gama rufeta.
"Ta so muje"
Tashi tai ta tafiyar cike da kunya shi kan tuni ya kai kofa har ya bude mata kofa yana jira ta fito, sai ta fita sannan ya fito, ba ko kunya ya kama hannunta zuwa gurin motarsa da kansa ya bude mata sai da ta shiga ta zauna sannan ya rufe ya zagoyo gefensa ya zauna, tukin mota yake amman gaba daya hankalinsa na kanta, minti biyu uku sai ya kalli inda na ke.
"Akwai abin da kike buƙata?."
Yayi mata irin wannan tambayar ta ba adadi kamin su isa gidan Ummy a harabar gidan ya faka motarsa har na kai hannu zata bude sai ya danna lock motar ta rufe, kallonsa tai sai ya fara mata magana a natse.
"Don Allah ki kula Kin dai ga cikin mutane ne, bana son ki je ki ci wani abun da zai lalata miki ciki Karki zauna da yunwa, Bazan iya yi Miki magana a gaban Amma ba, pls ki kula da kanki"
"Tau"
"Good girl".
Ya fada sannan ya cire lock it's kuma ta bude motar ta fita ta nufi Bq, sai ta ji ya kira ta.
"Muje mu gaida Daddy sannan".
Juyowa tai ta karaso inda yake tsaye ba tare da ta ce masa komai ba, a tare suka jera suna tafiya zuwa Ɓangaren Ummy yana ta kallon yanayin tafiya A falo suka same su zaune. "Daddy Ina kwana?" Suka gaishe shi a tare sanan suka gaida Ummy.
"Lafiya lau".
"An dawo lafiya Daddy?".
"Alhamdulillahi".
Adnan, da Afra da Afreen suka gaida Asad da Nainah cikin girmamawa.
Bayan sun gama Gaisawa Suka nufi Bq a tare Asad ya gaida Amma cikin girmamawa kaman ko yaushe sannan ya yi mata sallama.
Nainah ta tashi na koma kusa da Amma ta zauna a kasa ta dora kanta saman kafafuwanta, sai ta fara shafa kanta tana murmushi......
A gidan ta wuni sai dare yaje da kansa ya dauko ta sannan muka kamo hanya.
"Zaki ci tsire?"
Yana tambaya ta hade yawu dan na hango mai tsiren yana gasawa gefen hanya. Sai ya faka motarsa ya fita ya siyo mata ya dawo.
"Sauran ice cream"
"A a ba ki san sanyi yana effecting abunda ke ciki ba? Na lura da ke kullun sai kin sha ruwan sanyi fa".
"Ai kadan nake sha"
Be ce mata komai ba ya faka gefen titi ya sake fita ya siyo mata ice cream sannan ya dawo motar a lokacin ita kam har ta yi nisa da fara cin tsiren.
Ko da suka isa gida ta cinye rabi sai dai ba ita kadai ba har da shi dake tukin miko bakinsa yake ta saka masa. Yai parking motar ya zagayo ya bude mata kamar yadda ya saba ta fito rike da kedar sai ya rufe motar sannan ya karba ledar hannunta suka wuce cikin gida.
****** ********
"Bappa mun kammala bincike gidan da yarinyar nan take mai kama da Jumayma shekaran jiya mukayi waya da ɗan jaridan da saki video yaran dake bada haƙuri abin da suka aikata ya turomin Address ɗin Yaron".
"Kai ma sha Allah, yanzu kam sai mushirya tafiya kaman yadda nayi alƙawarin".
"Haka ne Bappa, cewar Junaid, amma Bappa ya kamata kafin mu tafi a sanar da Jumayma kar abin yazo mata a wani iri".
Bappa ya yi Murmushi yana shafa gemonsa kana ya ce,"An riga da an wuce wajen Jumayma ta san da komi yanzu haka ta matsu bata