Bin Maryam Book 2 Complete Sadiya Kaoje

Author :  Sadiya Kaoje Category :  Read Hausa Novels

Chapter   18 / 20

51K to 54K   out of 59.4K words

don Allah ku yafema Aliyu, da ni kaina haƙika nasan an zalunce ku, kuma Allah ya nuna muna ikonsa gashi da yau Allah ya sake haɗa a wajen ɗaya a inuwa ɗaya, sanan ga Asad da Junainah a matsayin ma aurata ko wannnan ma ya ishemu ishara. yana magana yana kuka.

Suna cikin koke kokensu Aliyu ya farka daga Nannauyan baccin da yake, ya riƙa bin Asad da kallo irin kallon mamakin nan, shiko Asad sai murmushi yake sakar masa,

Dr Kamal ya karaso kusa dashi ya kama hannu Asad ya ɗora kan na Aliyu yana faɗin,"ga ɗan ka Aliyu....!"

Gaban Aliyu ya yi mummunan faɗuwa. ya zato ido yana kallon Dr Kamal da Asad.

"Ɗan kane na wajen Balaraba....!"

Aliyu ya rumtse idanunsa da ƙarfi wasu zafafan hawaye na zubo masa yana ƙara damƙe hannu Asad.

"Abbie.....!" Asad ya kira sunansa da wata irin Sassanyan murya mai cike da natsuwa.

Ya tsurama Asad ido kammaninsa da shi kaman an tsaga kara, hawaye ya zubo masa a take ya ji tsakanin kyaunar Asad ya cika masa Zuciya baya son nesa da shi, ya riƙa shafa fuskarsa a hankali, yana zantuka a cikin ransa cike da nadama marar adadi.

"Ina Balaraba.....?" Ya faɗa da kyar domin har yanzu maganar bata fita sosai.

"Ga ta nan tare da Murjanatu....!".

Ya juyo a hankali yana kallonsu .

"Balaraba Murjanatu kune a gaba na? Kunga yadda Allah ya mayar da ni? Ku ya femin haƙina na zalunce ku na yaudareku ku kalli kuma yadda Allah ya yi dani, don girman Allah kuce kun ya femin wata ƙil na samu sassauci akan baƙarar azabar da nake ci nayi na dana na canza halayena Allah ya sani".

Duk da maganar tasa ba sosai take fita ba sun gane abin da yake faɗi, suka share hawayensu suka ce,"Mun yafe maka Aliyu Allah ya baka lafiya mai ɗorewa".

Gabaki ɗayansu suka amsa da Amin.

"Abbie me ya hadda maka wannan ciwon?."

Bakin sa ya yi nauhi kamar ko wane lokaci idon an yi masa tambayar, ya nemi amsa ya rasa bakinsa ya kulle ya kasa cewa komi, sai dai kawai yaci gaba da yayin kuka.

Junainah kam ta can gefe Abin ta banda kuka ba abin da take, saboda tasan da labarin Aliyu Amma bata ɓoye mata komi ba, sai yanzu ne ta tuna farkon ganin Asad da Amma tayi a Asbiti, abun ya yi matukar tsaya mata a rai sam bata yi zaton haka ba ko a marki. tayi kuka sosai har idanuwanta sun kumbura ta dawo suku suku kaman ba ita ba, tausayi Ummy fal a zuciyarta, idon ka ganta zaka dauka bata sha gwagwarmayar rayuwa haka ba, Shiyassa a kace mai haƙiuri yana tare da nasara, da bata yi haƙuri ba da bata kai ga matsayin da take ba, yanzu gashi Allah ya sake haɗasu a waje ɗaya, ko Auren ta da Daddy shima ka dai ya ishe su ishara. wani abun kawai kasan Allah ne kawai ke iya yin sa.sai gashi cikin sauƙi gaskiya ta bayyana.

Anan Dr Kamal ya yi Aliyu bayani koma ta yadda zai gane, hakiƙa Aliyu ya cika da mamaki da jin Balaraba matar Dr Kamal ce tsawon shekaru nan amman koma bai sani ba, daga bisani ya yi ma Dr Kamal godiya sosai na riƙe masa ɗansa da ya yi tsawon shekaru ba tare da ya ƙuntata masa ba.

Bayan wani ɗan lokacin Dr Kamal ya gabatar da Asad ga yan uwan Mahaifinsa,

"Wannan ita ce kakarka mahaifiya ce ga Mahaifinka, sai wannan kuma shine mahaifin Babanka, wayan nan kuma ƙannenn Mahaifinka ne, Sumayya, Hanafi, Hanifa, Haroon, Abbas, Hannatu, wannan kuma sunanta Umma kakace a wajenka sai wayan nan kuma ƙannen kane, ɗiyan ƙannen Mahaifinka ne, haka dai Dr Kamal ya riƙa nuna masa kowa yana faɗa masa yadda dangantakarsu take.

"Wannan abu da ya faru ƙaddara ce Allah ya riga ya rubuta akan zai faru, Allah ya baku lafiya ya kuma kiyaye gaba". Cewar Dr Kamal.

Gabaki ɗayansu suka amsa da Amin, Daddy ya sake neman gafarar iyalinsa, anan suka faɗa masa sun yafe masa, anan gidan suka kwana har wayewar gari basu runtsa ba suna hira abubuwan da suka shuɗe,Washe gari ma a gidan suka yini har zuwa dare, sai nan nan suke da Asad da Nainah, wasa wasa sai da Asad da Nainah suka sati a gidan sanan suka barsu suka koma gidansu, Ummy kam tuni sun koma gidan su sai dai tsawon satin nan ɗaya a gidan Mama suke yin sai bayan Isha'i su koma gida...........✍️

💋𝐁𝐈𝐍 𝐌𝐀𝐑𝐘𝐀𝐌💋

𝑵𝒂

𝑺𝒂𝒅𝒆𝒆𝒚𝒂 𝑲𝒂'𝒐𝒋𝒆

08149979652

*Book 2*

______kullum cikin saukar Alqur'ani da sadaka ake duk akan ciwon Aliyu, kuma Alhamdulillahi sauƙi nata samuwa, har gida Iya, Baba, Hamma Hamza,Umma Deedat Baby suka zo duba Aliyu, domin Ummy ta faɗa masu komi kuma bata ɓoye musu ba har labarin Amma ta basu sunyi mamaki sosai sun cika da al'ajabi, a yau Aliyu yaci Albarkacin Asad domin ba don Asad ba ba wani abun da zai sake shiga tsakaninsu, Asad ya yi farin sosai da zuwansu Iya,

Bayan tafiyarsu Aliyu ya jima yana kukan nadama da dana sani da kaico, ya yi su har babu adadi,

Bayan kwana uku da zuwansu Iya, Aliyu yana kwance a ɗakinsa kaman walƙiya Aliya ta bayyana a gabanta cikin kyakkyawar surarta da tayi amfani da ita wajen jan hankalin sa, a kiɗime ya mike zaune jikinsa na rawa hankalinsa duk a tashe bayyanar ta a gareshi alheri bane, baya ko son jin mai irin sunanta duk da cewa daman bai taɓa ji ba, ko a mafarki ya ji sunanta firgita yake balle a ce ya ganta a zahiri ya gaiga gabas da yamma babu hanyar tsira, sai kawai ya fashe da kuka yana runtsa ido baya son ganin ta ya haɗe hannayensa wajen ɗaya Zai yi magana ta ɗaya masa hannu tana cewa,"Aliyu kada kace komi a yau na zo gare ka ne da Alheri na zo ne domin na fitar da kai daga cikin halin da na saka saboda na tabbatar da kayi nadama kayi laushi, daman ina son ne wannan ya zamto ishara a masu halin cuta irin taka mu Aljannu ne ba mutane ba kamar ku ba tabbas muna shiga cikin ku muna rayuwa muna ganin duk abin da kuke irin mu kuma suna da yawa wanda Bama yadda da irin wannan zalunci irin naku na ƴan adam, kuma kowa da irin yadda zai zuwa domin ya yaudareku, wasu siffar mutum kamar yadda na zo ma ka ka kasa rayuwa cikin kwanciyar hankali, wasu da siffar dabbobi a yi ta tsorata ka a razana naka ko a saka maka muguwar cuta.

Aliyu da ace na so zan yarda ma ka yi amfani da daga ranar ba zaka ƙara kusantar ƴa macce ba har abada, A yau ni Aliyu Abduljabbar ƴa ga sarki Aljannu duniya zan mayar da kai yadda ka ke a da in ya so sai ka kula ka bawa yan baya labari....!"

Ta ɗaga Hannunta guda ɗaya ta yi nuni da shanyayyun ƙafafuwansa sai kawai suka dawo yadda suke a da, ta shafa bakinsa shima ya dawo dai dai haka Hannayensa bayan ta shafa suma suka dawo dai dai, nan take ta ɓace ɓat,

Aliyu farkawa kawai ya yi ya gansa kwance a kan cinyar Haroon surutai sun kaɗai ɗakinsa murna da farin ciki ya yi saurin buɗe idonsa sai ya miƙe a firgice yana bin jikinsa da kallon a ruɗe ya miƙe tsaye ya kanshi tsaye da ƙafafuwansa sai kawai ya zube jikin Haroon yana muka mai tsuma Zuciya.

Haroon ya ce,"Alhamdulillahi Ya Aliyu ba kuka za ka yi ba Allah zamu godewa da ya amshi Addu'a mu ya ba ka lafiya."

Su Sumayya baki ya ƙi rufuwa sai kwallonsa suke suna cewa ,"Alhamdulillahi Yaya Aliyu sannu Allah mun gode maka".

Umma ta ce "Allah shi ne abin godiya amma Aliyu ya akai ka samu lafiya cikin ƙanƙanen lokaci haka? Ganin kawai mukayi guguwa ta fita daga daga cikin dakinka hakan yada muka shigo da gudu, kayi muna bayanin yadda zamu fahimta".

Daddy dake zaune saman kekensa ya ce," Nima tunanin da na je kenan"

Aliyu ya share hawaye idonsa har lokacin yana duban jikinsa ganin yake tamkar ba shi ne ba sai fashe da kuka yana cewa," Ni na jawa kaina garin biye biye na ko miye ya faru da da ni ni ne sila na gamu da aljanna".

Nan ta ke ya soma ba su labarin komi tun haduwarsu da Aliyu har zuwa ranar dinner ya ganshi a daji ya basu labarin abubuwan da ta yi masa a dajin da irin ciwon da ta saka mishi har bayyanarta gare da take yi bai ɓoye musu komi ba.

Jikin kowa a ɗakin ya yi sanyi kowa ya cika da al'ajabi domin su duka zatonsu ya zama gaskiya daman sun yi zaton Aliya ita ta jefa shi cikin halin da yake ciki.

"Na yi nadama abisa kuskuren da na aikata a rayuwata, kuma na yi tsarkakkiyar tuba ga Allah, ba zan ƙara ba zan dawo natsastsen Aliyu da Mama take son ga ni".

Cikin sassarfa ya iso gaban Daddy ya riƙe ƙafafuwansa wanda shima kukan yake Aliyu ya ce," Daddy ka yafe min".

Daddy ya dafa bayansa a tausashe ya ce,"Aliyu ni ne ya kama na nemi gafarka Aliyu na cuce ka tun kana yaro na shogoɓa ka, ban baka tarbiyya mai kyau ba, domin duk abin da ka ke aikatawa ni ne mai laifi, Ni na ɗora ka bisa hanya, duk abin da ka yi na rashin kyautatawa goyon bayan ka nake da ɗaure maka gindi, haka yasa ka ke tunanin dai dai ka ke aikatawa.

Mahaifiyarka Laila da Umma sun sha nusar da ni illar da ke tattare da hakan a son su na dai abin da na ke maka amman karshe da faɗa zamu rabu da ka girma sai abu ya daɗa yin gama daman hausawa sun ce icce tun yana ɗanye ake ta kwara shi kayi haƙuri Aliyu ka yafe min ".

"Daddy na yafe maka". Aliyu ya faɗa yana kuka, Daddy ya ce,"Na ga illar da ke tattare da abin da na aikata ina kira ga iyyaye maza da mata da su ɗauƙi darasi akaina su Dena sagantar ƴaƴansu, Allah ya kiyaye gaba ya shirya mu ya tsarkake mana zuƙatanmu ga baki ɗaya".

Gaba baki ɗaya jikin kowa ya yi sanyi a gurin Allah mai ikon wai yau Daddy ne da yin wa'azi ya bawa Kowa tausayi,

Aliyu sai kallon jikinsa yake yana jinsa kaman a wata sabuwar duniya shi da ya cire tsammanin sake rayuwa mai kyau shi ne Allah ya dawo da shi dai dai kamar kowa.

Haroon ya riƙa lallashinsa har ya samu natsuwa ya ja hanunsa suka wuce ɗakinsa ya haɗa masa ruwan wonka masu ɗumi, bayan ya fito dama ya ware masa kayan da zai sa bayan ya saka kayan ya yi kyau ba laifi sai dai rama da baƙin da ya yi, domin gaba ɗaya ya sauya, Haroon ya kama Hannunsa suka wuce wajen Aski sai gashi ya fito ɗas da shi kammanin Asad suka sake bayyana a tare da shi.

A ranar Mama ta saka masu Aiki suka girka lafiyanyen abinci mai yawa akayi sadaka tare da ruwan masu sanyi. Aliyu kuma tun da ya dawo ya yi Alwala ya fara salloli babu da di domin nuna godiyar sa ga Allah, bayan ya gama ya ɗau carbin yana ta istigifari da salatin Annabi (S.A.W🤍)

Da Yamma suka fita tare da Haroon, Abbas, Hanafi, suka wuce gidan sauran matan da ya saka ya nemin gafararsu, Alhamdulillah cikin rahamar Allah ko wacce ta yafe masa bayan su Haroon sun basu labarin komi sosai suka tausaya ma Aliyu daman duk kansu sunyi Auren daga gidan mazajensu iyayensu suka kirasu su Haroon ba su basu baro gidajensu ba sai da suka cikasu da Alheri mai tarin yawa. Wata irin natsuwa ta samu gurbi a Zuciyarsa.

Lallai ya yi babban kuskure a rayuwarsa ko wacce a cikinsu Allah ya ɗaya darajjarta Allah ya yi masu kyakkyawan canji a rayuwarsu.

Kai tsaye suka wuce gidan Dr Kamal, lokacin suna a harabar gida zasu shiga mota kenan zuwa gidan su Aliyu ɗin.

"Wa nake gani nan kaman Aliyu? Ko dai gizo ne? Aliyu ne ta fe da ƙafafuwansa?".

"Ya Kamal da gaske ne ba gizo ba!, yau Allah ya amshi Addu'ar mu ya ba Ya Aliyu lafiya". Da sauri Asad ya ƙasaro wajensa ya rungumeshi yana kukan farin ciki. Sun jima a haka suna kuka sanan suka saki junansu,

Nainah ta ƙara so kusa da shi ta gaida shi cikin girmamawa ya amsa mata fuskarsa ɗauke da murmushi.

Su Adnan suka gaida shi cike da kulawa. Sanan suka wuce cikin falon.

Ummy da Amma suka zauna a gefe cike da al'ajabi ganinsa garau kaman bai taɓa wata jinya ba sai dai yar rama da baƙin da ya yi, a take su Haroon suka zaiyana musu komi daga abin da ya faru basu ɓoye musu ko mi ba. Sun cika da mamaki sosai kwarai da gaske. Aliyu yana kuka ya sake neman gafarsu.

Su Ummy su ka ce,"Ai ba bu komi tun tuni mun ya ce maka, sanan suka yi masa murnar samun lafiyar sa tare da addu'ar Allah ya ki ya ye gaba.

Cikin wani irin yanayi ya riƙa bin Ummy da kallo ta gefen ido yadda ya ga ta yi wani irin bala'in sauyawa kaman ba ita ba, idon kuma ya tuna yanzu ɗin ita ba halaliyarsa ba sai yaji ba daɗi a zuciyarsa Balaraba tana ɗaya daga cikin matan da so so na tsakani da Allah Amman kash! Son zuciya yasa ya rasa, da yanzu suna zaune abin su cikin kwanciyar hankali da kulawa wata ƙil su Adnan duk ƴaƴansa ne. A ɓoye ya rinƙa share kwalla da suka zubo masa, Ummy ko tuni ta lura da halin da yake ciki Amman bata ce uffan ba, sun jima a gidan suna hira Sanan suka wuce.

Cikin dan ƙanƙanen lokaci Aliyu ya yi mai da jikinsa saboda abinci mai gina jiki da yake ci Mama ta yi tsaye a kansa tana ba shi kyakkyawar kulawa kaman wani ƙaramin yaro, Asad kusan kullu sai ya aiko masu da kayan abinci masu inganci da gina jiki sanan Dr Kamal ma ya ɗora shi akan maganin turawa domin taimakawa lafiyar jikinsa. Daddy ma Alhamdulillahi zuwa yanzu ko'ina yana motsa jikinsa har tafiya ma yana ɗan taɓa sai dai ba sosai saboda halin tsufa, Aliyu yanzu ibada kawai yasa a baga da Azumin attanin da Alhamis basu wuce sa da sallar dare.

Kasancewar halin da suka tsinci kansu yasa aka ɗaga maganar baikonsu Afreen har zuwa abubuwa su dai dai ta,to Alhamdulillahi komi ya zo cikin sauƙi, a yaune ne za'ayi tambayar tun safe Ummy ke ta aikin dafa abin cin tar bon baƙi Su bayan sun gama sun Afreen sukayi kanka suka wuce gidan su Aliyu Junainah kawai aka bari a gidan tana murnar zuwan yan uwanta.wuraren shabi su Bappa suka iso kusan motoci goma duk kansu masu kyau da tsada ciki ko harda mota biyu na sojoji ɗaya a gaba daya baya. Sun samu tarba ta Mummunan a gadin Nainah ta yi farin ciki sosai da ganin yan uwanta du da dai maza ne ba macce ko ɗaya a cikinsu, daman wannan aikin maza ne. Bayan sun ci abinci sun huta suka gabatar da abin da ya kawo su, Aliyu, Haroon Abbas Hanafi Hamma Hamza, Nasir ƙannen Dr Kamal da su akayi komi har aka kammala duk wani abin da ya dace, sanan suka wuce.

Bayan sati ɗaya Daddy, Hamma Hamza, Aliyu, Abbas, Hanafi Haroon, Andan,Asad da sauran yan Deedat ta gefen Mahaifiyarsa suka wuce Sokoto wajen tambayar Auren Jumayma. Alhamdulillahi an yi komi bi sa tsarin musulunci. sun dawo da kwana ukku aka yi na Adnan da Baby. Duk wata hidima da ake tare da Aliyu ake yin ta , hakan ba ƙaramin daɗi ya yi Asad ba, hatta shi kansa Aliyu yana matukar jin daɗin hakan. Shiyassa ya saki jiki ana gudanar da komi yadda ya kamata, lokacin lokaci kuma yana kai ma su Iya ziraya wannan abun duk ya nayi ne saboda farin cikin Asad......

Ranar Weekend yan gidansu Aliyu suka je gidan Asad gabaki dayansu manya da yara a gidan suka yini sai dare suka watse, sun ji daɗi sosai yadda Asad da Nainah sukayi ta hidima da su, domin a restaurant ɗin Ummy aka shirya musu Abin mai rai da lafiya kusan kala biyar bayan kayan laƙumashe kala kala..

Washe gari Aliyu ya kaima Dr Kamal ziyara kaman yadda ya saba,

"Aliyu Mama ta yi min magana akan bata son zaman aka ka fitar da mata kayi aure".

"Haba Kamal duka duka yaushe na farfaɗo da har za'a kawomim maganar Aure?".

"Kamanta da komi Aliyu tun da kar ka tuba ka cire komi a ranka ka samu mata kayi Aure".

"So ka ke na koma gidan ji ya?".

"A'a wallahi bana fatan hakan, kuma kaina ka dena faɗin haka".

"Na ji".

"Wai ni me ma ke kawoka gidan bana so fa ana kallamin mata".

A tausashe Aliyu ya ce,"Kamal kasa a ranka ban taɓa sanin Balaraba a rayuwata balle ace munyi zaman Aure da ita kasa a ranka Asad ma ɗanka ne ba nawa,ni zumunci ke kawo ni gidan nan ba wani abu ba, ka ɗauka

18 / 20