Bin Maryam Book 2 Complete Sadiya Kaoje

Author :  Sadiya Kaoje Category :  Read Hausa Novels

Chapter   20 / 20

57K to 59.4K   out of 59.4K words

ta. tare suka ci abinci.

"Abinci nan ya yi daɗi zam zam, Allah na gode maka da ka bani mata mai kyau da ita kwalliya".

"Kwalliya kawai na iya?."

"Komi da komi kin iya Baby".

Ta yi Murmushi,"Yaya ina jin tsoron C.S ɗin?".

"Kwantar da hankali ki in sha Allahu ba abin da zai faru".

"Amma Yaya me yasa baka gayamin yan huɗu ba ne?".

"Saboda bana son ki shiga damuwa".

"Ni dai gaskiya sunyi yawa".

"Rawar ƴaƴa zaki min".

"Yanzu fa kowa ɗauka zaiyi da ban da bam aka same su".

Asad ya yi dariya yana faɗin wa ya ce miki haka shi da ciki lokaci ɗaya yake shiga komin yawansu".

"Da gaske Yaya?".

"Ehhh..."

Washe gari suka wuce birnin Kebbi hankalinsa zaifi kwanciya idon tana kusa da yan uwa,

Kwana huɗu da dawowarsu Birnin Kebbi ta sake jin irin wacan ciwon sai dai wannan ya ci uban wacan ta ko'ina domin ba kanta ba ba cikinta ba ba bayanta da marata ko'ina ji take yana murɗawa haka ta wuni tun safe har dare a haka Allah ya bata ikon yin girkina cikin karfin hali har na gama,sai da yamma abun ya tsananta mata idan zan zauna sai na ji kamar abu zai fito mata da baya, hankali be kara tashi ba sai da naje fitsari na ga jini sannan na kira Asad a waya na fada masa. Daga office ya dawo gida hankali tashe a lokacin har na fara fita haiyacinta tare suka iso da Ummy a tsorace suka kwasheta zuwa Asbitin tare da kayan haihuwa...

"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u, wayyo bayana wayyo cikina Ummy Amma Ammy zan mutu" hankali a tashe suka iso Asbitin

Su na ke ta fadi har aka shiga da ita dakin haihuwa, bata iya komai dai dai amman tana jin lokacin da akai ta rigima da Asad kamin a samo likita macce ta data mata theater.suna isa Ummy ta kira Amma cikin kanƙanen lokaci ta iso.

kamin a shiga da ita ɗakin theater babu wanda bata nemi yafiyarsa ba babu wanda bai yi mata kuka ba, Asad da har wani rama yai, ita kam har ga Allah ta dauka mutuwa zata yi,

Sai dai cikin ikon Allah da iyawarsa da yardarsa sai aka mata theater bata ma san anyi ba domin hankalinta baya jikinta a lokacin, sun dade suna kira sunana kamin na amsa musu domin numfashina yayi nisan zango ga jikinta ta jinsa kamar ba nata ba. Alhamdulillah likitar da fada tare da sauran nurses da kuma wata likitar ita ma mace Nurses din ma dukansu mata ne. Sun dade a kanta kamin dauko baby suke dora mata a kirji.

"Duba ki gani me kika haifa"

Cikin lumsasun idanuwana ta duba ta ce

"Namiji"

Suka sake dora mata dayan

"Namiji"

Suka sake dora mata wani.

"Macce"

Ta fada idonta na cika da kwalla, sai Nurses ɗin sukai hamdalla suka canja mata gado suka dora ta akan wani sannan suka rufe mata jiki suka turo ta akan gadon aka fito da ita. Ammi da Amma da Ya Asad ne rike da yaran uku babu komai a fuskarsu sai farinciki. Wani dakin dabam aka kai ta suka jona mata gorar jini suka saka min iskar da zata taimaka mata gurin numfashi sannan suka mata Sannu suka fita. Sai ga Asad ya shigo riƙe da Baby fari sol cikin kayan sanye masu kyau da tsada. Gefenta ya aje baby sannan ya doko ya sumbanci goshina ya rumgume ta hawayen farin ciki na sauko masa.

"Thank you so much, Allah ya miki albarka Allah yasa ki gama da duniya lafiya".

"Yaya nawa na haifa?"

"huɗu amman ɗaya ya koma, saboda da wahalar da ki ka sha".

Yana rufe baki sai ga Nurse ta shigo da daya Ummy kuma rike da daya, wani karamin gado dake kusa da ita na asibiti aka jera su, Ummy ta matso kusa da ita tana mata sannu.

Nan take kowa ya ji labarin haihuwar Naina yan uwa sun cika da farin ciki marar misaltawa

a take aka hau yi yaran hoto cikin har da Ubansu ya dora status dinsa . Sai a lokacin ya gane yana tsananin son Junainah da kaunarta, jin yai kamar ya lashe ta yake ji ita da abunda ta haifa ba ma.

Junainah taga kulawa da gata ba a gurin mijina ba, ba a Ummy ba duk wani abun da ya take bukata a gurin uwa Ummy tana matashi, Asad yadda yake dawainiya da ita da damuwa har tausayi yake ba ta Satinta a Asabitin aka sallameta suka dawo gida, a nan aka ce mata bata ga komai ba indai gata ne da kulawa, daga gurin yan'uwan Asad kamar wandanda basu taba samun haihuwa ba a dangi sai a a kanta haka suka rika kula da ita kamar zasu dafa ta su cinye.

Madara aka siyo ana hada musu da ita domin nonon baya isarsu bama kamar mazan da ba su iya sha kadan ba. Kayan barkar da Asad yai mata sai kace hauka ne ko kuma be san zafin kudi ba, bata cin wadanda tai ta samu gurin yan uwansa da kuma nata dangin.

Ranar da ta cika sati biyu da haihuwa a ranar akayi suna, ɗayan aka saka masa sunan Dr Kamal waton Kamaluddeen suna kiransa da Sudais ɗayan kuma Aliyu suna kiransa da Sultan, macce kuma Sunan Ummy Maryam suna kiranta da Nimra.

An yi shagali iya shagali har abunda ban taba mafarkin za a raba ba anyi, a ranar daga ita har su sun sha bachin gajiya daman tun da suka zo dubiya ba su da aiki sai bacci sai kuma shan nono.

Kusan rabin rainon su a hannun Asad yake indai yana gida to babu ruwanta da su sai idan nono za su sha ko madara, idan kuma baya gida Ummy na kula da su bata da matsalar daukarsu Ummy ke musu komi.

Sai da tai arba'in sannan ta tafi Sokoto ganin ƴan'uwanta, wata daya tai a can duk kuwa da kasancewar Asad be so haka ba amman bata bi ta kansa domin ta lura idan ta biye shi ba zan yi zuminci ba, domin shi ya fi son kullum tana kusa da shi ko dan ƴaƴansa, taga dangi na kusa da na nesa, kuma ta ga kauna da soyayya ita da ƴaƴanta ta ko wane bangare, har sai da ta ji kamar kar ta dawo.



Da ta dawo tayi sati biyu a gidan Amma sanan ta wuce gidan Iya ta yi masu sati ɗaya daga gidan Iya ta wuce gidan su Aliyu wajen Mama ta yi masu sati ɗaya a nanma sai dai ta zagaye dengin na nesa da na kusa domin tun da tazo kwana biyu kawai ta yi bata fita ba. da zasu koma yan Uwan suka sake cika su da Alherai musamman su Mama.

Bayan ta dawo gidan Ummy da sati ɗaya suka koma Abuja, tare da mai kula mata da yara wata dottijiwa da Ummy ta hado ta da ita domin ta riƙa taimaka mata wajen kula da yaran.

Ta dawo da sati ɗaya ta koma makaranta domin bata wasa da karatunta saboda burin da ta ke da shi na yin zurfi a ilmi ko da kuwa Asad ba zai barta tayi aiki ba

Su Sudais nada wata goma su Afreen suka haihu Afreen ta samu ɗiya macce Afra kuma namiji, anyi suna da kwana Ukku Jumayma da Baby suka haihu a rana ɗaya, Baby da safe Jumayma da Daddare. Jumaymah samu yan biyu macce da namiji, Baby kuma Namiji, Su Nainah basu koma ba Saida akayi zanen suna sanan suka koma.

Ta maida Hankalinta sosai akan karatunta da kula da mijinta da kuma yayanta karatu be hana ta ko daya ba, haka ma kula da mijinta da ya'yanta Ga goyon baya da ta ke samu da kauna ta ko wane bangare, kan kace kwabo na goge a makarantar cikin shekaru ukku ana dama da ni a cikin daliban da za su shiga aji na karshe wato Sss3

Daf da zasu gama na samu wani cikin hakan kuma yayi mata daɗi sosai Asad ya ɗaga mata kafa daga haihuwa duk kuwa da irin son yayan da yake har ta gama makarantar.

Cikinta na da wata uku Asad ya sama mata admission a university da ke Abuja, a lokacin da ya fada mata yadda tsari da daliban makarantar suke sai abun ya tsorata ta sosai tana ta ganin kamar ba zata iya ba, ashe abun saka kaine kuma karatun ya zo mata da sauki saboda ta yi nisa a qur'anen tana daf da sauka ma, sai hasken karatun ya kara bude mata kwakwalwata hadisai na ta iya ba laifi, da safe kullum sai Asad ya biya mata na qur'anen da na bokon ma inda bata gane ba yana mata karin haske, domin ya fada mata abunda bata gane ba ta rika tamyarsa ko wata mace, amman be yarda ta tambayi wani namiji ba da sunan class mate dina. Makarantar ma kamar wacan sai ta rufe komai ta ke tafiya shiyasa babu wanda ya san fuskata sai matan da muke shiri da su sosai shi ma waenda suke da contact dina suke ziyarar juna ko suke ganin status dinta.

Lokacin da ta fara zuwa ta maida Hankalinta da kuma yawan tuna burina sai abun ya zo mata da sauki, sai dai wannan cikin ba kamar wacan ba ne, wannan ta sha wahalar sa sosai ga shi kuma tana farko farkon fara karatun ne. A haka tai ta fama har cikin ya girma a lokacin suna daf da fara exam din shiga ug 2, a haka tai jarabawar cikin wahala Asad na ta tausayinta kamar yadda ta saba sai dai baya karya mata guiwa saboda ya san burinta kenan.

Bayan exam da wata ɗaya ta haifi yan biyu macce da namiji a gidanta akai bikin dattijiwar da ke kula da gidan ita ke hada ruwan zafi tai ma twins wanka wato mai sunan Amma da mai sunan mahaifinta Yusuf an musu lakani da Ayla da Affan,

BAYAN WADANSU SHEKARU.

Rayuwa ta yi daɗi ta kowanne bangare a yau wa zai ganta ya ce itace Janainah yar talla? Wa zai ce ita ce ta sha wahalar rayuwa ta fuskanci kalubale na rayuwa kala kala, mai hakuri madawaci kuma wanda ya rike Allah baya faduwa kasa, duk kuma wanda Allah yai masa gata to ya huta kuma ya dace. Ta rike Allah ta yi hakuri kuma ta ci ribar hakurinta Allah kuma be barta ta ji kunya ba, da duk wanda yake mata Kallonta a matsayin banza marar amfani ya koma yana mata kallon mai gata, Duk wanda ya gan ta yanzu zai zata daga sama na samu arzikin ita kaɗai ta san wahalan da na sha kamin na samu wannan. A yau ita ce riƙe ta takardar kammala bautar ƙasa ta yi karatu kan burinta ta ya cika ta yi degree Alhamdulillah ko a haka rayuwata ta kare ba tare da ta yi aikin da Asad baya son tai

Ta samu abunda ta ke kuma ta gode Allah , wata kila a gaba ya canja ra'ayinsa ya bar ta tayi aiki da daman kuma ba duka buri ne yake cika ba, ba komai ake nema a samu ba, ba kuma duk a abunda kake so ne alheri a gurinka ba, sai dai ba zata dena gode masa ba akan dukan kulawa da goyon bayan da ya bata....

Shekara biyu kenan da dawowarsu Ummy da Amma a Abuja Lokaci kuma su Asad suna zuwa birnin Kebbi Hutu wajen yan uwa, wani lokaci kuma yara kawai ke zuwa, haka suma suna kawo musu ziraya akai akai....

Bayan Isha'i, bayan sun gama cin abinci Nainah ta yima yara Wonka ta sanya musu kayan bacci ta Kwanar dasu sanan ta tofa musu Addu'a taja musu kofa, d'akinsu, ta shiga Nimra ta shiga ta samu har suma sunyi wanka dasu dayake duk zasu iyya ma kansu, Addu'a tasasu sukayi ta rufe musu kofa bayan ta tabbatar sun kwanta.

Ɗakin ta ta shiga, wanka tayi ta sanya wani ɗan iskan kayan bacci riga da wando yara yara jikinta sai kamshi yake ta wuce ɗakin mijinta, tura kofar tayi da sallama ta shiga.

Zaune yake akan gado yana aiki a laptop ganinta yasa sa kashewa ya aje akan drowern gado ya zuba mata ido ganin irin kyaun da ta masa.

Da sauri Nainah ta karaso garesa faduwa tayi a kansa wanda yasa dole ya koma kan gadon suka kwanta, yayinda yake kasa tana samansa fuskar su ya hade waje ɗaya Cikin kasa kasa da murya yake mata magana, wai Babyna menene sirrin ne kullum daɗa kyau kike kamar yau Aka kawo mini ke?yana maganar yana mammatsa mata jiki.

kamo hannun tayi sannan ta tallabo kanshi bakinta ta manna kan nashi tamai wani irin zazzafan kiss sannan tasa hannun ta wore rigar tata cikin lumshe ido ta jawo kanshi ta cusa a tsakiyar k'irjin ta yayinda tasa yatsunta kuma cikin sumar kanshi tana mai wani salon romancing mai ruɗarwa,

gaba ɗaya ta gigitashi sai juya kanshi yake a k'irjinta duk ta inda yaga dama hannun shi kuwa na shafa cikin ta da ker ya budi baki a hankali yace,

"Babyna.! Allah ya miki albarka kin gama min komai a rayuwa ta tunda kike samamin farin ciki".

Kai ta ɗan ɗago ido cike da kwallah tace,"Sweetheart.....! Ni ce da godiya ka gamamin komi a rayuwa ka mai dani cikakkiyar macce mai gata ina alfahari da kai mijina i love you so much.......!".

Murmushi yayi cikin jin dadi da tarin ƙauna ya rugumota yana murza k'irjin ta murya can ƙasa ya ye I love you too Soulmate........!"

Ya sumbance ta ta daga blanket din ya saka ta ciki shi ma ya lulluba ya rumgumeta...........

Hummmm bari dai na tsaya daga nan kar bin ƙwaƙwƙwafin ya yi yawa kuma😂.

*_ALHAMDULILLAHI! ALHAMDULILLAHI!! ALHAMDULILLAHI!!!_*

To My Novel's Fans

Na godewa Allah daya bani rai da lafiya da damar rubuta wannan littafin daga forko har zuwa k'arshe Alhamdulillah.

Abinda nayi dai-dai Allah ya taramu a kan ladan abinda nayi kuskure bisa ajizanci naɗan Adam Allah ya gafarta min.

Masoya na ina alfahari daku zanyi kewarku zakuyi kewata dan ina son hutawa sosai kafin na faro sabon novel.......

*TAKU HAR KULLUM SADIYA KA'OJE (MRS BBK)*❤️

20 / 20