Bin Maryam Book 2 Complete Sadiya Kaoje

Author :  Sadiya Kaoje Category :  Read Hausa Novels

Chapter   13 / 20

36K to 39K   out of 59.4K words

shiga maƙota nemanta da duk inda nake tunanin zata je Amman ban ganta, da ni da aka haka muka raba dare muna Nemanta har washe gari, munyu kuka har mun gode Allah, wasa har kusan kwana ukku ba labarin Jumaymah mun kai ƙarafin wajen yan sanda Kasan cewar babu mu da abin hannu sukayi watsi da maganarmu, sai na fara zargin mutumen da suke cewa yana zuwa wajensu mai kama da Mahaifinsu, sannan wani daga cikin samarin unguwar ya ce ya ga lokacin da Jumaymah ta fito daga gida ta nufi wajen mai motar ku ma yadda ta isa wajensa akwai kyakkyawar alaƙa a tsakaninsu, hankali ya tashi sosai harna fara zargin Kodai Yusuf ya Saida min da ɗata ne?, a lokacin ne ya nuna baçin ransa sosai wanda tunda nake dashi ban taɓa ganinsa cikin yanayin ba, tun daga lokacin ni kuma na daukin Alƙawarin baza sake yi masa maganar Jumayma, Saida a kullum ina mata Addu'a a duk in da take Allah ya kare ta,idon da rabon zamu gana Allah ya haɗa mu anan duniya ko lahira. Junainah tun tana tambatayar yar Uwarta har ta dena, haka mukaci gaba da rayuwarmu kaman yadda muka saba sai dai duk lokacin da na tuna da Jumaymah nakayi kuka sosai.... Ranar da Yusuf zai rasu yana cikin ciwon Ajali, muryarsa na rawa yake faɗa min wadansu maganganu da hankali ya kasa ɗaukar su a ganin kaman ciwone ya addabe sa har yake irin waƴan nan maganganu duk da a lokacin bana cikin haiyacina maganar ta tsamin rai," Murjanatu ki gafarceni a kwai abubuwa da yawa da na ɓoye miki a rayuwata ina fatan zaki ya femin sanan yarki Jumayma yana raye tana wajen dan uwana a duk lokacin da ta so gareki ki karɓe ta saboda yar ki ce".. Amma ta karasa maganar tana kuka mai tsuma Zuciya.

Jumaymah kukan take kaman ranta zai fita,

"Duk abin da Yusuf ya faɗa miki gaskiya ne". Cewar Bappa.

"Allah ya jiƙanka da rahama Yusuf Allah ya gafarta maka, na gode sosai da karramawarka hakiƙa kai miji ne na gari Allah ya yafe maka kurakuranka, yau gani cikin zuri'arka amma baka raye!".Har lokacin kukan take.

Suka Amsa da Amin.

Daga nan Amma ta basu labarin irin rayuwar da sukayi tun bayan Rasuwar Yusuf har zuwansu gidan Ummy da Auren Junainah.

"Ma sha Allah, Yanzu ke nan Junainah tana ɗakin Mijinta?".

Amma ta gyaɗa masa kai alamar Ehh.

Bappa ya yi ma Ummy da Dr Kamal gadiyar riƙe masa iyalin dan uwansa da sukayi.

"Ai ba komi yiwa kai ne, an riga da an zama ɗaya yanzu".

"Sai maganar gado akwai gadon Yusuf a hannuna iyayenmu suka bar muna, A kwai kuɗi nera miyan ɗari biyar sai gidan mai guda huɗu da filaye guda ashirin, gidaje talatin wanda duk sun kasance kason Yusuf ne. Wannan iya wanda Mahaifinmu ya bar muna ne, sai gadon Mahaifiyarmu Yusuf nada biyan ɗari biyu gidaje biyar filaye ukku". Duk kansu na wajena duk ranar da kike bukatarsu zanyi magana da lauyana sai a baki hakkenki dana Yayanki".

"Ni na yafe a rabama mabuƙata". cewar Amma tana kuka....

*ASAD*

A hankali ya yi parking ya fito daga cikin motar yana kallon sojojin dake kai komo a cikin gidansu, sannan ya wuce falon Ummy, zaune ya samu su Afreen suna kallo a tare suka gaisheshi sannan ya tambayi Ummy.

"Tana Falon Daddy Baƙi sukayi".



A hankali ya zauna saman sopa, sai ga kiran Ummy ya shigo ya ɗaga.

"Ka same ni a ɓangaren Dr".sannan ta kashe wayar.

Kai tsaye ya nufi falon ya tura ƙofa ya shiga da sallama a bakinsa.

Tare suka amsa mishi, Asad ya tsaya cak yana kallon Jumayma cikin matsanancin mamaki, "ƙara so mana" Ummy ta faɗa tana Murmushi, saboda tasan dalilin tsayuwarsa.

Har ya karaso cikin falon idanunsa na akan Jumayma, fuska aka sake ya gaishesu, Bappa ya amsa Mishi yana murmushi.

"Wannan shine surikin nawa?" Bappa ya tambaya yana kallon Asad

"Daddy ya ce shi ne".

"Ina yar tawa?"

"Asad yana murmushi ya ce tana,"gida...."

"Ne mi wuri ka zauna".

Asad ya zauna kasa kusa da Daddy yana kallon Jumayma ta ƙasan ido.

daga nan Daddy ya gabatar mi shi dasu Daddy da matsayin su a wajen Junainah, sannan ya bashi labarin yadda komi ya faru.

Asad ya yi mamakin sosai da jin Junainah Twins ne,

"Bari naje gida na dauko ta". Asad ya faɗa yana ficewa daga falon. Da kallo suka bi shi har ya fice..

da sauri ya muɓe motarsa ya shiga mai gadi ya buɗe masa gata ya fice da gudu sai da ya hau titi sanan ya kira ɗan wayarsa da ya barma Nainah gida tana game.

"Hello"

"Baby"

"Na'am ya aikin?"

"Alhamdulillahi ban je wajen aiki ba gidan Ummy na tsaya".

"Fada min me zan siyo miki?"

"Bana bukatar komi".

"Albishirin ki"

"Goro"

"Ki shirya yanzu zan zo in ɗauke ki mu tafi gidan Ummu".

"Me ya faru?."

"Idan na fada miki ai bai zama surprise ba, shirya kawai"

Kamin tace komai ya yanke wayar yana murmushi, mamaki ne ya cika ta jin yace zai mata albishirin na minene, tana ta tunani kala kala amman ta kasa cankar ko minene, tana zaune a dakin har ta ji karar bude gate, wanda hakan yai daidai da kiransa."fito mu tafi".

ta miƙe a hankali ta dauki hijab dinta sanan ta fice...

Tunda suka kusan isowa gidan Ummy gabata ya soma faɗuwa har suka iso mai gadi ya buɗe musu gate ya shiga ya yi parking ya fito ya buɗe mata mota sanan ya rufe.tafiya ta fara yi kadan kadan kamar wanda bata son tafiya a tsorace ta riƙa kallon sojojin gabata na ci gaba da faduwa, kai tsaye Asad ya wuce da ita Falon Daddy, ya buɗe kofar A hankali da Amma ta fara arba ta sako mata da sakon murmushi, sai ta mayar mata kamin idonta ya sauka gurin Jumayma tana kallonta, idonta cike da hawaye tsayawa tai cak tana kallonsu hawaye na sauko mata, zata ruga da gudu Asad yai saurin riketa ya rumgume sai ta fashe da kuka.



"Ya Asad ina ji a jikina kaman ina kusa da yan uwana?."

"Da gaske ne yan uwanki ne Baby harda Twins sister ɗinkin".

"Daman Amma ta ce tana raye kuma wata rana zamu ga juna a she gaskiya Amma ta faɗa".tana magana tana kukan farin ciki.

A hankali ya janyeta daga jikinsa suka ƙara sa cikin falon Jumayma ta rungumeta wani irin shock su kayi a.lokaci ɗaya, nan take suka fashe da kuka.

Kuka sukayi sosai kamin su samu natsuwa, sannan Junainah ta rikata suka zauna saman kujera daya, Amma na kallonsu idonunta cike da kwalla.

"Amma mi ke faruwa?." Junainah ta tambaya tana kuka".

A tsanake Asad ya yi mata bayanin komi daki daki.

"na fahimci komai yanzu kenan ina a gaban yayan Mahaifina da yan uwana?".

Ta fada hawaye na sauko mata, kuka take tana kallon ƴan'uwanta tana jin wani irin shaukin kaunarsu na ratsata.

"Yadda Allah ya tsara abu haka yake kasancewa, kin ga da Allah ya so sai ya sa ta wannan video zaki haɗu da yar uwarki, sai ki fahimci akwai hikima a cikin lamarin, ku yarda da kaddara ku gode Allah da yai muku tsawon rai har kuka gane junanku".

Asad ya faɗa Junainah tai murmushin.

"Haka ne, ni kaina na san Allah ne ya tsara min haka, sai kuma ya kawo kai acikin rayuwata don da ban haɗu da kai ba da ba'ayin wannan video ba"



"Ha ka ne"

Ita ma kan ta daga masa tana cigaba da kuka da yaki ya tsaya mata. Sai da Asad ya tabbatar ta daina kukan sannan Ummy da Daddy da Asad suka fice daga falon ya suka basu guri sun yu maganganu da yawa masu taɓa zuciya da tuna baya..

"Junainah Mahaifiyarki ta yi dacen ƴa tagari da ba ki saka mata ido har ta wulakanta ba Allah yai miki albarka".

Gaba daya suka amsa da amin, ita kuwa ta amsa a cikin Zuciyarta tana jin daɗi.

Tsakanin ita da Amma sai ta rasa wa yafi wani farin ciki a yau.

Da gudu ta tashi taje ta fada jikin Bappa ta rumgumeshi tana kuka, sai yai murmushi kowa da ke falon sai da tauyasa kuma yai murmushi

Ranar haka suka kasance cikin farin ciki da an nashuwa, Da Daddare Junainah ta sa kuka akan bazata bi Asad gida ba a la dole wajen yan uwanta zata kwana, saboda farin cikinta dole ya amince sai da bai bar gidan sai kusan 12:30 na dare ya koma gida.

Kwanansu Bappa Ukku gidan a yaune ne kuma zasu koma.

Ummy da su Afreen suka fito gaba ɗayansu suna musu sallama.

Junaid ne ya ciro kudi mai yawa ya bawa Afreen ya ce su raba, sannan ya ciro wasu ya bawa Ummy da Amma, Jamil kan sai da ya shiga mota a side din da yasan mutane ba zasu hango su ya sauke gilashin motar yace ta Afra ta zagoyo sannan ya rufee glass din. Zagayowa tai kamar yadda ya bukata sai ya mata sallama sannan ya mika mata katinsa da kudi mai yawa wai su raba. Godiya tai masa sannan ta matsa baya Junaid ya shiga mota Bappa yaje ya shiga tashi suka bar gidan Jumayma na daga musu hannu..............✍️

💋𝐁𝐈𝐍 𝐌𝐀𝐑𝐘𝐀𝐌💋

𝑵𝒂

𝑺𝒂𝒅𝒆𝒆𝒚𝒂 𝑲𝒂'𝒐𝒋𝒆

08149979652

*Book 2*

_______Bayan tafiyarsu, Nainah da Jumayma suka wuce Bq tare Amma sunsa Amma a tsakiya ko wannensu riƙe da hannunta ginin burgewa, kallo ɗaya zaka musu kasan cewa suna cikin murna da farin ciki.

Tun zuwan Jumayma kullum Nainah a gidan take yini idon Asad zaije office s

Zai aje sai dare su koma hakan yasa suka ƙara shaƙuwa da juna, tsakin Amma na Jumayma zuwa yanzu sun shaƙu sosai.

Kusan kullum Nainah sai tayi waya da yan uwanta da wayar Jumayma su Adda Aysha da Adda Nazlah kusan kullum sai sunyi video call.

A Ɓangaren Afra da Afreen ma sun shaƙu sosai da Jumayma saboda ko da yaushe suna tare da juna idon basu Bq wajen Amma to suna falon Ummy.

Yau ta kasance Weekend wuraren ƙarfe goma Su Jumaimah suka wuce gidan Asad tare su Afreen, Sosai Nainah ta yi farin cikin ganin su duk dai wannan ba shine zuwansu na farko ba, suna isowa bada jimawa Asad ya fice zuwa gidan Iya, haka wuni ranar cikin so da kyaunar juna har bayan Isha'i,

"Anty Afreen ina son kafin ku tafi mu danyi wata wasa, so nake Jumayma taje wajen Ya Asad a matsayin ni naga ko zai iya banbancemu".

"In dai ya Asad da na sani ne tsab zai gane ba ke ce ba".

"Anty Afreen da wuya zai iya ganewa Amma ma fa wani lokaci bata banbance mu ita kenan da ta faifemu balle shi".

"Toh wallahi Ya Asad zai banbance ku".

Daga nan suka soma musu wannan tace Asad zai gane wannan tace ba zai gane su ba, Afra ma ta goyi bayan Asad zai banbance su.

Jumaymah dai sai kallonsu take tana dariya.

Afreen ta ce," Na yadda ayi wasan Amma da sharaɗi idon har Ya Asad ya gane Anty Nainah nawa zaki ba ni?".

Kai tsaye Nainah ta ce,"Dubu Hamsin". Gaba dayansu sukayi Dariya.

"Ni kuma idon har bai gane ba zan baki Dubu Hamsin".

Afra Jumayma kune shaida".cewar Afreen, suka gyaɗa mata kai.

"Yanzu Jumayma ki cire kayan jikinki ki ba Nainah ita ma ta cire gayan jikinta ki saka.

Haka ko akayi Nainah ta sa kayan Jumayma, Ita kuma Jumayma ta sa Kayan Nainah. suka zauna suna jiran dawowar Asad. Bayan mintuna goma suka ji ƙarar motarsa da saurin suka boye bayan kujeru aka bar Jumayma dai zaune saman Sopa, Asad na buɗe kofar falon ta mike da sauri ta nufi wajensa tana ƙoƙarin rungumesa, da saurin yaja daya yana kallonta fuska a haɗe ba alamar wasa ko kaɗan a tattare da shi,

A karo na biyu ta sake yunkurin rungumeshi,

"Stop....". Ya faɗa da karfi.

"Yah Asad lafiya?". Jumaymah ta fafa Murya a sanyaye tana turo ɗan ƙaramin bakinta.

Duk abin da ke faruwa Su Afreen na kallonsu.

"Ina Junainah..!"

Jumaymah ta ce,"Akwai wata Junainah a gidan bayan ni?"

"Kaman ya? Ni ce fa Ya Asad..."

"Kinyi zaton ban gane ki ba....?".



Afreen ta fito daga bayan kuje tana faɗin,"Wallahi naci dubu Hamsin..".

Tana faɗi tana dariya,

Lokaci ɗaya suka iso wajen Asad suna dariya. Afreen ta faɗa mishi komi sanan ta kalli Nainah ta ce,"Sai a bani dubu hamsin ɗina...!"

"Anty Afreen ni da da wasa nake, ban da kuɗi".

"Sai mijinki ya fansheki,

"Nawa ne kuɗin?". cewar Asad.

"50k...".

"Zan tura muki 150k sai mu raba".

Godiya sosai sukayi mishi, basu bar gidan ba Saida sukaci takeaway da Asad yawo musu shi sanan suka wuce gida.

"Kinyi tunanin bazam gane ki ba? Ko cikin mutane dubu kike zan gane ki, amma me yasa baki taɓa faɗa min ku Twins ba ne?".

"Ba komi".

na aure ki ba tare da sanin kowa na ki ba sai dan nuna miki tsantsar kauna ni da Ummy, Wallahi Junainah ko da daga sama kika fado zan aureki ba tare da damuwa ba, saboda ke na ke kauna ba wani abun daya shafi dangantarki ba ko kuma asalinki ba"

Kallonsa ta ke hawaye taf a idonta wata irin kalar kaunarsa da begensa ne ke shiga cikin ruhinta Hakika Asad yayi mata abunda ba kowa ne ke yi ba, auren mace da baka san asalinta ba, ko da dan kyauna Asad ya aureta yayi mata hallacin tun da be taba bayyana hakan ba ya bari a cikin ransa kuma be taɓa nuna mata ba.

"Ko da ka tambaye ni asalina a wacan lokacin ko kuma anan gaba idan har wannan abun be bayyana ba, ba zan iya fada maka ba, saboda bana son bayyana abun da Amma ta fada min a matsayin sirrin"

Hannunsa ya kai ya riko nata

"Junainah Kina da karancin shekaru amman kina da wayo da hikima akan dukan abunda ya shafi mahaifiyarki, hakan na da kyau kaunarki na ta karuwa a raina ta ko'ina"

Dan murmushi tai tana hawayen da suka tsaya mata. Sai ya jata jikinsa ya rumgume ta ita kuma kuma ta lafe abunta domin ta fara sabawa da yanayinsa a yanzu.

"Na faɗa ma Ummy ki na da Juna biyu".Ya fada saitin kunnenta. Sai ta fashe da kuka.

"Me saya ka gaya mata? yanzu kowa sai ya san abunda ya faru ko? Idan aka gan ni da ciki"

"Daman ai an san dole wani abun zai faru"

"Amman dai akwai kunya"

"kunya kuma ai tunda kika yarda kika zauna gidan miji ta ƙare"

Kuka ta fara bana wasa ba tun yana rarrashina a hankali har abun ya koma bashi tsoro.

"Ni dai aje a cire cikin nan sai ka faɗa ma Ummy ba cike ba ne".

"Bayan kowa ya gama sani, sannan Ummy ta jima da sanin kina da ciki".

"A a nidai ba yanzu ba nidai bana ma so gaba daya"

Zaunar da ita yai saman gadon ya zuba mata ido yana ta kallonta

Baby Dan girman Allah ki daina kukan nan, kar kukan ya cutar da abunda ke cikinki".

"Ba zan iya iya kallon kowa ba kunya nake ji yanzu har Bappa sai yasan Abinda Ya faru?".

"Ciki ai kin riga kin yi, yi hakuri ba za a sake wani cikin ba"

"Da gaske?"

Dariya yai ya gyada mata kai. Sannan ta sausauta kuka shi kuma ya tashi yaje debo mata ruwa. Sanan ya nufi falo ya dawo

"Ga waya ke ma ki fara kiran yan uwanki kuna gaisawa"

Ba shiri ta zaro ido ta karbi wayar da sauri da daka wani irin tsalle kamin da dire yai saurin cabeta.

"Ke yanzu fa ba ke kadai kike ba, ki daina irin wannan abun"

Ina bata ma jin me yake fada sai ihu take ya rumgume shi sabar farinciki har da yi masa kiss a fuska.

“Na gode sosai".

Haka tai ta maimaitawa sai da ya rufe mata baki, sai kuma ta fashe da kuka kuka irin sosai din nan kamar wacce akai wani abu rasa tai me zata yi, ita a rayuwarta bata taba rika waya ba ko karama balle babba irin wannan mai screen kato. Rikota yai suka zauna, sai ya karbi wayar ya bude mata ya hada mata.

"Na gode sosai Allah ya kara arziki ya tsareka daga dukan sheri Allah ya biya maka bukatunka na alheri"

jin tai bata gamsu ba har sai da ta dawo saman jikinsa ta zauna ta rumgume shi.....

***** ***** **********

Da Yamma suna zaune a Bq Deedat ya shigo gidan cikin danƙareriyar motarsa ya yi parking,Afreen ta ce ,"Jumayma muje mu gaida Ya Deedat".

cikin natsuwa suke tafiya har suka soma hango Deedat jikin motarsa yana sanye da ƙananan kaya wanda sunyi matukar karɓarsa ya yi kyau ga wani irin sheƙi da walƙiya da yake Hannunsa sanye cikin Aljihunsa ya ɗan shingiɗa jikin motar yana waya.

Tunda Jumayma ta soma hango shi taji gabanta ya faɗi kamar ta koma Bq sai kuma tayi karfin hali ta daure tana kusantowa da kamanninsa suna bayyana, take kyakkyawar fuskarsa ta bayyana wani irin firgici da tashin hankalin ta tsinci kanta a ciki da saurin ta koma Bq, yayin da Afreen ke faman kiranta Amman ina bata saurareta ba, tana ƙarasawa ta

13 / 20