Author : Sadiya Kaoje Category : Read Hausa Novels
idan babu ilmi tarbiyar ma ya kake tunanin za ayi ta? Miyasa ake son auren mace mai ilmi ba dan wannan ba?"
"Ummy a gaskiya ni ba zan iya daukar wannan ba, ke ma fa Ummy kin san yadda ake bukatar abun nan yanzu kuma ki kawo wasu maganganu don Allah a riƙa yimin adalci"
"Haba dai? Yanzu kana ganin idan a gurin ƴaƴan Mahaifinta take kuma ya samu labarin bata iya komai ba batai karatu ba zai zuba mata ido haka? Yanzu ka fi son tai ta zaman banza a wata bakwai ko takwas da ke tafi wanda za tai nan gaba? Ai ya kamata ka saka ta ilslamiya ko kuma na nemo malamin da zai rika karantar da ita a gida, in so shi bokon idan ta haihu sai ta yi, baka sanan miye take son zama ba"
Ummy na fadin tai saurin cewa ,"Ummy ina son na zama likita abun na burge ni sosai".
Harara ya watso mata
" ki sake magana na buge miki ba ki a nan, haka nan za ki je ki yi karatun likita shekara nawa tare da maza?"
"Ai ansan ina da aure kuma zan rika saka hijab har da niqab ma"
"Wai ba za ki yi shirun ba? Ba ki san kyaunki hadari ne ba, kuma ba ki da wayo da za ki iya tattalin abunki balle har ki kare martabarki".
"Allah ya yaye maka wannan bakin kishin daya cika maka zuciya, amman karatu kan dole ne tai yarinya ba za tai zama haka ba, kai ma da yarka ce ai ba zaka barta haka ba, ko ka barta taci gaba da karatu ko na faɗa ma Bappa in ya so sai ta koma can da zama ga baki ɗaya har ta kammala karatun, ga Yar Uwarta nan Jumayma har taje University".
"Ummy za tai karatu, karatuna yana cikin burin da na ke da shi akan amman sai ta haihu ta yaye abunda ta haifa ya yi kwari sannan a fara maganar karatun shi ma idan bata samu wani cikin ba”
"Na tabbatar idon aka biye ta taka ba zaka bari Junainah tayi karatu ba, ina ga kawai zan sanar Bappa, tun da ni karena ni,Yanzu a maimakon zaman da za tai ai sai ka sakata ta fara daga matakin farko kamin ta haihu dan yai kwari ta san wani abu ka ga ci gaba kawai za tai"
"Momy mun ma kusa barin garin nan Kaduna za mu koma"
"Kadunar na ke nufin ka saka ta ba a nan ba, daman can sun fi makarantu masu kyau"
Junainah ta jidadi sosai da Ummu ta tunatar da shi batun karatun ta da kuma abunda ta ke ta mafarkin samu shekaru da yawa, domin ta ga kamar shi ya manta idan ma be manta ba to yana son shashantar da abun saboda kar dansa ko yarsa su wahala. Ita ko bata ga abun wahala a ciki ba domin bata jin komai ko aman da take ta dade bata yi ba sai dai yawan cin abinci da ta ke sosai
Shikenan Ummy daman can na san ai ba ke ce Mama na ba, shiyasa ba ki goyon baya na, da Umma ce ko Iya da yanzu ta sun saka baki".
“Daman can ai kai ba dan ba ne, balle kuma yanzu da na samu yata ta, ga su Afreen da Afra ga kuma Adnan sun isheni".
"Ai na sani ba sai kin faɗa ba Ummy kina son kowa ban ni, ga shi kuma ni ne ɗan ki don ni ake kira da *BIN MARYAM*na sukan tafiya na barki da su"
"Allah raka taki gona, karatu dai ne sai Junainah tayi shi in sha Allahu,kamayi tafiyar ka batar ta huta".
Dariya yai dan yana jin kamar ba da gaske Ummy take ba, Junainah dai ta yi yar dariya dan ta san Ummy ta fada masa abunda ba zai yiwu ba...............✍️
💋𝐁𝐈𝐍 𝐌𝐀𝐑𝐘𝐀𝐌💋
𝑵𝒂
𝑺𝒂𝒅𝒆𝒆𝒚𝒂 𝑲𝒂'𝒐𝒋𝒆
08149979652
*Book 2*
_______Suna karyo kwanar gidan gaban Amma ya yi masifar faɗuwa, ba ƙaramin ta shin Hankali ta shiga ba lokacin da suka shigo cikin gidan, haƙiƙa duk da shekaru sun ja. Hakan bai hanata gane gidan ba, sai ta ke ganin kaman jiya suka zo tare da Aliyu lokacin tana Amarya,komi sai ya dawo mata sabo, duk da an sabunta tsarin gidan sa sabbi sauye sauye masu matukar kyau da ɗaukar hankali mai kallon bai haka ta gane gidan ba, cikin sanyi jiki Amma ta fito daga cikin motar duk kan ilahirin jikinta a mace.
A ɓangaren Asad ma kusan hakan ne ya faru da shi, domin tun da suka shigo cikin gidan bugun Zuciyarsa ya tsananta sosai jikinsa ya yi sanyi, cikin wani irin yanayi ya yi parking ɗin motarsa suka fito yana kallon tsarin gidan.
"Ya dai?"Nainah ta faɗa tana kusanto in da yake.
"Ya yi Murmushi karfin hali mai kama da yaƙe sanan ya ce,"Ba komi".
"Da gaske? amma naga yanayin ka ya sauya sosai".
"Bana jin daɗi ne".
"Sannu, tun ba jimawa zamuyi ba idon mun koma gida sai yaya Adnan ya du ba ka". Nainah ta faɗa cike da kulawa. ya sakar mata murmushi.
Dr Kamal na gaba suna biye da shi a baya,tun da suka shigo cikin falaon hankali kowa ya dawo kan Asad suna kallon shi wasu daga kicinsu a Saida suka miƙe tsaye.
"Kamal har kun i....." ragowar maganar ta ma ƙale a bakinta sakamakon arba da fuskar Asad da tayi.
Mama ta ɗaga Hannunta da kyar tana nuna Asad da ɗan yatsa.
"Ka..mal.... Waye wannan mai kama da Aliyu?". Ummy ta runtse ido da sauri hawaye na zubo mata.
Amma tuni ta yi mutuwar tsaye da jin furucin Mama.
Dr Kamal ya kalli Mama yana murmushi karfin hali ya ce,"Ƴaƴan su Adnan ne".
"Asad ko sai kallonsu ya ke mamaki ƙarara a fuskarsa.
"Ya Aliyu ya zo ya ga mai kama da shi". Cewar Hanifa.
Haka suka nemi wuri suka zauna hankali Mama gabaki ɗaya yana wajen Asad da ke zaune ya saka sakewa ko kaɗan.
"Amma banda kallon Mama ba abin da take domin ta ganeta sai dai ita yana da matukar walaha ta iya ganeta wata ƙila sun mace ma da tarihinta a rayuwarsu.
"Mama ina wuni". Su Afreen suka faɗa tare da Nainah".
"Lafiya lau".
"Uwar gida ran gida, na yi kewarki sosai Mama". Adnan ya faɗa cike da zolaya. mama murmushi.
"Mama Aliyun yana ciki?".
"Ehh yana ciki Kamal sai dai bacci ya ke".
Yana gaba suna biye da shi a baya har zuwa ɗakin da Aliyu ya ke kwance.
Wani irin shock Ummy ta ji tun daga kanta har zuwa tafin kafarta lokacin da ta yi ido biyu da Aliyu dake kwance bisa gado kammanin duk sun sauya , duk da sauyawar da ya yi hakan bai hana Ummy da Amma ga ne shi ba, Ummy ta daga kanta dake juyawa cikin matukar gigita da ɗimauta tana zaro ido cikin ɗaga murya ta ce"Aliyu....!"
Hakan ya yi dai dai da juyiwar Amma da Mama Dr Kamal saboda jin kiran sunan Aliyu da Ummy ta yi a firgice,
"Innalillahi wa'inna Ilaihir raji'un wa nake gani nan kaman Aliyu" Amma ta faɗa a firgice jikinta na rawa.
A razane Ummy ta ce,"Kin san shi ne? ".
"Harna mutu ba zan taɓa manda Aliyu ba, shine mutumen da na taɓa baki labarin ya yaudare ".
Ummy ta rungume Amma kafin nan kuka ya suɓuce musu lokaci ɗaya suna rike da juna, Mama da Dr kamal suka zama yan kallo. Duk da cewa Dr Kamal cike yake da matsanancin mamaki, yana ganin halin da Ummy take ci jikinsa ya yi sanyi ya ƙara tabbatar da abin da yake zargi shekara da shekaru, tuni ya gano Aliyu shine mahaifin Asad kaman yadda ya ke zargi.
"Balaraba...! kukan ya isa haka pls".Nan suka saki junansu ko wacce na share hawayenta, da ƙyar suka saki jiki suka zauna saman lallausar carpet dake shimfiɗe a ɗakin. Ummy tsura mishi ido hawaye na zubo mata cike da ɗumbin mamaki, sam ba ta yi tsammanin ganinsa a wannan yanayi ba, duk irin yadda Dr Kamal ke faɗa mata ya nayin ciwonsa ba tayi tunanin haka ba,
"Amma ta sake juyawa tana ƙarema Aliyu kallo tsoro mamaki da tsananin al'ajabin a bin da ya mayar da shi haka ta shiga tsakanin ɗimauta da ganin yanayin da Aliyu yake ciki.
Yau ina gayun nasa? Ina kyau da yake taƙama da shi wajen ɗaukar hankalin yan mata har ya yaudare su, ina kuɗin da yake tun ƙaho dasu ? Ina Daddy mai ɗaure masa gindi yana duk abin da yaga dama wata ƙilma ya rasu, ta aiyana a ranta, wai yau Aliyu ne kwance kaman ba shi ba, ta riƙa tuno Irin rayuwar da sukayi a baya tun farkon yaɗuwar su har zuwa rabuwarsu.
Ba shakka tasan haƙƙin tane ke bibiyar Aliyu, da sauran matan da ya yaudara, domin ta jima tana kai ƙararsa a wajen Allah da nufin ya yi mata sakayya akan cutar da Aliyu ya yi mata, ta sake ƙura masa ido hawaye na zubo mata.Ummy ta dafe kanta dake juyawa.
Mama ta maida kallonta da Ummy jin sunan da Dr Kamal ya kira ta shi, a ruɗe take,"Balaraba kuma? kuyimin bayani abin da ke faruwa? Kamal su waye waɗan nan?" da ganin yadda mama take magana kasan a ruɗe take.
"Mama wallahi a halin da ake ciki yanzu ba zan iya ce miki wani abu ba, sai da abin da nake zargi kaman gaskiya ne".
"Zargin me?".
"Balaraba tsohuwar matar Aliyu ce......!".
Dai dai lokacin su Sumayya suka shigo ɗakin karab a kunnen su.
Amma ta ɗago da sauri tana kallon Ummy cike da ruɗu. ta ce kenan Asad Ɗan Aliyu ne?".
Baki dayansu suka mai da Kallonsu wajen Asad da ke zaune ya sunkuyar dai a ƙasa gumi na fita masa ta ko'ina a jikinsa, tun ya yi ido biyu da Aliyu ya shiga cikin wani irin mawuyacin hali da bai taɓa tsintar kansa a cikin ba, jikinsa ya yi wani irin sanyi ya kame a wajen ɗaya zuciyarsa na bugawa da karfin gaske tamkar zata fasa ƙirjinsa tafito waje...
Suka sake shiga ruɗu taya za'a ce wannan ɗan Aliyu ne amma basu sani ba, duk dai kammanin Aliyu da Asad ɗaya ne,
"Wannan wane irin al'amari ne taya hakan ya faru amman bamu sani ba?".
"Ummy ta share wasu sabbin hawaye da suka zubo mata ta ce,"Shi ɗin ba ɗan Aliyu ba ne!". Ummy ta faɗa cikin tsawa, da har Saida ƴaƴanta suka sha jikin jikinsu domin basu taɓa ganin ɓacin ranta irin na yau ba".
"Maryam...! ya kamata ki dena boye boyen komi a yanzu, ki sani abin da ke tsakanin ki da Aliyu iya kune bai shafi Asad ba da har zaki ɓoye masa gaskiya tsawon shekaru masu yawa,
"Bai cancanci zama Uba bansa ba". Ta faɗa tana rushewa da kuka mai tsuma Zuciya, wallahi ko bayan rai na ban yafe ba Muhammad Asad ya amsa sunan Aliyu a matsayin Mahaifinsa ba!".
Asad ya rumtse idanunsa da karfi wasu hawaye masu zafi na sauko masa nan take kansa ya riƙa juyawa idanunsa sun bala'in sauyawa sunyi ja sosai.
Cikin sassarfa ya ƙara so gaban Ummy ya dafa ƙafafuwan murya na rawa ya ce,"Ummy da gaske shi ɗin Mahaifina ne? Ummy daman da gaske Mahaifina na raye tsawon shekarun ki ka ɓoye min?".
Ummy ta yi shiru tana kallonsa hawaye naci gaba da zubo mata.
"Ai ga irinta nan, ki san ta yadda zaki gare kanki". Dr Kamal ya cikin faɗa.
"Ummy don Allah ki amsa min tambayoyi na, da gaske shine mahaifina?".
"Umfanin me zai maka idon nace shine Mahaifinka ne?".
"Ummy don Allah......". Ya faɗa yana fashe da kuka mai taɓa Zuciya. Nan take jin Ummy sanyi tausayinsa ya cika mata zuciya, domin abu ne mai matukar walaha gaka kusan Asad.
Ummy na kuka tace,"Maihaifinka ne, sai dai cancanci zama Uba ba nayi da nasanin zamowarsa Mahaifinka, na so ace ba ta hanyar Aure na sameka damin zaifi min farin ciki, duk da nasan kai baka so hakan ba Amman walaƙanci da Mahaifinka ya yi min bazan taɓa yafe masa ba, kai kanka don baka san yadda kazo duniya bane, shin wace uwa ce zata so Mahaifin ɗanta ya gujeta a lokacin da take buƙatarsa a kusa da ita, shi wace uwace tazo a ce ita ce ta yan kama ɗanta ragon suna? Ka zo duniya a lokacin da ko wacce uwa take farin cikin samun ƙaruwa, uban da bai san cinka ba bai san shanka ba, bai san suturarka ba, bai sai ilimin ka ba bai san makwancinka ba, bai san komi naka kaba, na renaka da gumina har ka zama abin ka zama a yau, tir yan tir yan Ummy ta soma bashi labarin haduwarsu har zuwa rabuwarsu da irin gwagwarmayar da tasha wajen wanin rayuwarsa ta inganta. Duk wanda ke cikin ɗakin Saida ya yi kwalla, tausayin Ummy da ya cika musu Zuciya.
Jikin Amma ya yi sanyi, sai take ganin ita tana da sauƙima, Allah ya sota da cikin ya ɓare da ita kam sai tafi Ummy cika damuwa.
Adnan, Afra ,Afreen, sun cika da mamaki sosai da jin ba Dr Kamal ne Mahaifin Asad ba, su a tunaninsu uwa ɗaya uba ɗaya suke da shi, saboda Dr Kamal bai taɓa banbanta su ba, hasalima sai suce yafi kyaunar Asad a kansu.
"Ummy haƙiƙa mahaifina bai kyauta muna ga baki daya ba, ina nema masa yafiya a wajenki" yana magana ne a yayinda Hannayensa ke haɗe a waje ɗaya, yana magana yana kuka.
"Ki dubu girman Allah Ummy ki yafe masa". ya faɗa a karo na biyu
Ummy ta sauke Nannauyan Numfashi, ta mike ta nufi wajen da Aliyu yake kwance, Allah mai yadda yaso kuma a lokacin da yaso.
Tasan dai Aliyu tun da yake a rayuwarsa bai taɓa zaton ko tsammanin akwai wani lokaci da zai zo ya tsinci kansa a cikin wannan halin ba, duk da abin da bawa yake Allah na kwallonsa ya kyale shi ne kawai ya gama abinsa lokaci ɗaya Idon ya tashi ɗaukarsa sai ya kama shi a zo a na dana sani marar amfani.
(Allah yasa mu dace)
Asad ya ja dogon Numfashi idanunsa akan Aliyu sai kuma ya juyo ya zubawa Ummy ido wadda ita ma Aliyu ɗin take kallo ya ce,"Ummy don Allah ki yafe masa kon halin da yake ciki".
"Ta rausayar da kai idonta a kan sa kafin ta ce,"Allah ya yafe muna ga baki ɗaya".
Asad ya saki murmushi karfin hali,. A hankali ya ƙara so kusa da Aliyu ya durƙusa har ƙasa ya kama hannunsa ya sumbata sanan ya rungumeshi yana fashewa da kuka mai tsuma Zuciya wani irin shock ya kama shi nan take soyayyar mahaifinsa ta cika ruhinsa, ya jima a jikinsa kwance yana kuka mai cike farin cikin.
Kowa dake falon sai kallonsu suke suna hawayen farin ciki, a hankali Sumayya ta karaso kusa Mama ta dafa kafaɗarta ta ce," Kin tuna yaron da muka gani a TV shakarun baya da suka shuɗe?". Mama ta girgiza mata kai tana kwalla tana faɗin "na tuna Sumayya".
"Shine yanzu a gabanmu a matsayin jinin mu, daman na jima ina zargin Matar Ya Kamal tsohuwar matar ya Aliyu ce". Haka abubuwan da suka faru suka riƙa dawoma Mama, sai yanzu ta tabbatar da abin da Sumayya ke faɗa mata a baya.
A hankali Asad ya janye jikinsa daga na Aliyu yana kallon surar jikinsa tun daga kansa har zuwa ƙafafuwansa, komai nasu iri ɗaya kaman an tsaga kara ba in da ya baro kammaninsa duk da shekarunsa sun ja kallo ɗaya zaka masa ka gane shiɗin tsatson sane.
Amma ta ce,"kar dai kuje min Asad jinin Aliyu ne...!"
gabaki ɗayansu suka maida kallonsu a wajen Amma dake zaune tana kuka, Ummy ta gyaɗa mata kai, hawaye na zubo mata.
"Innalillahi wa'inna Ilaihir raji'un!, Yanzu ke nan jina Aliyu ya aura? Ina bazai yu.....". Ummy tayi saurin toshe mata baki.
"Don Allah ki yi shiru karki ce komi".
"Wace wannan kuma". Mama ta tambaya a ruɗe.
"Itama tsohuwar matar Aliyu ce Murjanatu.....!".
Gabaki ɗaya fakon kowa ya saka satali cikin ɗimbin mamaki da al'ajabi, musamman Asad, saboda abin yazo mishi tamkar a mafarki taya za'a ce Amma ma sun taɓa rayuwar Aure da Mahaifinsa.Ummy ta basu labarin tun farkon haduwarsu da su har zuwa Auren Junainah da Asad.
"Allah mai iko...." Mama ta faɗa tana jinjina lamarin Allah.
"In jin dai ba yar Yaya Aliyu ba ce". Cewar Sumayya.
"A'a bayan sun rabu da Aliyu ne ta sake aure ta haifesu". Ummy ta bata amsa a sanyaye.
Suna zaune sunyi zugum Haroon ya shigo da Daddy wanda ke zaune saman keke marar lafiya ya shigo dashi har tsakin ɗakin, a hankali ya Daddy ya riƙa binsu ɗaya bayan ɗaya yana kallonsu Su Adnan, Afreen, Afra su kawai ya gane saboda zuwan da suke gidan wajen Mama.
Ummy da Amma suka riƙa kallonsa cike al'ajabi, ɗin daɗa tsinkewa matuƙa da ganin halin da Daddy ya ce ciki , domin abin da matuƙar tsoro da tausayi mummunan da ya kasance ba su da masanin akan abin da ya haddasa musu ciwon da suke fama da shi.
Cikin karfin Halin Umma ta Labarta mishi komi, sosai hankalin Daddy ya tashi har ciwonsa na ƙoƙarin ta shi,
Murya Daddy na rawa ya.ce,"As...ad..! zo nan jika na" da sauri Asad ya karaso wajensa ya rungume Daddy yana kuka a yayin da shima Daddy ke kuka kaman wani ƙaramin yaro, sai da sukayi mai isarsu sanan Daddy ya nemi ya yafiyarsu Ummy da shi karan kashi Asad ɗin
"Balaraba Murjanatu! Kunga yadda rayuwa tayi damu?