Author : Sadiya Kaoje Category : Read Hausa Novels
💋𝐁𝐈𝐍 𝐌𝐀𝐑𝐘𝐀𝐌💋
𝑵𝒂
𝑺𝒂𝒅𝒆𝒆𝒚𝒂 𝑲𝒂'𝒐𝒋𝒆
08149979652
*Book 2*
_______A firgice ya mike tsaye yana kallon Video Zuciyarsa na zillo tamkar ta fito waje wani irin gumi mai masifar zafi ya riƙa fita ta ko wacce kusurwa ta Jikinta idanunsa suka sauya kala zuwa ja,
"No! No!! No!! Wannan ba Junainah ba ce"
A guje ya fito daga cikin office dinsa ya nufi motarsa ya shiga ya fizgi motar da karfi zuwa gida.
Ikon Allah ne kawai ya iso da shi gida saboda yadda yake tuƙi da mugun karfi yana fisgar motar, gaba daya ya rasa ta ina zai fara tunani. Yana yin parking be tsaya kashe motar ba ya bude ya fita ya bar motar a bude, yadda ya tura kofar falon Ummy ɗai zai tabbatar kama ba lafiya ba, Nainah dake tsaye ta juyo cikin tsoro ta kalli kofar falon, domin yadda ya turo kofar falon ya shigo ya firgitata sosai Kai tsaye ya nufeta.
"Waye wannan....?" Ya faɗa yana nuna mata video.
"Ban san shi ba!"
"waye wannan na ce?" Ya faɗa da matsifar ƙarfi.
"Wallahi ban san shi ba".
Da mugun ƙarfi ya shaƙo wuyanta ya haɗeta bango kana ya jujjuyata ya jefar da ita ƙasa ta tana kwala ihu.
"Innalillahi wa'inna Ilaihir raji'un! Lafiya?"
ya sake miƙar da ita tsaye ya ɗauke ta da mari yana faɗin,"wa ye wannan ɗan iska?"
gabaki ɗaya ta ruɗe ta fita haiyacinta a karo na ukku ya sake ɗauketa da mari, nan take hancinta da bakinta suka fara fitar da jini.
Ummy ta iso da sauri ta rike Hannu Asad ta matsar da shi gefe ta kalli Nainah da fuskarta ta canza saboda a zaba.
"Mi ke fa ruwa?"
Nainah ta kalli Ummy sai kuma ta fashe da kuka domin ba zata iya fadar abun da ta yi ba, tambayarta yake wanda bata sani ba. da ƙarfi ya runtse ido ya bude zuciyarsa na masa wani irin bala'in zafi...
Ummy ta tambaya a tsawace tana kallon Asad kamin ta juyo tana kallon Nainah.
"Me kika yi?"
Nainah ta girgiza kai tana kuka,"Ummy ban ma sa komi ba"
Asad ya dago da kyar ya danna wayarsa ya miƙa ma Nainah. ta dauki wayar da sauri ta duba, wani tashin hankali da idanuwanta suka yi arba da shi da gaske ita ce din ko mai kama da ita? yaushe ta dauki hakan ya faru? A ina? hawayen da take suka tsaya cak.... Tun tana ganin hotuna daidai har suka koma mata biyu ta gizon , ta dago kai sai duhu ya mamaye idanuwanta bata iya jin sautin komai wayar dake hannunta ta sulale kasa itama ta yanke jiki ta faɗi , Ummy ta karasa ta dauki wayar tana du bawa,"Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un!lahaula wala ƙuwwata Illah billahil aliyul Azhim Hasbunallahu wani'imal wakil Allahumma Ajirni fii musibati wa'ahlifli khairan minha La'ilaha Illah anta subhanaka Inni kuntu Minal Zhalimin!"Shi ne abun da ya fito daga bakinta tana rufe ido, Afreen ta karaso gurin da sauri ta karbi wayar ta duba, bata gama ta kallo ba Asad ya karbe wayar a hannunta.
"Ummy bata numfashi fa".
Afra ta faɗa a tsorace.
"Na shiga Ukku! Karfa yaron nan ya kashe yar Mutane".
Hankali a tashe suka kwashi Nainah zuwa Asbiti.
Rai a ɓace Asad ya fice daga gidan,
Saman titi ya yi parking motarsa yana huci, wayarsa ya ciro ya kira Ringing biyu aka ɗauka",
"John pls zan turo maka wani video ina son ka bincika min video da gaske ne ko editing?".
"Okay Sir".
Ya sauke wayar daga kunnensa ya shiga Whatsapp ya aika masa da video sannan ya goge su a wayarsa, ya saka wayar aljihu ya fizgi motar da ƙarfi......
*JUMAIMAH*
"Innalillahi wa'inna Ilaihir raji'un! Me zan gani haka? Jumayma! Ammi dake zaune ta miƙe tsaye Jikinta na karkarwa dai dai lokacin Bappa ya shigo tare da wasu Samari guda biyu masu kyau kusan kammanin su ɗaya sanye da kayan sojoji, ganin halin da Ammi ta ke ciki yasa suka nufi wajen da sauri suna faɗin,"Ammi lafiya?"
Murya na rawa ta fara kiran,"Ju...mai...ma...!" A firgici Bappa ya fara tambatayar me ya samu Jumaimah ɗin?"
Wayar da ke hannunta Bappa ya karɓa, idunsa suka sauka akan video ,"Innalillahi wa'inna Ilaihir raji'un! Jumaimah". Ya faɗa a ruɗe zuciyarsa na bugawa da sauri ɗaya daga cikin samarin ya karbe wayar yana kallon video da sauri ya jefar da wayar ya haura sama da matsanancin saurin ɗan uwansa ya mara masa baya, bayan ya gama kallon video.
Suna shigowa dakin Jumaimah na fitowa daga toilet gadan gadan suka nufeta hankali ya yi mugun ta shi ganin yadda suka nufo in da take. Suna isowa suka ɗauke ta mari lokaci duka suka riƙa kai mata ta ko'ina kan kace kwabo Jumaimah ta jigata ta fita haiyacinta banda ihu ba abin da take... Koda Ammi da Bappa suka shigo dakin kwance suka samu Jumaimah rai a hannun don Allah tana numfashi sama sama.
*ASAD*
Idanunsa a rufe suke, amma ba bacci yake ba, baƙin ciki ne ya yi masa yawa, ga kuma yunwa da take faman addabarsa. Ya goge hawayen baƙin cikin da ke malala a kan kuncensa. da kyar ya iya ciro wayarsa dake Ringing ya manta a kunne,"Ummy.....!" ya kira sunanta a sanyaye,
"Me ka ke nufi ka illata diyar mutane Sannan ka tafi ka barta, ka same ni a Asbitin yanzu ina son ganinka".
cikin wani irin yanayi ya nufi Asibiti. Kafin ya iso ya kira Adnan ya tambaye wajen Ɓangaren aka Kwantar da Nainah ya faɗa ɗa masa..
kofar dakin ya tura ya shiga, Ummy na zaune saman gadon da Nainah take kwance.
ya karasa gaban gadon saitin inda Nainah take zaune ya tsaya yana kallon fuskarta. Hawaye na malala akan kuncenta.
"Junainah.....!"
Bata amsa ba,
Ummy ta ce tunda ta farka bata ce kala ba".
Asad ya hadeye yawu mai matukar ďaci a maƙoshinsa.
Murya Nainah suka ji tana faɗin,"Amma wallahi ban aikata ba Sherrin aka min".
Murya a sanyaye Asad ya ce" Junainah na yarda da ke. Kuma ina goyon bayan akan baki aikata ba, zanci gaba da baki kariya a kone haki, nayi Miki Alƙawarin ƙato Miki hakkin ki, wallahi tallahi±³ ko waye ke da hannu a wannan Al'amari bazan barshi ba ko da ko ya kasance jinana ne".
"Kasan bata aikata ba, shine zaka hukuntata?".
"Ummy jikina yana bani Junainah ba aikata ba".
"Amma komai ya kare a rayuwata mutuncina ya zube a idon jama'a Yanzu kowa a tsirara yake kallo na yanzu babu abun da ya rage min, kullum bakinciki yake kusanto ni yana nisanta ni da farin ciki".
"Nainah ki yi haƙuri kinji, in Sha Allahu komi zai wuce".
"Ummy Ina Amma?"
"Amma tana gida".
"Ummy a kai wajen Amma".
"Kiyi haƙuri zuwa an jima kaɗan zamu tafi gida".
Kiran da Jonh ya yi masa ne yasa ya fice daga dakin da saurin zuwa wajen motarsa. "John ka duba Video kuwa?
"Yes Sir na duba"
"Ya ake ciki? Editing ne ko da gaske?"
" Sir editing ne na duba na yi bincike sosai, anyi amfani da hoton su ne kawai, na turama ainihin video da aka amfani da shi".
ASAD ya kai hannu ya shafa kansa ya Murmushi.
"Sannan wannan number da aka turoma video da ita ita ce ta saki video a yanar gizo, ni da yarana munyi nasarar goge video".
"Good Job! Thank you so much Jonh".
"Ur wlcm Sir"
"Ba ku na wani masaniya akan yaron da ya saki video?".
",Mu na nan muna bincike".
"Okay"
Zuwa yamma aka sallami Nainah.Bayan sun koma gida Ummy ta sanar da Amma duk abin ya faru, sannan ta tabbatar da da maganar da Asad ya faɗa mata na cewa video editing ne iya fuskar Nainah kawai aka amfani da ita, anan Hankali Amma ya ɗan kwanta.
"Allah ya tsinewa wanda ya aikata miki wannan abun Junainah, in sha Allahu ko waye ba zai gama lafiya ba," Amma ta faɗa tana share kwalla............✍️
💋𝐁𝐈𝐍 𝐌𝐀𝐑𝐘𝐀𝐌💋
𝑵𝒂
𝑺𝒂𝒅𝒆𝒆𝒚𝒂 𝑲𝒂'𝒐𝒋𝒆
08149979652
*Book 2*
_______Amma na fita, Deedat ya shigo falon a hankalinsa a ta she, da sauri Asad ya miƙe tsaye yana faɗin,"Me ka zo a gidan nan?".
"Kaman ya me na zo yi a gidan nan,wajen Junainah na zo".
"Deedat daga yau na yanke duk wata alaka dake tsakanina da kai, kuma Sunan Junainah ya fita a bakinka", daga yau na datse duk wata alaƙa dake tsakanin mu".
Deedat yayi murmushi mai sauti.
"Duk wannan akan me?".
"Kan Junainah, karka sake raɓarta".
"Kishi? yarinyar da kowa ya gama ganin tsiraicinta kamin ka gani, mi ye abin boyewa".
da saurin Asad ya dauƙi yuƙar da Ummy ta yan kama Nainah Apple da ita ya nufi wajen da Deedat yake tsaye zai soka mi shi Ummy ya fasa ihun tana ɗora hannu saman kai.
“Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un,Asad Kisan kai zaka yi? na shiga Ukku".
Cikin baƙin ciki da takaici Deedat ya kalli Asad idanunsa na kwalla.
"Asad da gaske zaka iya sokamin yuƙar nan?".
"Ga zahiri kana gani? Deedat daga yau babu ni babu kai".
"Asad ban yi tsamman ni samun haka daga gareka ba, wannan ne karo na farko da ka taɓa nuna ni da makami da saboda Macce bai kamata soyayyar ta rufe maka ido ba, har ka manta waye ni a gurinka, a yau ka nuna min tsantsar kiyayya Asad daman na lura da wannan babin tuna ranar da ka gane ina son Nainah, amman karka manra har yanzu Ni ɗan Uwanka ne, be kamata ka manta wannan ba, domin jina ba wasa ba ne".
"Rufe min baki marar mutunci banza, daman kana ɗaya daga cikin mutanen da nake zargi akan abin da ya faru da Junainah idon ma kayi ne domin na tsaneta hakan ba abin da ya ƙara min face soyayyar ta har yanzu ina sonta kuma bazan dena sonta ba har abada!".
"Asad kamin shuru....!" Ummy ta faɗa cikin tsawa.
"Ummy Sorry idona ya rufe bana dan Allah ina rokon alfarmar karki sake cewa zaki alakanta ni da Deedat na riga da na datse duk wata a laƙa dake tsakanin mu".
"Wannan wane irin banzan magana ne Allah ya haɗaku sannan kace zaka raba, wallahi zan saɓa maka idon baka janye furucin nan ba.....! ran mutum ba abun wasa ba ne kuma a yadda kake Deedat be kamata ace kana barin Sheidan ya shiga tsakaninku ba, kana musulmi amman kake wasa da rayuwar wani wanin ma Dan uwanka na jini,
"I'm Sorry Ummy.....!".
Yana kaiwa nan ya nufi hanyar dakinsa. Ummy ta bishi da kallon tsoro, har lokacin jikinta rawa yake, bata tsamanin tsamanin fushin Asad ya kai haka ba sai yau.
yana shiga ɗakun ya zauna a kujerar yana jin zafin kalaman Deedat kuma yana mamakin kansa da be ɗau mataki a kansa ba.
"Kishi? yarinyar da kowa ya gama ganin tsiraicinta kamin ka gani, mi ye abin boyewa".
Kalaman Deedat na karshe sun dawo masa, sai yayi sauri miƙewa tsaye yana fesar da numfashi mai zafi, wayarsa dake Ringing ya ciro ya manna a kunne daga can Ɓangaren Jonh ya ce ,"Sir munyi na sarar cabken yaron da muke zargin ya saki video a social media yanzu haka yana hannun mu".
"Good job Jonh on my way".
"Okay Sir....."
da saurin ya fito daga dakin kaman wanda zai tashi sama.
Ganin Ummy Zauna tana kuka ya nufi wajenta da saurin yana faɗin ,"Ummy lafiya?"
Ta dago ta kalleshi hawaye na zuba a idonta.
"Asad zuciyarka tana ba ni tsoro ban san a ina ka dauko wannan zuciya ba, ban san me zaka aikata a gaba ba, idan babu kowa wata rana zaka iya kashe wani akan Junainah, ka bata da ɗan Uwanka miye amfanin haka? Duk akan yarinyar nan fa".
Asad yayi shiru na dan lokaci idonsa na cika da hawaye.
Ummy ban san dalilin da ya Allah ya sakamin kaunar yarinyar nan ba, ni dai kawai Allah ya saka min kaunarta, ina jin farinciki a duk lokacin da tana farincikinta nakan shiga damuwa a duk lokacin da naga tana cikin damuwa idan wani ya tsane ta ina jin kamar ya tsani cigaba na ne, ita kadai ce yarinyar da nake jin zan iya jure duk wani abu da ya shafe ta, zan iya daukar duk wani zagi da suka a duniyar nan, ban sani ba ko a nan gaba zan gane kuskuren hakan,a yanzu bana jin son kowa sai ita Ummy wallahi ina son Junainah".
Kukan da Ummy take ya tsaya cak ganin ďanta abin sonta yana kuka,
"Ummy wallahi idon na rasa Junainah zan rasa raina Ina sonta Ummy......!"
"Ya Allah.....!".
Ummy ta furta cikin tashin hankali ta rika fuskar Asad da duka hannayenta sannan kamin ta tashi ta rumgume shi tana hawaye.
"Ba zaka rasa ranka ba In sha Allahu Junainah ta ke ace har Abada....!"
Ta dago ta kalli fuskarsa ta sake rumgume tana jin kaunarsa har cikin ruhinta.
"Wannan irin so da kake yi ma Junainah Allah yasa ta zame maka Alheri.....!".
"Junainah Alheri shi ga reni Ummu....!".
Har cikin Zuciyarsa yake faɗa mata irin son da ya ke ma Junainah
domin be taba zaunawa da ita gaba da gaba ya faɗa mata soyayyar wata mace da karfi kamar yadda ya yi mata a yau ba, a yadda zuciyarsa take idan ya rasa zai iya jefa kansa a cikin wani mummunan hali wata kila fushinsa da zuciyarsa su karu har aikata abun daba shi ke nan ba, idan kuma hakan ta faru ta san ba zata yafewa kanta ba.
"In Sha Allahu zaka mallaki Junainah..."
Asad yayi murmushi yana jin dadi a zuciyarsa,
"Ina alfahari dake Ummy a matsayin ki na mahaifyata,Ina son ki ina sonki sosai Ummy na".
"Allah ya yi jagora".
"Amin Ummy na...".
Ya amsa mata kai yana murmushi.
Kana ya kwanta a jikinta kamar yadda yake mata idon shogɓarsa ta motsa, babu ruwansa da girman da yayi kwantawa yake a jikinta yayi ta zuba shagwaba, kamar wani ƙaramin yaro. Kansa ta shafa tana kallonsa ita kam ba zata iya jurar danta ya rasa abin da ya ke so, yadda yake da fushi ma wata kila haɗiye zuciya zaiyi ya mutu. Dan haka zata aje makamanta a gefe ta saka musu ido, gudun kar ta rasa ďanta kuma ya dauke ta a matsayin makiyiyarsa. Wannan ne abun da ta ayyana a zuciyarta. Sai da ya samu natsuwa sosai sannan ya faɗama Ummy kiran da Jonh ya yi masa, Ummy ta yi masa fatan Alheri sannan ya fice daga falon yana sauri....
Yana fita su Afreen suka shigo falon suna murmushi,"Ummy yau Yah Asad ya kwace muna fada".
Ummy ta dalla musu harara.
Afra ta ce,"Allah Ummy idon yana kwanciya saman cinyarki zai karyaki".
"Yau kam Yah Asad shine Auta ba Nainah ba". Suka faɗa suna dariya.
"Ku fita a idona na rufe".
Ummy ta faɗa fuska ba daure....
*JUMAIMAH*
Zaune ta je ta hade kai da quiwa tana kuka mai tsuma Zuciya, bata taɓa da nasin zuwanata duniya ba sai a yau, ta yunƙura da kyar ta tashi Zuciyarta na suya da ƙuna ba don kada ta kasance a cikin bayin Allah masu butulci ba, da ta roƙi Allah ya karɓi ranta a yadda take a yanzu da wane ido zata kallin iyayenta ta faɗa musu ba ita ba ce, sai dai ta san Allah shi ne shaida kuma zai nuna gaskiya duk ran daren daɗewa gaskiya zata yi halinta ko a nan duniya ko ina an je gidan gaskiya....
"Ke! Muke saurare". Ammi ta katse mata tunani.
"Ammi wallahi ba ni ce ba".
Ta faɗa tana kuka mai tsuma Zuciya.
"Kina da wata hujjar da zaki iya kare kanki akan ba ke ce ba?".
"Bani da Ammi, Allah ne shedata wallahi ban aikata ba".
"Jumaimah Karki maida mu ƙananan yara da bamu san abin da muke ba, daman abin da kika aika kenan shiyassa ki ke cikin damuwa?".
"A'a Ammi".
"Bappa ya sauke Nannauyan Numfashi kana ya ce,"ya kamata mubi abin nan a hankali, jikina yana bani ba Jumaimah ba ce."
Ɗaya daga cikin samarin ya ce,"Bappa maganar ba ita ba ce duk bata taso ba, tsawon wata na da Rayuwar Jumaimah ta sauya? wata ƙila gudun kar abin ya bayyana ne yasa ta shiga damuwa".
"Ya Junaid wallahi ban aikata komi ba wallahi ba ni ce ba......".
Bata marasa ba Junaid ya ɗauke da mari....
"Junaid karka sake marinta". Bappa ya faɗa cikin tsawa.
*ASAD*.
Cikin ƙanƙanen lokaci ya iso caji ofis kai tsaye Jonh ya wuce dashi ɗakin duhu da suka aje saurayin da ake zargin ya ɗa hotunan Nainah.
zaune a kasa daga shi sai gundun wando fuskarsa duk a kumbure hancinsa na jini sai nishi yake sama sama. Asad ya karasa ya duka a gabansa ya karbi wayar Jonh ya haska saurayin da kyau"
"Waye kai?".
Saurayin ya kalleshi ya kasa cewa komai, Jonh ya daka mishi tsawa yana faɗin ,"Ba magana ake da kai ba?"
"Nuhu...!" Ya faɗa Murya na rawa.
"Daman kasan Junainah?".
Ya yi shiru bai ce komi ba.
John ya murɗe masa hannu , Nuhu ya kwala wani irin ihu, "wannan kadan ne daga ciki