Author : Ameera Adam Category : Read Hausa Novels
nake kan binciken yadda aka yi Fulani Khadija ta mutu, da irin kisan cin zarafin da aka yi mata. Don abin da ya sa na gagara nutsuwa an tabbatar da an cire zuciyarta, wanda hakan yake alamta mini akwai dalilin yin hakan."
Jakadiya da ta shiga nazarin yadda suka dawo, suka samu Fulani Khadija a daidai gaɓar da take gargarar mutuwa ta ce.
"Allah Ya taimake ki duka zancanki a hanya yake, Allah Ya bayyana gaskiya duk ɗacinta."
Fulani Zainaba ta amsa mata sannan ta sallame ta, tare da ba ta kayan sha tara ta arziki. Don tana buƙatar ta huta, domin ta san ta yadda za ta tunkari turakar sarki Gambo. Saboda ta ci alwashin duk rintsi, ba za ta shafe mako guda ba tare da ta tunkari turakar sirrinsa ba. Don ta haka ne za ta samu sukunin karanta wasiƙun da za su yi mata iso zuwa ga wurin da aka killace Kursum kamar yadda Jakadiya ta sanar da ita, cewar ita ce ta san kowanne irin sirrin da ke cikin masarautar.
Fulani Sadiya
Jakadiya tana fita daga sashen Fulani Zainaba kai tsaye sashen Fulani Sadiya ta nufa. A lokacin da ta ƙarasa Baiwa Sakina tana zaune tana matsa wa Fulanin ƙafa, kamar an jefo ta daga sama haka Jakadiya ta faɗa ɗakin tana sauke numfashi ta ce.
"Barka da hutawa ranki shi daɗe, barka da wannan lokaci gatan marar gata. Shugabar kowa mai tausayin talakawa, Allah Ya taimaki tauraruwa mai haske sasarin samaniya. Hutawarki lafiya giwar sarki kuma 'yar gaban goshinsa."
Kafin Jakadiya ta gama bambaɗanci, tuni Fulani Sadiya ta gama karantar akwai wata muhimmiyar maganar da ke tafe da ita. Don haka cikin isa da ƙasaita ta ce, "Jakadiya muna saurarenki."
Satar kallon Baiwa Sakina ta yi ta ce.
"Allah Ya taimake ki maganar tana buƙatar sirri."
Fulani Sadiya ta dubi Baiwa Sakina, don ta fahimci abin da take nufi amma sai ta ce.
"Tafi kanki tsaye Jakadiya babu wata damuwa."
Baiwa Sakina ta cigaba da matsa mata ƙafa, kanta a sunkuye tamkar ba ta san wainar da ake toyawa ba. Jakadiya ta gyara zama sannan ta zayyane wa Fulani Sadiya duk yadda suka yi da Fulani Zainaba, sannan ta ɗora da cewa.
"Ranki shi daɗe babban abin da ya ba ni mamaki, da na ji Fulani tana cewa koda ta mutu ɓoyayyan ɗanta da ke cikin masarautar nan zai maye gurbin muradinta domin jini ba wasa ba ne."
A hargitse Baiwa Sakina ta ɗago, saboda tashin hankali har sai da ta ƙware da tari. Amma da yake maganar Jakadiya ta girgiza Fulani Sadiya sai ba ta lura da yanayin da Sakina take ciki ba, cikin tsananin mamaki Fulani ta ce.
"Jakadiya kina nufin ita Zainaba ce take da ɗa a cikin masarautar nan?"
Cikin son gwaninta da neman suna Jakadiya ta gyaɗa kai ta ce.
"Na rantse da Ubangiji mai girma abin da ta faɗa kenan ranki shi daɗe." Shiru Fulani ta yi tana nazari, sai kuwa ta ce.
"Idan kuwa da gaske ɗan Zainaba yana raye to waye Sarki Gambo ya kashe? Domin kuwa duka duniya kowa ya shaida an kai masa jariri, kuma Zainaba ta haihu a wannan lokacin."
Jakadiya ta zuba tagumi cikin nazari ta ce, "Abin da ya ɗaure mini kai kenan ranki shi daɗe, domin kuwa uwar bayi ce ta karɓi haihuwar Zainaba, idan kuwa haka ne ya zama wajibi ta amsa duka waɗannan tambayoyin."
Da sauri Fulani Sadiya ta jinjina kai ta saki murmushi mai ɗauke da ma'anoni sannan ta ce.
"Jakadiya!"
Yadda Fulani ta ambaci sunan Jakadiya ya sa ta ɗago gabanta yana faɗuwa, sai ta ga Fulani ta dubi Baiwa Sakina ta ce.
"Kin yi mini mai wuya da har kika binciko mini wannan maganar Jakadiya, sai dai akwai yuwuwar ki sake zuba mini ido a kanta sosai domin akwai muhimman bayanan da zan samu daga gare ki."
Jakadiya ta jinjina kai, sai Fulani Sadiya ta sake duban Baiwa Sakina ta ce.
"Ke kuma Sakina! Ina son damƙa miki kaso mafi girma na bincikena a hannunki."
A ɗan hargitse Baiwa Sakina ta ce, "Na'am... iye ranki shi daɗe."
Fulani Sadiya ta yi mata kallon tsaf sannan ta ce.
"Ina son ki nutsu, domin tun a wancan lokacin na ce miki ƙofa a buɗe take da za ki cigaba da sanin waɗansu sirrikana."
Gumi ya shiga karyo wa Sakina, ta shiga gyaɗa kai gabanta yana cigaba da faɗuwa.
"Don haka, na ɗora miki alhakin binciko mini yadda wannan yanayin ya kasance, zan kira Uwar Bayi na ji daga gare ta. Ke kuma daga yau ne za ki fara shiga jikin Zainaba, domin ki gano mini a wurin da ɗanta yake a cikin masarautar nan. Haka kuma, ina son ki kasance mata lumbu-lumbu wutar ƙaiƙayi, ta yadda zan dinga samun bayanan sirri daga gare ki. Idan ta kama ma..."
Sai kuma Fulani ta yi shiru kamar mai nazari sai ta cigaba, "Wannan wata magana ce daban zan neme ki."
Haɗiye yawu Sakina ta yi cikin tsananin tashin hankali ta ce. "An gama ranki shi daɗe."
"Koda wasa, idan har kuka kuskura kuka munafunce ni, ko kuka ci amana. Ko kuma na gano wani abu da kaina, na rantse da girman Yesu mai ceto sai na shayar da ku ruwan mamakin da har gawarku ta ɓace a ƙarƙashin ƙasa ba za ku taɓa mantawa da ni ba." Baiwa Sakina ba, hatta Jakadiya sai da ta razana da jin furucin Fulani Sadiya da kalaman rantsuwarta na ƙarshe. Sai kuma suka ji ta saki dariya ta ce.
"Ita kuma Fulani Zainaba ku bar ni da ita, sai na shirya mata tuggun da za ta da gwammaci mutuwarta a kan rayuwarta. Domin sai ta yi danasanin shiga ɗakin sirrin Sarki Gambo da za ta yi, ba zan sa ya kashe ta ba. Zan bar ta ne har zuwa lokacin da zan gano wanne jinin nata ne yake numfashi a doron ƙasa da take cin alwashinsa."
Duk jikinsu ne ya yi sanyi, tsoron Fulani Sadiya da kaidinta ya mamaye zuciyoyinsu. Ban da gyaɗa kai babu abin da suke yi, Fulani ta dube su ta ce.
"Za ku iya tafiya, zuwa an jima kowaccenku zan aiko mata da da turmin zani da kallabi. Idan Allah Ya kai mu gobe da safe, ku zo zan shirya liyafa tare da ku. Wannan somin taɓi ne daga irin manyan darajojin da zan ɗaga ku a gidan, matuƙar kuka cigaba da yi mini biyayya."
Duk da sun ji daɗi amma har lokacin zuƙatansu cike suke da fargaba da tashin hankali, cikin yaƙe suka russuna suka ce.
"Godiya muke ranki shi daɗe."
Umarnin fita ta ba su, bayan sun fita ta cigaba da zagayen ɗakin tana nazari sannan ta ce.
"Lokaci ya yi da zan yi amfani da ku, da zarar na gama cin moriyar ganga sai kuma na yasar da kwauronta."
Fulani Sadiya ta ƙarasa maganar tana sakin murmushin ƙeta.
Sarki Gambo
A hargitse Sarki Gambo ya miƙe tsaye cikin ƙaɗuwa da tashin hankali. Jikinsa har yawa yake idanunsa suka ƙanƙance, wata sharɓeɓiyar takobin da ke rataye a jikin bango ya zaro ya saita daidai wuyan Malami ya ce.
"Ka sanar da mu gaskiyar abin da kuka faɗa, idan ba haka ba za mu datse kanku."
A madadin Malami ya razana, sai ya saki murmushi ya ce.
"Ba za ka iya kashe ni ba Sarki Gambo koda kuwa a sume nake, kai ko ina gargarar mutuwa na fi ƙarfinka!"
Kalaman Malami suka ƙara harzuƙa Sarki Gambo, da sauri ya wurgar da takobin ya cakumi wuyan Malami ya shaƙe ya ce.
"Kada ku sake furta munanan kalamai akan jininmu, kun yi sa'a kune Malami. Da mun rantse da ubangiji haske sai mun azabatar da ku."
Duk da jikin Malami yana rawa irin na tsufa, amma hakan bai hana shi tattara ƙarfinsa ya hankaɗe Sarki Gambo ba. Ya furzar da iska mai zafi sannan ya ce.
"Da za ka ajiye zafin ranka a gefe, da na taimaka maka har ka samu ka ga hasken da zai haska maka hanya. Idan kuma kana tunanin hanyar da ka bi ita ce mafita, ga fili nan ga doki sukuwa kawai ya rage maka." Jikin Sarki Gambo ya yi sanyi, don haka ya zauna daɓar, kamar wanda aka zarewa laka a jiki. Sai da ya sauke ajiyar zuciya sannan ya ce.
"Malami zuciyarmu ta gagara aminta da mummunan labarin da kuka sanar da mu. Ta yaya aka haihu a ragaya? Me ya sa sai tagwayenmu? Wane ne ya aikata mana haka?"
"Tambayar da ni kaina nake wurga wa kaina kenan, sai dai har kawo yanzu da nake yi maka wannan maganar ban hangi wata alama, haske ko tauraron wanda ya aikata wannan mummunan sihirin ba."
Malami ya furta cikin damuwa, jin haka ya sa Sarki Gambo ya fashe da kuka. Cikin mamaki Malami ya girgiza kai, ya dafa kafaɗarsa ya ce.
"Haƙiƙa na haɗu da jajirtattun sarakuna, na yi mu'amala da sadaukai kuma jaruman mazaje. Amma ban taɓa cin karo da ingarman namiji mai dakakkiyar zuciya kamar kai ba Sarki Gambo, tabbas wannan hawayen naka na tabbata ba zai tashi a banza ba. Don na tabbata ƙashin gwiwar kura har abada ya gagari fiƙar gawurtattun karnuka."
Lokaci ɗaya Sarki Gambo ya goge hawayen idanunsa, ya dubi malami cikin cin alwashi, zafin zuciya da kalaman ɗaukar fansa ya ce.
"Mun yi rantsu da fatalwar iyayenmu, mun yi rantsuwa da abar bauta tsumbutuwa. Mun rantse da abar bautar da kakannin kakaninmu suka mutu a wurin bautarsu, haka kuma mun yi rantse da duk wani kaifin tsini da rashin imaninmu. Duk wanda ya aikata mana wannan mummunan al'amarin, sai mun azabtar da ruhinsa azaba mai raɗaɗi. Sai mum shayar da shi ruwan dalmar da har a ƙare danginsu za su dawwama a ƙarƙashin uƙubarmu. Malami!"
Ya kira sunan Malami da wata irin murya, yadda idanun Sarki Gambo suka kaɗa jajir ya sa tsoro ya ɗarsu a zuciyar Malami, don bai taɓa ganin mummunan yanayin haka a tatare da shi ba. Jiki a sanyaye Malami ya amsa, Sarki Gambo ya cigaba da ce.
"Ko numfashi da arzkinmu za su ƙare, ko bayi da sarautarmu za su ƙare ko lafiya da jininmu duka mutanen yankin nan zai ƙare, mun rantse da hasken rana sai mun ɗauki mummuna mataki a kan duk wani mahaluki da yake da saka hannu a wannan mummunan al'amarin."
Malami ya dafa hannunsa ya ce, "Ina tare da kai ɗari bisa ɗari sadaukin sadaukai, ni mai haska maka kowacce hanya ce da za ta bayyana gaskiya. Musamman da ya kasance waɗannan yara su kaɗai za ka iya mallaka har ƙarshen rayuwarka..."
"Mene ne mafita malami? Kuma ta ina za mu fara?"
Sarki Gambo ya katse shi, wani kan ƙwarangwal Malami ya ɗauka ya rubuta wata aya da alƙalami da tawada a tsakiyar kansa. Sai ya kafe shi a kan allon farin ƙarfe, ya hura masa wuta yana kiran waɗansu sunayen aljanu. Ya jima yana abu ɗaya sannan ya ɗago fuskarsa da ta haɗa gumi sharkaf ya ce.
"Na hango mafita guda biyu, wacce idan muka bi su za mu samu sukunin kamo bakin zaren."
Tsoho Sulaimanu
Kamar yadda ya kasance duk sati a kan buɗe ɗakin da tsoho Sulaimanu, shi da Kursum suke rayuwa ake ba su ruwa haka a wannan ranar ma ta kasance. Sai a gabannin wannan ranakun ba su dalilin da ya sa ake kawo musu abinci akai-akai ba, hakan ne ya rage musu raɗaɗin zaman ƙuncin da suke ciki.
Kamar yadda yake a bisa al'adarta, a yanzun ma tana zaune tana rubuce-rubuce a jikin bango duk da ba ta iya tantance abin da take rubutawa a kuma daidai wurin da take rubutawa saboda tsananin duhu. A wannan ranar tsoho Salaimanu ya ci alawashin sake tunkararta da tambayoyin da ya sha jifanta da su, duk da a duk lokacin da ya yi mata ba sa wanyewa lafiya ƙalau shi da ita. Saboda idan ya yi mata tambayoyin haka za ta dinga kartar jikinsa cikin huci da ɓacin rai, har sai da ya yi tunanin ko ba ta magana saboda tun da ya shiga ɗakin bai taɓa jin kalma ɗaya daga bakinta ta amsa masa ba. Ta yadda ya tabbatar da tana magana, da yake yawan jin tana zikiri da istigifari. Sai kuma idan ta tashi sallah ya ji tana karatun sallah, wani lokacin kuma haka za ta wuni tana kuka ko ta wuni tana karatun alƙur'ani.
Tsoho Sulaimanu a daidai wannan gaɓar shi kansa ya saddaƙar da rayuwarsa za ta ƙare a cikin wannan baƙin ɗakin, domin tun bai ɗauki shekaru a gidan ba Sarki Gambo ya sha turowa a tafi da shi, domin ya bada kai bori ya hau. Amma a kullum aka kai shi furucin da yake faɗa shi yake sake maimaitawa, don haka Sarki Gambo ya ce a ajiye shi su cigaba da zama da Kursum har ƙarshen rayuwarsu.
"A tsawon shekara sama da goma da muka shafe tare a ɗakin nan, ya kamata a ce zuwa yanzu kin watsar da duk wani kallo da zargi da kike yi mini Kursum. Na sha faɗa miki ni ba na daga cikin mutanen Sarki Gambo, amma a kullum gani kike lulluɓe kura nake yi miki da fatar akuya. Wallahi-tallahi ni ma zalincinsa ne ya kawo ni wurin nan, saboda na cika burin marigayi Najibullahi."
Tsoho Sulaimanu ya ƙarasa maganar cikin kuka, ƙashin da take rubutun a jikin bango ta wurgar. A tsorace tsoho Sulaimanu ya ja da baya, don ya yi tsammaninsa a wannan karon ma za ta fara yagar namansa kamar yadda ta saba yi a baya. Ya ji sautin tafiyarta ta ƙaraso wurinsa, cikin dakusasshiyar muryarta mai haɗe da tsufa ya ji ta ce.
"Wane ne kai? Me ya sa ka damu da sanin dalilin zuwana? Mene ne dalilinka na ambatar sunan Najibullah? Ya aka yi ka san shi? Yaushe Najibullah ya mutu?"
Da mamaki tsoho Sulaimau yake bin wurin da yake jin sautinta, cikin tsananin farin ciki ya gyara zama domin ya ba ta amsa, don ya fahimci haƙarsa za ta cimma ruwa ba har ya san wace ce ita.
*Ummou Aslam Bint Adam*
07062062624
[29/11, 23:41] Ameerah Adam: *KUNDI UKU*
©AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye.
Tsokaci: Daga Masarautu, Sarakuna da sunayen yanki duka ƙirƙira ne. Idan ya yi daidai da labarin wani/wata arashi ne.
SHAFI NA SHA ƊAYA
Masarautar Zulwara
Bayan fitar Jakadiya da ta isar masa da saƙon mutuwar jaririn Fulani Hauwa Kulu Sarki Dikko shiru ya yi yana nazari, ta wani fannin zuciyarsa ta fara ɗaci game da takunkumin da boka Tsumbur ya saka masa.
"Ba ni zan ba ka amsar wurin da Kursum tare da ɗan'uwana Sulaimanu suke ba, amsoshinka suna cikin littafin 'Ruwa A Wuta' wanda aka binne tare da gawar Sarauniya Humaira a cikin tsohuwar Fada."
Sarki Dikko ya tuna kalaman da tsoho Babagana ya furta masa, furzar da iska mai zafi ya yi a fili ya ce.
"Dole za mu ziyarci kabarin sarauniya Humaira, domin ranar biyan buƙata rai a ba a bakin komai yake ba."
Yana gama faɗar haka ya buɗe wata ƙatuwar randar ruwa, hannu ya zira ya ɗauko kuba a ƙasan ruwan. Har ya nufi ƙofar fita sai kuma ya yi turus, sakamakon tuna wasu sharuɗɗa shiga cikin kabarin nata. Shiru ya sake yi cikin damuwa, kamar wanda ya tuna wani abu sai kuma ya fita da sauri. Yana zuwa harabar sashensa ya sallami masu tsaron ƙofarsa, ko kaɗan ba ya son aikata abin da idanun masarauta za su hau kansa, duk da ya san yana da ikon aikata fiye da haka. Amma sanin kansa ne, haramun ne kuma kuskure ne sannan zunubi ne halartar kabarin sarauniya Humaira tun shekarun baya. Sakamakon camfin da suka yi a kan waɗansu miyagun al'amura da suke faruwa da su, tun yana ƙarami baya mantawa ya ji an ce mahaifin kakansa ya zartar da dokar hana shiga cikin kabarin ana ajiye kayan tsafe-tsafe, ko kuma ɗiban waɗansu kayan tarihi a fita da shi domin biyan buƙata.
Kabarin Sarauniya Humaira, tsohon kabari ne da ya ɗauki tsahon shekaru masu yawa. Asali an ce adaidai wurin da gawarta take, a nan ne aka gudanar da wani mummunan cin amana tsakanin wasu sarakuna da suka gabata har aka hallaka ta. Wasu kuma suka ce a wurin ne aka gudanar da yaƙin Durr, wanda shi ne silar tsaga masarautu ukun da su sarki Gambo suke jagoranta. Don a wani labarin kunne ya girmi kaka, an ce a da masarauta ɗaya ce a cikin daular. Wani hargitsi da ya gifta ne ya kawo musababbin rabuwarta gida uku, har ya zama akwai wata daɗaɗɗiyar gaba a tsakanin gidaje ukun.
Sai dai kuma a labari mafi shahara, wanda har su Sarki Dikko suka samu labari kuma suka yi na'am da shi. An ce Sarauniya Humaira wata jajirtacciyar sarauniya aka yi a lokacin, mara tsoro ga dakiya da ƙarfin zuciya. Uwa-uba baiwar da aka ce tana da ita, domin duk abin da ya shige maka duhu, ko dai game da sha'anin kasuwanci, aure ko mu'amalar abin da ya shafi mulki. Matuƙar ka kai kukanka wurinta, da zarar ta ɗebi wani ruwan ta zuba a wata 'yar ƙorama da ke tsakiyar fadarta. Nan take za ta samu ilimin duk abin da ya shige maka duhu, kuma ta samu sani a game da tarin tambayoyin da aka yi mata.
Asalin wannan ƙoramar an ce ta hada tushe