Author : Ameera Adam Category : Read Hausa Novels
ADAM
𝙒𝙝𝙖𝙩𝙨𝘼𝙥𝙥 𝙉𝙤: 09040772027
_Thank you❤_
Ummou Aslam Bint Adam🌚
07062062624
[30/11, 20:57] Ameerah Adam: *KUNDI UKU*
©AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye.
Tsokaci: Daga Masarautu, Sarakuna da sunayen yanki duka ƙirƙira ne. Idan ya yi daidai da labarin wani/wata arashi ne.
SHAFI NA SHA BIYU
Tamkar raƙuma da akala haka Indo ta cigaba da bin Uwar bayi, sai da suka wuce soro uku ganin tafiyar ta fara nisa ya sa Indo ta ce.
"Don Allah ina za mu je?"
A yatsine Uwar bayi ta waigo ta dube ta, sheƙeƙe ta ce.
"Idan mun je za ki gani."
Haɗiye yawu Indo ta yi cike da damuwa, ta sauke ajiyar zuciya tana kalle-kallen yanayin tsarin gidan sarauta, da zane-zanen da aka ƙawata na fari da ja ba ƙaramin birge ta ya yi ba.
Wurin wani babban fili suka ɓulla, daga nesa ta hangi dandazon maza a tsaitsaye waɗanda take tsammanin Dogarai ne. A ɗan tsorace Indo ta ƙarasa saboda yadda ƙirjinta yake dakan lugude.
"Sarkin tsaro shin wannan ce yarinyar da kuke magana a kai?"
Ƙuri suka yi wa Indo suna nazari, saboda lokacin da ta same su da dare hasken farin wata ne.
"Ƙwarai ita ce, ke zo nan!"
Nan take Indo ta sake rungume Batul, ta fara takawa a tsorace. A tsammaninta saukar duka za ta ji a jikinta, amma ga mamakinta sai ta ji ya sunkuyo daidai fuskarta ya yi ƙasa da murya ya ce.
"Yarinya ki faɗa mana tsakaninki da Allah, me kika yi wa ɗan'uwanmu har muka tsinci gawarsa a tsakiyar dajin da muka bi shi."
Ajiyar zuciya Indo ta sake saukewa ta ce.
"Wallahi-tallahi ban yi masa komai ba, tsakanina da Allah nake wannan maganar."
Indo ta ƙarasa maganar tana goge hawayenta, shiru suka yi suna nazari sai ɗaya daga ciki ya ce.
"Ka san fa dama hanyar ɗorawar can ba ta da kyau, ko dai wani abin ya takawa mazauna wurin suka huce fushinsu a kansa?"
Cike da ɗaurewar kai Dogarin ya ɗago yana dafe kai cikin jimami ya ce, "Na shiga ruɗani wallahi, to amma fa tun kafin ya shiga dajin ya fara surutai kamar mai magana da iskokai."
Duka shiru suka yi cikin jimami, Uwar bayi ta ja bawan da ya gama magana suka ɗan yi gaba. Sai da ta tabbatar da ta yi nesa da su ta ce.
"Bala an ya ba za ku bar wannan maganar ba, don idan Mai martaba ya ji wannan zancan ina ganin kamar da matsala."
Cikin sauri Dogari Bala ya riƙe baki ya ce, "Uwar bayi me ya kai mu aikata wannan ɗanyen aikin? Ni fa gabaɗaya tsoron yarinyar nake yi, don wallahi ganin idona Mamman yana gama dukanta ya fara wannan haukar, ai kawai ki ja ta ku koma ciki."
Jinjina kai Uwar bayi ta yi ta ce, "To shi kenan, mu kuma da muke tare da ita Allah Ya kiyaye mu." Kusan lokaci ɗaya suka saki dariya.
Indo tana zaune cikin zullumi Uwar bayi ta riƙo hannunta tana washe baki kamar ba ita ba ta ce, "Yarinya mu je kin ji, wai ya sunanki ne?" Da yake har lokacin Indo a tsorace take, jiki a sanyaye ta ce.
"Sunana Indo."
Cikin bugar ciki Uwar bayi ta ce, "Indo tsohuwa, wai kuwa tare da mijinki aka kawo ki gidan nan?"
Ras! Gaban Indo ya faɗi, cikin in'ina ta ce.
"Na'am... ai... a'a... ba tare muke ba, mijina ya mutu tun kwanaki."
Ƙuri Uwar bayi ta yi mata tana son gano wani abu daga kalaman Indo, sai ta ɗan kalle ta daga sama zuwa ƙasa ta ce.
"Amma kuma na ga garau kike tafiyarki jiya-jiya da haihuwa, kodayake ai kowacce mace da yanayin jikinta." Ita dai Indo shiru ta yi, a haka har suka ƙarasa sashensu na bayi. Indo tana shiga ta ga mutane suna bin ta da kallo, duk sai ta ƙara tsarguwa. Hakan ya sa ta raɓe can a gefe, zamanta babu jimawa Batul ta fara kukan yunwa. Da sauri Zuwaira ta matso kusa da ita ta ce, "Kawo ta na bata..."
"A'a zan nemo mata nonon akuya, saboda na ga jiya ta ji daɗinsa sosai."
Indo ta katse ta, tana miƙewa tsaye. Murmushi Zuwaira ta yi, Zinaru da ke gefe ta saki guntun tsaki ta ce.
"Ke dai wahala ta gan ki wallahi Indo, amma a juri zuwa rafi watarana tulun zai fashe."
Duka mutanen ɗakin kallon Zinaru suka yi, jikin Indo a sanyaye ta fita. Sai dai Indo tana fita ƙananan maganganu suka fara tashi, wasu suka shiga kare Indo yayin da wasu suka fara tsegumi a kan ƙanƙantar Indo a matsayinta na mahaifiyar Batul.
A wannan lokacin babu wanda ya hana Indo tatsar nonon akuyar, don haka ta cika cikin Batul taf sannan ta taso ta dawo sashen bayi. Duk jin ta take babu daɗi, saboda ta lura zuwa wannan lokacin Batul a gajiye take tuɓus, don har kawo lokacin ko ruwan zafi jikinta bai gani ba. Hatta sutura babu a jikinta sai zanin da mahaifiyarta Karima ta naɗe ta da shi. Tana komawa ta tarar da an kai musu abinci, kallon miyar kukar ta yi sau ɗaya ta ɗauke kanta saboda yadda ta ji zuciyarta tana tashi. Amma jin yunwa za ta illatata ya sa ta matsa kusa da su, har za ta saka hannu Zuwaira ta ce.
"Indo ga abincinki na ajiye miki, cikin jego ne da ke bai kamata ki shiga cikinmu ki ci abinci ba." Cikin jin daɗi Indo ta yi mata murmushi haɗe da godiya, suna cikin cin abinci uwar bayi ta ƙarasa kansu daga bakin ƙofa ta ce idan sun gama su fito, kowacce za a bata aikin da za ta dinga gudanarwa. Amsawa suka yi, sai da suka gama cin abinci, sannan Zuwaira ta dubi Indo ta ce.
"Akwai ruwan da na roƙi alfarma a wurin uwar tuwo na ɗora, idan kin gama zan yi mata wanka." Gyaɗa kai Indo ta yi, sai dai kuma har kawo lokacin zuciyarta ba ta gama nutsuwa da Zuwaira ba. Cikin ƙanƙanin lokaci bayin ɗakin duka suka watse, Zuwaira ta ɗauko ruwa ta surka a wata ƙatuwar kwarya sannan ta karɓi Batul ta fara yi mata wanka. Shiru Indo ta yi tana kallon yadda ake wankan, don dama ko kaɗan ba ta san yadda ake yi ba.
Sai da mutanen ɗakin gabaɗaya suka fita sannan Zuwaira ta dubi Indo ta ce.
"Indo wace ce ke?"
Da mamaki Indo ta yamutsa fuska ta ce, "Ni kuma? Me kika gani?"
Zuwaira ta gyara riƙon Batul ta naɗe ta da ɗankwalinta ta ce.
"Batul ba kowacce irin yarinya ba ce, haƙiƙa wannan yarinyar Suryu ce."
"Suryu! Me hakan yake nufi?"
Indo ta tambaya, Zuwaira ta sake ƙura wa Batul ido, ita ma Indo kallon Batul ta yi lokaci ɗaya suka ga idonta ya fara fitar da farin hayaƙi. Cikin sauri Indo ta ja baya ta ce, "Mene ne a idonta?"
Zuwaira ta sake jinjina kai ta ce, "Wallahi yarinyar nan Suryu ce, ita ce wacce tsoho Baushe ya sanar da ni."
Sake kallonta Indo ta yi, Zuwaira ta gyaɗa kai ta cigaba da cewa.
"Akwai manyan cutukan da suke addabar rayuwata, lokacin da na je wurin Baushe sai ya ce mini laƙanin makarin lalurar jikina sai na shayar da jaririya Suryu, wacce ta fito daga wani irin tsatso mai rikitarwa." Zaro ido Indo ta yi, Zuwaira ta cigaba da cewa.
"Sai dai ina jin tsoro, tun lokacin da na ga alamunta sun bayyana."
"Tsoro kuma? Tsoron me?"
Indo ta tambaya, Zuwaira ta sauya fuska cikin damuwa, sai ta gyaɗa mata kai ta cigaba da cewa.
Sarki Giɗaɗo
Tamkar wanda ruwa ya shanye haka Sarki Giɗaɗo ya yi tsuru yana sauraron bokanya Kande, sai da ya ji ta kammala jawabinta sannan ya ce.
"Ki gafarce ni yake mai cetona..."
"Yesu Almasihu shi ne mai ceto ba ni ba."
Bokanya kande ta katse shi a harzuƙe. Russunar da kai ƙasa ya yi ya ce.
"Tuba nake yi bisa aikata saɓo."
Gyaɗa masa kai ta yi, Sarki Giɗaɗo ya yi godiya sannan ya cigaba da cewa.
"Ki yi mini afuwa yake hatsabibiya bokanya Kande, haƙiƙa ina cike da ruɗu tare da tashin hankalin jin matata Karima tana raye."
"Wurin nan ba wurin ja'inja ba ne Sarki Giɗaɗo, idan har kuna tantama game da abin da muka faɗa, kuna iya zuwa ku duba kabarinta domin ku tabbatar da abin da muke faɗa."
Bokanya Kande ta furta fuska a haɗe, russunar da kai ƙasa ya yi alamar ban haƙuri, Sarki Giɗaɗo ya ce.
"Yanzu ta ina za mu fara wannan aikin yake Bokanya Kande?"
"Ba ma faɗar mafitarmu kai tsaye gabaɗaya, za mu sanar da ku ta cikin baccinku yau da dare idan kun kwanta. Duk abin da kuka gani ko muka bada umarni to hakan za ku zartar da shi, amma kada ku manta muna sake jan hankalinku da ku binciko Karima a duk inda take ko jininta, domin kuwa ita ce maganin matsalarku. Ragowar jawabin zan yi muku a cikin mafarki, kuna iya tashi ku ba mu wuri. Yesu Mai ceto zai yi alfahari da kai, matuƙar ka tabbata a kan addinin gaskiya ba na ɓata ba."
Jiki yana rawa Sarki Giɗaɗo ya russuna ya ce, "Ina godiya bokanya, sai dai ba a sanar da ni tukwicin da zan bayar ba."
"Tukuwinmu shi ma zai zo a cikin baccinka, domin daga jikinka za mu ɗauki abin da muke muradi."
A razane Sarki Giɗaɗo ya ɗago jin furucin Bokanya Kande ya ce, " A jikinmu kuma?"
"Kada wannan ya razana ka, ba za mu cutar da kai ba. Za mu ɗebi gumin jikinka, tare da duk wani gashi na jikinka, idan ka kuskure wa aljani Ɓugun, kai da sake samun gashi a jikinka har abada. Wannan ita ce magana ta ƙarshe da za mu faɗa." Daga haka sai ya ga Bokanya Kande ta miƙe ta bi ta jikin tafkeken cross ɗin da ke fuskantarsu, ajiyar zuciya ya sauke sannan ya miƙe ya fita harabar wurin da ya bar Galadima. Yana zuwa wurin Galadima ba su ɓata lokaci ba, sakamakon kalaman tsubbun da Galadima ya furta wanda bokanya Kande ta koya masa.
Sarki Giɗaɗo ya jima yana zarya a ɗakinsa, haka kawai ya ji soyayyar Zannira tana sake addabar zuciyarsa, ta yadda ba zai iya jure rashinta ba. Musamman da ya tuna tana ɗauke ciki a jikinta.
"Ka tabbatar da ka nemo duk wani jariri da aka haifa a cikin masarautarka, ka shafa masa wannan jan garin maganin nan. Matuƙar ka ga jini ya fito daga al'aurarsu mace ko namiji, to tabbas jinin Karima ne."
Sarki Giɗaɗo ya tuna kalaman bokanya Kande, cikin sauri ya miƙe ya nufi ƙofa. Har zai fita, sai kuma ya tsaya cak. Tunowa ya yi da Kabarin Karima, don haka ya yi saurin canja hanya ta ƙofar baya. Ya nufi ɗakin kushewa, babban ɗakin da ake binne duk wani ahali da ya dangancin masarautar. Mukulli ya saka ya buɗe, ya shiga ɗakin cikin sanyin jiki. Sai dai rana ta farko kenan da ya ji gabansa yana tsanannin bugawa, a bakin ƙaton kabarin Karima ya tsaya. Har ya kai hannu, sai kuma ya yi saurin komawa ya tura ƙofar ya rufe. Tamkar ba Sarki Giɗaɗo ba, haka ya zage ya dinga haƙar ƙasar kabarin har sai da ya yashe ta tas. Yana kwashe itacan kan kabarin ya cigaba da dubawa, sai dai sama da ƙasa ya neme ta ba tare da ya ganta ba. Hatta ƙashin da ya ji labarin an ce yana saura a jikin mutum, da likkafani duk bai gani ba. Wata ƙaramar fata ya gani, wacce aka yi rubutu a jikinta. Jikinsa yana rawa ya yi saurin kai hannu ya ɗauka.
"Ka yi kuskure da kake tsammanin za ka hallaka Karima. Sarki Giɗaɗo abin da ka guda shi ne zai faru a daidai gaɓar da ba ka yi tsammani ba, lokaci zai zo da zan yi ajiya mai muhimmanci a cikin fadarka. Sai dai ka sani, yadda ka dakushe mini farincikina, har bada ka yi bankwana da shi. Domin kuwa yadda ka zartar da miyagun al'amura a kaina da mahaifina tsawon kwana arba'in, daga lokacin da na mace a idanun al'umma, kowacce kwana arba'in za ta zame maka mafi masifa da uƙuba a cikin rayuwarka. Ragowar amsoshin da kake buƙata, za ka same su daga bakina a lokacin da ka fahimci Karima ba ta mutu ba. Sai dai ba za ka fahimci hakan ba, har sai lokaci ya ƙure maka. Ba za ka iya ja da ni ba Sarki Giɗaɗo, don a yanzu ba ka da tabbacin mutum ce ko wani jinsin daban."
Sarki Giɗaɗo yana gama karantawa ya yi wurgi da takardar, ko ƙasar kabarin bai mayar ba ya fita daga ɗakin a fusace ya nufi ɗakinsa. A lokacin dare ya tsala sosai, don haka ya haƙurewa washegari gudun kada Zannira ta fahimci wani abin ko ta tada hankalinta. Sai dai yadda ya ga rana, haka ya ƙarasa ganin darensa.
Sai da gari ya waye garau, sannan Sarki Giɗaɗo ya sa aka kira masa Jakadiya, uwar bayi da mai soron baƙi. Kallon fuskarsa kaɗai suka yi, suka fahimci ransa a matuƙar ɓace yake.
"Mun tara ku ne ba don dogon bayani ba, sai don mu sanar da ku. Muna son ku kawo mana duk wani jariri da yake rayuwa a cikin masarautar nan, muna nufin tun daga ɗan shekara biyu zuwa jaririn da aka haifa yanzu. Idan har kuka yi gangancin saɓa mana, mun yi rantsuwa da sarkin da ya busa mana numfashi sai mun azabtar da ruhinku."
Jin kalaman Sarki Giɗaɗo ya sa Uwar bayi ta yi saurin ɗaga hannu jiki yana rawa ta ce, "Allah Ya taimake ka akwai wacce ta haihu a masarautar nan jiya da dare, ɗaya daga cikin bayin da aka kawo ce."
Jin kalaman Uwar bayi ya sa Sarki Giɗaɗo ya miƙe zumbur, cikin kausasshiyar murya ya ce.
"A gaggauta kawo mana ita yanzun nan."
Masarautar Kajjura
A hargitse Baiwa Sakina ta fita daga sashen Fulani Sadiya, duk wanda ya ga irin tafiyar da take yi sai ya fahimci ba ta cikin nutsuwarta. A haka ta ƙarasa sashensu na bayi, tana shiga ɗaki ta hangi Ridwan a zaune yana biya karatunsa na allo. A fili ta sauke ajiyar zuciya har sai da ya waigo ya kalle ta, murmushi ya sakar mata ta ƙarasa kusa da shi ta zauna ta ce.
"Ridwan karatu kake yi?"
Gyaɗa mata kai ya yi yana murmushi, ta zuba masa ido tana kallon yadda tsantsar kyawun yaron yake sake bayyana. Dara-daran idanunsa ta kalla, sai ta ga kamar ƙwayar idonsa ta sauya zuwa irin ta maciji, gabanta ne ya faɗi amma sai ta kawar da damuwar abin da ta gani ta ce.
"Kada ka dinga fita waje ka ji Ridwan."
Riƙe bakinsa ya yi, yana yi mata alamar ya aikata wani laifin. Ɗan zaro ido ta yi, tun ba ta tambaye shi ba ya ce.
"Inna ban daɗe da dawowa masarautar nan ba, wai dama Inna ba ke kika haife ni ba?"
Da sauri Sakina ta zaro ido waje bakinta yana rawa ta ce, "A ina ka ji? Kuma ina ka je? Ridwan kana son ka saka mu a matsala ne?"
Kamar ba laifi ya yi ba ya saki murmushi ya ce.
"Allah ba ke ba ce, an ce mini mamana tana gidan nan."
Sai kuma ya yi fuskar tausayi ya ce, "To ko tana ina oho? Amma dai an ce min wai tana sona, kuma babana ma kafin a kashe shi yana sona."
Sakina da ƙirjinta yake bugawa ta rasa mafita sai kawai ta fashe da kuka, ganin tana kuka sai jikinsa ya yi sanyi. Ya matsa kusa da ita ya goge mata hawaye, riƙe hannunsa ta yi ta ce.
"Don Allah ka daina irin wannan maganar Ridwan, za ka saka mu a matsala. Ni da na ga yau kana cikin farinciki na ɗauka ma abokan wasa ka samu."
Wata dariyar ya sake yi, ya ajiye allonsa a gefe sannan ya ce.
"Inna ni ba na wasa da kowa a gidan nan, sai wasu mutane masu muhimmanci." Za ta tambaye shi su waye, sai ta ji ya cigaba da cewa.
"Kin san me ya sa yau nake cikin farinciki?"
Girgiza masa kai ta yi, ya miƙe tsaye yana 'yan tsalle-tsalle ya ce.
"Na ji daɗi yau Batul za ta mutu, ni dama ba na ƙaunarta."
A hargitse Sakina ta sake kallonsa, sai gani ta yi ya sake washe mata baki cikin murna.
Book 1 yana gab da ƙarewa, ga masu sha'awar karanta book 2&3 za su iya turo kuɗinsu.
700 ta Acc Aisha Adam 3090957579 Firstbank shaidar biya ta wannan lamabar 07062062624 idan ya kammala zuwa document 1k ne.
Ummou Aslam Bint Adam🌚
07062062624
07062062624
[30/11, 21:05] Ameerah Adam: *KUNDI UKU*
©AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye.
Tsokaci: Daga Masarautu, Sarakuna da sunayen yanki duka ƙirƙira ne. Idan ya yi daidai da labarin wani/wata arashi ne.
SHAFI NA SHA UKU
Sarki Gambo
Ƙuri Sarki Gambo ya yi wa Malami yana sauraronsa, kamar wanda yake nazari sai ya ɗago ya