Kundi Uku Book Compelet By Ameera Adam

Author :  Ameera Adam Category :  Read Hausa Novels

Chapter   3 / 14

6K to 9K   out of 40.4K words

na sani. Ni da ke muna amfani da Gambo domin mu cikar muradinmu ne, da zarar mun kai gaɓar da muke muradi za mu yasar da ƙwallon mangoro mu huta da ƙuda."

A fili Fulani Sadiya ta sauke gwauruwar ajiyar zuciya, sannan ta ɗora da cewa.
"Tun da haka ne, ina son haihuwa da Takawa. Ko babu komai zan bar magaji a masarautar Kajjura, masarautar da babu mai fahimtar gabanta da bayan har sai wanda ya gane sirrinta."

"Ba za ki haihu a masarautar nan ba."
Malami ya katse ta, ya cigaba da cewa.
"Haka kuma har yanzu ba ki san sirrin masarautar nan ba."

"Me ya sa ba zan haihu ba? Kuma wanne sirri ne ya rage da ban gama saninsa ba?"
Fulani Sadiya ta furta cikin damuwa, Malami ya saki murmushi ya ce.

"Saboda mahaifarki tana soke a dutsen Jaddum, haka kuma sirrin Masarautar nan ba za ki taɓa gane shi ba."
Malami ya furta yana buɗe ƙur'anin da ke gefensa, har za ta sake yin magana. Ya ɗaga mata hannu yana cewa.

"A yanzu ina da uzuri Fulani, kina iya dawowa bayan wani lokaci. Domin a daren nan zan sayi rauhanai biyar da za su yi mini wani aiki."

Sam ba haka Fulani Sadiya ta so ba, tana tafiya Malami ya saki murmushin da shi kaɗai ya san manufarsa. Sai da ya tabbatar da ta yi nisa, sannan ya ɗebi ƙasar sawun ƙafarta. Ya haɗe ta a cikin fatar farin maciji, sannan ya shiga bukkarsa ya ɗora a kan ƙaton shurin da ke tsakiyar gidajen tururwan da ke zagaye da shi.

SARKI GAMBO

Lokacin da Fulani Sadiya ta shiga ɗakinta, ta jima tana kaiwa da kawowa. Kamar wacce aka tsikara, sai ta ƙwala wa baiwarta kira. Cikin girmamawa ta zube ƙasa tana faɗin.

"Hutawarki lafiya uwar gijiyata, Allah Ya ja zamanin giwar sarki. Da yardar Allah Yarima yana bisa hanya, Aljanna mai masoya da yawa. Sikari ba ki yi farin banza..."

"A sanar da Jakadiya ta nemar mini izinin ganin mai martaba."
Fulani Sadiya ta furta a daƙile, jin haka ya sa Baiwa Indo ta sake zubewa ƙasa ta ce.
"An gama ranki shi daɗe, hutawarki lafjya mai farar zuciya."
Miƙewa ta yi ta fita kai tsaye ta sanar wa da Jakadiya saƙon Fulani Sadiya, babu jimawa Jakadiya ta nemi izinin shiga ɗakin Fulani Sadiya. A gaggauce ta amsa mata, don a ɗokance take da son ganinsa a wannan lokacin.

"Allah Ya taimake ki, Allah Ya tsare gabanki da bayanki. Takawa bai amsa goron gayyatarki ba, a yi mini afuwa ranki daɗe." Jakadiya ta furta tana sunne kai ƙasa, rai a matuƙar ɓace Fulani Sadiya ta ce.
"Saboda me Takawa zai yi mini haka?"

Jakadiya ta waiga hagu da dama, sannan ta sunne kai ƙasa ta ce.
"Allah Ya taimake ki, ki gafarce ni da abin da zan faɗa."
Kallon tsaf Fulani ta yi mata ta ce, "Tafi kanki tsaye."

Jakadiya ta sake yin ƙasa da murya ta ce.
"Allah Ya taimake ki wannan maganar ba za ta faɗu ba, sai dai na raɗa miki a kunnenki."
Kamar Fulani ta dakatar da ita, sai ta gyaɗa mata kai. Jikin Jakadiya har rawa yake yi, ta matsa saitin kunnen Fulani Sadiya ta fara yi mata raɗa a kunne. Ƙirjinta ne ya buga da ƙarfi, amma sai ta kawar da damuwar fuskarta ta ce.
"Jakadiya an jima zan aiko mini da kyautar alkaki, domin ba zan bar wannan albishir ɗin ya tashi a banza ba."
Jikin Jakadiya har rawa yake yi ta zube a ƙasa ta ce.
"Godiya nake ranki shi daɗe, an gaida farar mace alkyabbar mata. Allah Ya taimake ki ina neman alfarmar da a taimaka a rufa mini asiri."
Fulani Sadiya ta saki murmushi ta ce, "Kada wannan ya dame ki Jakadiya, ina mai yi miki albashir da yanzu ma muka fara." Jakadiya ta sake zubewa a ƙasa tana godiya sannan ta fita.

TSOHO SULAIMANU

Lokacin da sarkin ƙofa ya tasa ƙeyar tsoho Sulaimau tafiya mai nisa suka yi a cikin masarautar, sai da suka je bakin wata katanga sannan ya damƙa shi a hannun Sarkin horo da ke tsaye fuska babu ɗigon fara'a. Kallo ɗaya tsoho Sulaimu ya yi masa, ya fahimci rashin imani da ƙeƙashewar zuciya ya samu gurbin zama a zuciyarsa.
"Mai martaba ya bayar da umarnin a killace shi a kurkusun ƙasa, a tabbatar da a saka shi a ɗakin Kursum."
Sarkin ƙofa ya furta, sannan ya damƙa shi a hannun Sarkin horo. Kai kawai ya gyaɗa masa, ya dubi tsoho Sulaimanu da jajayen idanunsa masu kama da sabon borkono. Wanda suka sa cikinsa ya kaɗa saboda tashin hankali, da ƙarfi ya hankaɗa tsoho Sulaimanu. Suka bi ta wata siriiriryar hanya, sannan suka ɓulla gaban wata ƙatuwar ƙofa wacce aka sassaƙa ta da farin ƙarfe. Ilahirin saman wurin a zagaye yake da ƙarfe, sai wasu dogarai da ya ci karo da su fuska a murtuke babu alamar fara'a. A nan ma tafiya suka yi mai ɗan nisa, sannan suka ƙarasa wani wuri mai duhun gaske, harshen wuta ya ga an miƙe wa Sarkin horo. Ya karɓi itacen yana haska musu, a nan tsoho Sulaimanu ya ci karo da waɗansu ƙananun ɗakuna. Numfarfashin mutane ya dinga ji sama-sama, wasu kuma ya ji suna roƙon a taimaka a ba su ruwa.
Tsoro ne ya mamaye shi, har yana jin ƙafafuwansa sun yi wani irin sanyi kamar ba na shi ba. Wata mai tsohon ciki ya hango a zaune, cikin galabaita tana cewa.

"Ku taimaka mini da abinci, yau ne ranar da za a ba ni na ci. Wayyo Allah cikina, ku taimaka mini da ruwa ko cikin tafin hannu ne."

Cikin tsawa ya ji Sarki horo ya ce.
"Idan kika sake magana, sai kin maimaita kwanakin karɓar abincinki kafin a ba ki ki ci."
Ba ita kaɗai ba, lokaci ɗaya tsoho Sulaimanu ya ji hatta mutanen da ke numfarfashi sun yi tsit kamar an yi ruwa an ɗauke. Jikinsa a sanyaye suka ƙarasa bakin wata ƙatuwar rijiya, wacce aka sassaƙa murfinta da dalmar baƙin ƙarfe.

Mukulli Sarkin horo ya saka ya buɗe, ya dubi tsoho Sulaimanu ya ce.
"Wuce mu je."
Cikin tsoro, firgici da tashin hankali tsoho Sulaimanu ya ce.
"Ina?"

Tass! Ya sauke masa mari a fuskarsa, nan take ya ji kunnensa ya yi dum! Kansa ya yi masa nauyi, juwa ta fara yunƙurun taɗe ƙafarsa. Bakinsa da hancinsa ne yake zubar da jini, don tun da ya zo duniya bai taɓa jin marin da ya gigita kwanyarsa kamar wannan ba.
"Mu je na ce!"
Sarkin horo ya sake buga masa tsawa, tun bai rufe baki ba tsoho Sulaimanu ya yi sauri zura ƙafarsa, sai a lokacin ya lura da marattakalar benen ciki. A haka Sarkin horo ya tasa ƙeyarsa har suka kai ƙarshen matattakalar benen, sai dai suna gama shiga ya ga tsananin duhun wurin har ya ninka na baya da suka baro. Ƙananun ɗakuna ne ƙuntatattu, gaban tsoho Sulaimanu yana bugawa bai yi aune ba ya ji Sarkin horo ya buɗe wani ɗaki ya hankaɗa shi ciki. Ji ya yi ya ci karo da abu mai gashi, nan take hankalinsa ya kai ƙololuwar tashi.

Harshen wutar ya ziro musu, sai a lokacin ya lura da hallitar mai zubin mutum kuma mace ce a gefensa. Sai dai gashin da ya lulluɓe kanta zuwa jikinta ya sake hautsina hanjin cikinsa. Cikin muryarsa marar daɗi ya ji Sarkin horo ya ce.
"Shawara ɗaya zan ba ka, idan har wani abu Mai martaba yake nema a wurinka, yana da kyau ka ba shi haɗin kai domin amfanar gobenka. Idan ba haka ba, sai ka fi Kursum lalacewa. Domin ita kai tsaye ɗakin horo aka fara kai ta, taurin kanta ne ya kawo ta zuwa ga wannan matsayin. Kai kuwa tashin farko ɗakin ƙasa Mai martaba ya ce a saka ka, na tabbata hukuncinka sai ya fi naka muni matuƙar ba ka bayar da kai bori ya hau ba."
Sarkin horo yana gama faɗa ya fice daga wurin, sannan ya rufe rijiyar da mukulli kamar yadda ya same ta da farko.

Wani irin tsoro ne ya mamaye zuciyar tsoho Sulaimanu, gabansa yana faɗuwa ya ce.
"Sannu malama kursum."
Shiru ya ji ta yi masa, bai daddara ba ya sake maimaitawa. Bai yi tsammani ba sai ji ya yi ta karce shi da farcenta, wanda hakan ne ya sa shi jin ɗumin da ya tabbatar masa da jini ne yake zuba. A ɗarare ya ja gefe, duk da ba ya iya ganin koda tafin hannunsa. Sai kawai ya fashe da kuka, sannan ya ɗaga hannuwa sama yana roƙon Ubangiji Ya kawo masa ɗauki.

SASHEN BAYI

Tun sassafe da gari ya waye kowacce Baiwa ta kama gabanta, domin gudanar da aikin da ya zame musu ta kamar sallar farilla. Ɗakin shiru babu kowa sai Baiwa Sakina da ke rungume da jaririn hannunta, kallon fuskarta yake ƙir kamar yana tantance surarta. Murmushi ta sakar masa, ta kai hannu ta lakuci kumatunsa ta ce.

"Allah Ya raya mini kai Ridwan, sai dai ina jimamin yadda za ka taso a ƙasƙantacciyar rayuwar bautar da muke kai." Kamar ya san me ta faɗa, sai ta ga hawaye yana zuba daga idonsa. Nan take gabanta ya faɗi, tana shirin sake magana Uwar bayi ta ɗaga labulen ɗakin cikin faɗa ta ce.

"Sakina kin san duk wani adalci da zan yi na yi miki ko? Yau kwananki nawa da haihuwa, ina ce kin doshi kwana hamsim. Ko kuma don ba ki san zuru ba me shi ya sa za ki cigaba da laƙewa a ɗakina kina rungumar ɗa kina yi masa rawa. Ki fito ku tafi casar gero tun lokaci bai ƙure ba."
Jiki yana rawa Sakina ta zame Ridwan da ke cinyarta ta ce.
"Bari na goya shi, tuba nake Uwar bayi."
Uwar bayi ta saki dogon tsaki ta yi gaba tana cewa. "Daɗina da ku ba ku san harkar mutumci ba, ina laifi adalcin da na yi miki za ki shantake a ɗaki. Ai hutu ba na ki ba ne, tun da Allah Ya ƙaddaro miki rayuwar bauta a gidan nan."

Kwantar da Ridwan Baiwa Sakina ta yi, ta shiga uwar ɗaki domin ɗauko zanen goyonsa. Tana fitowa ta hango shi a kwance yana kallon kusurwar bango yana ƙyalƙayala dariya, da mamaki take kallon wurin sai dai ganin babu komai ya sa ta miƙa hannu za ta ɗauke shi. Da sauri ta ja baya, ganin yatsarsa sanye da da wata azurfa mai ɗauke da wani zanen da ba ta fahimce shi ba. A sanyaye ta miƙa hannu tana taɓa azurfar, sai dai jin ta da zafi zau kamar an ciro daga cikin wuta ya sa ta yi saurin yarfe hannunta gefe.

"Wallahi idan na sake magana Sakina sai kin yi aikin wata guda babu mataimaki. Iskancin banza da wofi wannan wanne irin wulaƙanci ne?"

Uwar bari ta katse mata nazarin da take yi, game da baƙon lamarin da ya faru da Ridwan bayan shigarta ɗaki. Jiki yana rawa ta ɗauke shi ta saka shi a baya, sannan ta fito daga ɗakin zuciyarta fal wasu-wasi.
Koda ta je wurin aiki hatta ragowar bayin da suke aiki sun lura da sanyin jikin Sakina, don duk yawan hirar da ake yi sai sun sako ta za ta jefa kalma ɗaya zuwa biyu. Sai da ta ji ya fara mutsu-mutsu alamar yana jin yunwa, sai ta koma can gefen wata bishiyar kuka ta sauko shi tana ƙare masa kallo. Da yake wurin ya yi nesa kaɗan da wurin da suke surfen, ba ta yi aune ba ta ji wata tsohuwa ta yi mata sallama. A ɗan razane ta waiga, don har lokacin zuciyarta ba ta daina rawa ba. Kallon mamaki take yi wa tsohuwar don ba ta taɓa ganinta a gidan ba, amma abin da ya ba ta mamaki ganinta sanye da irin kayansu na bayi. Sai da ta amsa mata sallamar sannan tsohuwar ta ce.

"Ɗazu muna filin sassaƙa na ga kin yar da ɗan kunnenki, ban samu damar miƙo miki ba saboda uwar bayi tana wurin."
A sanyaye Baiwa Sakina ta shafa kunnenta ta ji babu wari ɗaya, ta miƙa hannu ta karɓa sannan ta yi mata godiya. Sai ta ga tsohuwar tana kallon Ridwan, tana shirin yin magana tsohuwar ta cigaba da cewa.
"Allah Ya yi miki babbar kyautar da ba kowa yake yi wa ba, saboda haihuwa babbar ni'ima ce. Idan kika cigaba da riƙe wannan amanar ta hannunki, haƙiƙa za ki rabauta da lada mai yawa. Tabbas wannan yaron ba kamar sauran yara ba ne, ki riƙe shi hannu bibbiyu Sakina."
Tana gama faɗar haka ta saki murmushi ta wuce, da sauri Baiwa Sakina ta bi bayanta. Sai dai tana shan lungun da tsohuwar ta yi ta neme ta sama da ƙasa ta rasa. Kallon ɗan kunnen hannunta ta yi, sai a lokacin ta ga kamar ba nata ba. Ƙura masa ido ta yi, ta sake kallon zoben hannun Ridwan sai ta ga yana ɗauke da irin rubutun zoben hannunta.

"Zainaba! Wace ce Zainana?"

Ta samu kanta da furta haka, tana cigaba da kallon Ridwan da ke ta tsotsar hannunsa.

BAYAN SHEKARA GOMA (1835)

Tun daga bakin ƙofar ɗakin za ka fara jin salatinta, cikin galabaita ta dubi Unguwar zoma ta ce.
"Lami! Ki taimaka ki karɓo mini tofi a wurin takawa."
Cikin girmamawa Unguwar zoman ta ce, "Allah Ya taimake ki, yanzu haka Jakadiya ta tafi wurin Shamaki ta sanar da shi, domin ya faɗa wa Sarki Gambo halin da kike ciki."

Cike da zafin naƙuda, Fulani Khadija ta ce, "Ki bi ta Lami, ni na san abin da nake ji. Wayyo Allahna! Hasbunallahu wa ni'imal wakeel."
Ganin Fulani Khadija ta fara fita hayyacinta ya sa Unguwar zoma Lami ta fita da sauri, da fitarta babu jimawa Fulani Khadija ta ga an shigo ɗakin. Fuskarta a naɗe take cikin shigar kayan bayi, a daidai kanta aka tsaya ta ɗan ja da baya ta ce.
"Wace ce?"
Ba a tanka mata ba, aka yarfa mata wani baƙin ruwa a fuska. Ji ta yi kamar an zare mata laƙa, ta faɗi baya yaraf. A daidai lokacin ta saki nishi, nan take tagwayen jariranta mata suka faɗo. Murmushi ta yi tana ƙare wa matar tsugunnen da kallo, sai kawai ta saki wata irin dariya. Cikin shammata ta saka hannunta biyu a saman kawunan jaririn nata, ta fara motsa baki ba tare da ana fahimtar abin da ta furta ba. Ganin ana ɓata mata lokaci matar da ke tsugunne, ta zaro kaifaffan ƙahon da aka wasa ya yi tsini. Ta burma a saitin zuciyar Fulani Khadija, nan take idanunta suka lumshe tana fara motsa bakinta cikin azabar fitar rai. Cikin zafin nama, matar ta zaro zuciyarta wace ta haɗa da mabiyyar jariran ta ɗauka ta fice daga ɗakin.

*Ummou Aslam Bint Adam*🌚
07062062624

[23/11, 22:41] Ameerah Adam: *KUNDI UKU*

©AMEERA ADAM

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye.

Tsokaci: Daga Masarautu, Sarakuna da sunayen yanki duka ƙirƙira ne. Idan ya yi daidai da labarin wani/wata arashi ne.

SHAFI NA HUƊU

https://chat.whatsapp.com/LyQRbgQCzbL9iUHgPoeyO2?mode=ems_copy_t

Masarautar Judala (1835)

Fulani Zannira tana ƙarasawa turakar Sarki Giɗaɗo, bayin da ke biye da ita suna riƙe da alkyabbarta ta baya suka dakata. Cikin girmamawa suka zube ƙasa suna faɗin.

"A fito lafiya ranki shi daɗe, Allah Ya ƙara miki lafiya mai zuciyar zinare."

Ba ta tanka musu ba, ta tura ƙofar da shiga, sassanyan ƙamshin rumfar Takawa ta daki hancinta har sai da ta lumshe idonta. Cikin takunta na isa da jan hankali ta fara takawa har zuwa turakarsa, sallama ɗauke a bakinta ta shiga tana faɗaɗa fara'arta. A jingine ta hango shi kan ƙasaitacciyar shimfiɗarsa ta alfarma, sai dai ta lura har ta ƙarasa gabansa bai fahimci ruhinta ya wanzu a wurin ba.

"Barka da hutawa sarkin sarakai."

Ta furta cikin salo mai jan hankali, wuri ɗaya ta ga yana kallo don haka ta zauna daga ƙasansa. Sannan ta kai hannu ta shafa sajensa da ke kwance luf a zagaye da fuskarsa. Murmushi ta ga ya sakar mata, ya fara ƙoƙarin kawar da damuwar da ke kwance a saman fuskarsa.
"Barka da shigowa sarauniya."

"Damuwa ba ta dace da gwarzon mazaje ba, nannauyan tunani bai cancanci samun sukuni a tare da kai ba jarumina." Ta furta tana zuba masa idanu, sannan ta ɗora da cewa.
"Idan ban takura Mai martaba ba, ina son sanin damuwar da yake ciki domin na samu sukunin kawar masa da ita."

Janyo ta ya yi jikinsa yana jin tsananin soyayyarta tana mamaye zuciyarsa, haka kawai yake jin soyayar Zannira ta doke duk ragowar matan da ya aura a baya. Nan take ƙirjinsa ya buga, tausayinta da shi ya mamaye shi. Amma gudun kada ya ɗarsa mata damuwa ya sa shi kawar da damuwar zuciyarsa ya ce.

"Akwai baƙin al'amuran da ke shirin faruwa Fulani, kun san jan ragamar sarauta ba abu mai sauƙi ba ne."

Kwanciya ta yi a jikinsa, ta janyo hannunsa ta shiga wasa da shi sannan ta ce.
"Ni san mijina gwarzo ne, don haka babu gwagwarmayar da za ta dagula masa lissafi. Kai ɗin jarumin namiji ne, zuciyarka tamkar ta dakarun jarumai dubu ce."
Yadda a ɗan kwanakin da suka yi da Zannira take ba shi ƙwarin gwiwa abin ba ƙaramin birge shi yake ba, ta kai

3 / 14