Author : Ameera Adam Category : Read Hausa Novels
matsa gaban cross ɗin ya dafa shi haɗe da runtse ido. Murya da suka ji a farko, ita ta sake karaɗe kunnensa tana biya masa kamar haka.
"Ya Ubangiji Yesu, na yarda cewa kai .... Na furta cewa ni mai zunubi ne, kuma yanzu haka ga ni a gabanka ina neman gafararka. Na karɓe ka a matsayin Ubangijina, mai ceton rayuwata. Na buɗe maka zuciyata ka shiga ciki ka ceci rayuwata. Na gode maka da ka ceci rayuwata daga ɓata, Amin."
Muryar tana gama biya wa Sarki Giɗaɗo, ya ga ya sake tsintar kansa a wani babban kogon dutse. Ilahirin cikin dutse cike yake da cross manya da ƙanana, wata gajeriyar farar mace ya gani. Daga ita sai ganye a ƙirji da ƙasanta. Sarki Giɗaɗo yana shirin yin magana ya ji ta katse shi da cewar.
"Barka da shigowa sabon addini sabuwar rayuwa.
Jikinsa yana rawa ya amsa mata. "Barka dai Bokanya Kande." Yana shirin yin bayanin abin da yake tafe da shi ya ji ta ce.
"Duk matsalolinka na gama saninsu. Matanka suna mutuwa duk bayan kwana arba'in da aurensu, a yanzu haka kuma iyalinka tana ɗauke da juna biyu, kai kuma ba ka son ka rasa ta." Gyaɗa kai Sarki Giɗaɗo ya yi ta cigaba da cewa.
"Mafitarka ɗaya ce ka nemo mini tsohuwar matarka Karima, ko kuma ka kawo mini jininta wato 'yarta."
A firgice Sarki Giɗaɗo ya ɗago ya ce.
"Ya shugabata Fulani Karima ta shafe lokaci mai tsayi da mutuwa. Babu yadda za a yi na iya kawo miki ita, kuma a iya sanina da ita ni ne mijin da ta taɓa aure. Kuma a ɗakina ta mutu, aka binne ta a masarautata."
"Ba ta mutu ba!"
Bokanya Kande ta furta tana zuba masa manyan idanunta farare tas da sha kwalli ya ƙara musu kyau, ji ya yi ba zai iya cigaba da kallon ƙwayar idonta ba. Ta saki murmushi sannan ta cigaba da cewa.
"Har yanzu Karima tana doran ƙasa, domin binciken da na yi tauraron rayuwarta yana nan har yanzu. Amma ban gama tabbatar da shin ainihin ruhinta ne, ko kuma akwai wani ƙulumboto da aka aikata ba. Kuma ta haifi jininta a cikin masarautarka, domin tauraron jaririyar daga tsagin tauraron Karima yake, sai dai har kawo yanzu bincikena bai bayyana mini ainahin fuskar jaririyar ba. Sai dai yana kyau, ka binciki masarautarka. Duk sababbin jariran da aka haifa a ciki, ka shafa musu wannan jan garin maganin da zan damƙa maka. Idan har ka ga jini daga al'aurarsa, wala mace ko namiji ko kuma sauran alamomin da zan raɗa maka a kunne, to tabbas jinin Fulani Karima ne."
*Ummou Aslam Bint Adam*
07062062624
[25/11, 21:38] Ameerah Adam: *KUNDI UKU*
©AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye.
Tsokaci: Daga Masarautu, Sarakuna da sunayen yanki duka ƙirƙira ne. Idan ya yi daidai da labarin wani/wata arashi ne.
SHAFI NA TAKWAS
*MUM NIMRAH'S GRILL FISH AND SHAWARMAR*
'Yar uwata kema kina fama da kwadayin kayan kwalam da makulashe?To ina yi miki albishir da ki garzayo wajan Mum nimrah's grill fish and shawarma don farantawa bakinki, mai gidanki, yaranki, iyayenki da zuciyar ki da haddaden grill catfish or tilapia.😋💃🏻 Sai kuma beefshawarma Akan farashi me sauki.
zaki sameta akan number 08140365134 domin yin order a WhatsApp.
Location: Kano
Sai kun zo💃🏻
Masarautar Kajjura
Yadda Sarki Gambo ya maƙure wuyan Fulani Zainaba, abin ba ƙaramin tsoro ya ba ta ba. Don har sai da numfashinta ya nemi ɗaukewa, idanunta suka firfito ta fara fita hayyacinta. Wurgi ya yi da ita ta faɗi ƙasa, nan take tari ya turnuƙe ta. Zuwa ya yi ya tsiyayo mata ruwa a tulunsa, ya ƙarasa gabanta ya miƙa mata. A galabaice ta karɓa ta kai bakinta, sai da ta sha mai isarta sannan ta ɗago tana sauke ajiyar zuciya. Kafe ta ya yi da ido yana kallo, ita ma ta zuba masa idanu tana sake jadadda ƙarfin rashin imaninsa.
Sarki Gambo ya ɗago haɓarta, yana bin ta da wani rin kallo mai wuyar fassarawa.
"Zainaba ba yanzu zan kashe ki ba."
Ya furta a kausashe, kamar ta yi masa shiru. Sai kuma zuciya ta ɗebe ta, tana ayyana mata idan har ta yi shiru zai ga kamar ta fara jin tsoronsa ne. Cikin dakiya da taurin zuciya ta ce.
"Rashin kisana da ka yi, yana da nasaba da ganin gawarka da zan yi Sarki Gambo."
Ya ji ɗacin maganarta, don haka ya furzar da isa mai zafi ya ce.
"Lokaci kawai nake jira, amma mu koma maganarmu ta baya. Me ya sa kike son ɗora alhakin kisan Fulani Khadija a kaina, duk da kina da masaniyar a wurin haihuwa mummunan al'amarin ya faru da ita?"
"Saboda na san babu abin da ba za ka iya aikatawa ba saboda buƙatar kanka."
Fulani Zainaba ta ba shi amsa kai tsaye. Miƙewa ya yi ya fara zagaye ɗakin yana girgiza kai, sai da ya yi zagayen kamar sau uku sannan ya koma kan kujerarsa ya zauna suna cigaba da kallon juna ya ce.
"Tabbas ba ki yi ƙarya ba Zainaba, zan iya aikata komai kuma a kan kowa matuƙar buƙatata za ta biya. Domin dalilin haka ne ya sa na hallaka mijinki Najibullah da jaririn ɗanki."
Runtse idonta ta yi da sauri, tana jin wani irin ɗaci a ranka. Saboda duk lokacin da ta tuna irin kisan wulaƙancin da Sarki Gambo ya yi wa Najibullah sai ta ji abin ya dawo mata sabo. Murmushi mai sauti ta ji ya saki, sai a lokacin ta buɗe idonta sannan ta ce.
"Abin da ba ka sani ba Sarki Gambo, babban kuskuren da ka aikata a rayuwa shi ne rashin kashe ni a daidai lokacin da ka kashe mijina. Za ka maimaita waɗannan kalaman naka a gaba, kuma ina mai sake tabbatar maka da kamar yadda kake tare da ni saboda biyan buƙatar kanka. Na rantse maka da zatin Allah, ni kaina na jinkirta hallaka ka ne saboda manufar da ke ɗamfare a cikin zuciyata."
"Taurin kai, kafita da ƙarfin zuciyarki suna birge ni Zainaba. Sai dai abin da ba ki sani ba, tun da har zan iya juya wa Fulani Sadiya baya. Babu macen da za ta sha a wurina, idan kika tsame tagwayen 'ya'yana da abar bauta rana da ta ba ni."
Da sauri Fulani Zainaba ta dube shi saboda jin furucin da ya yi.
"Me kake faɗa haka?"
Jin tambayarta ya sa shi ɗaga mata gira ya ce.
"Kamar yadda kika ji a kunnuwanki."
Fulani Zainaba ta miƙe a hankali, sai da ta ƙarasa kan faffaɗar shimfiɗarsa ta zauna sannan ta ce.
"Wannan wani salon ne? Ko kuma kana son nuna mini hatta Ubangiji sai ka haɗa shi da waninSa?"
Sarki Gambo ya girgiza kai haɗe da cewa, "Ko kaɗan ba yadda kike tsammani ba ne, na kasance ɗaya daga cikin masu bin addinin gargajiya tun asalin iyaye da kakanni. Akwai dalili mai ƙwari da mahaifina ya ɗora ni a turbar nuna wa al'umma ni mai bin addinin Musulumci ne. Wannan furucin da na yi miki, kada ki yi tsammanin zai zame miki hujja da za ki nemi tarwatsa ni, domin har abada ba za ki iya da ni ba Zainaba."
"Ai ka riga da ka yi sake ɗan zaki ya girma Sarki Gambo."
Fulani Zainaba ta furta tana nufar bakin ƙofar fita, sai da ta gyara zaman alkaybbarta sannan ta waigo ta ce.
"Ni daga yau nawa aikin zai fara, domin duk kalma ɗaya da kake furta mini ina ajiye ta a mizanin da ta dace."
Murmushi Sarki Gambo ya yi ya ce. "Ina yi muku fatan samun nasara Zainabata, haka kuma a wannan daren muna buƙatar raya shi tare da ke. Sai dai zan ba ku dama domin ku je ku huta, ko za ku samu sukunin nazaratar abin da yake ranku." Ta fahimci sarai abin da yake nufi, amma sai ta kawar da zancan da cewa.
"Hankalina bai kwanta da zaman su Hasana a hannun Fulani Sadiya ba."
Jim ya yi kamar mai nazari, don haka kawai shi ma yake jin zaman tagwayensa bai samu gurbi mai kyau ba. Amma kuma a yadda ya san Fulani Zainaba ta yi masa mummunar tsana, ba ya jin zai iya damƙa raganar rayuwar 'ya'yansa a hannunta. Don ya tabbata ko ta ɓangarensu ne za ta iya yin galaba a kansa, hakan ne ya sa a fili ya ce.
"Ko da su ba jininmu ba ne, mun tabbata Fulani Sadiya ba za ta cutar da su ba. Mun aminta da Fulani fiye da yadda kuke tsammani, idan kuna mummunan tunani a kanta ya kama ku janye."
Murmushi Fulani Zainaba ta yi kamar za ta tanka masa, sai kuma ta girgiza kai ta yi gaba.
Tun da ta fita hadimai da dogarawa suke zubewa suna jera mata kirari, ba ta iya tanka musu ba. Sai ta wuce sashenta a gaggauce, don kanta ba ƙaramin cushe mata ya yi ba. Ta jima tana kai wa da kawowa, har ta zauna tana nazari kamar wacce aka tsikara sai ta miƙe ta fita ta kira Baiwa Lawisa ta ce mata ta gaggauta kira mata Jakadiya. Ba a ɗauki lokaci mai tsayi ba, Jakadiya ta ƙarasa jiki a sanyaye. Don tun bayan mutuwar Fulani Khadija, zuciyarta a cike take da zullumin yadda makomarta za ta kasance.
"Allah Ya taimaki Fulani, Ubangiji Ya tsare gabanki da bayanki. Ke kaɗai ce zarah a cikin taurari, hutawarki lafiya ranki shi daɗe."
Jakadiya ta furta tana sake dunƙule hannunta cikin jinjina, A ɗan gaggauce Fulani Zainaba ta ce.
"Jakadiya ina son sanin asalin tarihin Sarki Gambo, tarihin masarautar nan da kafuwarta."
A ɗan razane Jakadiya ta ɗago, cikin in'ina ta ce.
"Amm... amma... ranki shi daɗe me... yake faruwa haka?"
"Ba na buƙatar tambayoyinki, amsa kawai nake buƙata."
Jin furucin Fulani Zainaba ya sa Jakadiya ta sauke gwaruwar ajiyar zuciya ta ce.
"Allah Ya taimake ki tarihi ne mai cike da tarin al'ajabi da ƙalubale, ki gafarce ni ranki shi daɗe. Amma duk abin da zan sanar da ke harsashe ne, ko kuma labaran su kasance masu haɗe da rashin cikakkiyar gaskiya ko tabbacin waɗansu abubuwa. Amma akwai wani kundi guda ɗaya, wanda aka buga hatiminsa da rubutun ajami, bangon jikinsa da fatar tsohon zaki Guzugu, sai dai a yadda na ji labari. Mutum ɗaya ce ta san maɓoyar wannan kundin, kuma ta san mafi yawa daga cikin sirrin masarautar nan."
"Wace ce ita?"
Fulani Zainaba ta furta kai tsaye cike da zaƙuwa, Jakadiya ta yi ƙasa da murya tana ɗan waige. Sai da ta ƙara matsawa gaban Fulani Zainaba, ta yadda wani ba zai iya jin abin da suke tattaunawa ba sannan ta ce.
"Sunanta Kursum!"
"Kursum!"
Fulani Zainaba ta maimata sunan tana nazari, ta sake duban Jakadiya ta ce.
"Wace ce ita? Kuma a ina take? Mene ne alaƙarta da masarautar nan? Kuma a ina zan same ta?"
Jakadiya ta sake russunawa cike da girmamawa ta ce, "Allah Ya huci zuciyar Fulani, tuba nake abisa kalaman da zan furta. Amma kalamar ban sani ba, ita ce kalamar da duk wani mahalukin da ke zaune a cikin masarautar nan zai sanar da ke."
"Saboda me?"
Fulani Zainaba ta jefa mata tambaya, Jakadiya ta ce.
"Saboda babu wanda ya san yadda aka haihu a ragaya, amma a wani labari da na taɓa ji, na ji an ce akwai wasu ɓoyayyun wasiƙu da Mai martaba yake da su a turakar sirrinsa."
Wannan karon a bayyane Fulani Zainaba ta sauke gwauron numfashi, haɗe da jinjina kai saboda yadda take jin baƙin al'amura daga bakin Jakadiya. Fulani ta sake kallon Jakadiya ta ce.
"A ina turakar sirrin nasa take?"
FULANI SADIYA
Tun lokacin da aka aikawa Fulani Sadiya tagwayen marigayya Fulani Khadija, ta ji kamar ta shaƙe musu wuya su ma su mace har lahira. Amma gudun zargi ya sa ta haƙura, ta cigaba da nuna musu kulawar yaudara don tun dangin Fulani Khadija suna ɗari-ɗari har suka saki jiki da ita. Amintattun bayin Sarki Gambo biyu aka ware masu yi musu hidima da kulawa da su, don haka yaran ba su cika rigima ba tun da gari yana wayewa ake tatsar musu nonon akuya su sha.
SARKI GAMBO
Sarki Gambo ya jima a yana jiran Malami ya ƙarasa surukullen da ke gabansa, sai da ya kammala tsaf sannan ya dubi Sarki Gambo ya ce.
"Ban yi tsammanin ganinka a daidai wannan lokacin ba."
Sarki Gambo ya sharce gumin goshinsa ya ce.
"Dalilin hakan ne ya kawo ni ya kai babban matsafin da nake aifahari da shi."
Malami ya saki murmushin jindaɗi, don yana matuƙar son a fasa masa kai. Ya kalli Sarki Gambo alamun ya faɗi abin da yake tafe da shi, sai da ya gyara zama sannan ya ce.
"Mun zo ne domin mun san wanda ya kashe mana Fulani, kisa mafi muni da wulaƙanci."
"Sanin makashin ba shi zai fisshe ka ba Sarki Gambo, a yanzu babban ƙalubalen da ke gabanka ya ninka mutuwar Fulani Khadija, domin kuwa ita tuni ta mutu. Sai dai mu jira yi ruhinta tun da ya kasance mai tsarki, amma a yanzu tagwayenka sune manyan ƙaddarorin da za su taɗe duk wani burin rayuwarka."
A hargitse Sarki Gambo ya ce. "Ban fahimce ka ba Malami, mene ne zai faru da tagwayen da nake fatan su zame mini sanyin idaniya?"
"Ba matsalar ce za ta same mu ba, idan har kana tunanin haka ka dakata. Domin idan har matsalar a gaba take za mu iya cimma mata har mu magance ta, ina son Sarki Gambo ya sani. A halin yanzu Hassana da Husainarka sun kasance nakasassun da ba za su amfane ka ko su amfani masarautar nan ba. A taƙaice dai, kai da wanda ba shi da magaji a ɓangaren sarauta ɗaya kuke, ɗaya tana ɗauke da shanyewar ƙafa da hannuwa. Yayin da ɗaya ta samu matsalar makanta da ta ƙwaƙwala, wannan wani mummunan al'amari da zai iya daƙile komai na rayuwarka."
*Ummou Aslam Bint Adam*🌚
07062062624
[25/11, 22:11] Ameerah Adam: *KUNDI UKU*
©AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye.
Tsokaci: Daga Masarautu, Sarakuna da sunayen yanki duka ƙirƙira ne. Idan ya yi daidai da labarin wani/wata arashi ne.
SHAFI NA TARA
*MUM NIMRAH'S GRILL FISH AND SHAWARMAR*
'Yar uwata kema kina fama da kwadayin kayan kwalam da makulashe?To ina yi miki albishir da ki garzayo wajan Mum nimrah's grill fish and shawarma don farantawa bakinki, mai gidanki, yaranki, iyayenki da zuciyar ki da haddaden grill catfish or tilapia.😋💃🏻 Sai kuma beefshawarma Akan farashi me sauki.
zaki sameta akan number 08140365134 domin yin order a WhatsApp.
Location: Kano
Sai kun zo💃🏻
Masarautar Zulwara
Sai da Boka tsumbur ya gama sauraron tsawar da kogon dutsen yake yi, sannan ya dubi Sarki Dikko ya ce.
"Haƙiƙa akwai sabon al'amarin da zai faru a wannan zuwan naka Sarki Dikko, ta wani fannin nakan iya ce maka kai mai nasara ne. Sai dai kuma akwai duhun da na hango yana mamaye da tauroronka, tauraronka ya kasance Himlu don haka nake..."
"Amma mun jima da sanin tauraronmu Surdanu ne Boka tsumbur. Kuma wanne irin duhu aka hango mana, shin yana iya cutar da mu ko akasin haka?"
Sarki Dikko ya katse boka Tsumbur, bai tanka masa ba ya cigaba da shafa ƙasar shurin gabansa yana wani zane a kanta sannan ya ce.
"Tauraronka Himlu ne kuma ɗabi'ar nari, sannan duk wani bincikena bai bankaɗo mini ainahin abin da yake ƙunshe a cikin duhun ba."
Ajiyar zuciya Sarki Dikko ya sauke cikin damuwa, yana shirin yin magana boka tsumbur ya katse shi da cewar.
"Sarki Dikko kuna iya ba mu wuri, domin a yanzu haka muna da babban baƙo, shugaban rauhanai na ƙarƙashin ƙasa ya ziyarce mu. Matso kusa mu sanar da kai sharuɗɗanmu, da dokokin da za mu gindaya maka."
Sarki Dikko kamar yana jira, ya yi saurin matsawa kusa da boka tsumbur. Ya jima yana yi masa raɗa, sai dai tun bai kammala ba gumi ya jiƙe shi sharkaf saboda tsananin fargaba da tashin hankali. Har ya buɗe bakinsa zai yi magana boka tsumbur ya ɗaga masa hannu da cewar.
"Mun riga da mun gama zartar da hukunci Sarki Dikko, don haka dabara ta ragewa mai shiga rijiya. Amma muna iya baka shawara, idan har buƙatar hakan ta kama."
Jiki a sanyaye Sarki Dikko ya miƙe, suka fita da Waziri yana fargabar sharuɗɗan da boka ya gindaya masa.
Sarki Dikko yana komawa gida kai tsaye turakarsa ya shiga, kai kawo ya dinga yi a cikin ɗaki cikin matsananciyar damuwa da tashin hankali.
'Shin kana ganin za ka iya fita a kan muradin boka Tsumbur? Ta ina za ka fara?'
'Kada ka manta duk abin da ka yi, za ka yi shi ne domin kyawun goben 'ya'yanka. Idan har ka gagara yin haka, sannu a hankali watarana za a shafe tarihinka da irin sarautar da ka shimfiɗa a doron ƙasa.'
'Buƙatar boka ba abu mai sauƙi ba ce, ya zame maka wajibi ka zage damtse domin gujewa kuskure masa.'
Ire-iren kalaman da zuciyar Sarki Dikko ta dinga wassafa masa kenan, cikin tsananin damuwa ya sauke ajiyar zuciya