Author : Ameera Adam Category : Read Hausa Novels
tsohuwar ba. Juya kalaman tsohuwar ta fara yi ba tare da ta fahimci inda suka dosa ba, don haka jiki a sanyaye ta cigaba da tafiya har ta fita daga soron ƙarshe. Zaniru ta hango suna surfe, ta yafito ta da hannu alamar ta zo. Jiki yana rawa Zinaru ta ƙarasa ta ce.
"Barka da fitowa uwar bayi."
Uwar bayi ta sauke ajiyar zuciya ta ce, "Mene ne ma sunaki?"
Cikin sauri Zinaru ta ce, "Sunana Zinaru!"
"Yarinyar jiya da ta haihu fa?"
Uwar bayi ta tambaya tana zuba wa Zinaru idanu, shiru Zinaru ta yi tana nazari, cikin son gwaninta da neman samun wurin zama a wurin Uwar bayi ta yi ƙasa da murya ta ce.
"Uwar bayi Indo fa ba ita ta haifi jaririyar nan ba, hasali ma Indo budurwa ce ko auren fari ba ta yi ba."
Da sauri Uwar bayi ta dube ta ta ce, "Ke Zinaru ki fito ki yi mini bayani dalla-dalla, domin zancan da nake yi miki yanzu haka Takawa ne ya turo ni na kai ta wurinsa ita da jaririyarta. Kin ga kuwa tun da kin zo da ƙarin haske, za mu tafi da ke domin ki yi bayanin komai a wurinsa."
Ƙuuu! Cikin Zinaru ya bayar da sautin mai ƙarfi, hankali a matuƙar tashe ta ce. "Don girman Allah don zatinSa ki yi mini rai Uwar bayi, wallahi tallahi abin da na faɗa gaskiya ne ba sai an kai ni gaban mai martaba ba." Da wani irin kallo Uwar bayi ta dube ta, sai kuma ta haɗe fuska ta ce.
"Ke Zinaru ki shiga hankalinki, ni da kika gani ban taɓa faɗar magana an musa mini a wannan ɓangaren namu na bayi ba. Saboda haka dole ki wuce mu je har da ke gaban Takawa ki yi masa jawabin abin da kika sani, idan ba haka ba kuwa wani hukuncin daban zai iya biyo wa ta kanki." Uwar Bayi tana gama maganar ta yi gaba, wasu gajerun zafafan hawaye ne suka siraro daga ƙwayar idon Zinaru. Lokaci ɗaya ta ji nadama ta mamaye ta, tana danasanin ɓarin zancan da ta yi don ba ta yi tsammanin wankin hula zai kai ta dare ba.
Zuwaira da Indo suna tsaka da tattaunawa, ba su yi aune ba suka ga Uwar bayi ta bankaɗa labulen ɗakin. Da sauri duka suka dube ta, kusan lokaci ɗaya gabansu ya yanke ya faɗi. Saboda ganin yanayin da Uwar bayi take ciki, fuska babu walwala ta ce.
"Ke Indo! Ki ɗauko jaririyarki Mai martaba yana son ganinki cikin gaggawa."
A hargitse Indo ta ɗago, nan take jikinta ya ɗauki karkarwa har ta matsa gaban Uwar bayi ba tare da ta sani ba.
"Na'am... Uwar bayi... zuwa zan yi?"
Cikin masifa Uwar bayi ta ce. "Kin ji abin da na faɗa tsabar iskanci ne ya sa kike sake tambayata." Kamar Indo ta san abin da yake faruwa, nan take hawaye ya cika idonta. Tana waigawa suka haɗa ido Zuwaira, alamar ta kawo mata ɗauki. Amma sai ta ga ita ma Zuwairar ta sunkuyar fa kai ƙasa cikin sanyin jiki. Babu yadda Indo ta iya, haka ta rungumi Batul ta ja sagaggun ƙafafuwanta ta bi bayan Uwar bayi suka nufi sashen Sarki Gidaɗo. Indo ta yi mamaki da ta ga har da Zinaru aka nufi sashen Takawa, sai dai ko kaɗan ba ta kawo komai ba. Sai ta yi tsammanin ko an gano sun tsinci jaririya a masarautar ne ba tare da sun sanar ba.
Su uwar bayi ne a kan gaba wurin shiga ɗakin, sai Indo da take ƙarshen shiga. Tana tsoma ƙafarta ta ji baƙuwar murya a kunnenta ta ce, "Kada ki shiga, za a salwantar mini da ita. Kada ki manta Indo, amana ce na damƙa miki."
Cak! Indo ta tsaya tana nazari. Kuma ta tabbata muryar Karima mahaifiyar Batul ce, tana nan tsaye kamar an daskarar da ita ta ji muryar Uwar bayi cikin tsawa tana faɗin.
"Hattara Indo, kina gaban Mai martaba."
Ajiyar zuciya ta sauke, ta fara takawa a hankali kamar wacce aka zare wa laka a jiki. Tana shiga ɗakin ta ji Batul da ke rungume a hannunta ta tsanyare da kuka, a duburburce ta shiga jijjiiga ta gabanta yana cigaba da faɗuwa, sai dai har ta zauna Batul ba ta daina tsanyara kuka ba.
"Allah Ya taimake ka, wannan ita ce wacce na ce maka ta haihu jiya a masarautar nan. Sai dai kuma a yanzu maganar ta sha bambam da tawa ranka shi daɗe, domin wannan sunanta Zinaru ita kuma ta tabbatar mini da Indo ba ita ce mahaifiyar jaririyar ba. Amma idan ka lamunce mini ranka shi daɗe, zan gabatar da Zinaru ta warware mana zare da abawa."
Uwar bayi ta yi maganar cikin girmamawa, fuskar Sarki Giɗaɗo a murtuke take. Don haka murya babu walwala ya ce.
"Muna sauraren Zinaru."
Indo ce ta ɗan zunguri Zinaru, Zinaru da ta gama yin fiƙi-fiƙi da idanu ta kawar da kai gefe daga kallon Indo ta ce.
"Allah Ya taimake ka, abin da na faɗa haka yake. Indo ba ita ce mahaifiyarta ba, hasali ma Indo budurwa ce ko auren fari ba ta yi ba. Jiya da daddare mun fita na raka ta fitsari..."
Zinaru ta kwashe duk iya abin da ta sani ta sanar wa da Sarki Giɗaɗo, ƙuri ya yi wa Indo yana kallo. Cikin rashin imani ya zaro wata sihirtacciya kuma kaifaffiyar askarsa da ke walwali da sheƙi ya ajiye a gefen cinyarsa. Sannan ya dubi Indo cikin wata irin murya ya ce.
"A kawo mana jaririyar nan."
Kalaman Sarki Gidaɗo ya yi daidai da faɗuwar gaban Indo a karo na barkatai, idanuwansa ne suka yi mata kwarjini. Jikinta ya shiga karkarwa kamar mazari, don haka jiki babu ƙwari ta miƙe ta fara takawa har gaban Sarki Gidaɗo. Babu yadda ta iya, haka ta ɗora masa Batul a saman hannunsa, wani irin zummm ya ji, haka ita ma daga ɓangaren Indo. Tana nan durƙushe a gabansa ya ce.
"Wace ce ke? Wace ce ta damƙa muku jaririyar nan? Muna nufin wace ce mahaifiyarta."
Tun sarki Gidaɗo bai rufe baki ba, daga can bakin ƙofa ya ji muryarta ta ƙarade kunnensa da cewar.
"Ni ce mahaifiyarta."
Ba iya sarki Gidaɗo ba, hatta su Jakadiya mutuwar zaune suka yi suna bin ta da kallo.
Masarautar Kajjura
Jin Tsoho Sulaimanu ya yi shiru ya sake fusata Kursum, don haka a harzuƙe ta matsa wurin da take jin hucinsa. Cikin fusata ta kai hannu ta shaƙo shi, sai ta yi nasarar shaƙar daidai wuyansa. Nan take ya fara kakari tamkar numfashinsa zai rabu da gangar jikinsa, sai da ta ji ya fara fita daga hayyacinsa sannan ta yi wurgi da shi ya faɗi ƙasa yana mayar da numfashi.
"Na ce wane ne kai? Mene ne haɗinka da Najibullah? Kuma yaushe ne ya mutu?"
Tsoho Sulaimanu ya furzar da iska yana sauke ajiyar zuciya a galabaice ya ce.
"Sunana Tsoho Sulaimanu, kuma marigayi Najibullah tamkar ɗa yake a wurina." Sai ya haɗiyi yawu mai ɗaci, yana jin ɓacin rai da kewar Najibullah tamkar a lokacin sarki Gambo ya hallaka shi.
"Sarki Gambo ne ya hallaka Najibullah da kisa mai muni, kuma ya sa aka killa ce matarsa Zainaba da zummar idan ta haihu a kashe abin da ta haifa. Idan har kunnuwana ba gizo suke yi mini ba, na ji ya ce zai auri Zainaba idan ta haife cikinta." Kuka ya fara cin ƙarfin Tsoho Sulaimu, sai da ya share hawayensa sannan ya cigaba.
"Ni kaina ya kawo ni wurin nan me saboda na gagara bayyana masa maɓoyar kundin da yake kwana ya tashi da su. Kuma na san a tsawon waɗannan shekarun ya hallaka abin cikin Zainaba. Kaico! Da ban samu nasarar cika burin Najibullah ba."
Tsoho Sulaimanu yana gama maganar ya fashe da kuka, yaraf! Ya ji alamar zamanta a ƙasa. Yana nan zaune bai yi tsammani ba sai ji ya yi ta fashe da wani irin kuka mai cin zuciya. Jikinsa ne ya sake yin sanyi, don tun daga ranar da ya shiga ɗakin har ya shafe waɗannan shekarun masu tsayi a tare da ita. Bai taɓa jin ta yi kukan da yake jin zafinsa har a cikin zuciyarsa ba. Don haka bai hana ta ba, haka kuma bai san dalilin kukan nata ba. Sai da ta yi mai isarta sannan ya ce.
"Na jima ina jin sautin kukanki, sai dai ban taɓa jin makamancin irin wannan ba. Haƙiƙa akwai wata ɓoyayyar alaƙa tsakaninki da Najibullah, domin yanayinki ya sauya tun a lokacin da na ambaci sunansa."
"Tabbas kalamanka haka suke, domin hawayen mahaifiya ya sha bambam da kowanne irin hawaye a faɗin duniya. Wannan kukan da nake yi yana tuna mini tarun abubuwan da suka cunkushe rayuwata. Na farko rashin mijina, mahaifi a wurin ɗana. Na biyu killace ni da azzalumin wancan bawan ya yi tsawon shekaru, ba tare da na cimma muradin mijina ba. Na uku rashin ɗana Najibullah, wanda na ɗora amincewa ta ɗungurungum zai iya dawo da martabar ahalinsa." Kursum ta share hawayenta sannan ta ce.
"A baya zuciyata tamkar dutse take, sai dai a yanzu ta yi laushi tuɓus domin Sarki Gambo ya gama ruguza duk wata ƙwarin gwiwar da ke tattare da ni. Domin ya riga da ya hallaka duk wani..."
"Har yanzu Sarki Gambo bai yi nasara ba, domin bai san wurin da kundi ukun nan suke ɓoye ba. Najibullah ya san da ɗaya, ni kuma na san maɓoyar biyu."
Tsoho Sulaimanu ya katse Kursum, sautin murmushinta ya ji wanda ya alamta masa murmushin takaici ne take yi. Yana shirin yin magana ya ji ta ce.
"A naka tunanin da binciken duk wani mai tsafi ko binciken sirihi ne, ake tsammanin kai ne mutumin da ya san maɓoyar kundi biyun da na hannun Najibullah. Alhalin a zahiri kuma ba haka ba ne, domin kundi biyun da ake tsammanin kana da masaniyar maɓoyarsu ba su ne ainahin kundin da ake muradin mallaka ba."
Cikin tsananin mamaki Tsoho Sulaimanu ya ce, "Me kike nufi Kursum? Shin kina nufin kundi biyun da na sani, da wanda Najibullah ya sani ba su ba ne? Bayan har bokaye da 'yan tsubbu idan suka yi bincike kundin da muka sani suke faɗa."
Takunta ya ji ta fara tafiya, sai kuma ya ji ta tsaya cak! A karo na biyu ya sake jin murmushinta sannan ta ce.
"Kundin da ka sani da na Najibullah duka na jabu ne!"
Zumbur Tsoho Sulaimanu ya miƙe yana sake juya kalamanta a zahiri.
Yanzu ne wasan ya fara ɗaukar zafi😆 kada ku manta na faɗa muku shi fa wannan littafin kowa ba abin yarda ba ne.
Don Allah waɗanda suka yi payment su yi mini salam saboda gobe zan buɗe group, saƙonni wasu sun yi ƙasa zan iya manta wasu. In Shaa Allahu saura shafi ɗaya mu kammala book 1 mai son cigaban 2&3 zai biya 700 ta wannan Acc ɗin Aisha Adam 3090957579 Firstbank shaidar biya ta wannan lambar 07062062624 idan littafi ya kammala zuwa document 1k ne.
Ummou Aslam Bint Adam🌚
07062062624
[30/11, 21:57] Ameerah Adam: *KUNDI UKU*
©AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye.
Tsokaci: Daga Masarautu, Sarakuna da sunayen yanki duka ƙirƙira ne. Idan ya yi daidai da labarin wani/wata arashi ne.
SHAFI NA SHA BIYAR
Masarautar Zulwara
Tun Sarki Dikko yana jin ruwa mai sanyi yana mamaye shi, har ya ji yanayin ruwan ya fara sauyawa zuwa mai ɗumi-ɗumi. Wata irin tsawa ya ji ta tashi a cikin kabarin Sarauniya Humaira, ɗakin kabarin ya fara girgiza tamkar ƙasarsa za ta rushe ta haɗiye shi. Duk taurin zuciya irin ta Sarki Dikko, sai da ya ji wani matsanancin tsoro ya kama shi. Har ya fara saddaƙar da shi kansa tasa rayuwar ta zo ƙarshe, saboda ji ya yi ruwan da ya shanye shi ya daskare ta yadda ba zai iya motsa koda ɗan yatsansa. Yana cikin wannan yanayin, sai ya ji ruwan ya fara yin ƙasa. Wutar cikin ɗakin ta dawo kamar yadda take ci da farko, sai dai a ɓangare ɗaya ji ya yi jikinsa ya yi lakwas har da ƙyar yake iya motsa ƙafarsa. Ganin ya samu kansa, Sai Sarki Dikko bai daddara ba. Ya fara jan jiki a sanyaye ya tunkari wurin da littafin yake, yana miƙa hannu ya ji gabansa ya yanke ya faɗi. Amma haka ya yi ta maza ya miƙa hannunsa na hagu da zummar ya ɗauka. Wani irin sagewa mai haɗe da yin sanyi ya yi masa, ya janye hannunsa da ƙyar ya miƙa hannun dama a nan ya samu nasarar ɗauko littafin. Sai dai yana duba littafin ya ji daga bayansa an ce.
"Mutuwa, Rayuwa, Hatsari da Rai."
Da sauri ya waiga, sai dai bai ga komai ba, cike da mamaki ya sake maimaitawa.
"Mutuwa, Rayuwa, Hatsari da Rai. Me hakan yake nufi?"
Ya wurga wa kansa tambaya ba tare da hango wurin da amsar take ba.
Cikin ɗakin ne ya cigaba da girgiza tamkar ƙasar ciki za ta faɗa ciki, don haka cikin sauri Sarki Dikko ya fice daga ɗakin sannan ya sake biyo siriryar doguwar hanyar da ya shigo. Sai da ya ƙasara cikin turakarsa, sannan ya rungume littafin a ƙirjinsa ya runtse ido cike da tsananin farinciki.
"Haƙiƙa na yarda rayuwa kasada ce, cimma buri jajircewa ce. Duk wanda ya yi tseren agali tilas ɗayan biyu zai faru, kodai ya mace murus kuma ya kai ga hawa turbar tudun tsira."
Sarki Dikko ya furta cike da farinciki yana sake ƙanƙame littafin kamar wani zai ƙwace masa. Har ya kai hannu zai buɗe littafin, sai kuma ya saki murmushi ya nufi ɗakin da tsoho Babagana yake zaune. Sai da ya zauna a kujerar da ke fuskantarsa, cikin izza, isa da ƙasaita ya ɗago masa littafin.
Cikin tsananin mamaki Babagana ya ɗago a hargitse yana kallonsa, Sarki Dikko ya saki malalacin murmushi mai ɗauke da manufa da izgilanci ya ce.
"Babagana na sha sanar da kai ni mai nasara ne! Duk wani abu da na saka a gaba sai na same shi."
Babagana ya kawar da mamakin fuskarsa, don kada Sarki Dikko ya fahimci lagonsa ya ce.
"Kana da nasara a wurin da nasarar da ma can taka ce, Sarki Dikko kada wannan nasarar da ka samu ta sa ka fara jin ka a matsayin mai nasara."
A ɗan harzuƙe Sarki Dikko ya ce. "Me kake nufi?"
"Ina nufin kai ba komai ba ne, domin wannan abin da ka yi kowanne mai numfashi ma zai iya."
Babagana ya furta, duk waɗannan maganganun yana yin su ne don ya dasa wa Sarki Dikko wasu-wasi a zuciyarsa. Domin har a cikin ransa yake jin tsoro da shakkun makirci da taurin zuciya irin ta Sarki Dikko. Miƙewa tsaye Takawa ya yi, ya kalli Babagana ya bushe da wata mahaukaciyar dariya, wacce ta sake kaɗa hanjin cikin Babagana.
"Matuƙar wannan littafin shi ne zai ja mini gora zuwa ga ɗan uwanka Tsoho Sulaimanu da Dattijuwa Kursum. Ina mai tabbatar maka da nesa ta kusa zuwar mini kusa, haka zalika ina gab da mallakar manyan kundin da kowanne basarake yake fatan samu musamman Sarki Gambo da Sarki Giɗaɗo."
Sarki Dikko ya yi furucinsa yana sake sakin dariyar ƙeta, duk da kalamansa sun sayaya jikin Babagana hakan bai dakushe masa ƙwarin gwawa ba. Cikin yanayin jikin tsufa ya dafa bangon ɗakin ya miƙe, sai da ya yi taku biyu ya matsa gaban Sarki Dikko sannan ya ce.
"Na ji daɗi da rashin sani ya zama babban duhu ga kowanne mai numfashi. Ba zan ce maka uffan a kan maɓoyar Kundi uku ba, haka kuma ba zan dakatar da kai daga bulayin nemansa ba. Sai dai zan ce maka ga wani abu a kan matar sarki da ace da ido da tuni ta gani. Ko kuma na ce maka da magani a gonar yaro, amma rashin sani ya sashi bai sani ba." Babagana ya saki dariyar mugunta. Da sauri Sarki Dikko ya waigo ya ce.
"Akwai abin da ka sani Babagana, ka hanzarta sanar da ni tun ban ɗauki mummunan mataki a kanka ba.
Babagana ya gyaɗa kai ya ce, "Tabbas ina da masaniya, ina da sani mai zurfi game da wannan Kundin. Amma ba a yanzu ne lokacin ya dace na motsa ba, hukuncinka kuma a shirye nake da na karɓe shi kowanne iri ne. Amma ka sani, koda ka kashe ni na rantse da sarkin da ya busa mini numfashi. Ba za ka dakatar da wacce take ƙoƙarin ceton rayuwata daga nakasa taka rayuwar ba. Abu ɗaya zan ce maka Sarki Dikko, ita ɗin ta jima da yi maka illa, don ta kowacce fuska ta shammace ka. Ba za ka fuskanci haka ba sai a nan gaba, na tabbata ko ba na raye za ka tuna da kalamaina."
Shiru Sarki Dikko ya yi yana nazari, cike da sanyin jiki ya ce.
"Wace ce ita? A ina take? Me ya sa ban santa ba? Ko a binciken bokayena me ya sa ba su hango mini ita ba?"
"Saboda ita ma ba ta fito ba sai da ta shirya, ta kasance tamkar ingarman dokin da ke gudu a dokar dajin sahara. Ta kasance wuta mai laƙume duk wani makamashi, ita ɗin zakanya ce mai ɗauke da zuciyar gawurtattun zakuna dubu..."
"Ya isa!"
Sarki Diko ya katse Babagana daga maganar da yake yi, cikin ƙufula ya ce.
"Duk hatsabibancinta sai na tsamo ta da hannu."
Babagana ya saki murmushi ya ce.
"Ina maka fatan alheri."
Daga haka Sarki Dikko