Author : Ameera Adam Category : Read Hausa Novels
ya fice daga ɗakin cikin takaici.
Sarki Dikko zama ya yi a kan ƙasaitacciyar kujerarsa, ya ɗago littafin da aka buga bangonsa da fatar tsohon jemage. Daga ƙasan litttafin akwai wani gashi, wanda duk wanda ya san gashin ɗawaisu yana gani zai gane shi ne. Daga sama kuma wani gashi ne, wanda duk wani maharbi yana gani zai san gashin jelar zaki ce. Daga tsakiyar bangon littafin cikin rubutun ajami an rubuta 'RUWA A WUTA' Sai waɗansu ƙananan rubuce-rubucen ajami, wanda sai ka ƙura ido sosai za ka gane abin da aka rubuta. Ganin zai wahalar da kansa, ya sa shi buɗe shafin farko ba tare da ya karanta ba.
"Duk kalma ɗaya da ka tsallake daga cikin littafin nan, daidai take da gayyato masifar da ba ka yi tsammani ba a kundin rayuwarka."
Ya ji an furta da wata irin murya, wacce yaka jin kamar ya taɓa saninta. Yana sauke idonsa don ya cigaba da karatu ya ji sallamar Shamaki a bakin ƙofa, da sauri ya rufe littafin. Ya ƙarasa can ƙarƙashin gado ya zaro wata tsohuwar akwati ya zura a ciki. Sai da ya koma mazauninsa, sannan ya ba wa Shamaki izinin shiga.
"Allah Ya taimake ka, Allah Ya ƙara maka lafiya. Jakadiya ce take neman iso idan ka lamunce mata ranka shi daɗe." Shamaki ya furta yana sunkuyar da kai ƙasa.
"A ba su dama."
Sarki Dikko ya furta a taƙaice. Cikin girmamawa Shamaki ya ce.
"A huta lafiya ranka shi daɗe."
Miƙewa ya yi ya fita bayan Takawa ya ba shi izini, yana fita Jakadiya ta shiga. Sai da ta zube ta kwashi gaisuwa bayan ya amsa mata ta ce.
"Allah Ya taimake ka, Fulani Asiya ce take son ganawa da kai ranka shi daɗe."
Murmushi ta ga ya suɓuce masa, cike da annushuwa ya ce.
"A cewa Fulani muna nan zuwa gare ta, mun hutar da ita da zuwa wurinmu."
"Allah Ya ja zamanin amale, Allah Ya taimaki fari mai farar aniya. Garnaƙaƙin dutse kake, kowa ya yi faɗa da kai shi zai faɗi. Hadari mai zubar da ruwa, ƙasa mai karɓar shuka idan an gume ki rumbu ya kwana da yunwa. Ina gwanin wani ga nawa, ina wanda yake iƙirarin shi sarki ne ya zo ga ubangidansa. Sai ka yi gajimare mai ɓoye wata, sai ka yi damuna mai zubar da ruwan alheri. Sai ka yi ko da tsiya ko da ƙarfin ikon Allah."
Murmushi Sarki Dikko ya yi ya ce, "Kulawa da yabawa Jakadiya."
Cike da jin daɗi Jakadiya ta yi masa jinjina ta ce.
"Idan mai martaba ya lamunce zan iya tafiya?"
Amsa mata ya yi sannan ta yi masa godiya ta fita.
Da fitar Jakafiya babu jimawa Sarki Dikko ya kira Shamaki, ya sanar da shi zai ziyarci sashen matansa wurin Fulani Asiya. Sai da ya koma ya shirya cikin shigar ƙasaita, ya yi kyau sosai sai baza ƙamshi yake yi. Sabuwar alƙyabba ce ya saka ta, wacce ta sha adon jajayen duwatsu. Fitowa ya yi yana dogara sandarsa, fadawa da Dogarai suka shiga yi masa kirari suna take masa baya. Har sai da suka je sashen matansa, sannan ya dakatar da su. Ya tura ƙofar ya shiga, sashen Fulani Aisha ne a farko, sai sashen Fulani Halima, Sashen Fulani Hauwa kulu na ƙarshe shi ne sashen Fulani Asiya. Da yake a jere kamar yadda suke uwargida da mabiyarta har zuwa amaryarsa Fulani Asiya.
Duk a tsammaninsu zai leƙa sashensu ya fara ganim lafiyarsu, amma ga mamakinsu sai suka ga ya wuce wurin Fulani Asiya.
Fulani Hauwa kulu tana daga ɗaki ta ga giftawarsa, mamaki da takaici ya kamata. Tana nan zaune ta ga ya fito har zai fita ta yunƙura ta fita wurinsa.
"Ranka shi daɗe barka da hutawa."
"Barka!"
Ya amsa mata a daƙile, duk da bata ji daɗin abin da ya yi mata ba. Amma sai ta saki murmushi ta ce.
"Ranka shi daɗe idan ba za ka damu ba mu shiga daga ciki..."
"Duk abin da za ku faɗa, muna sauraronku ba sai mun shiga ba."
Ya furta fuska a haɗe, ajiyar zuciya ta sauke tana haɗiyar yawu mai ɗaci ta ce.
"Ranka shi daɗe haihuwa fa na yi, na aika Jakadiya ta sanar da kai ɗan babu rai, amma har aka binne shi ba ka zo ba. Kuma ba ka ga jaririn ba, sannan yanzu ka shigo ba ka leƙo ka ga lafiyata ba. Amma idan na yi kuskure ka yi haƙuri ranka shi daɗe."
"Tun da muka ji shiru ai kuna cikin ƙoshin lafiya, haihuwa kuma tun da babu rai mene ne amfanin ganinsa? Muna da magada masu yawa, don haka ku yi haƙuri idan ma kun haifa sun mutu. Domin tun asali mun fi son jinin Fulani Asiya ya gaje mu, kuma hakan ce ta faru tun da kwalliya ta biya kuɗin sabulu."
Cikin murmushi mai ɗauke da manufa ta ce, "Amma muna fatan waɗannan tagwayen su lafiyayyu ne da za su iya kula da sha'anin mulki?"
Da mamaki Sarki Dikko ya dube ta, sai Fulani Hauwa kulu ta cigaba da cewa.
"Amma kada ka sa a ranka su ne kaɗai za su iya zartar da mulkin masarautar nan. Wataƙila akwai wani jinin naka da zai shammaci magadan da ake tsammani."
Tana gama faɗar haka ta faɗa ɗaki, cikin ƙasa da murya ta ce.
"Sarki Dikko ka yi kuskure da kake tsammanin ni Karima zan lamumce maka, kuma ka yi ganganci da kake tsammanin tagwayenka za su mulki masarautar nan. Batul! Ita kaɗai ce za ta gaji karagar nan, ni kuma zan cigaba da yaƙi har na samu nasarar fitar da Babagana daga ƙangim bautarka."
Tana rufe baki Sarki Dikko ya ɗaga labulen ɗakin ya ce, "Me kuke faɗa haka?"
Fulani Hauwa kulu ta saki murmushin ƙeta ta ce. "A sauka lafiya ranka shi daɗe."
Masarautar Kajjura
Ɗan ɗagowa Sarki Gambo ya yi, ya zuba wa Fulani Sadiya idanu ya ce. "Matsalar da zan sanar da ke a kan su Hasana ne."
"Ni ma matsalarsu ce take tafe da ni, Sarkina akwai gagarumar matsala. Ka gafarce ni ranka shi daɗe, amma a yadda na lura da su Hasana kamar ba su da wadatacciyar lafiya."
"Ba kama ba ce Fulani..."
Nan take Sarki Gambo ya zayyane mata duk abin da ya faru, Fulani Sadiya ta kawar da kai gefe tana sakin murmushim ƙeta. Amma sai ta danne ta ce.
"Mene ne mafita Sakina, domin ba na son magauta su fahimci rauninmu. Ko kuma Malami ya kawo maka wata mafitar?"
Gyaɗa mata kai ya yi sannan ya sanar mata da bayanin Malami, sun jima suna tattaunawa. Sai da Fulani Sadiya ta kwantar da kai ta gama jin sirrin Sarki Gambo, sannan ta shiga nuna masa kulawa cike da soyayya.
Fulani Zainaba
A bayan ɗakunan bayi suka keɓe suna tattauna, cikin shigar ɓadda kama ta ce.
"Wanzam na kira ka ne domin na sanar da kai na san duk wani tuggu da kuke kitsa wa kai da Ciroma, kuma kai ka sani idan har na buɗe baki a wurin Takawa taka ta ƙare."
Wanzam da cikinsa yake kaɗawa ya ce, "Tuba nake ranki shi daɗe."
Murmushin cin nasara ta yi ta ce, "Idan ka ga wannan maganar ta mutu, to tabbas ka samar mini da jinin Sarki Gambo a gobe Alhamis idan za ka yi masa aski. Idan ba haka ba kuwa, tabbas zan bankaɗa masa sirrinka. Sannan na sanar da shi tuggun da kuka binne a cikin turakarsa."
Cikin sauri ya zube a ƙasa ya ce.
"Tuba make uwar ɗakina, zan yi duk abin da kike buƙata."
'A Gobe war haka na tabbata na samu nasarar ganawa da tsoro Sulaimanu tare da Kursum.'
Zainaba ta raya a ranta, daga can bayan bishiya Jakadiya da ke laɓe ta gyaɗa kai ta ce.
"Ƙarshenki ya zo Fulani Zainaba, na rantse da girman Allah sai na yi sanadin da Sarki Gambo zai tarfa ki a ɗakin."
A nan na zo ƙarshen book 1 na KUNDI UKU mai son karanta 2&3 zai tura 700 zuwa ga Aisha Adam 3090957579 shaidar biya ta nan 07062062624 idan littafi ya kammala zuwa doc 1k
Sarki Giɗaɗo ga shi da jaririya Batul, Sarki Gambo da Fulani Zainaba ga Jakadiya a gefe. Sarki Dikko ga Babagan ga Fulani Hauwa kulu/ Karima. Ba sai na ce komai ba, kun san dai akwai ƙura.👌🏻
Ummou Aslam Bint Adam🌚
07062062624